Showing 42001 words to 45000 words out of 47407 words

Chapter 15 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

3176



"Toh bari naje nayi sallar sai na dawo".

"Ya zakiyi idan kin je?" Suhana tafaÉ—a tana maida hankalinta ga fere Irish É—in da takeyi amma
kunnuwanta na wajen Jauhar É—in tana sauraren amsar da zata bata.

"Zan sa hijabi na sai na tsaya na duka na zauna nasa goshina akasa sai na sallame". Dariya ce
ta kusan kwacewa Suhana jin bayanin sallar Jauhar, amma sanin da tayi ba zancen da za'a
É—auka da wasa bane yasa ta juyo tana É—an haÉ—e rai tace.

"Jauhar ba haka ake yin sallah ba, kije ki samu ruwa mai kyau ki fara zuwa kiyi tsarki sannan
sai kiyi alwala, kin iya alwala ai ko?" Jauhar ta girgiza mata kai alamun a'a, iska Suhana ta

furzar ta baki kafin taci gaba da cewa.

"Akwai aiki kenan gaban mu." Sannan ta juya ta tsame irish É—in daga cikin ruwa ta ja hannun
Jauhar suka nufi toilet É—in É—akinta, ganin yanayin toilet din yasa ta dawo baya tana cewa.

"Muje ta can baya." Ta nufi bayan kitchen da yake akwai fanfo a wajen, cikin tsanake ta fara
nunawa Jauhar yadda ake alwala tana yimata bayani a saukake yadda kwakwalwar ta zata iya
dauka. Bayan ta kammala tace tazo tayi itama ba laifi tayi sai dai akwai Æ´an gyare-gyaren da
tayi mata. Daga nan ta tambayeta sau nawa ake dungurawa dan tasan dungure taga sunayi.
Nan Suhana ta gaya mata sallar asuba raka'a biyu ce saboda taga anayi sai dai bata tabbatar
da kowacce adadi nawa ake yi ba.

Sai da tayi mata bayani a gurguje saboda har karfe shida tayi sannan ta koma kitchen ta barta
tayi sallar. Ba'a jima ba Jauhar ta dawo har ta kammala tare da gaida Suhana É—in ta amsa mata
da lafiya ƙalau sannan ta kama mata aikin sukaci gaba tana yi tana tambayarta wasu abubuwan
da suka shafi ibadarta da kuma addini. A nan Suhana ta tabbatar da bayan rayuwar talauci da
Jauhar ke ciki har da jahilci na damunta sosai, dan bata san komai ba a ɓangaren addini balle
kuma boko.

Ƙarfe bakwai na bugawa sun kammala komai. Lokacin Hajja Maimoon ta sauko tana waya cikin
wata ƙawatacciyar doguwar riga ta yane kanta da mayafinta fuskarta ɗauke da wani ƙaton
parado daya rufe kusan rabin fuskarta, kasancewarta farar mace kyakkyawa ajin farko yasa
tafito tamkar wata balarabiya dan tayi matuƙar kyau sosai. Suhaila da Jannat ne bayanta cikin
shirin su na zuwa school Jannat na riƙe da school bag ɗinta. Yadda fuskarta take a ɗaure ba
wasa yasa tayi masu kwarjinin da bayan gaisuwa babu wacce ta iya cewa komai har sai da ta
kalli Jannat tace.

"Call your Dady kifaÉ—a masa breakfast is ready?" Dama haka takeyi idan sun samu
misunderstanding tsakaninsu komai sai dai ta aika yaran, Alhaji Sha'aban dake zaune yana aiki
da system É—insa yaji anyi masa knocking, tambayawa yai Jannat tace itace tare da faÉ—in sakon
Mommyn tasu. Wani takaici ya taso mashi dan ba tun yau ba yasha faÉ—a mata tadena saka
mashi yaransa cikin faÉ—ansu idan suna yi.

"Kice ina kiranta." Shine amsar daya bawa Jannat taje ta sanar da ita cewa Daddy na kiranta.
Ba dan ranta yaso ba ta mike ta nufi É—akin. Da kallo ya bita ganinta cikin shiri da irin kwalliyar
data chaɓa. Danne ɓacin ran dake cikin zuciyarsa yayi kafin yace.

"Wannan ya zama last warning tsakanina dake da zaki kuma turo yarana kirana, idan har kina
jin faduwa ce wajenki kizo kiyi min magana saboda mun samu matsala to ko meye kibarsa bana
buƙata". Hajja Maimoon bata ce komai ba har ya dasa aya. Ganin sosai ransa ya ɓaci yasa ta
É—an sassauta fushinta haÉ—e da cewa.
"Am sorry." A takaice tana dauke kai gefe, ba tare daya kalleta ba ya maida hankalinsa ga

system É—in dake gabansa yana cewa.

"Ki hada mani ruwan wanka." Da sauri ta ce,

"Time is going Ya Habiby, bana so yarana suyi late kuma customer na jirana a shago zan basu
kaya asa a mota delivery ne to Abuja, gashi to 8 kuma tun 6:30 suke jirana, zan turo Jauhar ta
haɗa maka duk abinda kake buƙata ta kuma gyara maka ɗakin, breakfast ɗinka kuma yana
dining." Ta kare zancen haÉ—e da juyawa ta fice daga É—akin. Da kallo ya bita dan duk a zatonsa
wasa takeyi, bai sha mamaki ba sai da yaji sallamar Jauhar a bakin kofar palournsa.

"What?" Yafaɗa da ɗan karfi yana miƙewa tare da zuro jalabiyarsa ya nufi palourn.

"Alhaji ina kwana?" Jauhar tafaÉ—a tana É—an russunawa, idanuwansa akanta yana kallon yadda
take ɗari-ɗari dashi, da alama bisa dole tazo ɗakin don bata taɓa takawa ko gefen da part ɗin
nasa yake ba. Sake binta ya yi da kallo ya ganta da kayan nan na gado, eh na gado mana dan
ko ɓata tayi sai mutane su gano ta saboda tsabar tafi sanya su. Kamar ya yi shiru sai kuma
yace.

"Me yasa kika cire doguwar rigar da Irfaan ya siya miki?" Kirjin Jauhar ya buga, zuciyarta ta
karye saboda ita kanta bata son ana tuna mata kayan saboda tana ganin samu sannan taga
rashi duk a guri guda.

"Hajiya ta kwace su." Dafe goshi ya yi yana jin takaici, besan me Maimoon take ji ba idan tana
ganin Jauhar a haka. Cikin danne fushinsa da yake sake nuna ɓacin ransa akan Maimoon ɗin
yake yace,

"Ya akayi?" Ya tambayeta yana tsare ta da kyawawan idanunsa da suka koma kalar ɓacin rai,

"Hajiya ce tace nazo na gyara maka sashenka kuma na haÉ—a maka ruwan wan.." Tun kafin
taƙarasa ya dakatar da ita yana runtse idanuwa, abinda ya gujewa kenan shi yasa bai amince
da buÉ—ewa Hajja Maimoon shago ba amma ta nuna masa ai ba wata matsala, gashi tun ba'a je
ko'ina ba komai na shirin sauyawa tsakaninsu.
"Kije kawai Jauhar, ina ita Hajiyar?"

"Sun fita."

"OKay Kije nagode." Alhaji Sha'aban yafaÉ—a tare da juyawa ya koma ciki. Zauniya yayi saman
gadonsa ya dafe kansa cike da mamakin Hajja Maimoon dako a mafarki aka ce masa zata
aikata hakan bazai yarda ba...
___________

Kimanin awanni biyu cif suka É—aukesa kafin ya kammala duk wani shiri nasa har lokacin

mamakin Hajja Maimoon na cike a zuciyarsa. Abinci ma ko da ya fito ya samu Jauhar tsaye
gefen dining table tamkar wata soja tana jiran ƙarasowarsa kamar yadda Hajja Maimoon ɗin ta
gargaÉ—eta, kasa zaunawa ya yi yaci, kallo É—aya yaiwa gefen da Jauhar É—in take ya É—auke kai ya
miƙi hanyar ficewa daga cikin palourn, cike da tashin hankali Jauhar da taga haka ta rugo ƙiris
kaɗan ta bangajesa ta sha gabansa tana haɗe hannayenta tamkar mai riƙon gafara take cewa.

"Alhaji ga abincin karin kumallonka can Hajiya ta haɗa maka duk abinda zaka buƙata, ta kuma
umurce ni dana tabbatar kaci kafin kafita bata son ka zauna da yunwa, dan Allah karufa mani
asiri kazo kaci kar na shiga uku idan tagano bakaci ba." Jauhar taƙare maganar tana duƙawa
agabansa cikin tsantsan tashin hankali haÉ—e da neman duka alfarmarsa.
Kallon yadda gaba É—aya tafita hayyacinta yai yana sake mamakin rainin hankali irin na Hajja
Maimoon, shi zata bada wannan umurnin akansa sai kace wani ƙaramin yaro? Ya tambayi
kansa zuciyarsa na sake kawowa a wuya duk da fushin zuciya ba nasa bane amma yau Hajja
Maimoon ta kaishi bango. Ƙwallar da Alhaji Sha'aban Sada ya hango na shirin sauko mata yasa
ya É—an ji zuciyarsa ta karye, dan tsaf Hajja Maimoon zata iya bin diddigi ta gano yaci abincin ko
bai ci ba saboda ta kama Jauhar É—in da laifin da zata iya mugun hukuntata da É—aya daga cikin
nau'ukan azabar da take bata.

"Mike Jauhar bana so kina ɗaga hankalinki irin haka sai na riƙa jin kamar nima ina zaluntarki,
nayi latti sosai zuwa wajen aiki bazan iya tsayawa cin abincin nan ba, amma ke ki É—auka ki
canye kin ji ko?"

Yana gama maganar ya raɓa ta gefenta ya fice ba tare daya sake bata damar yin magana ba,
tamkar Jauhar tayi kuka haka ta ji na rashin tsayawar Alhaji yaci abincin, ko ba komai a karan
kanta zata so yaci abincin kafin yafita duba da irin taimakon da yayi mata tsakanin jiya da yau.

_"Banda isasshen lokacin ɓatawa na tsaya yimaki bayanin abinda zakiyi, ki tabbatar kin
gyarawa Alhaji É—akinsa idan yafita haka kuma ga breakfast É—insa na haÉ—a masa abinda yake
so, bana so kibari yafita da yunwa dan zai iya wucewa idan yafito ya tarar har munci namu mun
tafi, ki kasance kusa yadda duk abinda zai buƙata ba sai yayi da kansa ba, hakan zai sa na
duba kaso É—aya daga cikin laifukan ki naga ko zan iya sassauta maki hukuncinsa, ki kula
nafaÉ—a maki kada yafita da yunwa!"_

Kalaman Hajja Maimoon kenan suka dawo mata a kunnuwa lokacin da take bata umurni cike da
gargaɗi da kuma jan kunne kafin ta fita. Hakan yasa tayi saurin miƙewa ta nufi kitchen ta janyo
wani lunch box ta nufi wajen dining ta zuge zip É—inta ta kwashe kaf kayan da Hajja Maimoon É—in
ta shirya masa da tasan yana so ta saka aciki ta zuge sannan ta nufi hanyar fita palourn har
tana haÉ—awa da dan gudu ta samu ta isa kafin ya wuce. Cikin Sa'a ta samesa tsaye yana
magana da Baba Bello ta ja can gefe ta tsaya tana jiran su kammala. Taku daya Alhaji Sha'aban
Sada yai bayan gama maganarsa da Baba Bello Jauhar tabi bayansa har ya shiga mota ya
tayar haÉ—e da É—an juyowa ganinta a gefensa.

"Jauhar akwai wani abune?" Ya tambaya fuskarsa ba walwala yana kallonta. Sai data dukar da
kanta ƙasa sannan ta miƙa masa lunch box ɗin tana cewa.

"Kayi hakuri Alhaji ba wai naƙi bin umurnin ka bane, ka tafi da abincin sai kaci acan dan Allah."
Yafi second biyar yana kallonta kafin yace.

"Shikenan saka mani a seat É—in baya nagode." Cike da jin daÉ—i Jauhar ta É—ago fuska cikin farin
ciki jin ya amince zai tafi da abincin tana jin ta samu natsuwa ta kuma kubuta daga tuhumar
Hajja Maimoon da kuma mummunan hukuncinta da za ta yimata idan tasan da rashin karyawar
Alhaji kafin yafita. Wanda hakan yasa shima Alhaji Sha'aban ɗin ya amince ya karɓi abincin dan
ya fahimci shi kaÉ—ai zai sa hankalin Jauhar ya kwanta. Yana kallon yadda ta sauke ajiyar zuciya
kafin ta buÉ—e murfin motar ta baya ta sanya abincin ta rufe tana cewa.

"Alhaji Allah ya tsare." Sannan ya tada motar ya fice dan tuni Baba Bello ya samu ya buÉ—e
masa gate É—in. Cike da farin ciki kamar yadda Jauhar ta saba kwana biyu taje ta taya Baba
Bello rufe gate É—in suka rufe tana cewa.

"Baba Bello sannu bari naje na kawo maka abincin ka, ina ga har da rashin cin abinci sosai
yasa gate ɗin nan ke nuna maka fin ƙarfi." Taƙare zancen tana dariya amma sai taga jikin Baba
Bello É—in a sanyaye yaje ya nemi gu ya zauna ba tare daya kulata ba. Hakan yasa taji jikinta yai
sanyi, taƙarasa kusa dashi walwalar fuskarta na gushewa tace.
"Baba Bello lafiya?" Ta jefo masa tambayar cike da kulawa kasancewar yana É—aya daga cikin
mutanen dake saurin gano damuwarta kuma su bata magana, sai daya É—auke hawayen da
suka zubo masa sannan yace.

"Alhaji ne ya sallameni daga aikin nan Jauhar." Dariya tayi tana cewa,

"To meye na damuwa Baba Bello? Kana bukatar kaje ka zauna ka hutu yanzu bawai kaci gaba
da wannan aikin karfin ba da yakusa gagararka. Ranar fa naji Uncle Irfaan yace tun waccan
Hajiyar kake gidannan, sama da shekaru kenan ai wallahi kaje ka hutu kawai."

"Bazaki gane ba Jauhar, ba sallamar ce damuwata ba dan yanzu haka yace zai bani isasshin
kuÉ—i naja jari naje nayi duk sana'ar da nake so, ina jin damuwa ne rabuwar da zanyi da mutanen
kirki na gidannan, wallahi koda babu albashi zan iya ci gaba da yiwa Alhaji gadi saboda
mutumin kirki ne da yasan hakkin ɗan Adam kuma yake ƙoƙarin ganin ya kyautata masa a koda
yaushe. Ina da É—a É—aya tilo da zai iya zuwa ya maye gurbina acikin gidannan saboda muci gaba
da samun rufin asiri, amma tsoro nake ji na kawosa yazo ya tabkawa Alhaji shirme shi da
iyalinsa, saboda rashin jinsa." Jauhar dake jin ina ma ace itace zata bar gidan nan yau! Da ƙilan
har kukan farin ciki sai tayi. Ta É—ago kai ta kalli Baba Bello wanda har ta soma jin kewarsa tun
yanzu tace.

"In dai yana da ƙarfin yin aikin Baba Bello kayi hakuri ka sanar da alhajin sai ka kawosa kada

suje su nemi wani a waje." Ta faÉ—a jiki a sanyaye,

"Ai nafaɗa masa Jauhar kuma ya amince, damuwata yanzu kar shi yaron yaƙi amincewa
saboda É—an yau ka haifesa baka haifi halinsa ba, É—an zaman banzar nan da karyace-karyacen
da yake faman yi duk zai daina indai har ya amince." Cikin sanyin jiki tace.

"Ka samu ka lallaɓashi Baba sai kaga ya amince."

"Shikenan Jauhar Allah yai miki mafita kema, an jima kafin mutanen gidan su dawo zan je na zo
dashi Allah yasa ya amince."

"Amin Baba, Bari naje nakawo maka abincinka." Ta miƙe jikinta duk a sanyaye taje ta kawo
masa abincin dan tabbas zatayi kewar Baba Bello itama ba kaÉ—an ba.....


   *ƳAN TAGWAYE BIYAR*

*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce

*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu

*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch

*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.

*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso

*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000

*BANK ACCOUNT*

8098456130
Opay digital services
Shaidar biya 08098456130

*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.



#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce
#Ƴan Tagwaye
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*PAID BOOK*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

NA

*BILLY S FARI*💎
Da
*HAJJA CE*👈

Page 16..

_Bayan kwana biyu_

Abubuwa da dama suka faru  musamman tsakanin Alhaji Sha'aban Sada da Hajja Maimoon
data ɗauki ragamar komai na gidanta ta damƙa a hannun Jauhar, ita kuma ta maida gabaɗaya
hankalinta ga business É—inta da ahalin yanzu shagon nata na daya daga cikin shaguna lamba
É—aya da ake ji dasu kuma suke tashe a garin Saboda ingancin kayanta da kuma kyansu,
*SUJASU COLLECTION* duk inda kaje shi zaka ji ana faÉ—a wajen kawo kayan da suka dace
daidai da zamani da kuma manya-manyan masu kuÉ—i dake ji da kansu, wanda yanzu haka
direct Hajja Maimoon take odar kayanta daga kasashe daban-daban ba tare data karɓa wajen
kowa ba ko kuma tayi haÉ—in guiwa, gashin kanta take ci da kanta saboda irin cinakin da take
samu a kowace rana. Sai hakan yasa ba tada wani lokacin kanta balle kuma na mijinta dan ko
yaushe cikin waya da lissafi take, su kansu yaran saboda rashin zamanta gida ya janyo indai ba
school tofa suna can tare da ita shago, sai abun ya fara damun Alhaji Sha'aban dan haka zai
dawo gida ba kowa sai Jauhar, itace zata yimasa duk wani abu da yake buƙata dan hatta ruwan

wanka ita take haÉ—a masa yanzun koda Hajja Maimoon É—in na gida, gyaran É—akinsa da wanke
undies É—insa, zuba mashi abinci yaci da gyaran kayansa duk ya koma kanta, wani lokacin har
tausayi take bashi amma saboda yana bukatar ayi masa duka wuÉ—annan abubuwan yake
hankurewa yabarta tayi tunda wacce yakamata tayi É—in batayi ba kuma hakan bai dameta ba.
A ɓangare ɗaya kuma rashin zaman gidan Hajja Maimoon ɗin ya yiwa Irfaan daɗi sosai, sai
yake samun isasshen lokacin da yake zaunawa da Jauhar ya karantar da ita addininta dai-dai
gwargwado tare da faɗa mata yadda zata riƙa kulawa da tsabtar jikinta dan sai da ita za'a karbi
ibadunta, ganin haka yasa Alhaji Sha'aban ya yi magana da Irfaan akan  sanya Jauhar islamiya
cikin awannin da Hajja Maimoon É—in bata nan. Hakan yai matukar yiwa Irfaan daÉ—i yaje ya
sanarwar da Hajiya shawarar da suka yanke shi da Æ´aÆ´an nasa, shiru tayi kamar tana nazarin
wani abu kafin tayi masu addu'a haÉ—e da sanya masu albarka tana mai alfahari dasu ko bayan
ranta.

Haka Irfaan ya sake zuwa ya ɗebowa Jauhar wasu kayan sai dai ba masu tsada ba da zata riƙa
sauyawa ba tare daya damu da wuɗan can daya siya mata ba Hajja Maimoon ta karɓe, ranar
data fara saka É—aya daga cikin kayan baki Irfaan ya saki yana kallonta, Jauhar kyakkyawa ce
sosai irin Black beauty sai dai bakar wahala da rashin sutura mai kyau yasa ba'a fahimtar
hakan. Wani irin sanyi Irfaan yaji a ransa na ganinta haka musamman farincikin dake dauke
akan fuskarta sai murmushi takeyi na jin sabon sauyi a tattare da ita, kasa banbancewa irfaan
yai shin da kyan nata da murmushinta wanne yafi tafiyar masa da zuciya? Murmushi ya sakar
mata yasa taje ta É—oro hijabinta akai sannan tazo ta zauna suka fara karatun boko daya fara
koya mata shima kafin mutanen gidan su dawo dan yau ma su Jannat nacan tare da Hajja
Maimoon É—in.

Duk wannan abun dake faruwa Hajja Maimoon bata sani ba dan babu abinda ya sauyawa daga
biyayyar da Jauhar keyi mata da kuma tsoronta da take ji. Abu daya ta lura dashi sauyin suturar
da Jauhar ta samu, wanda tana fara masifa akai Alhaji Sha'aban ya dakatar da ita ta hanyar
cewa lallai 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login