Showing 39001 words to 42000 words out of 47407 words

Chapter 14 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

3172

cewa.

"Me kike nufi kenan? ban isa nace ga abinda za'a yi ba kiyi ne ko?" Cikin rashin nuna damuwa
da sauyawar da fuskarsa tayi Hajja Maimoon ta kawar da fuska tana sake haÉ—e rai.

"Kizo ki wuce muje bana san kuma yin magana akan wannan." Zuciyar Hajja Maimoon ta shiga
yin zafi tana wani irin tururi ji takeyi tamkar ana ƙara garwashi. Idan har Jauhar tayi kwanan
farin ciki a gidan nan tabbas ba sunanta Maimuna ba dan kuwa abu ne da bazai yiwu ba indai
har tana cikin gidan. Yayi taku biyu yaji alamar bata biyo shi ba, hakan yasa shi juyowa ya ganta
tsaye ta kafe idanunta akan ɗakin da Jauhar ke ciki hannayenta naɗe a ƙirji. Ransa ya sake
ɓaci ya hango tsantsar raina shi da Maimoon tayi wanda besan ya kai har haka ba.

"Ya yi kyau." Haka kawai Alhaji Sha'aban Sada ya faÉ—a kawai ya wuce bai bi ta kanta ba.

Ganin ya wuce ita kuma ta nufi É—akin Jauhar ba tare data fasa yin abinda zuciyarta take umartar
ta ba. Tana shiga ta tarar da Jauhar É—in kwance ta saki baki tana ta sharara bacci dan tun
lokacin da Alhaji Sha'aban ya umarce ta da taje ta kwanta tana shiga É—akin kwanciya tayi dan
ba ƙaramin bacci ne ke damunta ba, dalilin da yasa ko kiran Hajja Maimoon bata jiyo ba duk
kuwa da cewa ko bacci takeyi sai ta dinga jin kiran matar nan. Kallanta kawai Hajja Maimoon
keyi cike da tsabar mamaki, abubuwa da yawa suka sanyata ta yi cak wajan kasa tashin Jauhar
É—in. Kayan jikinta, da kuma yadda take ta sauke minshari da alama baccin ya yi masifar yi mata
daÉ—i. Toilet É—in cikin É—akin ta shiga da niyar É—ebe ruwa ta watsa mata wani irin hamami ya doki
hancin Hajja Maimoon tayo baya tana jin tamkar zatayi amai. Cikin sauri ta fito daga É—akin, kai
tsaye ta nufi kitchen ta buÉ—e fridge. Ruwa ta ciro gora guda a freezer ta juye shi cikin wata roba
ta sake É—akko wani ta juyo sannan ta nufi É—akin Jauhar kamar zata tashi sama dan sauri. Tana
zuwa ta saita robar a saitin fuskar Jauhar kawai ta sheƙa mata ruwan sanyin nan duka.

"Wayyo Allah na na shiga uku na lalace." Jauhar ta faÉ—a a gigice tana mikewa tare da kai hannu
tana neman abinda zai ceceta. Kafin ta gama dawowa daga cikin tashin hankalin data shiga ciki
ne taji an shaƙota ana jijjigawa, Jauhar ta dinga ihu tana neman taimako can taji Hajja Maimoon
É—in na cewa.
"Ai dama nace ke kika É—auke zinariya ta munafuka kika siyar, idan ba haka ba a gidan uban
waye kika samu kudin siyar rigar nan?" Jin tambayar da takeyi mata ne yasa Jauhar da kyar ta
iya janyo kalamai dan har lokacin Hajja Maimoon bata sakar mata wuyan ba tace.

"Uncle Ir.. Ir.. Faan.. ne.. Ya bani."

"Ohhhh! Irfaan ne ya sake siya miki ko? Dama kayan da ya siya a shago na munafikin ke ya
siyawa da kuÉ—in zinariyata da kika bashi ya sayar?" Kai Jauhar ta shiga girgizawa alamun a'a
dan har lokacin Hajja Maimoon bata iya sakinta ba. " Idan basu bane Jauhar to ki gaya min
uban me kike yiwa yaron can yake yi miki wannan hidimar ko kuma nayi takakkiya muje wajan
su Baffa wallahi ayi min iyaka dake dan ba zakisa bakin tarihin abun kunyar da ubanki ya yi ba
ya maimatu acikin gidana ba. Dole ki gaya min uban me yake miki har yake jin daÉ—i yana siyo
miki kayan da ni zan iya sakawa ko kuma su Jannat?" Tana kaiwa nan ta saketa tana jiran jin
abinda Jauhar É—in zata faÉ—a. Ita kuma banda tari babu abinda takeyi saboda wuyan ta da take
jin kamar numfashinta zai tsaya. Gefe guda kuma kalaman Hajja Maimoon ne yake mata yawo
na cewa zata kaita wajan su Baffa, toh kodai tace itace ta É—auka? Tayi amfani da damar a kaita
wajan su tace ba zata biyo ta ba shikenan ta kubuta daga hannun jarababbiyar matar nan.

"Zaki gaya min ko sai na kasheki a cikin É—akin nan?" Hajja Maimoon ta faÉ—a cikin tsawa.

"Hajiya wallahi... Wallahi shine... Shine.. Ya..." Cikin zaro ido tun kafin Jauhar ɗin ta ƙarasa yin
magana tace.

"Ya yi me?" A gigice Jauhar tace,

"Ya bani."

"Ohhh! kina nufin dai ba kudin zinari na ne da kika bashi ba?"

"Eh wallahi Hajiya ban É—auka miki ba na rantse da Allah." Hannu takai ta fizgo Jauhar da karfi ta
haÉ—e da jikin ginin dakin tana cewa.

"Toh taɓa miki jiki yakeyi ko?" Jauhar taji maganar a wani iri, cikin sauri tace.

"A'a Hajiya."

"Zaki gaya min ko sai na yankaki dan ubanki?"

"Wallahi Hajiya kinji na rantse miki Alkur'an baya taɓa ni, kawai yana bani kayan yake tafiya
wallahi gaskiya nake gaya miki." Jin hakan yasa Hajja Maimoon ta taso ƙeyarta suka fito daga
É—akin tana cewa.

"Toh idan ma kin bari yana miki wani abun ke kika sani ba damuwata bace wallahi, sannan kina
gama gyara wajan nan kije ki cire kayan nan ki ajiye min su zanzo na É—auka ai ba kalarki bace
ba dan sunfi karfin ubanki ma bare kuma ke banza a banza."

Ta ƙarasa maganar tana tura ta wajan dining area ɗin da karfi sannan ta wuce ɗakinta tana
sakin tsaki da ƙarfi. Jauhar kuwa tana hawaye dafe da ƙasa dan turewar da aka yi mata sai da
ya kaita ƙasan taels sauran kaɗan ta fasa goshi. Tana kuka tana kwashe kayan takai kitchen, ta
rasa me yasa Hajja Maimoon ta zaɓi yin rayuwa da ita tun ƙanƙanuwa dan ta bautar da ita bisa
wasu dalilai nata da batasan koma meye ba.

Tsab ta gyara gurin tayi wanke-wanke ta ajiye komai inda ya dace sannan ta koma É—akin ta.
Jikinta ta kalla yadda rigar ta amsheta duk da cewar ta É—an yi mata yawa amma ba wani sosai
ba. Kuka taji yazo mata ganin an rabata dasu akaro na biyu. kenan ba damar ta saka É—ayar
rigar wacce ke cikin ledar duk da yadda ta burgeta! kenan har handbag É—in da takalman duka
Shikenan an rabata dasu? Bata san lokacin da ta durƙushe a kan carpet ɗin baccinta tare da
fashewa da wani kukan mai bala'in taɓa zuciya.
________
Hajja Maimoon kuwa tana komawa É—aki wardrobe ta nufa ta shiga nemo kayan da zata saka.
Wata orange É—in sleeping dress ta janyo sabuwa dal bata daÉ—e da siyan su ba, ta feshe su da
turaruka masu masifar ƙamshi sannan ta zare kayan jikinta tasa na baccin. Wajan mirror ta nufa
tana kallan fuskarta ta saki murmushi tuna shirin da tayiwa Habibyn nata na nuna godiya abisa
farin cikin da ya sanyata. Idan ta tuna cinikin da tayi a yau kaÉ—ai sai taji wani irin farin ciki yana
mamaye ta. Jan baki ta goga tabi jikin mata da khumras masu daÉ—i sannan ta fito ta nufi É—akin
Alhaji Sha'aban Sada. Cike da nutsuwa tasa hannu akan handle É—in ta murÉ—a ta shiga. Kwance

ta hango shi sai dai tasha mamaki ganin ko kallan ƙofar baiyi ba bare tasa ran zai miƙo mata
hannunsa kamar yadda yake yi mata idan tazo.

Kan bed É—in ta nufa ta hau still bai ko kalleta ba bare ya nuna yasan tazo ba. Mamaki ya kamata
ta kwanta sai taga ya juya mata baya. Shi kuwa ransa ne ya ɓaci ganin yace tayi abu taki duk
da cewa ba wai yau ne na farko ba, sai dai yau abin yafi bashi haushi saboda yana ganin kamar
so takeyi ta nuna masa tafi karfinsa bai isa da gidansa ba. Kasa yi masa magana tayi dan tana
jin wata irin izzah gani take idan har itama ta kulashi to ta ɓarar da ajinta matsayin ta na ƴa
mace. Shi kuma kamar jira yake dama ta shigo kawai bacci ya É—auke shi ya barta cike da
masifaffan mamaki. Ƙeyarsa kawai ta zubawa ido tama rasa uban me takeyi a wajan, ga wata
irin kulawa da take buƙatar ya bata bawai na kwanciyar aure ba, a'a tana buƙatar ya rungumeta
yana bata labari ko kuma nuna mata yadda take da muhimmanci a rayuwarsa kamar yadda ya
saba akoda yaushe, hakan zai bata damar sake yimasa godiya da nuna masa jin dadin abinda
ya yi mata yau na sake É—aga darajarta acikin yan uwanta mata.

"Kenan hakan bazai faru ba?" Ta tambayi kanta.

"To me nayi masa?" Ta sake jefa ma kanta tambaya a karo na biyu tana jin zuciyarta tamkar ta
fashe Dan tsabar takaici.

"Akan maganar É—azu ta Jauhar shine yayi fushi dake." Taji zuciyarta tana sanar da ita. Cije lips
tayi tana sake jin wani irin zafin Jauhar, lallai ma akanta ne mijinta yau ya juya mata baya? Allah
ya kaimu gobe mai raba ni da ita sai Allah, Hajja Maimoon tafaÉ—a cikin zuciya tana juya
kwanciyarta tare da kashe fitilar dakin ta kunna masu bed lamp...

#A heart touching story
#Gonar Sharri
#Billy s Fari
#Hajja ce
#Ƴan Tagwaye

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*

*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce

*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu

*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch

*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.

*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso

*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000

*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130

*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

NA

*BILLY S FARI*💎
Da
*HAJJA CE*👈
Arewabook@billysfari

Page 15..

Gabaki É—aya bacci ya kauracewa Hajja Maimoon, yadda Ya Habiby É—inta yai iskar kare da ita
yafi komai bata haushi. Sai kusan tsakiyar dare ta samu da kyar tayi baccin shima cike da
mafarkan Alhaji Sha'aban É—in wai tana masa magana yana shareta, sanin wacece ita da take jin

duk duniya babu É—a namiji da ya isa ya juya ta saboda tana ji da kyau tana kuma alfahari da
wayewar da take da ita yasa ta basar bata É—auki mafarkin abakin komai ba. Koda aka kira
assalatu yasha mamaki da yaga still tana cikin É—akin dan bai yi tsammanin kwananta a tare
dashi ba duk da sanin muhimmancin da take bashi wasu lokutan. Toilet ya shiga yayo alwala,
praymat ya shimfiÉ—a yayi nafila sannan ya zauna yaci gaba da tasbihi har aka kira asubahi ya
fita zuwa masallaci. Yana dawowa har zai wuce sashensa yaji kamar shesshekar kuka. Dama
da zai fita yaji hakan sai ya dauka kawai kunnensa ne. Ta inda yake jiyo alamun kukan ya dinga
bi, ga mamakinsa sai yaga yana nufar É—akin Jauhar. Da yake ba rufewa takeyi ba hakan ya
bashi damar ɗaga labulen ya leƙa idanunsa suka sauka akanta tana ta kuka.

"Subahanallahi Jauhar lafiya?" Ya tambaya yana kallonta bayan ya ƙarasa ciki. Kamar wacce
take jiran a kulata kawai ta sake sakin wani kukan gabaki É—aya.

"Meyake damunki?"

"Wajan Babana nake so." Tausayinta ya sake kamashi, yana sake kallanta yake faÉ—in.

"Zanso hakan ta kasance Jauhar, shin kinsan gidan Baban naki?" Ta girgiza masa kai a hankali
tamkar wata marar laka a jiki.

"Toh yanzu ya kenan tunda baki sani ba? Kiyi hakuri kinji zuwa gari ya waye sai muji yadda za'a
yi."

"Za'a yi me Alhaji?" Sukaji muryar Hajja Maimoon daga bayansu tsaye tafaÉ—a cikin isa da
gadara. Jauhar da tun shigowarsa tayi masa kallo ɗaya ta maida kanta cikin ƙafafuwanta tana
jin muryar Hajja Maimoon bata san lokacin da ta ganta a tsaye ba. Rawa jikinta ya hau yi tana
neman ɓoyewa a bayansa. Cike da dakewa yace,
"Gidan iyayenta zata koma, in sha Allah gobe zan bada kuÉ—in mai a maida ita in yaso ma samu
wata mai aikin." Wani malalacin kallo Maimoon ta sakarwa Jauhar É—in. A fili kuma taja numfashi
tare da yin taku uku tana naɗe hannayenta a ƙirji take cewa

"Ka tambayeta tasansu ko tasan inda suke? Duk wani abu da kake gani ina yimata wallahi
gatanta ta nakeyi akansu, dan haka kayi haƙuri Alhaji babu inda Jauhar zataje dan bata da
gurin zuwa wanda za'a riƙe ta kamar yadda nakeyi mata. Idan kuma tasan ina zata samu gidan
uban nata sai ta faɗa maka." Hajja Maimoon taƙare zancen tana kafewasa da idanuwa. Ganin
ya ɗauke idanuwansa ya mayar akan Jauhar ya sata sakin wani malalacin murmushi  kafin ta
haÉ—e fuska tana kallon Jauhar É—in tace,

"Bari kiji in gaya miki Jauhar, zamanki tare da ni shine rufin asirinki dan Uban naki da kike kira
É—an iska ne, É—an shaye-shaye ne kuma mahaukaci da bashi da wata daraja, shi yasa ma ba
wanda yasan duniyar da ya shiga ya janyo ƙaddara ta tilasta ni rayuwa dake waje ɗaya. Dan
haka ni É—in da kika raina nice rufin asirinki kuma mafi girman matsayi tunda har na amince na

riƙe ki tun yarintarki har girmanki."

"Amma kuma ina mahaifiyarta take? Sai a kai mata ita in har shi ba'a san inda yake ba." Alhaji
Sha'aban Sada ya tambaya dan yafi son yaga yarinyar tabar gidan ta samu inda za'a kula da
ita.

"Ta mutu." Hajja Maimoon ta faÉ—a babu alamar tausayawa. Jauhar najin haka ta fashe da kuka
tana faÉ—in.

"Wayyo Allah wayyo Mommy na shiga uku zan mutu wayyo Allah...." Jauhar ta faÉ—a tana
faɗuwa ƙasa ta shiga yin birgima kamar wata ƴar goye. Ganin hakan yasake ƙular da Maimoon
ta nufeta zata janyota yai saurin tarewa yana masifa.

"Meye haka ne Maimoon?!" Jin kalar tsawar da yai mata sai da ta firgita, kallansa take kamar
idanunta zasu fita taji yace.

"Karki kuskura ki doketa ina wajan nan, yarinyar nan ko jaka ce kika siyo a kasuwa ya dace ki
kyautata mata, ballantana kuma amana ce ita a gurinki bai dace kina treeting nata haka ba."

Tsabar gaskiyar da ta yiwa Hajja Maimoon yawa juyawa kawai tayi fuuu..ta bar wajen, dan a
wannan gaɓar ta tabbatar idan tace zata buɗe baki tayi magana to baza tayi masu daɗi ba.
ÆŠakinta ta wuce kai tsaye tana mai nadamar rikon Jauhar a hannunta gashi tana nema ta
haddasa fitina tsakaninta da mijinta, farin cikin ta, mai share mata hawayenta. Alhaji Sha'aban
kuwa duƙawa yai saitin fuskar Jauhar cikin sigar rarrashi yake yi mata magana.

"Ya isa haka kiyi shiru, in Sha Allahu zaki koma gun iyayenki kiyi shiru haka kada kanki yai ciwo
kin ji ko?" Yaƙare maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa ya goge mata hawayen da suka jiƙa
mata fuska. Saurin miƙewa tayi zaune da kanta tana share hawayen tace.

"Nagode Alhaji." Sai alokacin ya fahimci me yake ƙoƙarin yi ya damƙe hannunsa tare da miƙewa
tsaye yana sauke ajiyar zuciya sannan ya juya yabar ɗakin. Jiki ba ƙwari Jauhar itaka tamiƙe ta
nufi kitchen wajen haÉ—a breakfast dan kar wani bala'in Hajja Maimoon É—in ya sake hawa kanta.
Shigarta kitchen keda wuya ta isko Suhana aciki har ta É—ora ruwan zafi tana fere Irish taji wani
tashin hankali ya sake ziyarto ta, da sauri taƙarasa cikin kitchen ɗin hannunta na kakkarwa take
cewa.

"Dan Allah kiyi haƙuri Aunty Suhana ki kawo na ƙarasa aikin nan kar Mommy tafito ta sameki."
Suhana ta juyo tana kallonta murmushi É—auke akan fuskarta tace,

"Ba abinda zai faru ki bari naci gaba kije kiyi sallah idan kin fito sai mu ƙarasa tare." Tsaye
Jauhar tayi takasa motsawa dan ita kam ƙara ta ƙarasa girkin nan da taje yin wata sallah tunda
ba iyawa tayi ba, bata ma san muhimmancinta bare tasan wajibi ce a kanta ko ba wajibi bane,
burinta kawai kar ta jawowa kanta duka a banza.

"Jauhar me kike tunani?" Suhana ta tambaya. Jin shiru yasa ta ce.

"Dake fa nake magana." Suhana ta faɗa tana ɗan taɓa ta ganin ko motsawa batayi daga inda
take ba. Karkace kai Jauhar tayi kamar zatayi kuka haÉ—e da cewa,

"Ni dai kibarni kawai nayi ya fimun yin sallar nan Aunty Suhana." Zaro idanuwa Suhana tayi
kafin tace.

"Wal'iya zubillah! Jauhar akwai abunda yafi sallah aduniyar nan dama? Ashe da gaskiyar Uncle
Irfaan daya faÉ—a mani cewa bakya sallah?" Suhana ta tsureta da idanuwa tana neman sake
tabbatar da zancen uncle É—in nata daya kirata a waya jiya ya sanar da ita cewa Jauhar bata yin
sallah tace bata iya ba, dan haka tayi ƙoƙari ta taimaka mata tasan meye sallah dama yadda
akeyinta kafin ya yi tunani wane irin taimako zai bata ta wannan ɓangaren. Kai Jauhar ta shiga
sosawa cike da tsoro tace,

"Aunty Suhana akwai aikin da yafi na Hajiya? Ku aikin ku zuwa makaranta, bakiga yadda kuke
sauri ba idan kuna da jarababben malami?" Tsoro da mamaki ya kama Suhana jin kalaman
Jauhar. Ganin yadda Suhana take kallonta yasa Jauhar saurin juyawa ta nufi wajan kettle dan
taga alamar Suhana ba zata fahimci abinda take nufi ba.
"Jauhar bakiga yadda muke sallah ba?" Tace,

"Ina gani wata ran."

"Amma ya akai kika ce bakya yi." Jauhar da sanyin jiki tace,

"Toh Hajiya bata sani ba, tace kuma idan ba itace tayi abu ba nayi sai ta kasheni."

"Ai kuwa dole kiyi sallah Jauhar." Cewar Suhana cikin takaici. Jin yadda Suhana tayi furucicin a
kaurare yasa Jauhar tsorata dan haka tace,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login