Showing 27001 words to 30000 words out of 47407 words
Chapter 10 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
idanuwansa amma baya cewa komai. Bansan yaushe zuciyarsa takoma haka ba!"
Hajiya ta sauke numfashi, tabbas abun babu daɗi, gashi ita kam duk abinda zai taɓa mutuncin
Alhaji Sha'aban bata son shi, dalilin da yasa kullum gidan ta sai an sauke tukunyar abincin
sadaka da niyar Allah ubangiji ya ƙare mata shi ya kuma ci gaba da rufa masa asiri duniya da
lahira. Bata taɓa sanar da kowa dalilin yin girke-girken da take sawa ayi ba daga ita sai Allah.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faÉ—in.
"Allah ya kyauta, ita kuma Jauhar É—in Allah yai mata mafita ta alkairi, ni wannan abun duk laifin
iyayenta nake gani aciki, bazan hanaka taimakonta ba amma kariƙa yin taka tsantsan tunda
bata so, kuma ta fika kusanci da iyayan yarinyar." Jin Hajiya ta karfafa masa guiwa yasa yaji
nutsuwa ta fara saukar masa yace,
"To Hajiya amma fa indai ta sake yimin sharri wallahi ajiye girman Yaya zanyi nafaÉ—a mata ba
daɗi tunda zuciyarta ba imani da tausayi, yarinya ƙarama ki zauna kina azabtar da ita ko da me
hakan zai rageta..?" Duk suka yi shiru Hajiya ta kasa cewa komai. Haka Irfaan yai ta magana
Hajiya na kallonsa tana son gano wani abu tattare dashi akan yarinyar har ya gama faÉ—an ya
tashi ya fita.
__________
Kasuwar Rimi Alhaji Sha'aban Sada ya nufa yai parking a bakin wani katafaren store na
Muhammad gold accessories. Tare suka buÉ—e murfin motar suka fito yana gaba Hajja Maimoon
na biye dashi a baya riƙe da hannun Jannat, juyowa yai bayan sun shiga ciki yace ta duba ta
zaɓi duk sarkar data yi mata ta dai-dai adadin kuɗin waccan da aka ɗauke mata. Nan take Hajja
Maimoon ta saki murmushi ta shiga duba sarkokin gwalagwalan dake wajen. Sai da ta kusan
zagaye ko'ina can ta hango wacce tayi dai-dai da zabinta sannan ta nuna tace ita take so Alhaji
Sha'aban yace a É—akko mata ba tare daya damu da sanin ko nawa take ba har sai da aka
É—akko. Sosai Hajja Maimoon ta girgiza da jin adadin kudin sarkar dan sun kusa ninka na sarkar
ta da aka sace sau uku, amma ga mamakinta ko tsayawa tayawa baiyi ba ya fitar da kuÉ—in duka
ya biya aka miƙo masa sarkar tare da reciept ɗin ya miƙa mata. Tsabar farin ciki ruɗewa Hajja
Maimoon tayi ta rungumeshi a wajen tana zuba masa godiya dan ko a mafarki bata sa ran zata
mallaki sarka mai tsada irinta ba, hannun Jannat ta kama suka fice shi kuma ya tsaya wajen ya
duba wata sarkar gold É—in da zata dace da mahaifiyarsa ya siya ya jefa cikin aljihunsa.
A can waje kuwa Hajja Maimoon ƙawarta takira tana sanar mata haɗe da shaida mata
sarkartata da aka dauke har tana faÉ—a mata tsadar wacce Alhaji Sha'aban ya siya mata É—in
yanzu. Kasancewar tana cikin farin ciki har sanar da ita irin ribar da taci da wannan sabuwar.
Sosai aminiyarta ta tayata murna tare da sake É—ora ta akan hanyar da zata ribatu da kuÉ—in
Alhaji Sha'aban Sada É—in tunda baya iya bayarwa sai da dalili. Tana hango shi yafito tayi saurin
yin sallama da ita tana cewa sai takirata zasu ƙarasa magana idan takoma gida. Daga nan
kuma wajen shakatawa suka nufa suka É—an zazzagayo dan Alhaji Sha'aban mutum ne mai son
wayewa da kuma burge iyali. Bayan sun kammala suka nufi hanyar komawa gida, nan yake
yimata zancen a ina take son yin business É—inta? A online ko kuma a gida? Murmushi ta saki
haÉ—e da cewa,
"Gaskiya bana son business a gida, online kuma ai kaga kamar kafa ne da zan tallata kayan, in
son samu ne kawai shago zan kama a zuba kayan aciki ina sayarwa ko ya ka gani?" Shiru yai
dan har ga Allah duk abinda zai janyo tawayar samun kulawarta gareshi baya so, kuma gashi
yana son ya kyautata mata kamar yadda take kyautata masa shi da yaransa.
"Ya Habiby ya naji kayi shiru? I think is better da azo ana cika maka gida, kare da doki wasu ma
su cuce mu ta hanyar zuwa gidan da zasu yi." Juyowa yai ya kalleta kafin yaci gaba da tukin
yake cewa.
"Wannan ni ba matsalata bace indai zanci gaba da samun kulawarki, kin sani bana son kinayin
nisa dani inba dole ba shiyasa zancen shagon nan bai kwanta mani ba."
"Oh God! Ya Habiby hakan fa bazai canza komai ba a kulawar da nake baka, I promise you
that." Tayi maganar cikin kashe murya tana wani mammatsa hannunsa cike da salon son shawo
kansa. Sake juyowa yai yana kallonta yace,
"Are you sure?." Bata iya amsa masa ba saboda ta shagaltu wajen yimasa wani irin fitinannen
kallo daya kusa dakatar da bugawar zuciyarsa sai dai ta É—aga masa kai alamun
"Eh".
Take Alhaji Sha'aban Sada yaji jikinsa ya mutu ya samu daƙyar suka ƙaraso gida suka nufi
sashensa kai tsaye. Jannat kuma ta kwashi kayan kwalam ɗin daya siya musu ita da ƴan
uwanta ta wuce musu dashi.
A takaice duk da yadda lokacin magriba ya soma karatowa sai da Hajja Maimoon ta jefasa
duniyar da suka farantawa junansu haÉ—e da samawa kansu natsuwa. Bayan yafito wanka yace
tayi magana da ƙawarta da zata turo mata kayan ta turo mata account zai tura mata adadin
kuÉ—in da zata zabi duk abinda take so, ya kuma ce akwai shaguna acan farkon titi kafin a shigo
unguwarsu da ake talla zai kama mata guda biyu sai a haÉ—e a sake gyara mata su kafin kayan
su iso. Hajja Maimoon taji daÉ—i sai taji darajarta ta sake girmama, addu'a sosai tayita masa har
da kwallarta ta farin cikin ganin mafarkanta sun fara tabbata, sannan atake takira ƙawar tata
tace ta turo mata account É—inta, ba'a jima ba ta turo mata taba Alhaji Sha'aban É—in shi kuma
atake awajen ya tura mata kuɗin yace tafara gwadawa dasu, idan yaga kasuwar ta karɓeta to
zai ƙara mata wasu sannan ya mike ya nufi masallaci yana cemata daga can zai biya gidan
Hajiya ya gaisheta. Har mota ta rakosa tana yi masa adawo lafiya sannan takoma ciki zuciyarta
cike fal da farin ciki tana ganin auran ta da Alhaji Sha'aban nasararta ne kuma matakin
daukakarta ne.
__________
Tunda ya doso ƙofar gidan annurin dake kan fuskarsa ya soma gushewa har ya ƙaraso wajen
ganin ƙanwar tasa Husnah tsaye da wani agefen gidansu. Tsaye yai yana ƙarewa yaron kallo
tun daga sama har ƙasa, sanye yake da gajeren wando iya guiwa, sai riga armless mara
hannuwa wuyansa sanye da wata kafceciyar sarƙa ƴar Chaina. idanuwansa ne suka sauka
akan kunnen Guy É—in daya sanye da É—an kunne tamkar mace sai kansa daya sha wani irin aski
na Bobby, acikin mintuna biyu kacal yaƙare masa kallon da ya gama tabbatar masa da cewa
gaba ɗaya yaron ba musulmi bane, ransa ne ya sake ɓaci lokacin da idanuwansa suka sauka
akan takalman dake ƙafafuwansa wasu irin kafta-kafta farare irin canvas ɗin nan na gayu dake ji
da kansu. Rai aɓace Zain yai parking mashin ɗinsa a ƙofar gida ya sauko ya nufo wajen da
suke tsaye sun shagalta da aikawa juna wani irin kallon soyayya. Wata uwar tsawa ya dakawa
Husnah da tasa tayi wata irin zabura yace ta wuce cikin gida. Baki sake Zain yake bin yaron da
kallo lokacin daya miƙo masa hannu cikin girmamawa yana cewa,
"Assalamu alaikum, Yaya barka da dawowa." Me hakan ke nufi? Kenan wannan yaron yana
nufin shi musulmi ne yake cikin irin wannan shigar da ba ta da banbanci data ƙabilu? Daƙyar ya
iya buÉ—e baki ya amsa masa sallamar da yai masa yana cewa,
"Ko menene tsakanika da ƙanwata ka rabu da ita saboda karatu zatayi, a mutunce nake faɗa
maka hakan kafin akai ga ɓacin rai tsakanina dakai idan nakuma ganinka a ƙofar gidan nan,
babu kai babu ita kana jina ko?" Zain yaƙare maganar haɗe da kama kunnensa ɗaya alamun
jan kunne sannan ya juya rai aɓace ya wuce cikin gidansu. Saurayin kuma mai suna Iliya ya
bishi da kallo cike da mamaki kafin yaja tsaki yace,
"Wannan kwafsa min zai dinga yi kenan? Ahhh lallai za'a kwashi uwar watsi indai akan Huscy
ne. Kai..! Lallai ma gayen nan, wato duk wannan gayun nawa dana kwaso dan na burge
yarinyar nan sai da ya yimun bakin cikin yin hira da ita. Mtssss! wallahi ni da Huscybaby mutu
karaba dan bakin ciki kawai. Zaka gane waye ILLiyasmarter na rantse da Allah kuwa." Daga
haka yaja kafafuwansa da daƙyar yake ɗaga su yana jefawa irin tafiyar ƴan iskan nan saboda
nauyin takalmin. ILIYA É—an nan cikin garin su ne acan kauyen dake gabansu, ya jima yana son
Husnah tun tana jss 3 amma yadda yake ganin takunta irin na yaran masu kuÉ—i Æ´an gayu yasa
ya É—auki alwashin zama gaye kafin ya tunkareta dan yasan hakan kaÉ—ai zai sa ta saurararsa.
Yayi nasara kuwa domin tun a ganin farko da Husnah taji yes zai yi daidai da wanda zata iya
tsayawa.
Zain kuwa yana shiga gida Husnah na tsaye a ƙofar ɗaki ta cukuikuye hijabin ta na makarantar
boko data dawo dan ta maraice takeyi tana faman haÉ—e rai, bai tsaya wata-wata ba yana shiga
yayo kanta. Husnah kuwa da gudu ta ɓuya bayan mahaifiyarta dake kukkulle kayan yaji.
"Kai..kai wai lafiya Zain? Meye haka daga dawowarka zaka rufar min yarinya? Me kika yimasa
ne?" Taƙare zancen tana juyowa wajen Husnah dake faman tura baki,
"Ba dake nake ba ko sai nabarshi yayi miki shegen duka?" Cike da son a kareta tace,
"Mama ni banyi mashi komai ba.." Kanta da ya yo ne yasa ta kasa karasa maganar, Mama tayi
saurin tareshi. Cikin ɓacin rai yace,
"Mama da wani É—an iskan saurayi na ganta fa a waje sunq tsaye kana ganinsa kaga Christian."
Cike da jin haushi Husnah ta É—ago kai tana cewa.
"Ya Zain bafa Christian bane, sunansa Iliya kuma so na yakeyi." Da sauri Mama tace,
"To kaji amma zaka zo ka saukewa yarinya ɓacin rai, ai sai ka mayar da wukar tunda kaji
masoyinta ne, ko kuma kana nufin bata kai munzalin tsayawa da saurayi ba?" Baki Zain ya saki
jin abinda mahaifiyar tasa ke cewa kafin yace,
"Mama Husnah guda nawa ce da zata fara kule-kulen samar? kinga yaron kuwa? Na rantse
kada kibari na sake ganinki dashi idan ba haka ba na lahira sai ya fiki jin daÉ—i." Cikin sauri
Mama tace dashi.
"Toh sannu ubanta, nace sannu isasshe gawurtacce, idan bata kula samari ba taya kake so ta
zabo mijin aurenta? Ko kai zata aura? Nifa bana son haka tunda ba kamata kayi tana yin dabi'u
marasa kyau ba ka ƙyaleta ta kula duk wanda yazo wajenta, ta haka zata tantance mijin aure
tunda ba zama zatayi muna kallonta ba..." Wani irin haushi ya sake kama Zain yana kallan
Mama yama rasa ta yadda zai suffanta mata yadda Iliyan yake. Rai a ɓace ya nufi ɗakinsa yana
jin zuciyarsa na masa zafi, wai ace wannan guy ɗin ne zai nemi ƙanwarsa saboda ance ciwon
makanta ya kama su. Idan har yana numfashi bazai bar ILIYA tare da jininsa ba.....
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435 ko
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewabook@billysfari
Page 11..
Da yake yau tana cikin farin ciki gabaki É—aya ta manta da wata Jauhar a cikin gidan, su Suhaila
ta tarar a parlour suna ta cin kayan kwalam É—in da Jannat tazo musu dashi wanda ko tunanin
ajiyewa Jauhar basu yi ba, dama ita tsakanin ta da irin abubuwan sai idan sun rage taje gyara
gurin idan taji abu ya bata sha'awa koya burgeta sai ta É—auka taci idan na ci ne, idan kuma na
sha ne shima ta tsotse ta maida mugun yawu. Dukkansu kallonta sukeyi ganin farin ciki yaki
gushewa akan fuskarta yasa Suhaila gyara zama tana murmushi take cewa.
"Mommy sai farin ciki kike yi ko ƙanwa za'a yiwa Baby Jay?" Duk da kasancewar kalmar tayi
matukar nauyi da ya kamata ace Hajja Maimoon ta yiwa Suhaila magana akai, sai kawai Hajja
Maimoon ɗin tayi dariya kasancewar farin cikin da take ciki bata kawo wani abu na ɓacin rai a
lokacin bare har ta tsawatar tana cewa.
"No... No.. No Suhaila! Ni ai kun isheni hakan nan ba sai an sake kawo wani babyn ba. Ku
tayani murna zan fara business kamar yadda kuka san cewa dama tun da nazo ina yinsa.
Kunsan Æ´ar matsala na samu wacce tasa dole na ajiye komai. Kuma wannan karon ba a gida
kawai zanyi ba Daddyn ku zai kama min shago a can bakin titi." Gabaki É—ayansu suka tayata
murna wanda hakan ya sake farantawa Hajja Maimoon zuciya tana sake jin yaran a cikin
zuciyarta.
_____
Tunda ya nufi layin gidan mutane suke É—aga masa hannu yana yi musu horn alamar amsawa
fuskarsa kunshe da murmushi. Yana isa wajan gate ya yi parking bai shiga da motar ba
kasancewar ba daÉ—ewa zai yi a ciki ba. Har Alhaji Sha'aban ya shiga parlorn Hajiyarsu mutanan
dake shawagi a gidan basu dena gaishe shi ba. Zaune ya tarar dasu tana inda take zama tayi
sallah yayin da Irfaan ke kwance cikin 3seater ya É—ora laptop a saman cikin sa yana aiki a ciki.
Maryam ƙanwarsu wacce ta kasance auta a wajan Hajiya tana zaune wajan center table ta ɗora
handouts da alama assignment takeyi, shigowarsa yasa har Hajiya dake dama fura cikin ƙoƙo
sai da ta dawo da hankalinta wajansa, sosai take jinsa a ranta haka kuma bata haÉ—ashi da
kowa a kaf cikin yaranta, kauna take masa wacce ita kanta idan aka ce ta faÉ—i irinta ba zata iya
bayyanawa ba saboda mutum ne shi da yake bata matsayinta na uwa a gareshi fiye da tunani.
"Hajiya sannu da aiki." Ta amsa masa,
"Yauwa sannu da shigowa. Maimakon kayi kwanciyarka ka huta shine sai da ka taso kazo har
nan?" Murmushi yayi yace,
"Hajiya ai nazo naga lafiyarki, idan na kwanta banzo ba tunani zantayi ina jin babu daÉ—i."
"Yaya sannu da zuwa." Maryam ta faÉ—a tana karkaÉ—a biron hannunta.
"Yauwa Auta kina ganin Hajiya na aiki baki tayata ba ko?" Cikin sauri Maryam tace.
"Yaya wallahi cewa tayi in bar mata zatayi wai ban iya dama furar yadda takeso ba." Ta faÉ—a
tana maida idanunta kan takardun ta.
"Eh naji, amma da ta faÉ—i hakan maimakon kizo kiga yadda takeso É—in ki koya shine kika barta
tana yi." Irfaan dake kwance ne ya tashi zaune yana cewa.
"Yaya barka da zuwa." Yana magana yana haÉ—e rai tamkar wanda basa zaman lafiya.
"Yauwa Irfaan." Alhaji Sha'aban ya furta yana kallon yanayinsa, duk da cewar yawan tambaya
akan abinda ba'a nemi ya sani ba baya daga cikin al'amuransa. Sai dai a yanayin ɗaya ga ƙanin
nasa yasa shi son jin ko meye damuwarsa.
"Naga kamar kana cikin ɓacin rai, lafiya dai ko?" Irfaan ya sake tsuke fuska yana janyo wayarsa
dake gefensa yace.
"Ba komai." Hajiya najin su tayi murmushi jin abinda Irfaan yace. Dama zaiyi wahala ya iya
gayawa Yayan nasu abinda yake damunsa domin suna masa kallon uba ne dan shine tsaye
akan su. Hajiya tasan duk masifar da Irfaan yayi akan matsalar Jauhar da yake cewa harda
laifin Alhaji Sha'aban tasan ko da wasa ba zai iya rufe ido ya yi a gabansa ba. Kallon Maryam
Hajiya tayi tace.
"Zoki É—akko kofi na zubawa Yayanku fura da nono yasha." Da sauri Alhaji Sha'aban yace.
"A'a Hajiya kisha abarki." Maryam jin yace abarshi yasa ta koma ta zauna, Hajiya ta kalleta.
"Ke kuma daga yace insha abuna shine kika fasa É—akkowa? Yanzu fa naji ya yi miki faÉ—a akan
kulawa da abubuwa. Tashi ki É—akko ai ba mai yawa zan zuba maka ba."
"Nima fa nace zan sha." Cewar Irfaan jin ba'a ce a taho da nashi kofin ba.
"Kai da kace sai mai ayaba da kwakwa a ciki? Meye kuma na canza shawara?" Alhaji Sha'aban
yace,
"Kishi ne da alama." Gabaki ɗaya sukayi dariya. Kofuna uku Maryam ta dire tana durƙushewa a
gaban Hajiya tare da cewa.
"Kawo na zuba mana." Da sauri Alhaji Sha'aban ya nufi wajan, karɓar ƙoƙon ya yi tare da cewa,
"Kawo nasan wayo kika shirya yiwa Hajiya ta." Duk suka sake yin dariya ya zubawa kowa a
cikin kofi shima ya zuba Æ´ar kaÉ—an dan ma kartaga bai shaba taji babu daÉ—i shi yasa ya zuba.
Sai da ya fara miƙa mata wacce zata sha sannan ya miƙe ya koma kan kujera. Irfaan ya karɓi
tashi a hannun Maryam ya nufi wajan fridge, ƙanƙara da madarar freshyo ya zuba a ciki sannan
ya koma inda ya taso ya zauna.
"Wai meke faruwa tsakanin