Showing 6001 words to 9000 words out of 37818 words
Chapter 3 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt
jefarta da muguwan harare ba.
Bakinta na kyarma ta furta "waye kai?"
Hannu ya daga ya wanke fuskarta da maruka har guda biyu a jere,baya tayi zata fadi cikin sauri ta samu ta kyara tsaiwarta a hassale tace"saboda tsabar mugunta meye nayi maka ,mugu Allah ya isana,solofiyo kawai ka kare da dukan mace saboda rashin ilimi".
Sosai maganganun Hafsa suka daki zuciyarsa,kasa tsaida kansa yayi kawai ya kashe fitilan dakin ya fada mata,ihu kawai takeyi tana tsine masa, amma a haka saida yayi nasarar rabata da komai na jikinta ya shiga aeki ko kadan ba sauki babu tausayi a zuciyarsa komai na karfi yake mata,tun tana iya motsi hartakai ga sai yadda ya juyata ,a haka ya cinma burinsa na son daukar fansa ga yarinnan ,yayi mata kaca kaca,sai a lokacin zuciyarsa ta sanyaya ya murgina gefe yana maida numfashi sannan ya jawo kwalbar giyarsa ya daga kwalban saida ya shanye tas sannan yayi jifa da kwalban ya soma wurgi da duk abunda ya tari gabansa.
Wasu irin zafafan hawaye kebin fuskar Hafsa har lokacin dukda muryarta bata fita bata daina tsinewa Hafeez ba a hankali ta sauko kafanta kasa tanaso ta taka kafarta amma Sam taki takuwa bin kasan kafarta tayi da kallo ganin jini na bin kafarta yasa ta kuma kwallah ihu ta fadi kasa a sume.
Jin ihunta yasa Adam saurin tasowa ya bude dakin ya kunna wutan dakin,dariya yayi da yakai kallo gareta yace"gobe ma kya kuma ae "
Daukarta sukayi suka sakata bayan mota yaiwa yaran gargadi da kada su bari kowa ya gansu suje su jefar da ita a kofar gidansu.
Haka kuwa sukayi ba kowa a unguwan suka jefata bakin gate dinsu suka tafi,gate man dinsu ya fito waje anan ya ganta da gudu ya shigo cikin gidan yana fadin"Alhaji Hafsa kazo ka gani"waje kawai yake nuna masu.
Jin ya ambaci sunan Hafsa yasa sukayo waje har Riga rigan fita sukeyi,ganin halin da take ciki yasa Ummu fashewa da kuka tana kirgizata tare da kiran sunanta,cikin sauri Abbun ya jawo mota suka wuce hospital wurin family doctor nasu,da gaggawa ya amsheta kokari yayi ta farfado sannan ya gyara mata jikinta suka mata duk wani Abu da sukasan zai taimaka mata harda wankin ciki,sunyi sa'a babu abunda ya shiga mahaifarta,allurar bacci sukayi mata ya daura mata drip ya fito.a nutse ya masu bayanin fyade aka mata ,amma alhmdllh komai yazo da sauki bataji ciwoba sosai.
Ummu kuka take kamar ranta zai fita musamman da ta iske Hafsa kwance kan bed fuska ta kunbure tayi jajir bacci take amma hawaye nabin gefan fuskarta,waya Ummu ta Ciro ta kirawo Ummy ta fada mata tazo Hafsa ba lafiya,kafin tadan fita daga bakin dakin.
A hankali Hafsa ta bude idanuwanta da sukayi jajir,zare drip din tayi ta shiga tailet tana rusa kuka tana tunanin waye ya kawota nan,cikin gaggawa Ummy ta iso asibitin bata jira ta Ummu ba ta fado dakin jin kukanta a toilet yasa ta bude kofan ta fada ciki tun daga kasa takebin Hafsa da kallo har samanta jinin dakebin kafar Hafsa yasa hawaye suka farabin fuskar Ummy ta duka ta rungume Hafsa tana fadin"wayayi maki, Haka ".
Cikin kuka Hafsa ta bata labarin abunda ya faru murya na sarkewa tace"abun ban haushi bansan su waye ba,ko fuskarsu ban gani ba,bansan menayi musu ba suka illahtamun rayuwa Hafeez ya cuceni ashe soyayya na iya zama haka" kuka yaci karfinta ,kuka Ummy ta fashe dashi suna tsinewa Hafeez ,sannan sukayi alkawarin boye sirrin akan sucewa su Ummu basusan ko waye ba.
Haka aka hakura aka boye sirrin don rufin asirin Hafsa,kwanaki kadan ta warke sarai,saidai ta canza,lokacin ta zafafa kiyayarta ga duk wani D'a namiji bata kaunarsu kuma bata tsoran kowa kuma kullun cikin Neman Hafeez take don daukar fansa,ta koma mai zafin rai abu kadan ke hassalata bata shakkar kowa tayi alkawarin bata ba aure kuma bata ganin duk namiji da daraja.
Ci gaban lavari
Hawaye Maryam ta goge tace"amma gaskiya rayuwar Hafsa abun tausayi ce,sai yanzu na tabbatar bata da laifi ga duk abunda tayi,yaya Hafeez shine daidai daya aureta na tabbatar kodon zumuncinmu bazai goranta mata ba,zai tallafi rayuwarta".
Itama Ummyn share hawayen tayi tace"to ki boye wannan sirrin har abada maryam na rokeki".
*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
Muhphat luv
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}
🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*
NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*
SADAUKARWA GA
*HAFSAT* ( UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*
INAMA DUKKAN MUSULMAI BARKA DA SALLAH ,ALLAH YA MAIMAITA MANA
*PAGE* 9
Kallon fuskar Hafsa sukeyi data soma motsi tana budar idanuwanta da suka koma kalar ja a hankali,kallonsu kawai takeyi amma har yanzu hawaye basuyi niyyar tsayawa daga kyakyawar fuskarta ba.
Cikin sauri Ummy ta fita ta kira Dr ,a hanya ta hadu dasu Mom ,Ummu , Ammi cike da ladabi ta gaeshesu tana fada masu ta farfado Dr ma taje kira,
Hamdala sukayi ga sarki Allah tare da gode masa, kafin suka karasa cikin dakin.
Anan suka samu Dr harya gama dubata,yace a taimaka mata tayi wanka kafin tasha magani.
Babu ko D'ar Mom ta kamata tana mata sannu har toilet ta kaita bayan ta hada mata ruwa mai zafi domin ta gasa jikinta.
Badon tasoba tabi umarnin Mom,saboda ba zata iya jayayya da itaba ,gashi yanzu wata irin masifar kunyarta takeji.
Tana wanka tana kwaranyar da hawaye da tunanin asirinta ya gama tonuwa ,musamman ma da akace wai Hafeez ne mijinta mai shegen girman kai da nuna isa,uwa uba yacce ta tsani duk wani mahaluki mai irin wannan sunan,ba yacce ta iya a dole tayi wanka tare dayin alwala,kaya Ummy ta miko mata ,anan ta saka kayan sannan ta fito tana tafiya a hankali ,kafin ta fara jero sallolin da ake binta.
Bayan ta gama ,suka mata ya jiki,ta amsa ciki ciki,tea Ummy ta hada mata dakyar tasha rabin mug din ,kafin tasha magunguna ,ba dadewa bacci yaynawan gaba da ita.
Da misalin karfe 1 na rana ,su Ummu suka tafi gida,akabar Maryam da Ummy,Mom tace zata aeko Hafeez da abinci sannan ya dubata da jiki.
Tafiyarsu ba dadewa Hafsa ta farka, da sannu suka bita,kai kawai ta daga masu ta tashi zaune tana binsu da kallo da kuma sauraren firar da sukeyi.
Lokacin da Mom ta isa gida yan aekinta harsun gama hada abinci a basket don tayo masu waya ne,da kanta taje dakin Hafeez ,knocking tayi ,a dakile ya bada izinin shigowa,tura kofan tayi ganin Mom CE yasa ya mike da sauri yana kauda idonsa daga kan laptop din dake gabansa,da murmushi ta karaso inda yake tace"anata aeki son?".
"Um Mom,barka da rana".
A takaice ta amsa tace"ka shirya kaje ka duba Hafsa tana asibiti,ga abinci nan ka tafi dashi".
A zuciyarsa yaji wani kululun bakin ciki ya tsaya masa a fili kuma ya wayance da fadin"subuhanallah Mom bari n shirya da sauri naje dubata".
Be jira cewarta ba ya fada toilet, itama ta fice,40min ya fito sanye da farar bathtub da karamin towel a hannunsa yana goge ruwan kansa gaban mirrow ya wuce ya shafa mai tare da gyara kansa sannan ya nufi wadrope don nemo kayan dazai saka,black jeans ya dauko da farar T-shirt ya saka gefen bed ya zauna yana saka socks da daure igiyar shoe dinsa ,turarensa mai matukar kamshi da daukar hankali ya fesa sannan ya daura tsadaddiyar agogonsa ta azurfa a tsintsiyar hannunsa,masha Allah ba karamin kyau yayi ba ,ya dauki key din mota da wayoyinsa yayo waje, a parlo ya iske Mom,sannan yake fada mata zai wuce .
Shafa kansa tayi sannan tace"Allah yayi maka albarka ,ka gaeshemin da y'ar tawa ,an saka abincin a mota".
Akan labbansa ya amsa da Ameen ,sannan ya mike ya fita,tunda ya fito sojojin dake gidan suke gaeshesa ,amma hannu kawai ya daga masu ,da sauri driver dinsa ya iso zai karbi key din motar, jefa masa yayi be jira a bude masa mota ba,ya bude da kansa ya shiga,saida suka fita daga gidan sannan driven mai suna Solomon a girmame yace"yallabai ina zamuje?".
Kamar bazaiyi magana ba can kuma yace"general hospital "da muryarsa mai kama da an masa dole ,ba jimawa suka isa harabar asibitin ,da hannu yai masa nuni da bot din motar ya wuce cikin kasaita da izza,mutane sai kallonsa suke,cikin sauri Solomon ya dauko basket din abincin da Mom ta bada yabi bayan uban gidan nasa da sauri.
Knocking Hafeez yayi ,Maryam tazo ta bude ganin shine yasa ta basa hanya tana masa sannu ,itama Ummy gaeshesa tayi, sannan maryam ta karbo basket hannun Solomon ta ajiye sannan suka bar dakin.
Shiru d'akin yayi na tsawan mintuna ,kafin Hafeez yace" haba ke kuwa daga fara wasan harkin soma ziyartar asibiti duk jarumtar taki".
Kamar bazata tankamasa ba kuma dai ta d'ago rinanun idanuwanta tana watsa masa harara tace"meya kawo ka?".
Murmushin gefan baki yayi yana mamakin dauriyar yarinyar don tunda yake babu yarinyar dake kallonsa ido cikin ido ta fada masa magana ,a dakile yace"umarnin uwa".
Bata kuma kallonsa ba tace"dama ka daina boyeboye ka bayyana masu daukar fansar dake ranka,kuma kai baka isa kasa na daina abunda nayi niya ba".
Murmushin gefan baki yayi yana taunar lips dinsa yace"while zanyi maraba dake zuwa gidan bakin ciki ,nabarki lafiya".yana zuwa nan ya mike ya fice har yakai kofa ya juyo yayi saluting dinta ya fice abinsa.
Bayansa tabi da harara tare dajan siririn tsaki.
Da Dare Hafsa ta matsa a sallameta ta warke ,a dole aka bita yacce takeso suka dawo gida sannan drive yakai Ummy da Maryam gida.
Tunkan su dawo asibiti su Abbun suka yanke shawarar a maido da dukkan auran yaran nan da sati biyu ,ayisa rana daya ,don haka Abbun yace Ummu ta turo masa Hafsa.
Jikinta ba kwari taje ta durkusa gaban Abbun tana gaeshesa ,amsawa yayi yana tsura mata idanu ga tausayinta da yakeji amma a dole ya dake don bayaso ta maidashi karamin mutum dukta rame ta fita hayyacinta.
Gyaran murya yayi yace"Hafsa na kiraki ne na fada maki auranku ya dawo nanda sati biyu tare danasu Ummy saiki fara shiri umarni na baki".
Dukda hawayen dakeson zubo mata,amma ta rikesu tace" na gode Abbun Allah yasa haka yafi zama alkairi".
Da Amin ya amsa yana saka mata albarka ,sannan ta mike ta koma part dinta ta kwanta tana warwara da kullewa.
Washhhh na gaji gaskiya,nima bari n lula tunanin mai gira na🙊sora kuce zumudi nakeyi irinsu o'o
Allah ya gafarta ma iyayenmu ya kyautata karshenmu
*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}
🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*
NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*
SADAUKARWA GA
*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*
DAGA MARUBUCIYAR
*SANADIN GATA*
*DALILIN SO*
*YAUDARA KO BUTULCI*
*HANAN*
*ASALI NA*
*PAGE* 10
Rufda ciki Hafsa tayi tana tunano kalaman Abbun akanta,yanzu nan da sati 2 za'a daura mata aure?,duk da irin yacce taso su fahimceta sunki,itakam ya zatayi da rayuwarta da boyyen sirrin dake shirin tonuwa Wanda taketa faman boyonsa ,wasu zafafan hawayene suka gangaro busa kyakyawar fuskarta.
Dafata da Ummu tayi shine yasa ta dago jajayan idanuwanta tana kallon Ummu.
Murmushin karfin hali Ummu tayi ta tada ita zaune ,ta dafa duka kafadunta da hannayenta a nutse tace"Hafsa".
Cikin sanyayyar murya ta amsa da"na'am Ummu".
"Inaso ki saurareni ,ki kuma bude kunnuwanki kiji mezan fada,Hafsa kaddara ta riga fata,Allah yasan ba zuwa kikayi kika bada kanki ga wani d'a namiji ba,shiya kaddara komai a rayuwarki,komai zakiyi ki tsaida zuciyarki wuri d'aya ,abunda ya faru dake baya nufin ki yanke kauna,kice ke bazakiyi aure ba,sunnar manzonmu ,da iliminki,fargaba ba taki bace,komai zakiyi kiyishi da yakini,domin yakini na kawo nasara a rayuwa ,rashin karfin gwaiwa yana kawo rashin tabbas,kibarwa Allah komai,ki maida kanki garesa saiki samu saukakkar hanya,amma tunani da shiga kunci ba naki bane ,domin bazasu taba baki karfin zuciya ba".
Kalaman Ummu sun shiga Hafsa ,don haka ta goge hawayen idanuwanta ta fada jikin Ummu tana kokarin mayar da wasu hawayen dake kokarin zubowa.
Tun daga ranar Hafsa tadan rage nuna damuwarta ko kadan batason hankalin mahaifiyar nata na tashi musamman data riga tasan matsayin Momy a wurin Ummu,dole take boye damuwarta gashi da anyi auran zasu wuce London zaiyi wani cos acan da aka turashi tsawan shekaru biyu,shine abunda yafi damunta,musamman data lura rashin kunyar da taimasa shiya haddasawa zuciyarsa son auranta donko ya Dade da bayyana mata hakan.
Niko dake labe nace ah lallai akwai kallo,shiru nayi da bakina don kada ta jiyoni ta hadani da Mrs sardauna,a hanani binsu London kwaso rahoto🤪💃🏻💃🏻
**************
Kowanne bangaro na amaran da anguna shirin biki sukeyi,musamman su Ummy da suka dage saisunyi Dinner, itako Hafsa iyakarta ido ,bata cewa dasu komai duk tayi sukuku gata nan dai,sunsha gyara sosai ba kamar Hafsa da kowa yafi saka idanuwa kanta,bata fita ko ina ,fatarta sai sheki take ta kumayin sulub da ita tana sheki,musamman Momy ta dauko mai kyara daga Sokoto domin ta gyara mata yaranta,daran biki mai lalle da kitso tazo ta kunshesu tare dayi masu kitso ,ga kamshi daya kama jikinsu ko ina suka gitta saika juyo.
Da Dare da misalin karfe 8:00pm ,kowa sai shirin Dinner yakeyi ,ga kawayensu cike da gida Wanda su Maryam suka gayyata,a gidansu Ummy masu makeup suka iskesu domin shiryasu Momyce ta turosu,kafin angunansu suzo daukarsu zuwa holl din da za'ayi abun.
Maryam na hango shirye cikin kayanta pink and blue tayi masifar kyau sosai ,sai sheki take komai yaji ta fito tsab da ita,Ummy ce kefanta itama ta shirya kayanta purple and white tayi kyau sosai abun Das da ita gaskiya alhmdllh,sannan aka fito dasu domin angunansu sun iso ko wacce ta shige motar nata gashi dukan kwashe kawaye ,suka nufi wurin Dinner din.
Hafsa kuwa kwance take a bed tayi rufda ciki tana sharbar kuka da muryarta dishashiya,dakyar Ammi ta lallabata ta tashi ta d'arwayo face dinta tazo aka soma shiryata,ga wani masiffan ciwan kai da take fama dashi tun jiya badon tasoba ta tsaya aka shiryata cikin gown red colour sai head black, tayi matukar kyau sosai cikin shigarta ta red and black sai zuba kamshi take ,tana zaman jiran tsammani hakanan taji zuviyarta ta fara tsinkewa bata kara tsurewaba saida taji ance ta fito Hafeez na waje,raurau tayi da ido alamun kuka,Ammi tace kada ta sake taga kukannan indai tanaso su shirya,ba yadda ta iya ta jawo hillshoe dinta black colour ta daura a kyakyawar kafarta datasha zanan lalle ja da baki ,a hankali ta soma takowa har zuwa inda motarsu take.
Cikin sauri Adam ya fito ya bude mata baya inda Hafeez yake,tun kafin ta shiga kamshin turarensa ya addabi hancinta ,a hankali ta shiga motar,ya rufe ya dawo mazaunin driver yaja motar zuwa holl din.
Tunda ta shiga motar kanta ke kallon kasa batamasan sun isoba saidai ta tsinkayi muryarsa yana fadin"OK so kike na fito dake ko?".
Bata basa ansa ba ta zuro kafafunta ta fito,cikin rashin sa'a Ashe ta rufe da rigarta,Jan hannunta yayi, aeko tayo baya zata fadi,sora kadan takai kasa yasa hannuwansa ya rungumota ,aeko idanuwanta a rumtse gam harsun ciko da hawaye tana shirin tajita a kasa,siririn tsaki yaja ya bude motar ya fito da rigai ,yace"saiki tashi bakyauya kawai dake".
Jin furucinsa yasa ta bude daradaran idanuwanta tana aeka masa da kallon tsana,sai yanzu ma taga shigarsa sanye yake cikin red suit sai inner black da shoe black ga tsadaddiyar agogonsa ta azurfa yayi kyau sosai ,iska ya hura mata a fuska yace"yadai meye na kallon?".
Baki ta tabe tace"meye abun kallo jikin bakyauyen mutum"ta karashe maganar tana murguda baki.
Lips ya ciza alamar zakiyi bayani,ya kama hannun suka shiga cikin holl din ,komai a tsare wurin yayi matukar kyau,duka amaran da angunan sun hallara su kadai ake jira don haka suna shigowa aka para program.
Aradun Allah na gaji 🤪🤪
Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe
Muhphat luv
*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}
🌈kainuwa writers association
Sadaukarwa ga
Hafsat (ummu nabil)
Maimunath (ummy ontop)
Hafsat malami
Na
Maryam Ismail
Page 11
Take a wurin MC ya fara gabatar da shirye shiryen da suka tsara zasuyi a wurin,kowa ka gani fuskarsa dauke da farin ciki marar musaltuwa,fiddo amare yayi daya bayan daya a wurin sukayi rawa,har ya iso ga Hafsa a hankali ta tako har zuwa filin tsaye kawai tayi kanta a kasa,ko kadan batayi tsammanin fitowar Hafeez ba,saidai taji ya fara mata ruwan daloli yayinda Abduol ke gefansa yana zuba masu a tare,dara daran idanuwanta ta sauke akansa,murmushi ya mata tare da kashe ido d'aya,baki ta tabe ta juya.
Cake aka fito dashi na murnar auran nasu, wuka ya dora a cake din yana tsareta da ido alamar ta dora nata itama,kafin ta aekata haka ta tsinci muryar MC din yana fadin "Amarya ke muke jira,Ku yanka cake din tare da ciyar da juna".
A kasalance ta dora hannunta akan na Hafeez,wani sock sukaji gaba dayansu ,saurin kallon juna sukayi,a hankali suka yanka cake din ,kad'an ta dauka hannunta na kyarma takaishi bakin Hafeez ,saidai ya rike hannunta sannan ya idasa dashi baki yana wani kyataccen murmushi,harara ta watsa masa tace"ka daina wani zakewa malan".
Bece komaiba harya ebo cake din ,ciko hannunsa yayi ya dafe kanta ya tura mata a baki dukya bata bakin,murmushin mugunta yayi yana kashe mata ido,bata kuma tsinkewa da lamarinsa ba saida ta jiyo harshensa yana lashe na gefan bakinta daya bata mata,zaro idanuwa tayi hakan yayi dadai da ihun da mutane suka saka ana masu hotuna da lika masu kudade tare da sakin sauti,wani kululun bakin ciki yayi mata tsaye a zuciya tana kwabe fuska.
Cike da kallon tsana Suhailat ke kallon abunda ke faruwa ,hawayen idanuwanta ta tashe tana fadin"never,bazan taba bar maki Hafeez ba Hafsa kinyi karya soyayya tafi karfin nan mu zuba mu gani"
"Come down sister ,meye na tada hankali har haka,zaizo hannune" Adam ya fada yana kashewa kanwar tasa ido.
Murmushi tayi suka tafa.
Haka aka gudanar da wannan Dinner din wasu na farin ciki wasu akasin haka har lokacin tashi yayi
Next day
Da misalin karfe 11:00am dubban al-umma suka shaida daurin auran MAIMUNATH DA MUHAMMAD,MARYAM DA SAGIR,HAFEEZ DA HAFSA akan sadaki dubu dari dari,angunan na hango baki be rufuwa sunyi matukar kyau ,masallacin dankam da mutane ko kadan baka banbance wurinka wane yazo ko yaya.
Faduwar gabace ta ziyarci Hafsa daidai lokacin da aka daura tare da sakin cup din hannunta hawayene suka fara ambaliya a kyakyawar fuskarta ,da kyar aka lallasheta aka shiryata haka dai akayi yinin ranar jikinta sukuku.
Da yamma aka kaisu Abbun da Daddy da Abba suka masu huduba