Showing 3001 words to 6000 words out of 37818 words

Chapter 2 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

na don iskanci,to wallahi wacce ta karamin dariya sai munyita kuma taja ban zuwa bikinta ehee"ta karashe maganar tana murguda baki.






Da misalin karfe 10:30am part din Abbun naga mutane ciki sai farin ciki suke sun gama raba kaya an saka aure wata Daya suna cike da farin ciki sannan sukayi bankwana kowa ya kama gabansa.






Kallonsu Hafsa takeyi ta window dukda taji gabanta ya tsananta faduwa sosai tace"waini me akeyi a gidannan haka".






Babu Wanda ya bata ansa daga cikinsu.




Ana komawa aka fadawa Hafeez part dinsa ya koma suka tafa shida Adams cike da farin ciki suke tsara abubuwan da zai kasance.Hafeez kuwa daukar fansace zurhwan a zuciyarsa da tsanar Hafsa.






Saida kowa ya tafi Abbun ya aeko Ummu ta kira masa Hafsa,har part dinta ta shigo tace"tashi muje Abbunki na kira".jiki a sanyaye tabi bayan Ummu.








Suna shiga dakin Abbun haka kawai taji kafarta na neman kasa daukarta,da sauri ta duke kasa a gaban Abuun a hankali ta furta"gani Abbun".






Nisawa yayi yace"Hafsa ki bani aran hankalinki kiji mezan fada ,meye matsayin Alhaji Muhammad da Hajiya Safiya a gidannan?".




Murya na rawa tace"Momy aminiyar Ummu CE tun yarinta sanadiyar zumuncinsu har kuka fara aminci kaida Daddy tunda na tashi tare na sanku".






"To Alhmdllh naji dadi da kikasan wannan ,kuma kinsan babu abunda dayanmu zai nema a wurin dayansa yaki samu,matsayinsu yafi gaban nan,jiya sukazo nemawa Hafeez auranki ,kuma na basu yau an saka auranku wata daya kije ki fara shiri".






Tunda Abbun ya ambaci aure Hafsa ta daina gane da wanne yaraye yake magana,zafafan hawaye ne masu dumi suka soma zarya a kyakyawar fuskarta lokaci daya zuciyarta ke barazanar tarwatsewa idanuwanta suka sauya launi daga fari zuwa jajaye suka firfito jijiyoyin kanta suka fito radau kana ganinsu barobaro,murya na sarkewa ta furta" Abbun kada kumun haka,bazan iyaba na tabbata Hafeez baya sona,kuma nima bazan taba yin aureba banaso mutuncina zai ida zubewa kunsan meya faru dani,pls Ummu na ki fada masa bazan iyaba".






Tsawa Abbun ya daka mata Wanda yasa ta firgita ta juyo tana kallonsa yace"ki nitsu ba shawara nake dakeba ,umarni nake baki indai ni mahaifinki ne".








Bata kara furta komai ba illah kukan daya kwace mata ta mike kafa sanyaye ,jansu kawai take harta iso kan stairs inda ta kasa daga kafar numfashinta yayi tsaye cak jiri ya soma dibarta kafin kace me ta fara gangarowa daga stairs har kasa a sume ga gefan kanta daya fashe.






Ta window su Ummy suka hango da gudu suka fito suna saka ihu,ihunsa yasa Ummu itama fitowa a razane.








Share and comment




Yawan comment yawan typing,luv u all








*MUHPHAT LUV*
















*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}






🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*








SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*






*PAGE* 5








Jijigata Ummy takeyi tana kiran sunanta amma ko motsi balle ya nuna alamun tana da rai,ruwa Ummu ta ebo tanata zuba mata hakan besa ta farfadoba,cikin gaggawa suka dauketa sai Asibiti,suna zuwa aka shiga emergency da ita likitocine akanta suna kokarin ceto ranta.






A wajeko sai safa da marwa su Ummu suke,Ummy kuwa tuni ido ya raina fata kuka take kamar ranta zai fita,Maryam ce rike da ita, tana bata baki dukda itama hawayene kebin fuskarta.








A sanyaye Ummu tace"Abbin Hafsa don Allah kodai a fasa abun nan dukna tsorata".




Bata ida magana ba ya daga mata hannu alamun tayi shiru kafin yace"badai a gida na ba,waye zai zama karamun mutum,dole sai abunda takeso,kinsan auranne bata so kuma ba abu bane mai juwuwa,idan an daura akai gawarta a gidan".yana zuwa nan ya wucewarsa office din Dr din da yake kula da ita,dama family doctor nasu ne.








Alhamdulillah an samu nasaran ceto ranta,daki aka ajeta drip ne a hannunta sai bacci take sanadin allurar baccin da aka mata,Ummy ko rike take da dayan hannunta tana kallonta cike da tausayi lokaci daya tayi zuru zuru damuwa ta nuna karara a jikinta dukta fada.
Sai a lokacin Maryam ta Ciro waya ta fadawa Momy sannan ta kira Hafeez ta fada masa.
Wayan ya kashe yana binta da kallo,taboshi Adams yayi yace "mutumin ya"




Dariya yayi sannan yace"wai Hafsa aka kwantar a asibiti,shine nike tunanin tun yanzu tunkan tazo hannu ta fara karaya".




"Lallai da aeki gabanka,Ashe ragguwace matar taka" Adams ya fada,duka Hafeez yakai masa ya goce.








Ummu ko su Ummy ta bari nan taje gida ta shirshirya before ta dawo.




Cike da damuwa Maryam ta dafa Ummy tace"wai don Allah meke damun Hafsa haka,wannan wacce irin kiyayya CE tsakaninta da maza me sukayi mata?".






Ummy dago runannun idanuwanta tayi takai dubanta ga Ummy na tsawon wani lokaci sannan ta numfasa tace "wannan wani boyayyen sirrine da muka Dade da binnewa a zukatanmu,amma Maryam mun zama daya kiyi kokarin rufe mana sirrinmu don Allah,abun ya farune muna da shekara sha biyar muna ss 2".




*ASALIN LABARIN*




HAFSA ta kasance yarinya kyakyawa ajin farko y'ar gata gaba da baya kowa na sonta ko kadan bata da kwaramniya saidai masifaffiyace ta gaske bata daukar raini muddin zaka shiga gonarta to zaka tantance zakasha ruwan wulakanci duk girmanka kuwa bata kunya kuma bata da tsoro,wannan halin nata na damun Ummunta,musamman da idan tayi la'akari Ummy tafi Hafsa hakuri ko kadan ita ranta baya baci akan abu kuma kawartace tun yarinta.






Tafiya sukeyi a hankali gefan scul dinsu,suna labari,da sauri Ummy ta jawota daga kan hanyar tana duban motan data taho.






Kallo kawai Hafsa tabi motar dashi zuciya tazo mata kusa,tsayar da motar sukayi har inda suke samarin biyu suka iso sanye suke cikin kakin sojoji fuskar ko kadan ba Annuri Adams da Abdul kenan a fusace Adam yace" ku yan yarannan rashin kunya ke damunku da bazaku iya matsawa a hanya ba,saimu takeku mun take banza".








Kallon sama da kasa Hafsa ta bisu dasu"cikin fushi tace nafi karfin nayi daku saishi wancan ogan naku aeku yaransa ne"tana zuwa nan ta bankade Adams ta nufi inda suka aje motarsu ,wani kyakyawan saurayine ajin farko jikin motar tsaye idanuwansa rufe cikin bakin glasses.






Da isarta wurin hannu kawai tasa ta zare glasses din idon nasa tace"a gida irin tarbiyar da aka samu kenan,ko kuwa uniform ya baku damar hakan,maybe kuma titin na Abba ne shiyasa bakwa da bakin bada hakuri Ku nemi bige mutane amma Ku dauki ransu kamarna dabbobi bako hakuri sai tashen balagar rashin kunya,aeda kun takemun wallahi da kaf Family naku saisun shaida"glasses dinsa ta jefa masa a fuska taja hannun Ummy sukabar wurin.






Sake da baki Hafeez yakebin hanyar da sukayi da sauri,wani irin zuciya da tukukin bakin ciki na damunsa,duka yakaiwa motan dake gabansa yana fadin"ni Hafeez ,za'ayiwa haka,banga y'arba"tuni fuskarsa tayi jajir be jira wata ,wata ba ya figi mota yabarsu Adams anan tsaye,yana zuwa gida ya fada part dinsa ya rufe tuni ya soma farfashe kayan dake dakin yana jifa daduk abunda ya tari gabansa frige ya bude ya zaro kwalbar giya ya daga kai sama ya shanye tas ya jifar da kwalbar seda yasha yayi mankas sannan ya fadi kasa bacci yayi awan gaba dashi.












*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻










Share and comment








Muhphat luv














*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}






🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*








NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*










*PAGE* 6












Bugawar kofar da Momy keyi ya tashi Hafeez daga bacci ganin yanayin da yake yasa ya mike a rude ,cikin sauri yayi kokarin gyaran dakin ya wanke fuskarsa yazo ya bude kofan kansa a sunkuye.






Rike masa kunne tayi tace"ananan ana baccin da aka saba ko,maza ka wuce masallaci "




Ido a lumshe ya kalli Momy sannan yace"Momy bari n watsa ruwa to"


Shafa kansa tayi sannan ta juya ta koma part dinta,toilet ya shiga cikin muntina kadan ya shirya sannan ya fita zuwa masallaci.










Cike da Mamaki Ummy kebin Hafsa da kallo sannan tace"gaskiya banji dadi ba Aminiya,abunda kikawa wannan guy din kinga bashi yayi miki ba".






Yatsine fuska Hafsa tayi tace"dallah dama indan ke za'ayi abu da ba'ayi ba,kawai saimu bari su rainamu,nikam yanzuma na fara eheeee,kinga ni kizo ki rakani muje naga Hafeez don yau banganshi ba,kuma nawa Mama aeki".






Bata jira cewarta ba taja hannunta kai tsaye suka wuce gidansu Hafeez.






Hafeez saurayin Hafsa ne,tun tana primary Allah ya hadata dashi suna matukar son juna da kuma soyayyar juna ,mahaifinshi ya rasu kuma talakkawane saidai sunada rifin asiri.








Da sallama suka shiga gidansu Hafeez, cike da fara'a Mama ta taso tana masu sannu da zuwa,gaesheta sukayi bayan sundan taba hira Hafsa ta cire hijab din scul dinta ta somawa Mama shara yayinda Ummy ta tattaro wanke wanke.




Fitowar Hafeez kenan daga daki,ko kadan besan Hafsa tazo ba tsayawa yayi yana kallonta cike da tsantsar soyayya ,a hankali yabi bayanta ya tafa mata hannuwa a kunne,da sauri ta dago tana kallonsa ta rausaya idanuwanta kafin tace"Ya Hafeez ni mun bata Allah kuwa duk yau ban ganka bafa".




Kara kura mata ido yayi sannan yace"haba Hafsatu na,ke saikiyi fushi dadan dolon yayanki yanzu ki kallah zan kirga hannu so ukku saiki ,1,2,3" cike da soyayya Hafsa ta rungume yayan nata.






Zaunar dashi tayi gefe duk inda tayi yana binta da kallo harta karashe aekinta sannan sukawa Mama sallah ya tashi ya bisu suka fara raka Ummy gida sannan ya tafi rakata.






A gate suka bankwana da kyar suka rabu,da sallama ta shiga gidansu a main parlor ta samu su Ummu ita da Abbu,da Kallo Ummu ta bita sannan tace"ke Hafsa zo nan ina kika tsaya?".




Dukawa tayi gaban Ummu a rayuwar Hafsa batasan karya kuma ta tsani karya a hankali tace"Ummu naje gidansu Yaya Hafeez ne na dubashi kuma na tsaya taya Mama aeki".








Sake da baki suke kallonta,dukda abun ba mamaki ya basu ba,don ta saba zuwa gidan nasu.




"Tashi ki tafi" Abbun ya fada,mikewa tayi ta wuce dakinta.








Har akayi sallar la'asar Hafeez na masallaci,sannan ya dawo dakinsa ciki ya iske Adam da Abdul sai wani Wanda be saniba ,be kulasu ba ya fada a bed yana kallon sama idanuwansa sunyi jajir da Alana ranshi a bace yake.






"Pls friend banason bacin ranka,na samo mana solution kaga wannan yasan komai akan wannan yarinyar ya fada mana tana da saurayi kuma tafi sanshi da komai data mallaka inaga shine mafitarmu musa a satoshi talakkawa ne mu siyesa ya kawo mana Hafsa har gidana ,daga nan ya kama kunnensa ya rad'a masa wani abun ".






A razane Hafeez yace" anya kuwa Adam bazan iyaba".




"Pls be aman so daya kadai,kuma don daukar fansa kada kaban kunya mana"Adam ya fada.






Shiru Hafeez yayi alamar tunani sannan yace" aje a kaimanshi gidan Adam da dare",yana fadan haka ya juya ya kwanta .








Haka ko akayi ,har bakin gate Hafsa ta rako Hafeez hada hawayenta wai tun dare beyiba sosai zai tafi,hakuri ya bata ya fada mata gobe zaizo suje har scul,har Hafeez ya bace Hafsa na tsaye tana daga masa hannu sannan ta dawo gida.






Kasancewar unguwar ba mutane,hakan yaba sojojin damar dauke Hafeez a jeeb din su suka rufe masa ido ,koda suka kaisa gidan Adam a gaban Hafeez suka jegasa ,shiko juye juye yake kasancewar sun dauresa kuma sun rufe masa baki.










Don't forget to




Share
Comment
Like








Muhphat luv






: *TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}






🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*








NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*






*PAGE* 7






Warware masa idonsa sukayi amma hannuwansa na baya a daure tun daga kasa Hafeez ya soma kallon Captain har sama bakinsa na rawa ya furta"Don Allah menayi maku,Ku barni naje wurin Mama na".






Fuskar Hafeez a daure yace"karka damu in kaso tana cikin koshin lafiya,mu ba wani abun mukeso daga gareka ba,indai kayi to zakaga Mamanka lpy lau zata rigaka komawa gida ma".






A razane Hafeez ya dago yace"kuna nufin Mama na na wurin ,pls kada Ku cutarmin da ita".






Murmushi Adam yayi yace"look Hafeez mamanka nanan lafiya ,kawai dai mun dauketa ne domin muyi musaya ,munaso gobe karfe 8:00am ka kawo mana Hafsa ,zamu baka gida ,kudi,da mota mahaifiyarka taji dadin rayuwa ka kula da ita,kaima ka fito kamar ko wanne D'a a duniya".








Kallonsu kawai Hafeez yakeyi don tunaninshi ya kuma rudewa tunda yaji sun ambaci sunan Hafsa saidai kuma soyayyarta baxatasa ya rasa gatan da ake shirin yimasa ba Wanda ya Dade yana mafarki yana so yayi kudi sosai a hankali yace"me zakuyi Hafsa ,metayi maku".






Basu bashi amsaba aka aje masa jakar kudi da mukullin mota da mukullun gida ,ga cheque ya rubuta dadin kudin da yakeso,tuna cikin bakin talaucin da sukeyi yayi,sai su yini su kwana basuci ba,saidai Hafsa ke basu abinci,Hafeez naso ya shana da rayuwa kawai yace"za'a kawota,amma Ku kulamin da Mama na"






Basu tanka masa ba waya Adam ya basa yace "daka daukota ka kira da wannan number din,muma zamu cika maka alkawarin da muka dauka,Ku mayar dashi"






Daukarsa sukayi har kofar gida suka kaisa,yana shiga ya soma zagaye gidan yana zancen zuci ,da yanzu Mama na na gidannan,shin zanko iya canza ra'ayi soyayyata ta fiyemin dukiyar dazan samu,na zauna cikin jin dadi na more rayuwa ,bazai yiwuba,kiyi hakuri Hafsa dukiya da mahaifiyata tafi man komai mahinmanci a rayuwa.




Wayarsa ta soma ruri hakan ya dawo dashi daga tunanin da yake ya dauko yana duba screen din MY WIFE ya bayyana a kai dauka yayi tare da sallama.






Sanyayyar ajiyar zuciya Hafsa ta saki cikin sauri tace"Ya Hafeez ina ka shige ,tunda ka taho nake kiran wayarka amma kaki dagamun kakosan wanne irin hali na shiga".




"Sorry my wife bazan sakeba,wayan n silent ne ,amma ae kinsan ina tare dake zuciyar na wurinki" Cewar Hafeez.


Haka yaita mata kalamai masu dadi da ratsa zuciya,ita kuma tana fadawa don tana matukar son Hafeez duka rayuwarta ta ta'allakata ga Hafeez dinsa,sun dade suna waya kafin yace ta shirya wurin 7:30am zasuje wani wuri tare,bata musaba ta amince masa,sannan sukayi bankwana.




Wayan yabi da kallo da rubabbar katifar da yake kwance,ya tuna inda Hafsa ke kwance ji yayi ya kagara safiya tayi.




Hafsa kuwa tunanin Hafeez takeyi da irin soyayyar da take masa,ko meyasa yace kada ta fadawa kowa tare zasu fita oho,koma menene kuma ko inane zata bishi saboda tasan bazai taba cutar da ita ba,murmushine ya subuce mata a lokacin da idanuwanta sukaci karo da makeken hoton Hafeez dake makale a bed dinta daukosa tayi ta goge sosai ta rungumesa a kirjinta har bacci yayi awan gaba da ita.






Next Day




Tunda wuri ta farka tasan Hafeez beson jira before 7:30 ta shirya cikin riga da siket na atamfa ta daura dankwali ta feshe jikinta da turare ta yafa gyale ta fito,rokon Ummu tayi tayi akan ta barta ta fita,bazata dadeba kawarsuce ba lafiya zasuje dubiya ,saida Abbun yasa baki yace ta barta amma kada ta jima kuma ta kula da kanta sukayi mata Allah ya tsare sannan ta fito cike da farin ciki.
Waya tayiwa Hafeez gashi ta fito ,mahada sukayi,kafin ta iso yayi waya da new phone din da aka basa, aeko ba jimawa aka turo masa da mota da driver, sannan ta iso cike daso da kauna ta gaeshesa sannan ya nuna mata motar da zasu shiga.




Dan cijewa tayi,murmushi yayi yace"yau kuma rashin yarda ga Hafeez ta juyo?,ko baki yarda dani bane?".






Lumshe idanuwa tayi tare da murmushi tace"har abada zanci gaba da yarda dakai,zan yi komai dominka kama daina fadan haka".




Hannu kawai ya mika mata,babu ko d'ar a tare da ita ta Dora kyakyawan hannunta akan na Hafeez ,shiko ya rike ya jata suka shiga mota,driver yaja sai gidan Adam.




Bata kuma tambayarsa ina zasuje ba har suka shiga wani tankameman parlo suka zauna ,,yayinda Captain Hafeez yana bed room yana kallonsu ,fuska rufe Adam ya shigo idanuwansa kawai zaka iya gani shida Abdul jikka suka mikawa Hafeez da takardun gida da keys komai suka masa alkawari sun cikashi da murmushi ya dauka ya mike zai wuce.




Rike rigarsa Hafsa tayi,a hankali ya juyo yace"menene ki zauna nan zasu mayar dake gida anjima ,Niko bazaki sake ganinaba,kinga abunda soyayyarki ta samaman shine nima na samu yanci na Faso gari kamar kowa".






Tunda ya soma magana Hafsa tunaninta ya dauke take binsa da kallo,zafafan hawaye suka soma safa da marwa a kyakyawar fuskarta baki na rawa tace"Ya Hafeez kana cikin hankalinka kuwa,Ashe dama soyayya karyace,ko a mafarki ban taba tunanin zaka iya sayar da soyayyata ba ,cin amana kainefa amintacce na a tunanina ko wani kaga zaimin haka zaka iya sayar da rayuwarka akan tawa,kaico daso irin wannan don Allah kacemun mafarki nike ba gaske ba".




"Kiyi hakuri,na zabi kudi da jin dadin rayuwa a kanki".




Cikin tsawa Hafsa tace"Hakuri yayi kankanta ya hana zuciya fashewa,ka cika namiji,ka Dasamun Tabon da bazai taba warkewaba ,bazan taba daina Dana sani akanka ba,kuma zakaga karshenka tun a duniya Allah ya isarmun Hafeez"




Hannu yasa ya bankadeta daga gabansa harta fadi kanta ya bigi class table din dake tsakiyar dakin ,ya fice yaja motarsa ya wuce gida,a tsakar gida ya iske Mama tanata Kaye kaye.






Wani razanan kuka Hafsa ta saki ga jini dakebin goshinta .








Don't forget to
Like
Comment
Share






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻








Muhphat luv
[10/13, 7:52 PM] +234 903 095 3294: *TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}






🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






NA
*MARYAM ISMAIL MUHPHAT*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*




*PAGE* 8








Tsawa Adam ya daka mata yace"dallah rufemin baki,Ashe karyar rashin kunya kikeyi ma"




Be kula ta kanta ba,ya shige bedroom din da Hafeez yake kwance yanajin komai suke fada,dafashi yayi yace"ka shirya zan shigo da ita yanzu"




Ajiyar zuciya hafeez ya saki yace"anya friend inajin kamar bazan iya ba".




"Haba karka bani kunya,yarinyar nan bafa zata taba ganin fuskarka ba rufe fuska zakayi ka mance furucinta a kanka wai mazinaci inaso ka nuna mata ne".






Jin kalaman da Adam ya maimaita ga Hafeez Wanda Yarinyar ta jefesu dasu,tuni zuciyarsa ta hassala yaji wani sabon kululun bakin ciki face Max ya dauka ya rufe fuska yace shigo da ita.






Da karfin tsiya Adam ya saka Hafsa cikin dakin ya rufe kofar da key ya dawo ya zauna shida Abduol suna fira.




Ci gaba tayi da kallon dakin ta ko ina tana juye juye a tsorace ,cikin kasaita da isa ya fito gabanta dukda fuskarsa na a rufe hakan besa ya fasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login