Showing 33001 words to 36000 words out of 37818 words

Chapter 12 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

Mama dagani sai laure, Daddy yanzu ma ko zama bayayi memakon ki tafi dani".


Wasu hawaye me radadi suka zubo masa, da sauri yayi dakinsa cike da kewar mahaifiyarsa da tausayin y'arsa fal a ransa.




London
HAFEEZ kam aeki yake tukuru baya da hutu, busy yake sosai, time to time yake waya da y'an gida abubuwa sunyi yawa, kuma Alhmdllh ana samun nasara komai na tafiya daidai saidai yana fargabar case din daya bari gida, kuma ga tausayin matarsa fill aransa, ga wata azababbiyar soyayyarta dake dawainiya da zuciyar sa duk ya wani zama sukuku kullun tunaninta ke hanashi sukuni.


Nigeria
"To idan kun tafi yaushe zaku dawo"Suhailat ta fada tana duban Mom da Fadila.


Shafa fuskarta Fadila tayi tace"Dear just 3days kinsan bana iya zama wuri in baki"


Dariya sukayi duka, kafin sukayi bankwana suka shiga mota suka nufi birnin kebbi, Suhailat ta danna motarta tayi wurin Adam a wani store da sukayi zasu hadu zasuyi siyayya, bata jima a hanyaba ta isa kai tsaye suka shiga suna zabar kaya.


Ko kadan beyi auneba yaji ya buge mutum, wayar hannunta ta fadi ta fashe, ko kadan basu kula wayarba suka shiga kallon kallo tsakaninsu.


Nisawa Suhailat tayi tace"ke bakya ganin mutanene gawa taki rami"ta idashe maganar tana jan tsaki


"Kuskuren da bakinki zaiyi shine na fadamun magana, cos kinsan bazan daukaba, da Sannu kema zakije inda kikakaimin y'ata kisan na cika uwa maibin fansar ran y'arta"HAFSA ta fada.


Wata irin zufa ce ta karyowa Suhailat ta fara magana muryarta na cracking tace"wacce y'a kuma, waya Santa, da kika bawa ashe sharri kika koyo".


Kallonsu Adam yayi cike da mamaki yace"y'a kuma, aena dauna matsalarku ta dabance meya kawo maganar y'arki a ciki".




Kallon sama da kasa HAFSA tayi masa tace"ka iya yiwa kanwarka Wannan tambayar inka matsu, but inaso ki sani rai zai biya rai, jini zai fanshi jini, toke in aka kawar dake ae an rage mugun iri a gari"wata iriyar wutar kiyayyar tsanar Suhailat ta kuma darsuwa a zuciyar HAFSA, kasa ida magana tayi saidai ta nunata da dan yatsa tace"one day one time"ta hada hannuwanta sukayi kara ta juya tabar wurin zuciyarta cike da Kuna kamar ta fasa ihu takeji kota samu sassaucin abunda takeji a ranta kai tsaye mota ta shiga Samuel yaja sukayi gida.




Kallon tuhuma Adam yakebi Suhailat dashi, figar hannunta yayi ya jefata mota, kai tsaye gidansa ya nufa da ita, suna shiga ya jefata a chair yace"bansan munafunci ki fadamun gaskiya, wacce y'ar kika kashewa HAFSA? ".


Shiru tayi kanta kasa, ko dagowa ta kasayi bare kuma tayi magana.


Wata razannar tsawa ya daka mata(nima aradu saida na dibi hanya don tsoro), har cikin kwalwarta ta jita tsaye ta mike jiki na rawa ta soma zare ido.




Ganin haka yasa Adam zare belt a hassale yana huci yace"al qur'an, ko kiyi magana, ko kici jibgar banza munafuka kawai kije ki jawo mana bala'i"ya fada yana aeka mata da harara.






(Tofa readers shin Suhailat zata fadi gaskiya kuwa)


Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe
👏🏻


Emm Iyy luv

*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


By
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat(ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


34
Tun daga stairs Mama ta gane ummy wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta, saboda irin soyayyar da takewa yaran, hannunta rike yake dana little tanata zabga mata surutu har suka iso kasa inda Mama ke fadin"lale maraba y'ata, Sannu da zuwa, yaushe rabo, ashe zan sake ganinku"ta iso tana karbar Affan daga hannun Ummy, tare da zama kusa da ita.


Ummy kam har kasa ta duka, kanta kasa tace"ina wuni Mama, na sameku lafiya? "Ta fada murya a nutse.


"Alhamdulillahi y'arnan ina Hafsatu? ".Mama ta fada cike da kulawa, tare da ruko hannun Ummy ta zaunar da ita a chair kusa da ita.


Tuni ta bada umarni aka cika gaban Ummy da kayan ciye ciye.


Little Hafsa kuwa tuni ta dare cinyar Ummy tanata zabga mata surutu, sai sakasu dariya take famanyi.


Bayan sun d'an taba hira Ummy tace"Mama wurinki nazo, Allah yasa zaki fahimceni, kuma maganar tanada matukar muhimmanci".


Gyara zama sosai Mama tayi tace"Ina jinki Ummy".


Bayan ta Kira Mai aiki ta tafi da Affan da Little.


"Mama maganane kan sirrin da HAFEEZ ke b'oyo, ni kuma naga lokaci yayi da zakisan gaskiyar abunda ya rabasa da HAFSA, HAFEEZ ya sayar da mutuncin HAFSA saboda son abun duniya, yaci amanarta ya zabi kud'i akan kyautatawar da take masa"nan ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta fadawa Mama cikin natsuwa da girmamawa.




Mama kam tuni ta jike da hawaye, ga zufa na karyo mata, a hankali tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, yaushe hafeezun ya zama haka?, ni ba haka ya fadaman, cemun yayi ya samu aiki kasar turai, kuma uban gidansa nada kirki, wai sune suka daukeni na kwana wurinsu". Share fuska tayi da hannunta taci gaba da cewa "lokacin da na dawo gida na sameshi yana kuka da shaida mini HAFSA tace bata sonshi, kuma ba zata aureshi ba, don haka zaibi uban gidansa koya samu saukin zuciya, nikam na yarda da Hafeezu a lokacin na tausaya masa sosai saboda nasan irin shakuwar dake tsakaninsu da HAFSA, muka had'a kaya muka koma kasar masu jan kunnuwa, da kyar na shawo kansa ya auri Sadiya wacce take matukar sonsa wato mahaifiyar hafsa karama, wacce ta rasu wurin haihuwa, shikuwa dukiya sai kara habbaka take, saida yarinyar nan tayi wayo muka dawo, ashe abunda ya kulla kenan"rushewa tayi da kukan bakin ciki.




Jikin Ummy sosai yayi sanyi ta soma bawa Mama hakuri da maganganu masu dadi.


Tsagaitawa tayi da kukan tace"naji dadi da kika fadamun, kuma zaizo ya sameni, don Allah kuyi hakuri sai nazo gidan".


Bankwana sukayi, ta karbo Affan ta dawo gida abunta.


Mama ko zuciyarta ke wani irin bugawa, tana mikewa jiri yayi nasarar d'ibarta ta fadi kasa a sume.


Ihu ladi mai aiki ta buga, yayi daidai da shigowar Kabir, da gudu ya karaso yana jijjiga Mama da kiran sunanta, amma shiru, ciccib'arta sukayi sai mota, kai tsaye Asibiti suka kaita aka shiga da ita emergency.


Ban garen HAFSA kuwa, tana ganin HAFEEZ ya fita, ta kwashe da dariyar keta, ta jima tana bincike a laptop sannan ta sabo bag dinta ta fito suka wuce gida.


Mai gadi ya bude masa gate ya fito bayan sun gaisa ya shige gidan da sauri, don jiyo kukan Amira, da sallama ya shiga a bakinsa.


Murmushi Ammi tayi ta amsa tace"barka da zuwa"tana mika masa y'ar tasa, sannan tabar wurin.


Kallonta yake cike da soyayya, yarinda yarinyar tai masa zuru ta daina kukan, kuyi hakuri haka Allah ya tsara dole kusha wuya farkon zuwanku duniya, mamanku tana cikin rud'un makiya bata da lokacin kula daku, kuma tana hakane dukdon rayuwarku tayi kyau, duk a zuciya yake maganar, yayinda hawaye ke gangarowa a fuskarsa.


Shigowarta kenan parlon take bin fuskar HAFEEZ da kallo sai hawaye yake, jikinta ne yayi sanyi, a hankali ta tako zuwa garesa ta rungumesa ta baya, ta dora kanta bisa kafad'arsa tace"please lokacin daina kukanka yazo husband ".


Ajiyar zuciya ya sauke ya shafi gefan fuskar ta, ya juyo da ita ya matseta gam a jikinsa yana shakar kamshin jikinta, a hankali yace"ina alfahari dake, lallai ke d'aya tamkar da dubu ce, mai iya daukar duk wata matsala data tunkarota, HAFSA ina matukar sonki, naso a kwanakin nan mu zauna tare domin mu shawo kan matsalarmu, amma abun ya canzamin, jiya da dare Ogana na London ya kirani akan na koma yau, lokaci na kure mani, kuma kinsan cost din wai na karin girma ne".


Murmushi HAFSA tayi sannan tace"haba don Wannan, aini nafi kowa jin dadi, dama inaso nayi aikin ni kadai, insha Allah lokacin da zaka dawo saidai kaji labari"ta karashe maganar tana tsokanarsa.


Rikota yasoyi ta mike ta gudu tana masa kwalo, hakan kuma yayi daidai da safkowar mai aiki ta kawowa HAFSA Amir daya tashi a bacci.


Karba tayi, tasa aka kawo abinci, nan take ta ciyar da mijinta, shigo sai kara narkewa yake, kallonta yayi ya ciro ATM a aljihunsa ya mika mata yace"gashi ki rika amfani da kudin ciki, bance Ki tambayi kowa wani abuba, ko kiyi amfani da kudinki ba a'a, komai kukeso kuyi anan, sannan gasu Samuel nan insha Allah zasu kula daku, please wify kada kimin wasa da rayuwarki kiyi komai a hankali kinga ni zan wuce kuma bansan ranar dawowa ba".


Shafar sajensa tayi dukda batajin dadin tafiyar da zaiyi amma ta daure cos bataso ya fahimci wani abu tace"karka damu, matar soja ae soja ce, zanyi komai daidai insha Allah, banison damuwarka ".




Dariya yayi saboda yanayin yadda tayi maganar, ya hadata da yaranta ya rungume, kiss yayiwa yaransa a goshi ya mike yana daga mata hannu ya tafi, hawaye ne masu dimi suka sauka akan fuskarta da tunanika daban daban, tuni kwalwarta ta dauki zafi tana niyar tsayawa tsak, alkawarin data daukar wa kanta kanta ta tuna, dandanan ta goge fuskarta ta sabi yaranta ta wuce daki, zuciyarta cike da kewar mijinta.


Shima hawayen yake a mota, da kyar ya iya yiwa Momy bankwana ya wuce filin jirgi mintina kad'an jirginsu ya Lula cikin gajimare.


***
Waya Kabir ya dauko ya soma kiran wayar HAFEEZ.


HAFEEZ kam kallon wayar yake kamar bazai daukaba, candai ya dauka ba tare da yace komaiba.


Tsaki Kabir yaja yace"Mama na asibiti"be jira cewarsa ba don har yanzu fushi yake dashi ya latse wayarsa.




HAFEEZ kam hello, hello yake maimai tawa a hargitse jin ance Mama na asibiti, ko kallon Adam beyi ba ya fice da gudu, mota ya shiga ya wuce cos yasan asibitin da ake kaita.


Da Kabir ya hadu a kofar dakin, zai tafi kiran da Doctor ke masa, ko kallonsa beyiba ya wuce, shima a baya ya bisa suka shiga tare.




Ya dade yana y'an rubuce rubuce sannan ya dago tare da zare gilashin idanunsa yace"me yake damunta a rai, bayan nace ku kula da ita, abu kadan zai iya sawa zuciyarta ta buga"


Zaro ido sukayi HAFEEZ ya fara magana muryarsa na cracking yace"pls Dr Kar kabar haka ta faru, ita kadai gareni".


"Munyi iya yinmu sauran hikimar Allah ne, tace tana bukatar ganinku kwa iya shiga but kada ku tada mata hankali tana room 6"Dr ya fada.




A nutse suka mike, suka shiga room 6 inda Mama ke kwance a bed tana fitar da numfashi dakyar dakyar, cikin sauri suka isa gareta suna mata Sannu.


Cikin karfin hali ta bude baki tace"HAFEEZ meye dalilin canza halinka?, nasan ba tarbiyar dana baka ba kenan, me HAFSA ta aikata maka haka harda ka zab'i cutar da rayuwarta haka?, shin yanzu in y'arka akawa haka ya kake tunanin zuciyarka zata kasance? ".


Hawayene suka gangaro gefan fuskarta, shima HAFEEZ kuka yake yana goge mata hawaye yana fadin"don Allah Mama ki yafemun, ki daina mani kuka, wallahi sharrin shaidan ne, Mama na daina"kuka yaci karfinsa.


Kabir ma hawaye ya fara yace"Mama ki sanyaya zuciyarki, ki dainawa HAFEEZ kuka, mama ya daina".


Murmushi tayi tace"kabir Allah yayi maku albarka, ba HAFEEZ nakewa kukaba, ina kukan irin halin da Hafsatu ta shiga lokacin da abun ya faru, kabir ka tallafi rayuwar D'an uwanka ka rika nuna masa daidai da rashinsa".


Maido kallonta ga HAFEEZ tayi tace"dazu aka sanar dani komai, ka daina kuka na yafe maka, amma ka nemi gafarar Hafsatu in kana son dacewa, ka kulamin da y'ar jikalleta kuma ku rike junanku da amana kaida Kabiru, Hafeezu ka rage zafin zuciya, ka sanyaya zuciyarka, Allah yayi maku albarka ya saka farin ciki a rayuwarku kuma kuyi aure"tarine ya toshe sauran maganar dandanan ta fara aman jini dannuwan kabir da HAFEEZ ta rike tana hawaye kalmatushshahada ta farayi bata ida karsheba ta sankare idonta na kallon sama.


Ihu HAFEEZ ya kurma ya rungume ta yana jijigata tare da kiran sunanta.


Kabir da gudu yaje ya kirawo Dr suka dawo tare, da kyar Kabir ya cire HAFEEZ daga jikin Mama, dube dube Dr yayi sannan ya jawo zani ya lullube Mama yace"am sorry ta rigamu gidan gaskiya"😭


Komai na jikinsu tsayawa yayi cak musamman HAFEEZ wani irin bakwan yanayi ya ziyarcesa, faduwa yayi kasa ragwab hawaye nabin fuskarsa, shima Kabir hawaye yake da kyar sukayi karfin halin daukar gawar mama suka wuce gida.


(Innalillahi Mama ta rasu, na tayaka bakin ciki HAFEEZ, dama haka duniya take, Allah ya kyautata namu karshen)


Tuni y'an uwa suka cika gidan, wasu na kuka wasu na addu'a cos Mama ta mutanece ba HAFEEZ kadai yayi rashiba harda duka unguwar don Mama akwai taimako, little kam batasan wainar da ake toyawa ba har aka rufo Mama tsalle tsalle kawai take, yayinda kowa ke tausayinta na gani wazai kula da ita,HAFEEZ kam daya kalleta sai hawaye.




Hafsa lokacin da taji rasuwar Mama tayi kuka kamar ranta zai fita, daga karshedai tasawa ranta hakuri.


Ta dan tsaida abubuwan da take na tsawan sati daya.


Yayinda sun gama shirya komai da Muhammad sati na cika sai a wakanar da komai, gasu Amir sai kara wayau suke duka har Amira sai rikidewa sukeyi suna komawa zallar kamar mahaifinsu, kallo d'aya zaka gano tsantsar kamarsu.




Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe👏🏻


Emm Iyy luv


*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}


🌈kainuwa writer's association


By
Maryam ismail


Sadaukarwa ga
Hafsat(ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malamie


36
Cike da tsantsar mamaki Suhailat kebin fuskar HAFEEZ da kallo cikin kausashiyar murya tace"Adam ni zaka daka? "


Before ta rufe baki ya zabga mata belt a baya yace"don kutumar ubanki, ke bakiga bala'in da kike shirin janyo mana ba, ashe ke tosashiyar kwalne dake, ala wadaran aeki ba shawara, to wallahi in ta kaiki kotu kasheki za'ayi jahila kawai dama ni na taba baki shawarar mu kashe wani".


"Dallah tunda ba kai ka haifani ba, zaka iya yimin shiru, tunda kai ka kasa samarman abunda nake bukata, toya kake tunanin bazanbi ko wacce hanya ba".


Bata karasa maganaba taji safkar duka dukanta yake kota ko'in yana halbata, ihu kawai take da tsine masa tana aeban tashi, be sarara mata ba saida ya tabbatar tayi lilis tukunna ya zauna gefe zuciya na cinsa, yayinda ita kuma ta takure gefe tana sharbar kuka mecin zuciya tana kuma fadin"Allah ya isar mani mugu kawai kuma saina hadaka da Mom ".




Me gadi ne ya shigo ya durkusa gaban Adam yace"ranka ya dade ana sallama a waje".


Saida yayi shiru kamar bazai tankaba can dai yace"Kace su shigo"


Jiki na rawa me gadin ya mike yayi waje ya sanar masu da sakon me gidan nasa.


Tun daga kasa har sama yake kallon matasan sunsha bakar suit sosai sukayi kyau, musabaha sukayi sannan ya basu izinin zama.


Da murmushi dayan yace suna Kamal abokin aekina kuma Basher, ga sako muka kawo wa kanwarka".


Mika hannu yayi ya karba, sannan sukayi sallama suka wuce, bude takardar yayi kara maimaita abunda ya gani yakeyi sannan ya dago rinannun idanuwansa yace"bakar shegiya saiki taso ki karbi takardar tuhumarki da akeyi da kisan jariri, kuma wallahi idan kika kuskura kika ambaci sunana hmm"ya fada tare da jefa mata takardar.




"Aekin banza yo kaima duk abunda mukeyi tarefa, wallahi kasa kanka a shiri before Monday don saina tona asirin duk abunda muka aekata in yaso kowa ya mutu, kuma wallahi inaso kasan ba tsoranka nikeji ba azzalumi kawai"Suhailat na karasa maganarta ta figi bag dinta tayi gidansu tana rusar kuka tana kuma takaicin rashin Mom da Fadila a kusa da ita.


Shiryawa HAFSA tayi tsaf cikin blue hijab mai stones tayi matukar kyau sosai ta shirya yaranta sukawa Ammi bankwana ta wuce gidansu don gaeshe da Ummu, gobe kuma gidan Momy zataje, da fara'a mai gadi ya iso wurin motarsu yana masu Sannu da zuwa, gaeshesa tayi da fara'a sannan ta shiga parlon gidansu bakinta dauke da sallama, da Affan taci karo ya tako zuwa wurinta dariya ta saki tace"wow my Boy "ta Kara she maganar tana ajiye Amir a chair ta dauki Affan, sallamar Ummy ke ansawa tana safkowa daga stairs, da gudunta ta karaso tana sungumar su Amira tare da saka musu albarka tana cewa"don wulakanci shine ta ajiyeminku nan ta dauki bardan goyo".




"Kudai kuka sani ae, wa yake tataku"HAFSA ta fada tana kawallawa Ummu Kira.




Tare suka safko ita da Abbui fara'a dauke a fuskarsu, saida suka zauna sannan HAFSA ta duka har kasa tace"na sameku lafiya".


Lafiya lau suka ansa suna tambayarta lafiyar yaranta, kanta kasa ta ansa da lafiyansu qlau, Ummy ce ta miko masu yaran.




"A'a nikam baxan dauki kishiya ba, ku bani mijina naji diminsa dukda haka nan na ta rasu ba cefane"ta Kara she maganar tana lakace hancin Affan, cewar Ummu.




Dariya suka saka Ummy na fadin"a'a Ummu zasu kawo ae, kin bada kishiya bari ta kwace Abbui din".


Saida suka gama fira sannan Abbui ya fita suka masa Allah ya kiyaye, sannan Ummu ta wuce dakinta dauke da twins tana jaye da hannun Affan.


Zama sukayi suka fuskanci juna sannan Ummy tace"yanzu ya ake ciki ga case dinnan? ".


"Eh komai ya tafi yadda Daddyn Affan ya tsara, ankaima HAFEEZ da Suhailat takardar sammaci Monday zamu shiga kotu kinga anan zasusa a kamo Dr Anas shida ya basu goyon baya". Cewar HAFSA tana duban Ummy.


"Lallaima sweetheart kunyi tuya kun manta da albasa to Wannan kawarton dakikin Adam dinfa ubanme kuke jira dashi bakin munafuki ae shine maciyin amanar cikinsu wallahi"Ummy ta fada.




Dariya HAFSA ta kwashe dashi sannan tace"kai Sweetheart baki da kirki, duk Wannan zagin shi kadai, kada ki damu Wannan Abduol yace abar masa shi, kotun sojice zata hukuntashi".




Murmushi Ummy tayi tace"yanzu naji batu, amma kinsan Abduol dinnan wallahi yanada kirki shine abokin tsakani da Allah ga matarsa itama babu ruwanta".


"Donma baki zauna dasu ba, ae akwai kirkin Ummun Ahmad ga yaronta na matukar sona".


Haka dai sukaitayin fira har yamma sannan sukawa Ummu sallama, saida HAFSA ta aje Ummy gida sannan ta wuce gidan Ammi.


*****


Abduol ne tsaye a gaban kotunsu na soji yana cikin uniform dama abunda ya kawoshi Nigeria kenan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login