Showing 1 words to 3000 words out of 37818 words

Chapter 1 - TABON DA NAMIJI Compelet Book Writing by Maji Dadi .txt

ο»Ώ
*TABON D'A NAMIJI*


{LABATIN HAFEEZ DA HAFSA}




*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTERTAIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSA MALAMI*






NOTE : *NOVEL DINA BA NAYISHI DA WATA MANUFA BA ,KO KUMA ACE NA WANDA N SADAUKAR GA LABARIN GARESU BA,SUNA KAWAI NAYI AMFANI DASHI KAWAI N MALLAKA MASU NE,BAWAI DONYA FARU GA DAYA DAGA CIKINSU BA ,KIRKIRAR LABARI NE*






*BISMILLAHIR RAHMANUR RAHEEM*






*PAGE* 1






Zaune take cikin makeken parlon su sai cika take tana batsewa da alamu ranta a b'ace yake, taci kwalliya juyi kawai take ta cika tayi makil.
Kallonta Ummu keyi dake gefan tana girgiza kai kasa daurewa tayi tace"Hafsa waimeke damunki?,ke a duniya bazaki taba mance abu ba, kizo kina bata rai a banza"
Sassauta murya tayi tana sonyin magana sai hawaye suka gangaro ga kyakyawar fuskarta kasa furta komai tayi ta dukar da kai tana kwaranyan hawayen bakin ciki.
Sallamar Ummy tasa Ummu tago kai tana fadin yauwa"gara da kikazo a daidai".
Da fara'arta ta iso wurin Ummu ta gaesheta,ganin Hafsa na kuka yasa hankalinta yai natukar tashi ta isa wurinta da sauri tana tambayan ko lafiya.
"Kema da b'ata lokaci,aekinsan damuwa,waifa daga ta fita,tayo saurayi shine ta tsaya ta zageshi tsab sannan ta shigo da bakin rai ae bata iya barin wannan halin data sawa kanta".
" haba Hafsa yanzufa shekara Uku kenan da faruwar abubuwannan ya isa mu sallama ki tsaya ki samu mijin auranki babu wanda k'addara bata fadawa rayuwarsa ta yiwu mu tamu kaddarar kenan.Ummy ta fada.
A razane Hafsa ta mike tsaye,tana aekawa Ummy da mugun kallo a fusace tace"Sahibata Aure,lallai banga D'a namijin da zan iya aura ba,na dade da sallama zuciya daga yin aure,mazan yanzu duk yawancinsu yan yaudara ne, kuma yan iska,ya kamata kisan na daura dammara da duk wani mugun saurayi a cikin duniyarnan musamman ya shiga harkata,ke na tsani maza na fada da babbar murya kuma zanci gaba da tsine musu harnabar duniya"
Tana gama magana daidai da lokacin wasu zafaffan hawaye ke zubo mata idanuwanta harsun fara canza launi tuni *Tabon d'a namiji* ya dawo mata wata irin sabuwar kiyayya ga maza ta kuma bijiro mata,da gudu ta haye stairs ,cikin sauri Ummy ta tashi zata bi bayanta Ummu ta tiketa ,fadawa jikin Ummun tayi itama ta fashe da kukan bakin ciki.
Cikin sauri naga driver ya fito har rawar jiki yake yana zubewa a gaban uban gidan nasa dake fitowa daga mota mota,duk inda ka kallah a gidan sojine ke yawo rike da bindigu suna tsaran *CAPTEIN HAFEEZ MUH'D* ,Hafeez kyakyawan saurayine hadade kyansa nada daukar hankali sosai gaduk Wanda ya kallesa farine Sol kyakyawa ajin farko.
Bebi takan kamewar da ake masa ba kawai ya shige cikin makeken gidan nasu.da Murmushi Momy ta tareshi tana oyoyo my Son,murmyshi kawai yayi ya rungumeta a hankali ya furta"miss u Mom and swt home".
Ya fada a daya daga cikin makamakan royal chairs dake kawace a parlon ya dagowa Mom kafa,dariya tayi tace "badai ka canza hali,gaskiya kazo kayi aure,nikam na gaji ace mutum belt da shoe bazai iya sakasu ba duk girmanka saini nayi", sannan ta sunkuya tana warware masa daurin takallan.
Glasses din idonsa ya cire ya kalli Mom ,yana tunani a zuci waishi aure tab,yaga yarinyar dazai aura kam badaishi ba.
Next Day
Wannan shekarar su Hafsa suka gama Neco don haka suna gida,babu inda suke zuwa,fitowa Hafsa tayi cikin Doguwar riga rova kanta ko Dan kwali babu,Hafsa bata da haske sosai tana da tsayi bata da giba saidai tanada shape daidai gwargwado ga yalwataccen gashi a kanta bakikirin doguwar fuskarta na dauke da daradaran idanuwa farare Sol,ga sarbadeden dogon hanci,fuskar na dauke da d'an karamin cute bakinta mai sulbi.a hankali take saukowa daga stairs kai tsaye wurin Abbun ta nufa ta zauna daga gefansa tana gaesheshi.
Cike da tsantsar soyayya ya amsa tare da shafa kanta yace" y'ar albarka kin fito ina Ummy?".
Dariya tayi jin an ambaci Ummy a hankali tace"Abbun Ummy tana shiri ne".
Kallon agogo Ummu tayi tace "har 12 fa kokin manta nace zan aekeki gidan Alhaji Muhammad wurin Hajiya Safiya ki karboman sako,amma kuka tsaya bacci ko".
Dafe kai Hafsa tayi tace"sorry Ummu na manta be,amma bari muyi break saimu shirya muje ".
Ba jimawa Ummy ta fito da yake anan ta kwana ,Abbun ta gaida da Ummu before sukaje sunayin break ,basu wani b'ata lokaci ba suka tafi suka shirya cikin dogayen jallabiya purple colour sai suka yafa black veil a kansu sai zuba k'amshi suke turo baki Hafsa tayi tace"sahibata ina bakin cikin ganin sojojin gidannan wallahi".
" kin fiye korafi meya ruwanmu dasu tunda ba taremu sukeyi ba,u know mun zama yan gidan,Allah yasa Maryam nanan ma ".Ummy ta fada.
" inako zataje kinsan ta dawo dukanan Mom batason zama ita kadai a gidan"cewar Hafsa.
Note Maryam y'ar kanwar Mom ce,ta dauko daga Abuja saboda mijinta da Danta ba mazauna bane.
Tare suka iske Ummu ta fada masu sakon ,suka fito yau basasan Driver ya kaisu don haka Hafsa ke driven dinsu kai tsaye suka dauki hanyar gidan Hajiya Safiya.
*ALKALAMIN MARYAMA*
Ur comment is needed pls












*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}








🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*


*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTERTAIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT*(UMMU NABIL)
*MAIMUNATH*(UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*








*PAGE* 2






Ba dogon lokaci suka dauka ba,suka isa gidan Hajiya Safiya dake GRA ,kota Ina ka duba sojojine ke zagaye da gidan daga cikin yaran Hafeez Wanda duk in zaizo tare suke zuwa,duba motansu sukayi kafin suka masu izinin shiga.






HAFSAT dake driving bakin ciki ya cikata tayi makil tana kallon sojin dake nuna masu hanya,tsaki taja sannan taja motar zuwa ciki.




Da murmushi Ummy ta kalleta tace"sahiba yanzu sai kice har ranki ya baci ko".




"Karma ki kara kular dani don tsabar iskanci sai an wani dubamu uban meye zamu dauko a gidan,dama nasan wannan banzan na gari tunda na gansu" HAFSAT ta fada tana murguda dan karamin bakinta .






Hmm kawai Ummy ta fada suka fito suka shiga gidan,daidai shiga parlo HAFSAT taji tayi karo da mutum Kansu ya bugu take wayanta da key din hannunta suka fadi,bata tsaya jin zafin dake kanta ba saidai ta dago da muguwar harara cike da masifa,tana jefawa Hafeez kallon tsana da kiyayya tsantsa cike da masifa tace"dallah kai makahone koko baka iya bada hakuri bane kamar ka daki dutse mugu kawai".








Cike da mamaki Hafeez yake bin HAFSAT da kallo amma ya kasa furta komai tsaki yaja ya kauda idonsa yabi ta gefanta ya wuce ba tare daya juyoba.






Ummy ce ta duka ta dauki key din da phone dinta ta fizgi hannunta suka shiga ciki.




Daidai Maryam na safkowa daga stairs da gudu ta iso tana masu oyoyo.




"Ni sakeni tunda kika dawo ae baki nememuba saida mukazo,kuma wurin Mom mukazo ba wurinki ba" HAFSAT ta fada




"Ayyah friend kuyi hakuri wallah ya Hafeez in yana gari baka fita,kuma wayana ya lalace saiyau ya bani wani" Maryam ta fada.






"To kin kare kanki munji,ina Mom" cewar Ummy.






Jawosu Maryam tayi tace "zoku zauna tana fitowa yanzu".






Kafin ta rufe bakinta saiga Mom ta fito,Mom mace mai tsananin kirki da tausayi dason mutane musamman tunda wata kaddara ta fadawa HAFSAT take mutuwar sonta take kula da ita ta dauketa kamar y'ar cikinta,oyo yo take masu tazo ta zauna kusa dasu.




Har kasa Su Ummy suka duka suka gaesheta cike da girmamawa,ta ansa cike da soyayyarsu.




Kafin kace me,tuni an cika masu gabansu da kayan marmari Dana ciye ciye kalakala.






Sannan HAFSAT tace"Momy Ummu ce tace ki bada kayan a kai mata".






" Allah sarki,da ina cewa Hafeez yaje ya gaesheta ya kai mata,dama shiya siyo gold din daga California, tunda kunzo saiyaje ya gaesheta".








Kallonsu Maryam tayi kafin tace"kuzo muje daki mana anjima saimu fita tare".






Mikewa sukayi suka tafi dakin Maryam suna zuwa suka baje a bed,"ohni Ummy ina Al-ameen wai kuna tare ko".






Hannu Ummy taba Maryam suka kashe tace"yana nan k'awa shirin saka biki akeyi ma".






Wata iriyar guda Maryam ta saki tana taka rawar murna,tana fadin "abu namu nima kinga Sagir yayi magana gida,ina gidansa zumuje level 2 ".








" Haba waime ke damunku Ku wani cikawa mutane kunne da firarku marar amfani ,wallahi sai nayi tafiyata namiji har abun yarda ne,mtrsssss taja tsaki".










"Har yanzu kinanan da halinki ,baki taba canza HAFSAT ,niko dasu Ummu zasu biyeni wallahi su hadaki aure da Ya Hafeez ,cos halinku daya kufitini mutane".








Wani irin uban harare da mugun kallo HAFSAT tabi su Maryam dashi cikin masifa tace" Wanda ya fasa,kuma ae kun isa dani naga su mama".






Haka dai sukaita firarsu mafi aka sari ta Hafsa tafi masifa cos sudai suna labarin bikinsu ne da ake kanyi.






Basu wani jimaba suka tashi tafiya gida,Mom ta cikasu da kayan arziki sosai ta basu tsara,tare da Maryam suka tafi ,da dare Hafeez zaije gidan saisu dawo tare.










Da Dare.






Ba musu Hafeez ya shirya cikin manyan kaya shadda blue da hula ga tsadaddiyar agogonsa ga wani mugun kamshi da yake zubawa n dadar turare mai dadin shaka,sallama yawa Mom ya dauki key yayi waje,shida kansa yayi driving har gidansu HAFSAT.








Kwankwasa kofar da zata sadashi da babban parlon gidan yayi .




HAFSAT HAFSAT ,Ummu ke kwallah mata kira"zoki duba waye a waje".








Turo bakinta tayi sannan ta mike ta nufi kofar tana zuwa ta bude kofar,kallon tsana ta kuma jefa masa kafin tace"inkaga dama ka iya shigowa koka dawwama anan kaji".bata jira amsarsa ba ta wuce ciki.








Cije baki yayi ya furta a fili"lallai yarinya ".


Sannan ya shiga gidan,sosai Ummu taji dadin ganinsa suka gaesa ,HAFSAT da Ummu tasa ta kawo masa abun sha,ta hado komai amma tana zuwa ta dungura masa a kasa tana tsaki ta wuce part dinta.




Be wani jima a gidanba suka tafi da Maryam da tasha kayan arziki,kuma take murnar dawowa da wuri cos gobene ake sawa Ummy biki nata kuma sai next week.










*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Comment and share






Luv u all








*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}








🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTERTAIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






SADAUKARWA GA




*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*








*PAGE* 3




HAFSA kuwa da harara ta rakasu daki ta shiga tana kaiwa da komowa tana fadi a ranta wai Ummu tasa nawa wannan Dan rainin aeki,ae sai taja ya rainani ya daukeni sakara kuma abunda bazai taba yiwuwa ba kenan.






Kallonta Ummy tayi tasan me take sakawa a rai,shareta tayi ta fada a bed ta soma waka.




Wata zuciyan ne ta kara ciyo HAFSA aeko ta haye bed din ta daidaici bayan Ummy ta Dada mata duka a baya.






Juyowar Ummy yasa HAFSA sauka daga bed din tana toshe baki don dariyar mugunta ke shirin kwace mata.






"Lallai HAFSA kinci abinci,Toni na bata maki raine,kawai na gaji da kulaki ne ke kullun fushi ko an baki shawara baki dauka ,Allah ma yasa a zaba maki miji,uwar mugunta".






" ke dakata daga nan,ae kece muguwan,aure ga HAFSA to duk Wanda ya kwatanta aurena yayi babban kuskure a rayuwa,ni wama zai aureni bayan kinsan meke faruwa gori dai saina shashi shiyasa nayiwa kaina alkawari kinji malama"ta ida fada tana murguda baki.








*********


Driving Hafeex keyi amma bakin ciki ya damu rayuwarsa sitiyari yakaiwa duka,ya Ciro wayarsa ya kira Adam yace su hadu gida yanzu.




Koda suka karaso gida kokarin daidaita natsuwarsa yayi suka gaesa da Mom sannan ya wuce dakinshi,yana shiga tamkar an dawo masa da abunda HAFSA ta masa duka tsigar jikinsa ya tashi idanuwansa sukayi jajir firij ya nufa yasa key ya bude ya Ciro kwalbar giya ya balle marfin ya kafa baki cikin kankanin lokaci ya kusa shanye fiye da rabinta hakan yayi daidai da shigowar Adam a dakin.






Adam abokin Hafeez ne tun yarinta suke tare komai zasuyi a tare abotarsu harta koma yan uwantaka.






Kamo Hafeez yayi suka zauna,ran Hafeez na tafarfasa ya fadawa Adam abunda ke faruwa tun ranar da suka hadu da HAFSA a gidansu har kawo yau.numfasawa yayi yace"tayi babban kuskure a rayuwarta da har ta shiga gonata y'ar ficiciyar yarinya take nema ta zama kawar fadana lallai ko ba dade ko bajima saitayi Dana sani a rayuwarta kaban shawara abokina".








Numfasawa Adam yayi yace"mafita d'ayace da zaka rama komai cikin sauki babu Wanda yaji balle ya gani,ka nemi auran HAFSA duk abunda zata maka a yanzu ka hakura,idan tazo hannu zatayi bayani inka dauki fansa saika saketa".








Dariya sosai Hafeez yayi cike da murna ya yarda da shawarar abokin nasa,sannan taci gaba da kurbar giyarsa a haka har bacci ya sacesa.








Next Day




Lafiya lau Hafeez ya tashi agogo ya duba har kusan 11 tunda ya dawo sallar asuba yake faman bacci wanka ya tashi yayi ,ya shirya cikin kananun kaya ya gyara gashin kansa ya koma kwanin kyau sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu dadi,kai tsaye part din Mom ya shiga bayan sun gaesa tana zaune a chair kasa ya zauna ya kwantar da kansa a cinyar Mom yace "Mom please ki taimaka Ku aura min HAFSA ina sonta sosai Mom".






Da sauri ta dagosa tana kallon kwayar idonsa tabbas taga da gaske yake babu alamar wasa daga ciki,sannan tace"nidai y'arta HAFSA daya na sani diyar aminiyata ".








" na sani Mom,ita nike nufi"






Guda sosai Mom tayi tana sakawa Hafeez albarka tace"lallai kai Dan halak ne,na Dade ina sakawa raina wannan alamarin kodon rufuwar sirrin rayuwar HAFSA inaso taje inda ba za'a wulakantata ba,na godewa Allah aure anyi an gama Hafeez".








Kallon Mom yayi a zuciyarsa yace tab son da kuke mata ne yasa ta raina mutane toko zata gane kuranta sai nayi maganin duk wannan isar da iskancin da takewa mutane.










Da yamma Mom ta shirya ta iske Ummu gidansu Ummy aka gama saka bikinta 2month sannan suka dawo gida,nan Mom ta fadawa Ummu abunda ke tafe da ita.








Ummu ta nuna farin cikinta akai sannan tace"ae y'arki CE zaki iya yadda kikaso babu Wanda zaice donmi".






Dama mom tayi tsammanin haka,don haka tace babu inda zataje sai Abbun ya dawo sunyi magana before ta turo Daddy.






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻










Share and comment


Luv u all




By
*MUHPHAT*










*TABON D'A NAMIJI*
{LABARIN HAFEEZ DA HAFSA}






🌈 *KAINUWA WRITRER'S ASSOCIATION*




*UNITED WE STAND AND SUCCED:OUR AMBITION IS TO ENTARTEIN & MOTIVATE THE MIND OF READERS*






SADAUKARWA GA


*HAFSAT* (UMMU NABIL)
*MAIMUNATH* (UMMY ONTOP)
*HAFSAT MALAMI*






INA BADA HAKURI GA MASOYA WANNAN NOVEL ,NAJINA SHIRU KWANA BIYU HAKAN YA FARUNE TA WASU DALILAI,INA BARAR ADDU'ARKU FATAN ALLAH YA BIYAMANA BUKATUNMU NA ALKAIRIπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»






*page* 4








Bayan dawowar Abbun aka fada masa Momy tazo wajensa ,a parlorn sa suka samesa ita da Ummu ,kafin Momy tayi masa bayanin komai ke faruwa.




Girgiza kai yayi sannan yace"aekinfi karfin wannan Hajiya Safiyya Hafsatu ae y'arki ce,balle kuma D'ana Hafeezu keson auran ,magana ta kare Alhaji yazo mu kira rana kawai Allah ya shige mana gaba".








Wata iriyar murna ta ziyarci Momy ta soma ma Abbun godiya ta mike sukayi bankwana ta wuce gida tun'a mota ta kira Daddy ta sanar masa,shima yayi murna sosai da yaji HAFSAT ce wacce Hafeez keso hakan yasa yace gobe zai dawo gari.








Tana zuwa gida a parlor ta samu Hafeez yanata danne danne a system kallonta yayi sai wani farin ciki take,mikewa yayi ya tarbeta sannan yace"Mom irin wannan kallo haka,ga murna kinayi meya faru"






"Ae dole ka ganni haka son ,mun samo aure gidan dattawa yarinya nitsatsiya y'ar albarka ,Gobe Daddynku zai dawo a saka ranar auranka da HAFSA iyayenta sunmin kara sun bani auranta".






Wani irin Murmushi ya subuce masa Wanda beyi niyaba a ransa yace yarinya zaki biyane yanzu aka fara wasan,a fili kuma yace"Mom bansan dame zan gode maki ba,naji dadi sosai Allah ya barmin ke Momyna".








Maryam dake tsaye tana kallonsu farin ciki yayi kamar ya kasheta wata irin guda ta saka sannan ta daga hannu tana godewa Allah,tana murnar Samun Yaya kamar nata dazai tallafi rayuwar Hafsa tasan ba shakka zaiyi hakuri da halinta,musamman da taga farin ciki a guskarsa alamun yanason auran.da gudu tayi daki ta dauki waya ta danna number din Ummy bugu daya ta dauka tana fadin"Amaryar gobe"cos gobene kiran ranar auran Maryam da Sagir.


" ke kiketa wannan,abun farin ciki yazo gobe za'a kira ranar auran Yaya Hafeez da Hafsa".




Wata irin ihu Ummy ta saki ta fado daga Bed tace"Maryam banason wasa pls ki sanarmin da gaskiya".






"Wallahi da gaske nake,amma karki fada mata ki Bari su Ummu nasan zasu fada mata ".






" Alhmdllh Allah mun gode maka,nayi farin ciki sosai Allah ya tabbatar mana"Ummy ta fada.
Sannan suka kashe wayar.








********




Tunda safe Daddy ya iso gari,gida ya dauki kamshi ko ina yasha gyara anata farin cikin dawowarsa wurin karfe 9:00am Hafeez ya shigo dashi dama shiyaje daukosa.
Cike da murna suka shiga gida sai faman sannu Momy take masa,har kasa Maryam ta duka tana masa sannu.






Part dinsa suka wuce shida Momy yayi wanka yadan huta sannan suka hadu dining area sukayi break fast mai rai da lafiya.




Sannan Daddy yace"to Alhmdllh naji abun farin cikin daya faru,karfe 10:00 zamu gama saka na Maryam saimu wuce a saka na Hafeez shin a hade rana daya ko kuwa ya kika gani".








Murmushi Mom tayi tace inada wani bikin na y'ata Ummy nanda 2weeks,na Maryam kunce 3weeks zaku saka,to ina rokon alfarma a banni na gama wa'annan a sakamunshi 1month Donna shirya y'ar tawa sosai".






Dariya sosai Daddy yayi yace "Allah ya kaimu".




Mikewa Maryam tayi tace"Momy zan tafi munyi waya da Ummy zamu hadu gidansu Hafsa".






Sai kin dawo sukayi mata kafin ta dakko mayafinta da Bag driver ya kaita acan ta samu Ummy zata shiga,tare suka ida shiga kai tsaye part din Ummu suka shiga suka gaesheta sai shirye shirye akeyi a gidan.




Da murna ta tarbesu suka gaesa sannan" ta masu Allahsa alkairi,tace Ashe da rabon duk zaku tashi lokaci d'aya "




Dariya kawai sukayi suka tashi suka fita.




Tsaye sukayi cak,suna kallonta ,tsaye take jikin Mirrow less ne blue colour da manyan pattern na pink a jikinta zane da buba simple makeup ne fuskarta tayi masifar kyau sosai sai zuba kamshi take ga daurin dankwalin da take bugawa ta daurashi kamar ta Dora gwargwaro.






Juyowa tayi tayi masu fari da ido tace"yada kallo haka,kuka wani sakani gaba kaman gunkuna kuna karemin kallo".






Idasa shigowa sukayi a bed suka zauna Maryam tace"wallahi Aunty na kinyi masifar kyaune".






Dariya Ummy ta saki tace"ba doleba ranar face"suka kwashe da dariya suna tafawa.






Harara ta bisu da ita kafin tace"yan guguwa kawai don'ana saka maku biki tashen balagar tsintsaye na ibarku,hada kirana da Aunty

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login