Showing 36001 words to 39000 words out of 47407 words

Chapter 13 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

3175

cewa.

"Zoki karɓa." Ta ɗago kai ta kalli ledar da yake miƙo mata. Ƙofar shigowa palourn ta ƙalla
sannan ta girgiza masa kai tana cewa.

"A'a Uncle Mommy kasheni zatayi idan na karɓa, wancan ma.." Sai kuma tayi shiru haɗe da
rufe bakinta tana kallon stairs cike da tsoro dan kada ɗaya daga cikin su Suhaila sufito su jita.
Haɗe rai Irfaan yai yana kallonta yace.

"Ta karɓe ko?" Bata iya bashi amsa ba ta sake kallon stairs ɗin, ya taso ya iso gabanta yana
cewa.

"Karɓi wannan bazata karɓar ba in sha Allah saboda a wajenta na siya miki. Ko da bazaki saka
ba kifito kiyi ƙoƙarin sauyawa idan kikayi wanka da kuma idan zakiyi sallah, dan bana tunanin
ubangiji na karɓar sallarki acikin wannan shigar Jauhar."

"Ai bana yin sallar ma." Jauhar ta tsinci kanta da faɗar hakan ba tare data sani ba, zaro idanuwa
Irfaan yai yana haɗe gira jin abinda ta faɗa.

"Me kikace Jauhar?" Ya faɗa cike da mamaki yana kallonta, sadda kanta tayi ƙasa tana ɗan ja
da baya ganin yadda fuskarsa ta sauya dan a tsammaninta zai iya kai mata duka. Jin ya sake
jeho mata tambayar rai a ɗan ɓaci yasa tace,

"Bana yin sallah Uncle ban iya ba!."

"Ban gane baki iya ba Jauhar, bakyayi ne saboda wani dalilin ko kowa bakyayi gaba ɗaya."
Irfaan yai maganar cikin ɗan sassauta murya ganin yadda take ja da baya saboda ta tsorata da
yanayin yadda yakeyi mata magana.

"Ban iya ba Uncle Mommy bata koya mun ba."

"A islamiya fa?" Ya tambayeta with so much shock,

"Ban taɓa zuwa ba." Itama ta bashi amsa cikin sanyin jiki.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Jauhar bakiga ƙawayenki nayi bane? Ko bakya ganin Mommyn
nayi da sauran mutanen da kike rayuwa zagaye dasu? sallah fa Jauhar? Baki san sallah itace
cikon musulunci gaba ɗaya ba?." Irfaan yai maganar cike da tashin hankali da tausayin Jauhar
idanuwansa cike da ƙwalla." Ganin haka yasa jikin Jauhar ɗin ya mutu ta duƙa agabansa tana
cewa,

"Uncle kayi hakuri Mommy bata bari na, ina kwantata yadda sukeyi, amma dana fara ma zakaji
ta kwala min kira, ko ta shigo taga ina yi sai tace, kinibibin banza me na iya banda na dinga
daukarwa kaina zunubi. Uncle zan fara yin sallah daga yau, kuma idan an kirani bazan amsa ba
sai na gama. Banda ƙawaye shiyasa ban koya daga wajensu ba, Mommy dasu Aunty Suhaila
kuma bana fahimtar abinda sukeyi ko sunayi ina gani, na dai san sallah sukeyi kamar yadda
naji sunanta abakin mutane." Jiki a sanyaye Irfaan ya kalleta yana cewa.

"Tashi kije idan kin gama aikin kin zan nemeki." Yafaɗa yana sake miƙa mata ledar dan gaba
ɗaya kansa ya kulle da jin wannan sabon al-amari acikin rayuwar Jauhar da bai taɓa zato ko
tsammani ba, yana bukatar tunani mai zurfi domin nema mata mafita acikin rayuwarta kafin ta
lalace. Karɓar ledar Jauhar tayi haɗe dayi masa godiya sannan ta ɗauke ƙyallen da ta gama
goge-goge ta wuce ɗakinta saboda ta kammala aikinta gaba ɗaya.

Irfaan kuwa kallo yabi upstairs ɗin da ɗakunan su Suhaila suke dashi yana jin wata irin damuwa
a ransa, ya buɗe baki kenan da niyar kiran Suhana ya ji ankira sallar magariba sai kawai yasa
kai yafice daga cikin parlorn. Anan bakin fanfon dake laƙe a jikin katangar dake jikin ɗakin Baba
Bello mai gadi ya tsaya yai alwala ya shiga Masallacin dake cikin gidan Baba Bello ya jasu jam'i
sukayi sallah.
__________
Gidan Kawu Ibrahim yana zaune sun idar da sallah yana ta kwararawa Alhaji Sha'aban Sada

addu'a domin ya kasa mantawa da tarin alkairansa. Ayusher ƴah ce tilo a wajan Kawu Ibrahim
ɗin, ita kaɗai Allah ya bashi aduniya, suna matuƙar sonta shi da Ummanta irin son da baki bazai
iya faɗa ba. Hakan ne kuma yasa ta taso cikin kulawa da gatantawa dai-dai karfinsu, sai dai duk
da haka basu bari son da sukeyi mata ya rufe masu idanuwa ba sun kasa bata tarbiyya, kama
daga ilimin boko har na Arabia dan tsaye suke akanta tun tana ƙaramar har zuwa yanzu data
kammala secondry ta shiga jami'a kuma take kan yin haddarta ta alƙur'ani da yanzu ta haddace
hizif arba'in, Ayusher yarinya ce mai natsuwa sosai da kuma alkunya da rashin son hayani,
hakan yasa tunda ta taso ba tada wasu ƙawaye in ba ƙawarta Khadija ba da kusan halayensu
suka zo ɗaya. Kyakkyawace sosai mai matsakaicin tsawo kuma tana da hasken fata data gado
wajen mahaifinta. Sun yi matuƙar shakuwa da Irfaan tun suna ƙanana kafin daga bisani
shakuwarsu ta juye takoma soyayya tare da yiwa juna alkawarin aure bayan ta kammala
karatunta, wanda sai alokacin suka ɗauki alwashin zasu bayyanawa iyayensu soyayyar dake
tsakaninsu dan har yanzu kowa ɗauka yakeyi shakuwa ce kawai. Wannan dalilin yasa kuma
Ayusher bata saurarar kowa duk da irin tarin samarin dake kawo mata hari, wasu ma sai dai su
biyo ta hanyar mahaifinta idan yayi mata magana sai tace ita karatune gabanta sai ta kammala,
da yake mahaifin nata shima yafi bukatar hakan sai kawai ya ƙyaleta ya basu haƙuri. Wannan
shine.
___________
Bayan su Irfaan sun kammala sallah awaje ya tsaya wajen Baba Bello ya ciro wayar ya kira
Ayusher suka sha firarsu da ita har aka kira sallar isha'i sannan ya yi mata sallama ya shiga
masallaci sukayi sallah. Yana fitowa ya koma cikin gidan ya tadda yaran gaba ɗaya sun sauko
palour sun zauna suna kallo, Jannat kuma na haɗa homework ɗinta da batayi ba.
"Uncle Irfaan Ina wuni." Duk suka faɗa ya amsa masu fuskarsa a sake yana cewa.

"Ɗazu na shigo ban taddaku ba sai Jauhar na samu tana aiki, in ce dai ba baccin yamma kukayi
ba." Yafaɗa yana zaunawa kusa da Jannat haɗe da gyara mata wasu errors da har ya hango
tayi wajen calculation saboda hankalinta data raba biyu rabi wajen kallo rabi kuma wajen
homework ɗin. Suhana ce ta amsa masa da, "Wallahi Uncle wani irin bacci ne ya ɗauke mu da
muka dawo mu duka saboda gidan ya zama empty."

"Saboda Momynku bata nan ko?" Irfaan ya faɗa yana kallon suhana

"Exactly Uncle Irfaan wallahi gidan duk ba daɗi." Suhaila dake kwance tafaɗa tana miƙewa
zaune da ɗan damuwa ɗauke a fuskarta. Murmushi ya saki haɗe da cewa,

"Ai kuwa sai ku fara sabawa tun yanzu tunda Momynku kuɗi take so."

Muryar Dady ce ta katse firar daya shigo hannunsa riƙe da ledoji. Suhaila ce ta miƙe ta karɓi
ledojin hannunsa haɗe da yi masa sannu da zuwa tana ƙwalawa Jauhar kira suma su Suhana
da Jannat suka miƙe suna yi masa sannu da dawowa.

"Sannu da dawowa Yaya." Irfaan ya faɗa yana miƙewa saboda dama ɗaya daga cikin shi da

Mommyn yake jira su dawo ya wuce gida.

Daidai lokacin Jauhar data fito wanka tana gwada ɗaya daga cikin rigunan da Irfaan ɗin ya saya
mata ta saka har da handbag ɗin da takalmin tana jujjuyawa cike da farin ciki, tana san gayu,
tana san abu mai kyau sai dai anyi mata shamaki da samun duk abinda zai sakata farin ciki.
Can kuma sai ta jiyo muryar Suhaila na ƙwala mata kira, bata tsaya wata-wata ba ta fito da
sauri cikin ruɗewa ba tare data tsaya cire komai ba ta nufo cikin palourn saboda sanin halin
Suhaila da tayi har tana gurɗewa tana faɗuwa saboda rashin iya tafiya da takalman da batayi
ba. Zaro idanuwa duk sukayi suna kallonta mayafin abayar ya rufe mata fuska sai kiciniyar
yadda zata buɗe fuskar tata takeyi gata sagale da jaka. Da kyar ta iya fito da fuskar daga cikin
vail ɗin, yadda ta zaro idanuwa tana fiƙifiki dasu haɗe da kallon mutanan wajan tamkar mara
gaskiya yasa Suhana ta kwashe da dariya, Irfaan ma murmushi yai yana kallon yadda ta saƙala
jakar da takalman kaɗai da ya isa yasa ƙasan bata saba saka irin kayan ba. Jannat data buɗe
baki tace.

"Sata kika yiwa Mommy? ba tace bazata baki ba?" Rai aɗan ɓace Irfan yace,

"Wane irin shirme ne haka kike yi Jannat? Ba sata Jauhar tayi ba ni ne na saya mata na kawo
mata." Yai maganar saunding so very angry.

"Uncle ka siya mata? Wannan yarinyar zaka siyowa kayan nan? Hmmm!" Suhaila tafaɗa tana
taɓe baki cike da takaicin Uncle Irfaan ɗin ta ajiye mata ledojin agabanta ta haye sama abunta.
Daddy kam da kallo yabi Jauhar data kwashi ledojin ta wuce kitchen dasu kafin ya maido
hankalinsa ga Irfaan yace,
"Har zaka tafi kenan bazaka tsaya kaci abinci ba?" Girgiza kai kawai yai tare da sake kallon
gefen kitchen ɗin sannan ya yiwa Yayan nasa sai da safe ya wuce. Ajiyar zuciya Daddy ya
sauke ya wuce part ɗinsa, da kansa ya haɗa ruwan wankansa bayan ya rage kayan jikinsa. Sai
a lokacin yaji ƙarar shigowar motar Mommy ta dawo. Kai tsaye ɗakinta ta wuce dan agajiye take
tafara shiga ta watso ruwa tayi sallar isha'i da batayi ba sannan ta wuce ɗakin su Su haila. Da
gudu Jannat ta taso tana yi mata oyoyo tayi hugging ɗinta tana cewa.

"Daughter bakiyi bacci ba? Kinci abinci kuwa?"

"Eh Mommy yau gidan so boring da bakya nan." Jannat tayi maganar tana sake shigewa jikinta
tamkar wadda ta daɗe bata ganta ba. Ta bayanta taji Suhaila da Suhana sun rungumota suma
suna cewa,

"Welcome home Mommy we missed you." Ta shafo fuskokinsu da hannuwanta atare tana
murmushi tace.

"I missed you too yarana, Ina fatan ba wata matsala kunci abinci ko?"

"Eh Mommy." Suka faɗa atare suna breaking hug ɗin tare da komawa kan gadajensu. kayansu
da suka zubar a tsakiyar palourn ta shiga tattarawa tana kwashe su takai washing mashin
sannan ta dawo tana cewa.

"Oya akwai school gobe kun sani ya kamata ku kwanta da wuri, bari naje gun Dadynku."
Taƙarasa zancen tana ficewa tare da ja masu ƙofar. Hajja Maimoon na sakkowa Dady nafitowa
dan yunwa yake ji,

"Sorry Ya Habibi wallahi customers suka riƙeni. I can't believe yadda aka samu kasuwa yau
daga buɗe shagon nan." Taƙarsa maganar tana janyo masa kujerar dining da suka nufa,
murmushi ya saki yana cewa.

"Masha Allah abu yayi kyau Allah yaƙaro kasuwa, ina fatan ba wani abu wurin yayi miki sosai
ko?"

"Ai ina faɗa maka wajen nan is extremely good, yau ɗinnan da aka  buɗesa har anyi cinaki over
1.5million, gaskiya alhamdulillah mun shiga kasuwar nan da hannun dama." Tayi maganar tare
da jawo kujera ta zauna itama, tana kai hannu zata fara saving ɗinsu wayarta tayi ƙara, duba
kiran tayi taga wata customer ce da tazo ɗazu sukayi maganar tana son turarukkan ƙamari zata
siya, ba shiri ta miƙe tana ƙwalawa Jauhar data soma bacci kira sannan ta ɗaga wayar takai a
kunne,  da gudu Jauhar da bata san da dawowarta ba ta iso wajen ta zube ƙasa tana cewa.

"Sannu da dawowa Hajiya gani." Ɗan janye wayar tayi daga kunnenta tana cewa.

"Ki zubawa Daddy abinci, Ya Habiby ina zuwa customer ce." Ta wuce abunta zuwa ɗakinta tana
ci gaba da wayar ba tare data tsaya saurar abinda zai ce ba. Da kallon mamaki Alhaji Sha'aban
Sada ya bita har ta haye sama kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Jauhar data ɗauki plate
da serving spoon tana cewa.
"Alhaji me zan zuba maka?" Mamaki ne shima a saman fuskarsa, kayan ɗazu ne a jikinta,
kalmar Jannat ta dawo masa cikin kwakwalwarsa dan haka yace,
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*

*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce

*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu

*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch

*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.

*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso

*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000

*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130

*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.


#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

NA

*BILLY S FARI*
Da
*HAJJA CE*
Arewabooks@billysfari

Page 14..

"Ina kika samu wannan kayan?" Jauhar tayi saurin kallon jikinta, bata kalli fuskar Alhaji
Sha'aban ɗin ba dan sai take ganin kamar shima bai yadda cewa Uncle Irfaan ne ya bata ba
tunda ai a gabansa Irfaan ɗin ya faɗi cewa shine ya kawo mata. Jin tayi shiru yasa yaji kamar
tambayar ce bata fahimta ba, yadda jikinta yake rawa yasa tausayin ta ya kama shi, plate ɗin da
ta ɗakko zata zuba masa ya janyo tare da cewa.

"Barshi Jauhar jeki kwanta." Ganin yana ƙoƙarin zubawa da kanshi yasa tayi saurin durƙushewa
a gabansa tana sake waigawa ta kalli hanyar da Hajja Maimoon tabi, bakinta yana kyarma take
masa magiya.

"Kayi haƙuri Alhaji wallahi Uncle Irfaan ya bani kayan ɗazu, sannan dan Allah ka kawo na zuba
kar Hajiya taga bani na zuba ma ba." Karo na babu adadi da tausayin yadda yaga duk ta firgice
ya dirar masa cikin zuciya. Cike da nutsuwa irin tasa da Allah ya wadata shi da ita yake girgiza
kai yana faɗin.
"Irfaan ya kyauta sosai, sannan karki damu dan na zuba da kaina ai ni nace ki barshi. Oya
koma ɗakin ki kiyi kwanciyarki dare ya yi, kinci abinci dai ko?" Ya tambayeta cike da son gyara
kulawarsa da baya bata a da har sai da aka lurar dashi. Cike da mamakin yanayin da ya yi
furucin Jauhar ta kalleshi. A cikin jikinsa yaji cewa kallansa ake domin da ya tambayeta sai
kawai ya maida hankalinsa wajan zuba abinda yake da buƙata. Kallansa ya mayar saitin inda
yake jin idon a jikinsa, yadda yaga Jauhar ɗin tana ware ido yasa shi saurin yin magana.

"Ya akai?" Ta sauke ido dan bata iya kallansa saboda yana da mugun kwarjini. Muryarta tana
rawa tace.

"Alhaji naci."

"Masha Allah toh kije kiyi kwanciyarki Allah ya huta gajiya Allah yai miki albarka." Jauhar ta
durkusa tana amsawa dan ba ƙaramin daɗi addu'ar tashi tayi mata ba, shine mutumin da yake
yi mata wannan daddaɗar addu'a sai kuma idan Hajiya tazo wacce idan ba wani babban abu
bane ya faru a gidan bata cika zuwa cikinsa ba. Ɗaki ta koma tana shiga kwanciya tayi akan
carpet ɗin dake shimfiɗe a ciki wanda shine ya zamar mata kamar katifa da take kwanciya tayi
bacci. Sai da ya kusan kammalawa Hajja Maimoon ta karaso inda yake tana jan kujera ta
zauna. Dube-dube ta shiga yi ko zata hango Jauhar amma ba ita ba labarin ta. Kira ta shiga
kwala mata Alhaji Sha'aban ya dakatar da ita.

"Me kuma zatayi?" Mamakin tambayar tashi tasa Hajja Maimoon kallon cikin idanunsa.

"Idan abinci za'a zuba miki madam kina dani a kusa meye na kiran yarinya?" Nan da nan farin
ciki ya kamata tayi ƙasa da kanta cike da nuna kunya tana janyo boul, karɓa yayi da kansa ya

zuba mata fresh milk ɗin a ciki sannan ya zuba mata cornflakes ɗin cikin extra boul dan ya lura
shi tafi bukata a gurin. Suna ci suna hira har ta kammala suka mike zasu wuce ɗaki ta shiga
kwalawa Jauhar kira dan tazo ta gyara wajan. Alhaji Sha'aban yana riƙe da hannunta yace,

"Me zatayi?"

"Ya Habiby tazo ta kwashe kayan ta gyara wajen ko?"

"Ki bari idan Allah ya tashe mu gobe sai tayi mana abinda tana nan ba wani guri zata je ba."
Ɓata rai tayi tace,

"Yanzu Ya Habiby haka za'a bar gurin nan har sai da safe? Haba Ya Habiby sai kace gidan
ƙazama? Tana nan fa meye amfaninta a gidan nan?" Ya ɗan sanyaya murya yana janyota cikin
jikinsa dan harga Allah baya son a taso yarinyar nan yanzu tunda har shine yace taje ta kwanta.
Hajja Maimoon kuwa ta sake haɗe rai dan tunda taga yana wani matseta cikin jikinsa tasan
lallaɓata zaiyi ta haƙura tabar Jauhar zuwa safiya, ita kuma tana jin tamkar idan ta barta
zuciyarta ƙonewa zatayi dan bata farin ciki idan taga Jauhar na hutawa ko tana samun walwala
a gidan.

"Pls.. Nasan gobe tana idar da sallar asubahi zata fito ta gyara, yanzu dai kam kiyi hakuri ki
kyaleta." Ganin da gaske hanawa zai yi sai kawai ta zare hannunta daga cikin nasa ta janye
jikinta fuskar nan tata a matukar haɗe tace.

"Gaskiya Ya Habiby idan har na bar yarinyar nan bata gyara gurin nan ba shikenan haka zata
dawo kazanta sai wacce batayi niyar yi ba. Kabar ni da ita kawai Allah sai tayi aikin nan." Kallon
yadda ta kafe tana yi masa gaddama yake ya ji abun yai matukar ɓata masa rai, a tunaninsa
duk abinda yace mata ya kamata ta dinga yi babu jayayya koda ranta baya so kamar yadda
shima yake hakura da wasu abubuwan koda ba dai-dai bane dan gujewa ɓaci ransa, amma ya
lura sam bata tunanin hakan, takan yi masa kafiya musamman idan abun ya shafi Jauhar takan
nuna masa bai isa ba itace wacce take da iko da ita. Ransa a ɗan ɓace da yake ba saba bari ya
yi ɓacin rai ya yi tasiri a zuciyarsa ba ya sauke nauyayyen numfashi yana ambaton Allah
abakinsa. kallanta da idanunsa yai cike da san nuna matsayinsa na mijinta agareta yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login