Showing 30001 words to 33000 words out of 47407 words
Chapter 11 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
Maimuna da yarinyar nan da take mata aiki?" Hajiya ta jefo
maganar wacce sai da Alhaji Sha'aban yaji ta har cikin zuciyarsa dan bai taɓa tunanin zatayi
masa ita ba. Irfaan yai saurin tashi zai bar gurin dan bai shirya yin wannan maganar da Yayansa
ba.
"Dawo ka zauna Irfaan ai da kai za'a yi maganar." Cike da wata irin kunya ya koma duk da yana
jin zuciyarsa tana karfafa shi akan karya ƙi yin abinda yake ganin mafuta ce a wajan Jauhar.
Kamar marar gaskiya haka ya koma ya zauna yana jujjuya spoon É—in hannunsa yama kasa
shan furar yadda ya kamata.
"Hajiya wani abun ne ya faru? Daga gidan nake amma banji ance da matsala ba." Hajiya bata
ce komai ba sai kallon inda Irfaan yake da tayi tana jiran ya yi bayani. Dariya ce ta kwace mata
ganin ko inda suke zaune Irfaan É—in be kalla ba dan haka Hajiya ta daure tare da cewa.
"Sanar masa abinda ya faru Irfaan." Cike da jin nauyi dan baisan a yadda Alhaji Sha'aban É—in
zai É—auki maganar da zai yi ba. Da kyar Irfaan ya daure jin da yayi shi ake jira ya yi bayani, ya
daure yace.
"Yaya kamar dai yadda kasani ne, ni wallahi kawai bana son ana cin zalin yarinyar nan saboda
duk abinda ya sameta a gidan Yayana ne. Bana son naga ana musguna mata kuma wai a
gidanka Yaya kai da kake mutum mai tausayi akan komai..."
"Please kayi min bayani sosai meke faruwa a gidan nawa?" Alhaji Sha'aban ya katse shi dan ya
matsu yaji. Murya Irfaan ya sanyaya tare da sake yin ƙasa da kanshi yace.
"Jauhar koda ta kasance Æ´ar aiki a gidanka, sam bai dace ana yi mata wasu abubuwan ba.
Yaya kaga kai ne kace mu tafi da yarinyar nan asibiti amma wallahi karkaga da yadda suka
yadda ta shiga motar nan, munje asibitin ma aka rubuta magunguna amma haka Aunty
Maimoon tace ba zata siya dana Jauhar É—in ba tasa aka bada na Jannat kaÉ—ai. Duk da haka
Yaya na fito na siyawa Jauhar É—in magani da kuÉ—i na sai na haÉ—a da wata Æ´ar riga nace tayi
amfani dasu dan naga a yadda take rayuwa kuma wai a gidan ka Yaya. Shine Auntyn ta kwace
kayan harda cewa wai...." Da sauri Alhaji Sha'aban ya katse shi dan yanaji a ransa maganar
karshen babu alkairi a cikinta kuma yasan itace mafi munin ji a duk maganganun da yake ji
daga bakin ƙanin nasa. Shi kansa yafi su jin rashin daɗin yadda ake yiwa yarinyar, ya yi kuma
iya yinsa wajan nunar da Maimoon hakan ba daidai bane amma ta nuna masa cewa tun daga
wajan iyayenta komai yake faruwa, ta kuma tabbatar masa da cewa idan har ta bari Jauhar ta
samu kwanciyar hankali toh tabbas ita kuma zata kasance cikin damuwa. A lokacin ya hango
tsantsar haushi, bakin ciki da kuma damuwa akan fuskarta wanda ya tabbatar da har ranta take
jin haushin cewa da ya yi ta kula da yarinyar.
"Wai kana sane ake yiwa yarinyar nan haka? Kulawarta yana kanka fa yanzu ba wai dan tana
mai aiki ba kayi shiru ana mata ba daidai ba. Kuma ita kaÉ—ai ce ake samun matsalar nan ko
masu gadi sun fita jin daɗi da kwanciyar hankali ita da take mace mai ƙananun shekaru. Idan ba
zaku kula da ita ba ya kamata ku maidawa iyayenta abarsu suyi yadda zasuyi da ita, bana son
zalunci ban kuma koya muku shi ba, haka zalika bance ku bari ayi ba." Shiru Alhaji Sha'aban ya
yi yana jin damuwa a cikin zuciyarsa, shi kam besan yadda zai yi da matsalar nan ba harga
Allah, amma saboda ya kwantar musu da hankali tunda dai sun shiga damuwar ne saboda shi
dan haka cikin taushin murya yake cewa.
"Insha Allahu za'a gyara Hajiya, ni nafi ganin laifin iyayen Jauhar saboda tun lokacin da nake
neman auran Maimoon tare suke kuma babu abinda ya canza na game da yadda suke rayuwa
da ita. Naso yiwa mahaifin Maimoon magana amma ya nuna min cewa gwara abarta a wajanta
yafi mutunci akansu su riƙe ta."
"Kasan É—an kauye kuma da muguwar kafiya, ana nuna masa gabas yana cewa yamma yafi.
Duk da haka kayi ƙoƙarin ganin an sassautawa yarinyar, haka duk sanda Maryam taje gidanka
sai tayi min ƙorafin yadda take ganin yarinyar, kuma wai da kazantar nan take yi muku girki ku
cinye." Alhaji Sha'aban dai ya yi shiru baice komai ba dan shi kansa abun nan yana bashi
haushi yadda Jauhar take rayuwa dasu cikin rashin daraja. Ganin Hajiya tasa baki yasa Irfaan
yaji hankalinsa ya É—an kwanta, sannan yaji karfin guiwar samun damar taimakawa Jauhar É—in.
Sun taɓa hira sosai kafin yasa hannu cikin aljihu ya zaro sarƙa da ɗankunnen da ya siyawa
Hajiyan, ya miƙe tare da isa wajanta ya durƙusa har ƙasa ya saka mata a cikin tafin hannunta.
Kallon hannun Hajiya tayi kafin ta kalleshi da sauri tana cewa.
"Na menene wannan?" Cike da soyayya yace.
"Naki ne Hajiya." Kallon hannun ta sake yi tana jin zuciyarta na karyewa, ta kalleshi kamar
zatayi kuka dan muryarta har rawa takeyi kafin tace.
"Me yasa kake san wahalar da kanka? Haka kawai kaje ka kashe kuÉ—inka maimakon kasasu
cikin kasuwancin ka shine zaka siyo min zinari? Ina dasu fa wajan guda nawa ma amma kaje ka
sake siyo min." Murmushi ya yi tare da miƙewa tsaye yana cewa.
"Haba Hajiya, duk wani abu da zan miki koma bayan abinda kika yi min ne, ko shagon zinari na
kawo miki Hajiya ban isa na biyaki ba bare dan ma siyo miki wannan. Allah ya kara miki lafiya
da nisan kwana domin ke ɗin garkuwa ne a garemu." Maryam ce ta taho da gudu, karɓar
Æ´ankunnayen tayi tana jujjuyawa kafin ta narke fuska tana turo baki take faÉ—in.
"Toh Yaya nifa?" Ya kalleta tare da faÉ—in.
"Ohhh haɗa kanki kike yi da Hajiyata?" Sai da ta sake shagwaɓewa tana noƙe kafaɗa tace.
"Ni da nake Æ´an mata ai ni zaka dinga kashewa kuÉ—i Yaya, Hajiya fa tana dasu da yawa."
"Ki bari idan kasuwa ta sake yin kyau sai na bawa Irfaan kuje a siya miki." Alhaji Sha'aban ya
faÉ—a yana kallonta.
"Yaya kasuwa fa tana kyau, ko addu'ar da Hajiya keyi maka kaÉ—ai ta isa tasa kasuwancinka
habɓaka bare mutane da bakinsu baya gajiya wajan yi maka addu'o'i. Kawai nidai Yaya ka ce
zaka tura masa kuɗin." Maryam ta faɗa tare da langaɓe kai. Sai da ya saki murmushi yace.
"Shikenan Irfaan zan tura maka sai kuje tare ta siyo." Farin ciki ya kama Maryam ta shiga murna
tana yi masa addu'a Hajiya kuma na sake sanya masa albarka. Sallama ya yi musu inda Irfaan
ya tashi yabi bayansa sukaje har bakin motarsa.
"Kayi amfani da Atm É—ina na wajanka Sai kuje a siyawa Maryam É—in, ina so a siya kayan abinci
a kaiwa Kawu Ibrahim karka manta dan Allah Irfaan." Cike da girmamawa Irfaan É—in ya amsa
daga nan Alhaji Sha'aban ya shiga motarsa yaja yabar unguwar.
______
Tsaki ya dinga saki ba ƙaƙƙautawa, banda zafi babu abinda zuciyarsa keyi, yaso Mama ta
barshi ya faffallawa Husnah mari ko zata farka daga nannauyan baccin da takeyi na ganinta da
Ilyasmater dan shi a ganinsa mafarki kawai takeyi shi yasa har ta tsaya tana sauraransa harda
cewa wai saurayinta ne. A hankali ya zare rigar jikinsa yaje ya sagaleta yana sake jin wani
ɓacin rai a ransa. Jikinsa babu kwari ya shiga ɓalle belt ɗin dake ɗaure a ƙugunsa ya kasa cire
hotan guy ɗin nan a cikin idanunsa dama zuciyarsa. Ba irin mazan da yake son ƙannansa su
dinga kulawa bane, yana da wani irin buri akan ƙannansa dan haka ne ma yake da mugun taka
tsantsan akan tsare mutunci da kuma ƙimarsa dan kar yaje shima a yiwa wata a cikin
ƙannansa. Jeans ɗin jikinsa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wanda da black singlet, Wanka
yake son ya yi sai dai baya son sake komawa cikin gidan. ÆŠakinsa yabi da kallo yana jin
takaicin rashin bathroom da babu a ciki. Da kyar ya iya karfafa zuciyarsa ya janyo jallabiyarsa
da yake shiga wanka da ita ya sanya bayan ya cire singlet É—in jikin nashi. Kwandan wankansa
ya ɗauka sannan ya fito tare da janyo ƙofar ya shiga cikin gidan. Cikin sa'a ya tarar da Husnah
tana tarar ruwa a fanfo bataji motsinsa ba sai ji tayi kawai an sakar mata rankwashi a tsakiyar
kanta, kafin ta É—ago taji yana cewa.
"Sakarai kawai, wannan gayen meye abun burgewa tare dashi? Idan na sake ganinki dashi sai
na miki shegen duka a gidan nan, bazan bari ki janyo mana surutun mutane ba." Yana kaiwa
nan ya É—auke bokitin ruwan da ta tara ya shige toilet ya barta. Husnah ta saki kuka tana rugawa
cikin parlorn Mama da gudu kamar wacce aka biyo.
"Mama kinga Yaya Zain ko?" Cewar Husnah tana dafe da tsakiyar kanta.
"Kai innalillahi Wainna ilaihir raji'un wai dama bekyale ki ba da nace babu ruwansa?"
"Kuma har cewa ya yi idan na sake kula saurayi sai ya min shegen duka." Husnah ta faÉ—a tana
sake rushewa da kuka.
"Ina jin dai auran ku zai yi, banda haka banga dalilin da zai sa yaron nan ya dinga takura muku
ba dan kun kula samari, bari ya fito zai sameni gwara ya yi min bayani naji idan ya yi shirin
auran ku ne sai naji dalili." Ta ƙarasa maganar tana ɗaga murya yadda Zain ɗin zai jiyo.
Rufe bakinta keda wuya sai ga Abba ya shigo. "Haba! Dawa kike wannan faÉ—a ake jin muryarki
har ƙofar gida?" Yafaɗa yana miƙawa Husnah dake yimasa sannu da zuwa ledar dake
hannunsa.
"Sannu da dawo." Itama Mama tafaɗa cikin ɗan ɓacin rai tana miƙewa daga kwance da take
Husnah kuma ta karbi ledar da yake miƙo mata ta nufi kitchen da ita. "Ni da waye banda Zain
kuwa yabi duk ya takurawa yarinyar nan sai kace ba ƙanwarsa ba." Sai da Abba ya zauna
saman kujera sannan ya amsa sannu da Mama tayi masa yana cewa.
"In banda abunki meye laifi idan ya tsawatar mata tunda yayanta ne? Ai hakan shine dai-dai
tashi ki je ki kawo mani ruwa." Yaƙare zancen haɗe da cire hular kansa ya ɗora saman hannun
kujera.
Mama bata ce komai ba taje ta kawo masa abincinsa da ruwa ta ajiye masa agabansa sannan
ta zuba masa ya soma ci. Bayan ya kammala ta tattare wajen ta kwashe kayan takai kitchen ta
dawo. Nan ta shiga labarta masa abinda ke faruwa ba tare data tuna da halin mijin nata ba da
ba goyon bayanta zaiyi ba akan wannan, dan in dai akan tarbiyar yaransa ce a tsaye yake
sosai. Sauke lumfashi yai cike da mamaki yana kallonta kafin yace.
"Ina tunanin Alhamdulillah girma yazo kin sauya daga Halimar dana sani ada kin koma wata
kamilalliyar Halima uwa da zata cigaba da tayani ba 'ya'yana tarbiyya idan bana kusa ashe har
yau akwai sauran rina a kaba? Yanzu fisabilillahi wannan dan iskan yaro Iliya da naji ya ma
sauya sunansa ya koma Iliyasmaster tsabar rashin ji ko ke kika ganta tsaye dashi baza ki koreta
ki hanata sake tsayawa dashi ba? To bari kiji in faÉ—a maki ba Zain ba wlh koni na sake samun
labarin angata tsaye da wannan ɗan iskan yaro lalatacce sai na ɓaɓɓallata kuma kema saina
saɓa maki dan bazan lamunci wannan shashancin ba acikin gidana." Ya ƙare maganar cikin
faÉ—a haÉ—e da É—aukar hularsa ya maida akai ya fice daga gidan dan an kira sallar magrib, da
kallo tabishi bata iya cewa komai ba saboda ranta aɓace yake itama akan ƙa'idojin nan nashi da
yake kira tarbiyya dake hanata rawar gaban hantsi ita da yaranta...
#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce í ½í±ˆ
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Arewabook@billysfari
*Assalamu alaikum*
_Ina masu son ayi masu Logo ko flyer, E-book cover's ko stickers, invitation card ko kuma
invitation vedio domin ƙawata kasuwancinku da janyo hankulan customers ɗinku? To ku matso
kusa ga S fari graphic design sun shirya tsaf domin yimaku abinda zai zo daidai da ra'ayinku
bisa farashi mai sauƙi._
Sai ku tuntuɓemu ta
CALL OR WATSAPP
07040402435/07081675855.
Mungode.
Page 12..
Ɗaya daga cikin ƙananun shagon Alhaji Sha'aban Irfaan ɗin yaje ya kwaso duk wani abu da ya
sani na daga kayan abinci kafin ya nufi gidan kawun nasu. Sai da Irfaan É—in yasa almajirai suka
sauke masa kayan abincin dake makare a boot É—in motar suka shiga dashi ciki sannan yabi
bayansu. Anan cikin zauren gidan ya iskosa zaune tare da almajiransa yana biya masu karatu.
Gefe ya samu ya tsaya haÉ—e da fiddo wayarsa yana latsawa har sai da su kawun suka
kammala almajiran suka tashi suka tafi, jefa wayarsa Irfaan ya yi cikin aljihu ya ƙarasa bisa
tabarmar ya zauna cike da girmamawa yana gaida kawu Ibrahim É—in dake tattare littafan gaban
nasa waje ɗaya yana mayarwa gefe. Fuskar kawu Ibrahim a sake ya ɗago kai tare da miƙa
masa hannu sukayi musabiha yana amsa gaisuwar da ya yi masa yana É—orawa da cewa.
"Sannu da ƙoƙari malam Irfaan ya mahaifiyar taku da ƴan uwan naka?"
"Duk suna lafiya Kawu sunce na gaisheka sosai, ga saƙonan inji Yaya yace akawo maka."
"Masha Allah, agaida Alhaji Sha'aban, ubangiji Allah yai masa albarka ya jiƙan mahaifinku.
Yadda kuke kula dani tamkar ni na haifeku Allah ya kula da zuri'arku gabaki É—aya. Nagode
nagode sosai Allah ya saka da alkhairi kaima Allah ya yi maka albarka."
"Amin ya rabbi kawu."
"Taso mushiga ciki kasha ruwa kafin kawuce." Kawu Ibrahim ya faɗa yana miƙewa haɗe da
gyara babbar rigarsa sannan ya yi gaba zuwa ciki. Ba yadda Irfaan ya iya dole ya miƙe yabi
bayanshi suka shiga ciki.
Zaune take tana wanke kwanuka Umma na jiranta zata kwashe abinci saboda bata jima da
dawowa wajen haddar Alqur'ani da suke tasowa ba bayan sallar magriba. Sallamar mahaifin
nata daya shigo yana ƙwalawa Umma kira yasa ta ɗago kai, karaf sukayi ido biyu da masoyin
nata da ya kafeta da idanuwa, dan tunda Irfaan yake da ita bai taɓa zuwa gidan ya iskota cikin
irin wannan shigar ba ta riga da skert, da yake wuyan rigar na da É—an faÉ—i zaka iya hango tudun
albarkatun ƙirjinta da take dasu masha Allah. Da su Irfaan yai tozali lokacin dayake shigowa,
hakan yasa yakasa É—auke idanuwansa akanta har sai data lura da hakan ta shiga Æ´an
kame-kame. Murmushi Irfaan ya sakar mata ta sadda kanta ƙasa cike da jin kunya shi kuma
yaƙarasa ciki ya zauna saman tabarmar da Umma ta shimfiɗa masa suka shiga gaisawa da ita
tana tambayarsa ya Hajiya take.
Ganin haka yasa Ayusher ta miƙe ta kwashe kwanonin ta nufi kitchen kirjinta na bugawa ta
shiga kwashe abincin kafin Umma tazo.
"Tashi kije ku gaisa da Yayanki sai ki kai masa ruwa na ƙarasa kwashe abincin sai kizo ki
É—aukar masa nashi ki kai masa." Ayusher taji mahaifiyarta ta data shigo kitchen É—in yanzu
tafaɗa tana ƙoƙarin karɓar abun kwashe abincin a hannunta. Ɗaki Ayusher tafara shiga ta
sanyo hijab É—inta haÉ—e da dakko ruwan leda guda biyu masu sanyi ta É—oro akan plate ta nufo
wajensu. gabansa ta ajiye plate É—in ruwan ta zauna, ceke da natsuwa take cewa.
"Ya Irfaan sannu da zuwa, ina wuni?"
Daidai nan aka aiko yaro ana yiwa kawu Ibrahim sallama awaje dan haka ya miƙe yafice daga
gidan ya basu waje. Da idanuwa Irfaan ya bita yana ƙara jin ƙaunarta na ratsa masa zuciya,
kunya da natsuwa na ɗaya daga cikin abubuwan dake sashi yake ƙara jin sonta akoda yaushe.
ÆŠan lumfasawa yai sannan ya amsa mata da cewa.
"Lafiya kalau Ayusher har an taso daga wajen haddar?"
"Eh, ya Hajiya da Ya Maryam da wajensu Suhana?"
"Kowa lafiya kalau." Daga haka shiru ya ratsa tsakaninsu na mintuna sakamakon ruwan da
Irfaan ya É—auka yana sha,
"Alhamdulillah." Yafaɗa yana ajiye sauran ruwan a plate, miƙewa tayi da zimmar zuwa ta karɓo
masa abincin kamar yadda Ummanta ta buƙata yai saurin dakatar da ita.
"Ina zuwa kuma bayan ko lafiyata baki tambaya ba?" Murmushi ta saki kafin tace,
"Ai naga lafiyarki ƙalau shiyasa ban tambayeka ba, bari nazo Umma tace na karɓo maka
abinci."
"A'a dawo ki zauna alhamdulillah a ƙoshe nake."
"Wane irin ƙoshe kuma Irfaan ga abinci angama, ke Ayusher je ki dauko masa kinji ko?" Suka ji
muryar Umma tafaÉ—a daga tsakar gidan. Kallonsa tayi ta sakar mashi murmushi tana É—age
kafaÉ—a alamun ba ruwanta, 'yar hararar wasa Irfaan É—in ya aika mata da