Showing 24001 words to 27000 words out of 47407 words
Chapter 9 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
Tunawa tayi
da glass É—in window tayi saurin juyawa ta fito daga É—akin nata dan zuwa taga yadda tayi.
Karaf sukayi ido huÉ—u da Hajja Maimoon, baki buÉ—e take kallonta cikin kayan da daga gani
masu tsada ne. Jauhar tayi cak ta kasa barin wajan da take tsaye sai hankalinta da ya tashi dan
bata son ganin matar nan a cikin idanunta. Kallonta kawai Irfaan keyi daya fara kokarin barin
wajen yana ji zuciyarsa tana biya masa wani irin karatu akan Jauhar É—in. Muryar Hajja Maimoon
kawai sukaji tana tafa hannuwa tana kallon Jauhar da tayi ƙasa da kanta tana jiran jin yadda
za'a yi da ita. Suhaila da Jannat suka fito da sauri yayin da Suhana ma ta baro kitchen É—in duk
suka zubawa Jauhar idanuwa bakin su a buÉ—e tamkar sunga abin tsoro.
"Wannan yana nuna cewar da ta sace min gold É—ina bayar dashi tayi sai ake siyo mata kaya
ko?" Maido idanuwansa Irfaan yai jin kalaman dake fitowa bakinta masu kama da gugar zana
yace
"Wait Aunty please dan Allah haba mana, wane irin gold É—inki aka siyar? Me kika É—auke ni ne?
Kinsan ni ba matsiyaci bane, sannan bandogara da kowa ba ballantana kice sai an sammin
wani abun nake iya gudanar da rayuwa ta ba. Enough is enough na kawowa Jauhar kaya ne
saboda bai kamata dan tana matsayin mai'aki amma ace a yadda take jage-jage a gidan nan
haka take rayuwa tare da ku ba. Bansan wane gold kike magana ba dan haka maganarsa ta
tsaya iya nan." Ya faÉ—a yana juyawa zai bar wajan, cikin gadara da nuna isa Hajja Maimoon ta
ƙarasa wajan Jauhar tana cewa.
"Iskancin banza zanyi lokacinka ne, ke kuma muje ki ciro su bazaki saka su ba dan baki
cancanci irin waÉ—annan kayan ba, saboda rainin hankali za'a baki wannan kayan salon a kasa
ware ki da yaran gidan? Ina son kowa ya tsaya a matsayinsa, Jauhar kayan nan ba kalar
darajarki bane ba dan baki cancanci saka irin su a jikinki ba. Oya muje ki ciro su kafin ma ku
saba dasu, ina nan ina jiran ki fito min da gold ɗina shine ke kina gefe guda kina zaɓar
abubuwan da suka fiki mutunci da daraja." Kallanta kawai Jauhar keyi tana jin wani baƙin ciki
yana mamaye mata zuciya. Kallan da takeyiwa Hajja Maimoon ne yasa ta buga mata wata uwar
tsawa wacce tasa Jauhar É—in shigewa cikin É—aki da gudu. Wani irin gigitaccen kuka ta saki mai
taɓa zuciya tana yi tana cire kayan daga jikinta, ita kam ta rasa irin ƙiyayar da Hajja Maimoon
keyi mata. Idan ta gaji da ganinta ta kaita inda ba zata sake ganinta ba mana, ta kaita ayi mata
auran da take ta faɗa koda zata samu sassauci daga zaman ƙuncin nan da takeyi yanzu. Ta gaji
bazata iya jurewa ba dan kuwa babu alamar Hajja Maimoon zata ji ƙanta bare ta bata farin ciki
dai-dai dana rana É—aya.
"Ki gaya min gaskiya Jauhar me kike bawa Irfaan da har yake miki irin waÉ—annan abubuwan?."
Abinda Jauhar ta jiyo Hajja Maimoon na faɗa daga bakin ƙofar zuwa shigowa cikin ɗakinta.
Kafin tace wani abun ta ƙaraso ciki tasa hannu duk ta kwashe kayan, ta kalli Jauhar ɗin ta
hango bra É—in jikinta, da sauri ta É—aga zanin da Jauhar É—in tayi É—aurin kirji dashi, nan ta hango
sabon pant mai kyau. Gabanta ne ya faɗi ta zaro ido tana damƙo wuyan Jauhar ɗin cikin tashin
hankali take magana.
"Harda waÉ—annan abubuwan ya siya miki?" Jauhar cike da tsoro tace,
"Dan Allah Mommy..." Kau...! Hajja Maimoon ta kwashe mata kumatu da mari mai zafin gaske.
"Kiyi hakuri Hajiya." Kallan juna suka yi Hajja Maimoon da ranta yake sake ɓaci tace.
"Ki gaya min ya akai yasan baki da kayan ciki? Naji wannan ya siya miki ne saboda baya ganin
kina saka masu kyau, amma pant da bireziyar nan na jikin ki ko ki sanar dani yadda akai yasan
size É—inki ko kuma yanzun nan nayi gunduwa-gunduwa dake dan na kashe ki dan ubanki." Wani
irin kuka ya kwacewa Jauhar take cewa.
"Allah kuwa babu abinda na bashi." Hajja Maimoon ta sake shaƙo mata wuya Suhana tayi
saurin zuwa tana son kwatar Jauhar cike da tashin hankali.
"Mommy ki rabu da ita please." Cikin sauri Hajja Maimoon ta kalli Suhana tana cewa,
"Doughter kinsan abinda tayi ne? Ko kin gane abinda nake tunanin ta aikata Suhana?" Girgiza
kai Suhana tayi alamar bata gane ba, Jannat dake bayan su ce tace,
"Ta fara canza É—abi'a daga sata tana son fin karfinki Mommy." Hajja Maimoon taja tsaki jin babu
wanda yake tunanin abinda take zargin Jauhar É—in ta farayi. Cikin fushi ta ture ta tana faÉ—in.
"Wallahi baki isa ki janyo min wata masifa ba Jauhar, bazan ɗauki ɓacin rai da tashin hankali ba
kamar yadda ubanki bai É—auka ba son zuciya yasa da shaiÉ—anci baki rayu a hannunsa ba
sannan ni kuma ki jefani a damuwa. Aure É—aya tak nayi a rayuwata kuma bana son ganin wani
abun yazo ya min shamaki a cikin sa. Ki kiyayeni Jauhar bake ba Irfaan da duk wani namiji ma.
Babu ke babu soyayya dan kuwa baki da rabon yin ta a cikin duniyar nan." Kuka Jauhar É—in keyi
amma babu mai lallashinta, Suhana ma da taje zata tayar da ita hanawa Mommyn tayi. Tassss
ta kwashe duk wasu abubuwan da Irfaan ya kawo har maganin bata bar mata ba. Jiki a
sanyaye Jauhar ta maida kayanta masu dauÉ—a sannan ta dawo kitchen lokacin sauran kaÉ—an
Suhana ta kammala soya dankalin. Kallonta Suhana tayi ganin yadda take kuka kamar ranta zai
fita tace,
"Kiyi hakuri Jauhar ban san me yasa Mommy bata tausaya miki ta kowane yanayi ba. Shin wai
ina ne garin ku Jauhar?" Jauhar ta share hawayen fuskarta tana cewa.
"Mommy ce komai nawa tun bansan wacece ni ba, ban san kowa ba sai ita. Kuma idan zataje
can garin na mu bata tafiya dani sai dai muyi waya da Kakanni nawa idan taje. Lokacin da zasu
yi aure da Daddyn ku a gidan da take zaune a nan Æ´an uwan namu suka zo aka É—aura a kuma
ranar ne na gansu inda suka yi ta bani haƙuri suna cewa Allah zai saka min. Ban san me yasa
basu jani wajan su ba suka barni a wajan ta kuma bata sona." Yadda tayi maganar ya matukar
sanyaya jikin Suhana, cike da tausayinta take ce mata.
"Kiyi haƙuri dama haka Allah yake abubuwan sa akan bawa, mu ma kinga bamu rasa komai ba
gashi nan amma mahaifiyar mu bata tare da mu." Cikin sauri Jauhar tace,
"Ni da ku ba É—aya bane Suhana, ku ga mahaifin ku nan kuma kunsan inda mahaifiyarku take. Ni
kuma ban rayu dasu ba, tun sanda naji Kaka na yana cewa. Allah bazai kyale iyaye na ba akan
zarafi na da sukaci na kan so naji me yasa suka barni? Idan nazo tambayarsu ina iyayen nawa?
Sai Hajiya ta make min baki tace na fiye shegiyar tambaya sai kace in naji inda suke wani abun
zasu tsinana min." Jauhar ta ƙarasa muryarta na daɗa karyewa.
"Kiyi hakuri." Suhana ta faÉ—a dan bata da wani abun sake faÉ—a. Suna kammalawa suka jera
komai a dining table, su Suhaila kamar zasu mutu dan ganin yadda Suhana ke yiwa Jauhar É—in.
Jannat ta dinga yin kwafa tana ji a ranta bazai yiwu su bar Suhana ta dinga biyewa Jauhar ba,
yau kawai sunga ta canza tamkar ba Suhana da suka sani a baya ba. Kujera Suhana ta janyo
ta zauna duk da tana kallon yadda Æ´an uwan nata suke harararta bata kulasu ba. Jauhar na
gefe tun lokacin da suke aikin taji wata irin yunwa tana taso mata, nata yana kitchen wanda
Suhana ta É—ibar mata tace idan ta kammala komai ta zauna taci. Tana son komawa kitchen É—in
amma tana tsoran juyawa ta bar gurin wata ta buƙaci abu aga bata nan. Fitowar Hajja Maimoon
yasa Jauhar sake kama nutsuwarta kanta a ƙasa tana tsoran kallonta. Da hannu Hajja Maimoon
ta nunawa Jauhar É—in hanya alamar tabar wajan bama ta san ganinta bare har wani abun ya
haɗa su. Hakan ba ƙaramin daɗi yaiwa Jauhar ba dan sai takejin tamkar an yaye mata wani
nauyi da ya tsaya a kirjinta. Kitchen ta zauna ta janyo abincin da Suhana ta rage mata, zama
tayi ta fara ci tana tunanin yaushe daÉ—i zai zo mata kamar yadda take ganin mutane cike da
walwala Ali yaushe.
******
Kunnensa sakale da wayarsa yana magana a haka ya shiga bedroom É—insa, Hajja Maimoon ya
tarar ta fito daga bathroom fuskarta duk ruwa da alama wanketa tayi. Murmushi ta sakar masa
tare da ƙarasawa wajansa tayi hugging ɗinsa rightside dai-dai lokacin da ya sauke wayar bayan
sunyi sallama da wanda yake wayar. Sosai ya janyota cikin jikinsa tare da janta suka isa wajan
madubi yana cewa.
"Madam ki shirya zamuje wajan siyan zinarinki, sonake daga can É—in a yau É—in nan kiyi magana
da mai kayan da kika ce zaki fara business É—insu. KuÉ—i ne suka zo min so bana son kuma su
tafi cikin harkokina ba tare da na cika miki alƙawuran dana ɗauka ba." Hajja Maimoon ta ware
ido duk irin ajinta da kwalisarta sai da ta bayyana farin ciki tana yi masa godiya tare da addu'o'i
na karin buɗi da kuma gamawa da duniya lafiya. Sake riƙo hannunsa tayi tana kallon fuskarsa
take cewa.
"Ya Habiby me zanyi dan na biyaka kwatankwacin irin wannan farin cikin daka sani?" Kafin ya yi
magana tace.
"Ka sanar da ni komenene I will definitely do it yadda ka sani farin cikin nan." Murmushi ya yi
kawai shi a ganinsa wannan abun da zai yi mata ba komai bane ba, hasalima yana ganin
tamkar hakkinsa ne ya yi mata shi musamman ma jarin da yake son ya bata. Kallonta ya yi
yana matse kafaÉ—unta yake cewa......
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewabook@billysfari
Page 10..
"Mommyn Jannat babu abinda nake buƙata a gareki sama da kulawar da kike bani, wannan
kaÉ—ai ya wadatar dani domin duk abinda zanyi miki wajibina ne nayi miki, but akwai alfarma
ɗaya da nake son roƙonki sai dai bana so kiyi tunanin ko don zan yimiki waɗannan abubuwan
ne zan roƙeki ita...." Ɗan yatsa Hajja Maimoon ta ɗora a saman labɓansa tun kafin yaƙarasa
rufe bakinsa, cike da kulawa ta riƙo hannunsa tana matsawa a hankali tare da kallonsa tana
narkewa haÉ—e da cewa.
"Ka faɗi abinda kake so kai tsaye ina tabbatar maka da zanyi maka ba tare da ɓacin rai ba ko
musanta maka ba, faɗamun meye Ya Habiby?" Taƙare zancen tana kallon cikin idanuwansa.
Murmushi yai haɗe da ɗago hannunta dake riƙe da nasa ya sumbata sannan ya kalleta yace,
"Ina so kada kisake ɗakko zancen gold ɗinki daya ɓata, Please kibar zancen nan ya wuce kada
ya zama wata damuwa tunda Allah zai baki wanda yafishi kin ji ko?" Ya faÉ—a yana nuna mata
son abar zancen akan fuskarsa. Sai da tayi murmushi tare da shigewa jikinsa tace,
"Shikenan Ya Habiby bazan sake É—akko zancen ba in sha Allahu." Hajja Maimoon tafaÉ—a ba don
ranta ya so hakan ba tana ƙara jin tsanar Jauhar acikin zuciyarta. A cewar ta ba dan ta ɗauke
gold ɗin ba idan ta haɗasa da wanda Dady zai saya mata yanzu ba ƙaramar kaddara zata tara
ba, gashi ta janyo mata asarar da batasan ranar maidata ba koda kuwa kullum zata samu ƙarin
gold don ta riga ta rasa wancan ɗin da ba ƙananan kuɗi ne dashi ba. Tana wannan tunanin taji
yai hugging É—inta duka yana cewa.
"Thank you so much Madam. Ya jikin Æ´ar taki?" Sai da Hajja Maimoon ta sake shigewa cikin
jikinsa sannan tace,
"Taji sauƙi." Har zai tambayi jikin Jauhar ɗin sai ya tuna ba lallai hakan yayi mata daɗi ba, dan
haka ya kama bakinsa yayi shiru ya shiga ƙoƙarin rage kayan jikinsa Hajja Maimoon na taimaka
masa.
Alhaji Sha'aban Sada na kammala shiryawa cikin kaya marasa nauyi da suka karɓi jikinsa sosai
suka nufo palour shida ita, duka yaran na kwance saman kujerun palourn suna kallo Jannat ce
kaɗai ke zaune riƙe da wayar Mommy tana buga game, tana ganin Daddyn nasu ta taso tayo
wajensa yasa hannu ya rungumeta yana kallonta cike da kulawa. Cike da sakalci take rungume
hannunsa tana kwantar da kanta.
"Dady sannu da dawowa." Suhana da Suhaila suka faÉ—a atare, cike da jin daÉ—in ganin su ya
amsa hankalinsa nakan Jannat É—in yana tambayarta ya jikin nata ita kuma tana sake shigewa
jikinsa cike da shagwaɓa take amsa masa da taji sauki. Da haka suka ƙarasa wajen dinning da
Jauhar ke sake gyarawa saboda basu jima da kammala lunch ba. Cikin girmamawa kan Jauhar
a ƙasa ta gaishesa tana ƙoƙarin barin wajen saboda mugun kallon da Mommy ke wurga mata,
sai taji Daddyn ya dakatar da ita yana tambayarta.
"Ya jikin naki?"
"Naji sauki Dady."
"ALLAH yaƙara sauƙi." Yafaɗa yana basar da zancen ba tare daya bi takan Mommy data juyo
tana kallonsa ba na jin tambayar da yai wa Jauhar. Ita fa sam bata son duk wani abu mai kama
da tausayi ko kuma kulawa ya dinga ta'allaƙa da Jauhar bare har ta sameshi acikin gidan, so
takeyi ko yaushe Jauhar ta kasance cikin kunci da baƙin ciki kamar yadda ta zamo silar shigarta
cikinsu a lokutan baya. Da wannan tunanin ta shiga zuba masa abinci yaci, yana kammalawa
yace ta shiga ta dakko mayafinta suje yana jiranta a waje.
"Dady zan je nima." Jannat tafaÉ—a har lokacin hankalinta na akan game É—in da take bugawa.
Hannun da Hajja Maimoon ta miƙawa Jannat ɗin ne yasa Jannat ta miƙe mata nata Hajja
Maimoon É—in tana cewa,
"Oya taso muje ki sauya kayan jikinki." Jannat tamiƙa mata hannun suka wuce Dady ya bisu da
kallo cike da so dan idan ka gansu tamkar Hajja Maimoon É—in ce ta haifeta, wannan na daga
cikin dalilan dake sa a kullum yake ƙara jin kaunar Hajja Maimoon tare da hauhawar matsayinta
a cikin zuciyarsa yanda ta É—auki Æ´aÆ´asa tamkar ita ta haifesu. __________
"Wai lafiya ka samu waje ka zauna kana faman cika ina yi maka magana ka ƙyaleni? Meke
faruwa ne Irfaan?" Hajiya ta faÉ—a tana tsaresa da idanuwa, jin yai shiru bai amsa mata ba yasa
takira Inna Deeje mai aikinta tace takawo masa ruwa, ba'a jima ba sai gata ta dawo É—auke da
ɗan ƙaramin tray ta ɗoro gorar ruwa mai sanyi da cup data wanko ta ajiye masa agabansa,
"ÆŠauki ruwa kasha." Hajiya ta faÉ—a tana ba Irfaan É—in umurni. Sai da yai kamar bai jita ba kafin
ya É—auki ruwan ya tsiyaya yasha, ya dire cup É—in lokaci É—aya tare da nauyayyen numfashin
dake nuni da zuciyarsa daskare take da ɓacin rai. A karo na biyu Hajiya ta sake jeho masa
tambayar da tayi masa a farko da take cike da son jin amsar ta, dan yanda tasan halayyar ɗan
nata da dabi'unsa ba ƙaramin abu bane ke jefasa a irin wannan yanayin damuwa da kuma
ɓacin ran ba.
"Hajiya wai meyasa sam babu É—igon tausayin yarinyar can a zuciyar Hajja Maimoon, me yasa
take wulakantata da ƙasƙantar da ita haka? bayan Allah ya ɗaukaka ɗan Adam ya kuma
darajasa? Shin ita ba mutum bace ko kuma ita ta zaɓawa kanta rayuwa a yadda take? Duk da
itace ta zo da ita gidan a ganina be daje ana treeting yarinyar nan haka ba." Nauyayyar ajiyar
zuciya Hajiya ta sauke dan bata É—auka damuwar É—an nata akan wannan matsalar bace da ita
kanta ta jima tana cimata tuwo a ƙwarya, kawai ba yadda zatayi ne tunda tare ta gansu da
yarinyar. Amma sam bata jin daÉ—in yadda ake kawo mata labarin irin wahalhalun da yarinyar ke
sha da tsangwamar da akeyi mata a gidan É—an nata. Kallonsa tayi tace,
"Bansan dalili ko hujjar da tasa Hajiya Maimuna take yin hakan ba bayan ita tazo da yarinyar
nan gidan, meke faruwa ne halan?" Nan fa Irfaan ya kwashe komai ya sanar da Hajiya har yana
ƙarawa da cewa.
"Hajiya nafahimci so takeyi kowa ya guji yarinyar nan ya cutar da ita kamar yadda takeyi, sai dai
ni bazan taɓa yin hakan ba saboda har cikin zuciyata nake jin tausayin yarinyar nan. Kuma
wallahil azhim Hajiya tayi duk abinda ta yi bazan fasa taimakon Jauhar ba da dukkanin karfina
da kuma dukiyata ba sai dai tayi min duk sharrin dataga zata iya ni kuma zan É—auka kuma zan
jure har lokacin da Allah zai kawowa Jauhar mafitar tafiya daga wannan kangin bautar da
takeyi. Ni wallahi Yaya ne ma har mamaki yake bani akan abubuwan da akewa yarinyar nan
agaban