Showing 21001 words to 24000 words out of 47407 words
Chapter 8 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
ya shiga duddubata ya yana sake cigaba da
tsokanarta ita kuma tana yiwa Mommy ƙorafi da taɓara, a haka likita yazo Zain ya gaggabatar
masa da abubuwan da ya yi wanda aka sakawa kowa cikin files É—insa dan shine on duty yau a
emergency É—in.
Yaso a fara duba Jauhar saboda tafi Jannat buƙatar kulawa amma yadda su Mommy suka tsare
komai ya sanya sai da aka kira su Jannat likitan ya yi mata duk abinda ya kamata kafin aka
kirawo Jauhar, tana isowa likitan dake rubuce-rubuce akan folder din tata ya É—ago kai don ganin
kowaye saboda yadda yaji tsamin kayan dake jikinta ya cika musu hanci. Irfaan kuwa gabaki
É—aya ya fara jin haushin Zain ganin yadda yake ta yi musu wani irin faran-faran duk da ya lura
da cewa hakan yake yiwa mararsa lafiyan dake wajen gabaɗaya, wanda cikin ƙanƙanin lokaci
yaga sunyi wani irin sabo shida Jannat ta yadda komai zai ce sai yaji yace mata 'Mommy's
daughter' Ita kuma yaji tace 'likita'. basu wani jima ba aka gama duba Jauhar da Jannat, inda
Doctor Habu ya sanar dasu cewa a kula da Jauhar sosai dan a wannan stage É—in tafi Jannat
buƙatar taimako da kuma kulawarsu, ganinta a yanayi irin na ƴan aiki yasa shi sake cewa idan
baza'a iya kula da ita ba to a kaita wajan iyayenta zama tafi samun kulawa a wajan su sosai. Da
Jauhar taji abinda Doctor Habu yace ba ƙaramin daɗi taji ba dan ko babu komai tasan zata huta
da wannan masifar ta cikin gidan Alhaji Sha'aban Sada. Nan likitan ya miƙo takardun
magungunan da za'a siya masu daya rubuta Uncle Irfaan ya karɓa suka fice, Har sun kusa
shiga mota Jannat ta kasa yin haƙuri tasan idan har suka bar asibitin nan zai yi wahala ta sake
ganin Zain gashi sosai ya burgeta lokaci É—aya saboda yadda yayita kanta da wasa tana dariya.
Hannunta ta zare daga cikin na Mommy tace.
"Mommy please aron wayarki." Hajja Maimoon ta miƙa mata, cikin sauri Jannat ta juya tare da
shigewa reciption tana wurga ido dan gano inda zata ganshi. Tsaye ta hangoshi gaban wata
mata yana taɓa goshin yarinyar dake kan cinyar matar da alamar dubata yakeyi. Waya kawai
yaga ana miƙo masa, kallan wayar ya yi kafin a hankali ya ɗora idanunsa akan wacce take miƙa
masa ɗin. Murmushi yayi tare da miƙewa sosai yana kallon wayar yake faɗin.
"Mommy's daughter yae za'a yi? Duba maki wayr zanyi itama bata lafiya?" Dariya Jannat tayi
kafin ta turo baki cike da salon rigima tace,
"Dama banda mutane har wayoyi kana iya dubasu in basa da lafiya?"
"Ban taɓa ba amma da alama rigimar Mommy's doughter zatasa nafara yau."
"Ni dai a'a i just need Your phone number please." Zaro idanuwa yai cike da mamakin rigimar
Jannat yana naɗe hannayensa a kirji haɗe da lasar lips ɗinsa na ƙasa ba tare daya karbi wayar
ba. Jannat ta sake shagwaɓewa kamar zatai kuka tace.
"Please take it mana kasa mani kada uncle yai mun fada." Jin abinda tafaÉ—a shima ga patient
na jiransa ya sashi dan duƙowa saiti ita yana cewa,
"Wayar kice?".
"No ta Mommyna ce." Zain ya sake ware ido akaro na biyu yana miƙewa tsaye da ƙafafuwansa
yake cewa.
"Toh ba ruwa na haka kawai Daddyn ki yaga sunan namiji a ciki, da alama so kike nayi kwanan
police station Ko?" Sai da ta kuma turo baki wanda yasa Zain kai hannunsa kamar zai janyo
mata shi sai kuma ya karkaÉ—a mata yatsunsa guda biyu yana cewa.
"Ba ruwa na." Haɗe da ƙoƙarin juyawa.
"Please dan Allah dan annabi kasaka min, kaga idan bani da lafiya kawai kiranka za'a yi aji ko
kana asibitin." Lumshe ido ya yi yana jin girman Allah da ta roƙeshi ya tsaya masa a wuya, ya
karɓi wayar tare da saka mata dama already taji yadda abokan aikinsa suke ta kiransa dan
haka bata tambayi sunan ba ta juya tana saving fuskarta kunshe da farin ciki ba zaka taɓa cewa
ita aka kawo ranga-ranga ba. Babu wanda ta kula kawai ta shiga motar ta zauna, wannan karon
a can wajan glass suka bar Jauhar a cewar Suhalai iska zata fi É—aukar warin da Jauhar É—in keyi
tana fitarwa waje ba sai sun shaƙeta ba.
"Ke kuma me kika koma yi ciki?" Irfaan ya jehowa Jannat tambayar ba tare da ya juya ya kalleta
ba hankalinsa yana wajan tuƙi. Jannat dake karewa sunan Zain da ta gama saving kallo tayi
murmushi kawai ba tare da ta bawa Irfaan amsa ba dan ita kanta ba ta san me zatace ba, kuma
bata san dalilin da yasa taji nurse É—in ya shiga ranta da wuri haka ba. Jauhar kuwa duk ta matsu
suje gida zama tare da su a wannan yanayin yana sake É—aga mata hankali saboda fargabar
maganganun da suke jefa mata ƙasa-ƙasa dan ma Suhana bata cewa komai amma yadda take
kauda kai zaka san cewa tsamin jikin Jauhar ɗin yana damunta. Suna zuwa kuwa ta ɓalle ƙofar
ta fito tare da rakuɓewa tana jiran su wuce ciki sannan tabi bayan su.
Hannun Jannat Hajja Maimoon ta kama ba tare data kalli gefen da Jauhar take ba tana jin wani
irin jiri na addabarta. Kallon su ta shiga yi tana jin kuka na shirin zuwa mata, ina ma ace itama
za'a kaita inda za'a ji ƙanta a kula da ita a kuma yi jinyarta cikin kulawa. Sanin bata da wannan
gatan ne yasa ta fara ɗaga ƙafa jin Suhana tana cewa tazo su shiga ciki. Har ta juya taji Irfaan
ya kirata, ta juyo a hankali ba tare da ta kalleshi ba dan ba kaÉ—an ba takejin kunyarsa.
"Zanje na kawo miki magunguna sai ki samu kisha kinji ko?" Jauhar ta É—aga kai alamar to
sannan ta buÉ—e baki da kyar tace.
"Nagode Uncle." Tausayinta ya sake shigarsa yace.
"Ki samu ki kwanta saboda jininki ya dawo dai-dai. Please ki cire komai a ranki kiyi addu'a kinji
ko?." Kanta kawai ta É—aga amma ita bata ma san wace irin addu'a zatayi ba saboda ba wani
koyar da ita aka yi ba ballantana ta dinga yiwa kanta. So yake ya tambayeta shin bata da
bireziya ne da bata sakawa? Amma sai ya kasa saboda girman maganar gashi kuma baya son
girmansa ya ɓare a wajan ta. Ko a hospital yaso yiwa Suhana maganar amma ya kasa. Har ta
shiga ciki bai É—auke ido akanta ba, yana son ya taimakawa Jauhar kota wani irin yanayi ne koda
kuwa Hajja Maimoon zatayi masa sharrin da har ya koma ga Allah ba zai yi mutunci a idanun
duniya ba. Yana fita daga gidan kai tsaye gidan su ya nufa ya É—akko atm card É—insa ya fito,
pharmacy ya wuce already Jannat tun a hospital aka siya mata nata magungunan, Jauhar ce
Hajja Maimoon taki siyawa shi kuma bai fito da kuÉ—i ba. Yana siyo magungunan ya biya ta wani
boutique ya siyo mata bra wacce bashi da masaniyar zatayi mata dai-dai ko zatayi mata yawa,
kawai ya siyo mata ne gwara tasa akan ta dinga yawo a haka tana saka mutane cikin yanayin
da sai sunyi shahada zasu iya rike kansu. Ya siya mata harda su pant da skirt underwear sai
wasu riga da skirt kala É—aya dan bai san awonta ba karya jidar mata kaya a samu matsala.
******
Jauhar na shiga cikin parlorn ta tarar Hajja Maimoon tana tsaye tana jiran shigowarta, tunda ta
hangota taji kirjinta yana bugawa tasan kawai wani bala'in kecin matar tunda a iya saninta babu
abinda tayi wanda zai sa ayi mata irin wannan jiran. Suhaila da Jannat suna kwance akan soofa
Suhana ta shiga cikin É—aki da alama ko tsayawa batayi a parlorn ba. Kanta ta sake sunkuyarwa
tana jiran taji da wane bala'in za'a tare ita, cikin zuciyarta tace mutum bashi da lafiya amma
matar nan ba zata ɗaga mata ƙafa ba taji da abinda yake damunta. Abinda yake bata haushi
kuwa tamkar bata santa ba batasan wacece ita ba da ta wofintar da al'amarinta ta fifita wasu
akanta wanda duk matsayin su a wajanta ai basu kaita ba, kuma tare aka gansu bare ace a
gidan ta tarar da ita a matsayin mai aiki.
"Wato saboda nayi maganar ki fito min da gold É—ina shine dan bakin munafunci kika fara rashin
lafiyar karya ko Jauhar? Toh bari kiji na gaya miki ko asibiti ne gabaki É—aya a jikinki sai kin
amayo min da abubuwana dan ba zakici banza ba. A iya zamana dake tun lokacin da aka liƙa
min ke kika zame min jaraba na taɓa nuna miki yadda ake sata?" Jauhar ta shiga girgiza kai
alamar a'a, hakan ya sake tunzura Hajja Maimoon ta ƙarasa inda take tsaye tare da shaƙo mata
wuya tana cewa.
"Dan ubanki da ka nake miki magana da zaki dinga amsa min da kanki?" Jauhar da taji matsar
tana shirin kaita ga mutuwa yasa ta fara ƙoƙarin kwacewa, jikinta babu karfi hakan yasa ta kasa
har sai da Suhana ta taho da gudu wacce fitowarta kenan daga cikin É—aki ta hango su. Da kyar
ta iya kwace Jauhar daga hannun Mommyn tasu wacce takejin ko mutuwa Jauhar tayi ba zatayi
nadama ko da na sani ba koda kuwa ace zata mutu a gidan gyaran hali ne.
"Na kusa sallamaki wallahi Jauhar, da kaina zanje wajan waɗanda suka liƙa minke su san
yadda zasu yi dake ko kuwa aure ne suyi miki da ko uban waye nima na huta da kallonki da
nakeyi kina manne dani ko na dena sakaki a cikin idanuwa na." Jauhar dake rakube a bayan
Suhana tana jin duk kalaman da Hajja Maimoon ke gaya mata, ita da za'a kaita É—in da taji daÉ—i
koda auran ne ayi mata ko zata samu Æ´ancin kanta, amma zama tare da matar nan ba alkairi
bane a tare da ita.
"Mommy dan Allah ki barta bata da lafiya fa." Suhana ta faÉ—a kamar zata yi kuka. Duk suka
kalleta baki buÉ—e, bata damu da irin kallonta da sukeyi ba burinta kawai ta aikata abinda zai sa
mahaifiyarsu ta samu sassauci a makwancin ta kamar yadda Uncle Irfaan ya tunatar da ita.
"Zoki wuce ki shirya mana breakfast." Cewar Hajja Maimoon tana dakawa Jauhar É—in wata
gigitacciyar tsawa. Jiki na rawa hankali a tashi zuciya a cunkushe Jauhar ta nufi kitchen tana
share hawayen da yake yawo a kan fuskarta........
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
   (Batch C)
NA
*BILLY S FARI*í ½í²Ž
Da
*HAJJA CE*í ½í±ˆ
Areewabooks@billysfari
Page 9..
Koda ta shiga kitchen É—in rasa abinyi tayi dan gabaki É—aya komai na cikin kwakwalwarta
tsayawa ya yi cak na wucin gadi. Suhana ce ta shigo kitchen É—in ita sai yanzu take lura da irin
matsin da ake yiwa Jauhar a cikin gidan wanda tasan da mahaifiyarsu tana raye tabbas ba zata
bari su dinga yin abunda suke yiwa yarinyar ba. A bayanta ta tsaya tare da yi mata magana
cewa.
"Jauhar kije É—aki kiyi wanka mana, bari na fara tayaki kafin ki dawo." Jauhar ta girgiza kai dan
ba zata iya fita ba Mommy ta ganta tasan sai ta kusan kashe ta musamman idan tace mata
wanka zatayi.
"Idan na gama sai naje nayi." Cewar Jauhar É—in tana sake share hawayen fuskarta.
"A'a kije kiyi saboda kayan jikin ki ma suna buƙatar ki sauya su." Ganin yadda Suhanar ke yi
mata magana cike da jin ƙai ita duk tsoro ma sai ya kamata, tun a asibiti ta lura da sauyi a
wajanta sosai. Tsoro take karta saki jiki da ita daga baya tayi mata sharrin da zata kasa fitar da
kanta tunda ba haka ta saba ganin tana yi mata ba tunda tazo gidan nan. Amma ganin ta dage
akan sai taje tayi wankan yasa taje wajan sink tasa hannunta ta tsiyayo liquid soap ta juya zata
fita Suhana da ke kallanta da mamaki tace,
"Meza kiyi da shi?" Kanta a ƙasa tace,
"Zanje ne na É—an goga a jikina ne."
"You mean dashi zaki wankan?" Suhana tafaÉ—a cikin tashin hankali tunda yasan ba na wanka
bane har tana turo idanuwa waje, Jauhar ta É—an dago ta kalli yanayin fuska da Suhana ta koma
jiki ba kwari take faÉ—in.
"Dan Allah kiyi haƙuri shi nake ɗan ɗiba na goga a jikina idan zanyi wanka, kingani ba da yawa
na tsiyaya ba." Tayi maganar tana buÉ—ewa Suhana hannun alamar ta duba ta gani dan a
tunaninta ran Suhana ɗin ya ɓaci zata ce tayi masu sata. Karo na farko da Suhana taji mugun
tausayinta ganin da abinda zatayi wanka, su suna can sabulu sai sun zaɓa kuma duk masu
tsada amma ita Jauhar tana nan ta rasa yadda zatayi tana ta raɓe-raɓe da abinda zata tsabtace
jikinta ko tsoron yayi mata illa bata yi
"Ina zuwa." Cewar Suhana tana ficewa daga kitchen É—in. Jauhar tabi ta da kallo, bata san me
yasa tace tana zuwa ba dan haka da sauri taje ta É—auki sosan wanke-wanke ta juye soap É—in a
jiki tare da zuwa tayi saurin É—akko kettle taje ta tara ruwa a sink ta É—ora akan gas. Tea spieces
ta zuba sannan tayi saurin É—akko roba mai É—an faÉ—i ta É—ebo Irish a ciki tana ferewa, zuciyarta
bugawa kawai takeyi duk a zaton ta Suhana taje ne ta sanar da Hajja Maimoon cewa da abun
wanke-wanken su take wanka bayan kuma Hajja Maimoon É—in taja mata kunne akan cewa
karta sake ta ɗauki abun su idan har ba bata aka yi ba. Suhana ta dawo tare da miƙa mata
sabulu sabo dal a cikin kwalinsa tace taje tayi wankan bari ta ƙarasa mata aikin. Baki a wangale
Jauhar ke kallonta ta kasa karɓar sabulun saboda tsabar mamaki har sai da Suhana ta riko
hannunta ta saka mata sabulun aciki.
"Angode." Jauhar ta faÉ—a hawaye yana zuba a cikin idanunta haÉ—e dasa hannu tana shafewa.
"Ba komai jeki yo wankan ki dawo."
Fitowa Jauhar tayi ta shige É—akinta, jiki babu karfi ta cire kayan ta nufi banÉ—akin dake cikin É—akin
nata. Ba ƙaramin daɗi taji ba yau tana wankan ƙamshin sabulun yana sa taji kamar ta lashe
jikinta. Tana fitowa ta É—auki yagalgalallan pant É—inta wanda ita kanta ba zata ce ga tsawon
shekarunsa ba duk ya buɗe ya tale ya yi baki ya dafe robar ta buɗe sai dai ta ƙulleshi ta gefen
kugunta ta sanya shi yadda zai zauna mata.
Irfaan ne ya shigo parlorn da sallamarsa babu kowa duk sun koma É—akunan su tun É—azu. Kai
tsaye ya nufi É—akinta dan yasan yadda bata da lafiyar nan zai iya kasancewa tana ciki a
kwance. Sai da ya yi knocking sannan ya murÉ—a handle É—in ya shiga a nan ya tarar da ita tana
saka kaya.
"Sorry Jauhar." Ya faɗa yana juya bayansa tare da miƙa mata ledar hannunsa yana cewa.
"Ga kaya nan ki saka karki maida na jikin ki, sannan da magani a ciki idan kinci abinci sai
kisha." Jauhar mamaki ya kamata ta isa inda yake da kyar tasa hannu ta karɓi ledar, bai jira me
zata ce ba yabar É—akin daidai lokacin da Mommy ta fito ganinsa yana fitowa daga É—akin Jauhar
yasa ta ware idanunta tare da kafeshi da idanun tambaya mai cike da zargi, hakan da Irfaan ya
gani ne yasa zuciyarsa ta É—an yi rawa sai dai ya karfafa kansa tunda yasan babu abinda ya yi a
cikin É—akin saboda yana ganin kamar akwai wata manufa a kallon da Hajja Maimoon keyi masa
ya tsuke fuska yana ƙoƙarin raba ta gefenta ya wuce.
"Lafiya naga ka fito daga É—akin Jauhar?" Tayi maganar tana haÉ—e fuska.
"Na kai mata maganin da likita ya rubuta shine na siyo."
"Ohh good! Toh Irfaan daga yau daga yanzun ina so ka fita daga rayuwar Jauhar babu ruwanka
da ita bana so." Duk da Irfaan besan me yasa Hajja Maimoon É—in tafaÉ—i haka ba sai da maganar
ta dakar masa zuciya dan baisan ya take son rayuwar Jauhar É—in tazama ba, Jauhar kuwa yana
bata ledar bayan ya fita tazaro duka abubuwan dake ciki, ganin irin kayan yasa ta rintsa ido
sunyi matukar kyau sai dai tasan bai zama lallai abar mata ba dan ansha bata kaya amma Hajja
Maimoon sai ta kwace. Murmushi tayi lokacin da ta zaro bra ɗin ga wata kunya da ta lulluɓeta.
Cike da jin nauyi tamkar ance mata Irfaan É—in yana wajan. Da sauri ta rintsa ido lokacin da ta
gama sakawa taga fitulun nata sun yi kyau a ciki duk kuwa da cewa ba wai manya bane suna
kan fitowa. Duk kunya ce ta kamata a haka ta kammala saka komai sai ta dinga jin tamkar ba
ita ba, zata so ganin yadda tayi a cikin kayan dan kuwa babu madubi a cikin É—akin.