Showing 45001 words to 47407 words out of 47407 words
Chapter 16 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
idan bazata iya bashi kulawar da yake buƙata ba tofa bazai zauna da yarinyar da ita
ke kula da cinsa da shan sa da komai nasa ba da ƙazanta, ko dai ta bashi lokacinta ta dawo
yimasa duk wani abu da yake dolenta, ko kuma tabar Jauhar dayi masa amma ba'a cikin
ƙazanta ba ko kuma ta sallami Jauhar ta dauko wata mai aikin dake da tsabta, amma shi ya gaji
bazai jurewa cin abinci da kazantar da Jauhar keda ita ba. Dole Hajja Maimoon tabar zancen
dan cikin zaɓi uku ɗin ɗaya bata sam bata jin akwai ɗaya da zata iya karɓa, dama-dama ma taci
gaba da zama da Jauhar É—in a haka tunda ba zaman gidan takeyi ba akan ta koreta ko kuma ta
dauko wata mai aikin da bata sani ba tazo ta wargaza mata farinciki ko ta rabata da mijinta.
Jauhar kuwa tasan ko a mafarki tsakaninta da mijinta sai kallo.
(Anya Hajja Maimoon! Muje zuwa. Hajja ce da Billy s fari suka faÉ—a suna sake gyara zamansu).
__________
Kusan mintuna goma kenan dattijon nayi masa magana amma yaƙi koda ɗago kai ya kallesa
sai wani rangaji da kai yakeyi yana magana can ciki-ciki.
"Iliya dakai fa nake magana wai har sai yaushe zakayi hankali kasan ciwon kanka, kaje ka
nanewa yarinya duk da kashe É—in da ake buga maka amma kaki fita harkarta so kakeyi ka janyo
mani masifa, wannan wace irin rayuwace ance kaje kayi aiki ka ƙi sai dauko mani magana
kakeyi agari."
"Babcy bafa Iliya ba, Iliyasmaster zaka ce, kuma da kake zancen Huscybaby wallahi baka san
irin ƙaunar da nake yi mata ba shiyasa kake cewa na rabu da ita, to naji wa kake so na kula
akaf faÉ—in garin nan idan ba ita ba? Ka fadamun naji Babcy wace yarinya ce tazo dai-dai
method É—ina da kuma equal É—ina? Na rantse Babcy ko kai ne a wannan shekarun nawa kaga
Huscybaby sai ka kwaye mata, da kuma kake zancen aiki to wabillahillazi bazanyi tsaron gate
ba full gaye dani, aiki sai kace gado ka wani ce sai nayi bayan haka nan tunda na tashi kake
yinsa amma har yanzu bakayi arziki ba sai ma wane mokaÉ—ewa da kayi tsabar wahala, a haka
ma dan Alhajin na kyautata maka ne da yanzu kafi ɗan duƙushi mokadewa har ka son cin nani
a wahala na kare kamar kai a matsayin mai gadi har tsawon rayuwata. Gaskiya Babcy na girmi
gadi kawai ka bani kuɗi naje naja jari nima ko nayi arziƙi".
Girgiza kai Baba Bello ya yi da kwana biyu kenan da barowarsa wajen aikinsa bayan Alhaji
Sha'aban yayi masa sallama mai tsoka tare da kawo wani mai gadin dan har lokacin Baba Bello
mai gadi bai samu ya shawo kan Iliyasmaster ba yaje, amma Alhaji Sha'aban Sada yai masa
alƙawarin duk lokacin da ɗan nasa yaji yana da sha'awar yin aikin to kai tsaye ya turoshi ba
damuwa sai su rikayin duty shi da maigadin da aka kawo yanzu,
"Allah ya shiryeka Iliyasu, ni ba wani master dana sani Iliya na yanka maka da ragon sunan ka
shashasha. Da kuma kake zancen kai baza kayi gadi ba mantawa kayi ne dashi na reneka har
ka girma ka kawo wannan matsayin da kake jin kai ka girmi gadi? Ni shine rufin asirina kuma
yayi mani sutura Alhamdulillah, ya rage naka kayi tunani kaje ka kama aikin nan tun wuri bai
kure maka ba ko kaci gaba da zaman banza ana lissafaka acikin ɓata gari da basu san ciwon
kansu ba. Husnah kuwa indai a haka zaka zauna daga ni har yan uwana babu wanda zai je ya
nema maka aurenta tunda baka san ciwon kanka ba." Baba Bello yai maganar haɗe da miƙewa
yabar gidan yana mai nemawa ɗan nasa shiriya da ƙasa ta jima da rufe fuskar mahaifiyarsa,
matarsa kuma ba saurararta Iliyas keyi ba balle ta tama shi yimasa faÉ—a.
Iliyasmaster kuwa sai daya tsaya ya yiwa matar mahaifin nasa surutu da tunda mahaifinsa keyi
masa magana bata ce komai ba amma duk da haka bata tsira ba sai cewa yakeyi duk ita ke
zuga mahaifinsa ke zuwa yana yimasa faÉ—a. Nan ma bata tanka shi ba har ya gaji yaja
ƙafafuwansa dake saye da takalman da suka zame masa tamkar na karfe yafita.
Bai zame ko ina ba sai anguwar su Husnah, cikin Sa'a ya hadu da ita ta dawo wajen yiwa
Umma cefane zata É—ora girki rana dan har karfe sha biyu ta wuce. Washe baki yai haÉ—e da
nufota yana wani jefa kafa tare da watse hannuwa irin na gayu yana kaiwa inda take ya shiga
sosa kai irin na munafukai din nan yana cewa.
"Sai ni sai ke Huscybaby, kina shigo kwanar nan wani haske yazo ya dakar mani zuciya, anya
kaf garin nan akwai yarinyar da tayi kyanki da hasken fuskarki?" Dariya Husnah tayi tana
kallonsa haÉ—e da cewa.
"Akwaisu mana ilyas kaine kawai baka ganinsu".
"Ahhhh! Ai ni dama bana son naga kowace mace idan ba keba, Huscybaby kin fa riga kin sace
zuciya, duk abinda kike so zan yi maki duniya koda kuwa sama kika ce na hau na ciro maki
wata!" Yaƙare zancen yana karɓar kayan hannunta ita kuma ta zaro idanuwa tana cewa,
"Allah Ilyas."
"Toh ko za'a gwada Huscybaby yanzu nafara zo maku da rana kafin dare yayi na dauko maki
watan?"
"A'a a haka ma na yarda kana sona." Da haka sukaci gaba da tafiya Iliyasmaster sai tsarata
yakeyi da karya kala-kala ita kuma tana hawa, dan ita kalaman ilyas kadai na tafiyar mata da
zuciya tare da ƙara mata son sa, sai da suka iso ƙofar gida Iliyasmaster yaja ya tsaya haɗe
dayin nildown yana miƙa mata ledar kayan daya riƙo mata. Karba tayi tayi masa godiya sannan
ta nufi cikin gida, har ta kusa shigewa cikin É—aga murya Iliyasmaster ya ware hannuwa irin
yadda indiyawa keyi da ƙarfi yana cewa.
"I love youuu Huscybaby, ina san ki." Hakan yasa Husnah da taji saukar muryar tasa da karfi ba
zato ba tsammani ta saki ledar kayan mutane data siyo ta runtuma da gudu cikin gida, ilyas na
ganin ta saki kayan ta ruga sai shima ya shige gidan aguje yana ihu dan ya zata abun tsoro
Husnah ta gani shiyasa ta guduwa, dan haka sai shima yabo bayanta dan ya tsira da kansa.
Husnah na zuwa tsakar gida ta tadda Ummanta na shanya kaya a igiya take ta ɓuya tana sauke
ajiyar zuciya.
"Ke lafiya?" Umma tafaÉ—a cike da mamaki, kafin ta bata amsa sai ga ilyas aguje yanayi yana
faɗuwa shima yake fadin.
"Wayyo Umma ɓoyemu." Tare da ƙoƙarin zuwa bayan Umman ya ɓuya, ihu Umma ta saka tana
sallallami kafin tayi ƙarfin halin daka masa tsawa dan ta lura kamar bai da hankali.
"Kai É—an gidan uban waye kai? me tayi maka ne zaka biyota har cikin gidansu? Sallallahu alaihi
wasallam wane irin lalaci zan gani haka ni Bilkisu.?"
Sai alokacin Iliyasmaster ya dawo hayyacinsa yana zarar idanuwa yake kallon Umman haÉ—e da
duƙawa ƙasa yace.
"Umma ina wuni? Nifa wallahi tsoro muka ji." Ya sake zaro mata idanuwansa a kanta. Juyawa
Umma tayi tana maida kallonta ga Husnah tace,
"Waye shi?" Sai da ta É—an turo baki sannan tace,
"Ilyas ne Umma baki ji wata ƙara daga waje ba yanzu? Shine fa naji tsoro na gudu." Taƙare
maganar tana turo baki,
"Huscybaby ba wata ƙara ai ni ne nake ce maki i love You irin yadda indiyawa keyi." Ilyas
master yafaÉ—a cike da dan jin kunyar Umma data saki baki tana kallonsu.
"Ok yadda indiyawa keyi ko? To jiranki." Umma tafaÉ—a tana sakin fuskarta haÉ—e da barin wajen,
ilyas da sai aikawa Husnah da wani irin kallo yakeyi ko kunya kawai ya hango Umma ta nufi
wajensa dauke da taɓarya. Ai aguje ya tashi ya fice daga gidan Umma na biye dashi tana cewa,
"Ashe kai ƙaramin ɗan iskan yaro ne lalatacce, ai da ka tsaya kaga yadda zan dawo maka da
hankalinka tunda na lura ba kada shi."
Sai data kai shi har ƙofar gida sannan ta juyo ta samu kayanta watse a tsakiyar zaure mangiɗa
da manjan duk sun fashe kayan mutane kuma wajen gudu ilyasmaster ya tattakesu, ai kuwa
cike da masifa ta koma cikin gidan tayo kan Husnah tana cewa.
"Ai wallahi baki isa ba maza jeki ki karɓo mani kudin kayan miyana da kuka yimani asara, banda
lalaci husnah me zakiyi da wannan yaron da ko kansa bazai iya karewa ba balle ke, wannan ai
sauro ne kika kwaso mani ba saurayi ba, dan haka na rantse jeki karbo mani kudina dan bazan
dau wannan hasara da takaici ba."
Takoro itama Husnah É—in daga gidan akan taje wajen ilyas master ya biyata kuÉ—in kayan
miyanta ta kuma kasa ta tsare a tsakar gidan, Husnah na lekowa zatayi kanta ta sake korarta
daga cikin gidan...
__________
Yau ta kama Friday Hajja Maimoon Bata fita shago ba sai zuwa da marece saboda yanayin
yinin ranar da bai cika tsawo ba, zaune take tana yiwa Jannat tsifar kai ita kuma tana latsar
waya, kamar ance ta shiga contact sai ga lambar Zain data sakawa _Likita Zain_ ta gani,
murmushi ta saki dan tun ranar ta manta da takarbi lambarsa sai yanzu, É—ago kai tayi ta kalli
Mommy tana cewa.
"Mommy Dan Allah nakira?"
Ba tare da Hajja Maimoon ta damu da wanda zata kira ba ta amsa mata da eh tana cigaba da
tsere mata kan.
Zain na zaune a office É—in Dr Farouq da suka gama ganin patient tare yana ta mining na
Notcoins da yakeyi wanda shine dalilin yawan latsar wayarsa da Abban nasu ya tsana in dai
yana shi kaÉ—ai sai ga kiran Jannat ya shigo.
Kasancewar baƙuwar number ce bai santa ba sai kawai yai minimizing yaci gaba da mining
É—insa da lambobin suka nuno million goma da dubu É—ari tara da hamsin da bakwai a screen É—in
wayar, wanda hakan ke nuni da tabbas yana gab da cimma burin da yake dashi akan wannnan
crypto din na Notcoins shiyasa ya dage sosai haÉ—e da maida hankali dan ya cimma point É—in da
yake buƙata. Sake kira akayi a karo na uku wanda hakan yasa yai minimizing game din ya ɗaga
kiran. Ji yai ta cikin wayar ance .
"Hello likita Zain." Ana dariya alamun mai kiran taji daÉ—in É—agawarsa, shiru yai jin muryar
yarinya ce yana son tuna inda yasan muryar kawai yaji tace,
"Common likita Zain Jannat ce, the Mommy's doughter fa." Ta ƙara masa da sunan da yai mata
yadda zai fahimta. Murmushi Zain ya saki tare da cewa.
"Mommy's doughter kece? Kina lafiya?"
"Lafiya kalau likita ya aiki?"
"Alhamdulillah ya jikin naki kin warke sosai ko?"
"Eh daga ranar nan sake jin ciwo ba asibiti ku nada kyau kun iya kula da marasa lafiya."
"Nagode ina ɗayar yar uwar taki? Itama taji sauƙi ta warke sosai?" Gefen kitchen Jannat ta kalla
da Jauhar ke ciki tana haÉ—a lunch tace,
"Ni kadena kiranta yar uwata bamu da hadi da ita yar aikin mu ce."
"Allah ya baki hakuri tunda bakya so na tambayeki ita to kibata wayar sai naji ya jikinta." Jannat
bata kawo komai a ranta ba ta ƙwalawa Jauhar kira tana turo baki, Hajja Maimoon kuwa tuni ta
gama tsefe mata kan dama ta É—aure ta koma akan system É—inta da tasa Suhana takawo mata
tana tura kayayyakin da take so akawo mata a next odar da tayi, shiyasa bata maida hankali ga
abinda Jannat É—in keyi ba har sai da taji tana cewa.
"Kiyi magana yana jinki kada ki tabawa Mommyna waya."
Dai-dai lokacin Irfaan ya shigo palourn da saƙo Alhaji Sha'aban Sada yasa ya kawo, daga Hajja
Maimoon É—in har Irfaan zuba idanuwa sukayi cike da mamaki suna jiran suji muryar wanda
Jannat ke cewa Jauhar tayi magana dashi da tasa a handsfree, cikin kulawa Zain daya ciro
wayar yana kallo yaga ana online har lokacin yace.
"Hello ƙawata ya jikin naki kin warke ko azo ayi maki allura."
Ya yi maganar cike da barkwanci kamar yadda ya saba ga marasa lafiyan da yake kula dasu.
Jauhar na jin haka ta zaro idanuwa tana ɗan ja da baya, haka Irfaan cikin ɓacin rai yake kallon
Jauhar ɗin yayin da Hajja Maimoon itama ta zaro idanuwa tare da miƙewa daga wajen zamanta
cike da wani matsanancin ɓacin rai daya bayyana ƙarara akan fuskarta ta nufo wajan...
_LAST FREE PAGES_
_*Hmmm..! Tirkashi! Yanzu fa labarin zai fara*_
_*Wacece Hajja Maimoon?*_
_*Wace alaƙa ce tsakaninta da Jauhar?*_
_*Shin ina iyayen Jauhar suke?*_
_*Menene dalilin da yasa Hajja Maimoon ke azabtar da Jauhar har take iƙirarin dole akayi mata
tare da tirsasata zama da ita É—in?*_
_*Shin Jauhar zata samu ƴantuwa daga ƙangi bautar da takeyi ko kuwa?*_
_*Ina labarin Irfaan? Shin zai iya zamema Jauhar bango ko kuwa?*_
_*Menene matsayin Zain a cikin labarin nan?*_
_*Ilyasmaster zai auri Husnah ko kuwa? Meye matsayinsa a labarin?*_
_*Shin ina dangin su Hajja Maimoon suke? Meyasa basa zuwa inda take ne? Ko ita Hajja
Maimoon É—in bata zuwa inda suke?*_
_*A ina suka haÉ—u da Alhaji Sha'aban, wace irin rawa yake shirin takawa acikin labarin nan?*_
*Abubuwa da yawa suna cikin labarin nan wanda zasu baku mamaki da al'ajabi. Mu kanmu
munyi iya kokarin mu wajan tsifewa da kuma tacewa dan samun darasi a cikinsa. Bamuyi
labarin nan da ka ba sai da mukayi bincike muma muka samu tarin ilimi a cikinsa. Karki bari
karanta labarin GONAR SHARRI ya wuceki. Daku muke ko muce dakai muke mai son ƙara
samun ilimi. GONAR SHARRI ya cika sunan nasa idan har kuka karanta daga farko har
karshe*í ½í±Œ
*Domin samun duka waÉ—annan amsoshin kutaho muyi tafiyar atare ku masu karatu. Gamai son
cigaban wannan littafin zai biya ₦500 kacal ta wannan account*
BANK ACCOUNT
8098456130
Opay digital services,
shedar biya ta wannan number 07040402435 ko kuma a kira kai tsaye dan karin bayani, idan
muka kammala rubuta complete document ɗin littafin zai koma ₦1000 in Sha Allah*
Mungode.
#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce
#Ƴan Tagwaye