Showing 18001 words to 21000 words out of 47407 words

Chapter 7 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf

Hajja Ce   

03 Mar 2025

3180

ta, bari na shiga wankan kar na makara." Alhaji
Sha'aban ya faɗa yana ƙarasa shigewa cikin toilet ɗin ba tare da ya jira taje ta haɗa masa ba.
Mintuna ashirin yafito ta taimaka masa ya shirya, tana cikin fesa masa turare wayarsa ta É—auki
ƙara lokaci ɗaya kuma sukaji ana buga musu ƙofa da ƙarfi ana kiran su,
"Dady..!, Mommy..! kufito Jannat zata mutu." Suhana dake buga ƙofar da ƙarfi tafaɗa cikin
tsanani tashin hankali, kusan atare suka ƙaraso bakin ƙofar Mommy na faɗin,

"Me ya samu Jannat É—in?"

"Ciwonta ne ya tashi." TafaÉ—a hawaye na sauko mata dan tunda asuba da suka tada ita suka ga
ta sake shigewa cikin bargo wai sanyi take ji, shine fa yanzu ko da suka ga lokacin zuwa school
na ƙoƙarin yi bata tashi ba suka janye bargon suka ga ta kakkame a cikin bargon, shine Suhaila

ta tallabota zuwa jikinta tasa Suhana É—in tazo takira su Mommyn. Already Dady ya riga da ya
saba da ciwon Jannat dan haka cikin nutsuwa bayan yaje yaga yanayin da take ciki ya kira
Irfaan a waya, bugu É—aya ya É—aga suka gaisa kafin yace yayi maza yazo gidan yana nemansa,
dama jiya ba'a gidan ya kwana ba gidan Hajiya yayi tafiyarsa ya kwana acan saboda ɓacin ran
abinda Mommy tayi masa da rashin iya jurewa ganin halin da Jauhar ke ciki da bazai iya ba.

Bayan mintuna goma sai gashi ya iso, lokacin an fito da Jannat nan palour, kallonsa Dady yai
haÉ—e da cewa,

"Yanzu aka kirani akwai mutunen da zan gani urgent, ka É—auki Jannat ka kaita asibiti ciwonta ne
ya tashi, duk yadda ake ciki ka kirani kafin nazo.

"To Yaya." Irfaan yafaÉ—a tare da É—aukar Jannat Mommy tabi bayansa ita dasu Suhaila da gaba
É—aya hankalinsu ya tashi. Har Alhaji Sha'aban ya shiga motarsa ya tayar suma sun shiga wacce
zasu wuce asibitin ya saukar da glass É—in motarsa yana cewa Irfaan.

"Yauwa Irfaan da kun dawo yarinyar nan ku dubata ku gani idan lafiya take saboda da asuba da
na fito zanje sallah naji kukanta ƙasa-ƙasa na manta bamuyi maganar da Maimoon ba." Yana
ƙarasa faɗar hakan yafice daga gidan bayan mai gadi ya buɗe masa gate. Irfaan kuwa yana Jin
haka ya kashe motar, har yakai hannunsa zai buɗe murfin ƙofar Hajja Maimoon ta dakatar
dashi,

"Ina kuma zaka je baka ga halin da yarinyar nan take ciki ba ne? Kana ganin fa yanda take
kokuwa da numfashinta."

"Ita waccan ta cikin gidan ba mutum ba ce? Bazai yiyu abarta ita kaÉ—ai ba har sai mun dawo
tunda ba'a san halin da take ciki ba, ki je ki dubota in lafiya take sai mu tafi, I know Jannat will
be ok in sha Allah ba abunda zai faru da ita." Tsabar ɓacin rai kasa magana Hajja Maimoon tayi
ta ɗauke kai kawai zuwa can gefe, ganin haka yasa Irfaan ya ɓalle murfin motar yafita zuwa
cikin gidan zuciyarsa duk babu daɗi. Kai tsaye bakin ƙofar ɗakin Jauhar ya nufa ya kwankwasa
mata, jin shiru bata amsa ba ya sashi tura ƙofar a hankali. Adunkule ya ganta cikin zannuwan
data rufa dasu har lokacin jikinta na rawar sanyi, sai kukan da takeyi wanda dan tsabar wahala
ko fita baya yi sosai dan tayi kukan har ta gaji.

"Subhanallahi." YafaÉ—a yana takowa cikin É—akin tare da jaye zannuwan jikin nata, halin É—aya
ganta aciki ba ƙaramin tsorata yai ba yaciro wayarsa da sauri yakira Suhaila da itama ta cika
tayi fam ganin yadda uncle ɗin nasu yake ƙoƙarin fifita mai aiki akan ƴar uwarsu. Kamar bazata
É—auka ba sai kuma ta É—aga tana turo baki take cewa,
"Uncle ko naja motar kawai mutafi ne?" Tayi maganar cikin nuna shi tunda yana da uzuri bari su
tafi.

"Short up Suhaila bake zaki sani yin abinda ya kamata ba, ai Yayan yasan kun iya mota amma

ya taso dani nazo. Kuyi sauri ku shigo ke da Suhana ina jiran ku, ki faÉ—awa Mommy yarinyar
nan batada lafiya sosai." Ya ƙarasa maganar yana kashe kiran tare da kiran sunan Jauhar ɗin
har sau biyu amma takasa amsawa. Cike da ɓacin rai Suhaila ke faɗin.

"Mommy wai kinji Uncle Irfaan yace Jauhar batada lafiya sosai."

"Wannan ba damuwar mu bace Suhaila, kije kifaÉ—a masa idan bazai kaimu asibitin nan ba ke ki
dakko makullin motarki kizo mutafi kawai, ina ruwanmu da matsalarta? ta mutu mana."

"Mtss Allah Uncle Irfaan yacika matsala." Suhana tafaÉ—a tana balle murfin motar suka nufi cikin
gidan. Saka su yai suka tallabo Jauhar wacce da daƙyar take iya tafiya suna faman kumbura
fuska tare da riƙe numfashin su kamar sun riƙo kashi suna kauda kai suka shiga da ita cikin
motar, dama Hajja Maimoon na gaba ta runtse idanuwa zuciyarta na tafarfasa haÉ—e da juyar da
kanta gefe. Babu yadda zatayi ne amma da ba za'a taɓa yin tafiyar nan da Jauhar ba, kawai
dan bata son a ɓata lokaci ne ba'a kai Jannat ɗin ba wani abun yazo ya sameta tasan sai tafi
kowa damuwa saboda ta shaƙu da yarinyar fiye da sauran yaran.

Ba tare da Irfaan ya kulasu ba ya dakawa Suhaila tsawa data yi tsaye a bakin ƙofar motar ita a
dole bazata shiga motar ba yana cewa,

"Suhaila karki bari na saɓa maki da sanyin safiyar nan, karki kai ni bango wallahi." Tana turo
baki ta shiga cikin motar ganin yanayin yadda yai maganar ba wasa a fuskarsa ta ja murfin da
ƙarfi ta rufe sannan ya buɗe ya shiga shima ya fizgi motar aguje suka nufi Fedral Medical
center. Suna zuwa ya yi parking, Jannat kawai suka fitar dama tun a ciki sukayi ta mintsinin
Jauhar wacce hawaye kawai take ta kasa bayyana kukan nata a fili. Ciki suka shige ganin haka
yasa Irfaan yiwa ma'aikata mata dake cikin asibitin magana suka karaso wajan motar suka
taimakawa Jauhar aka shiga da ita ciki emargancy dan gabaki ɗaya tafi Jannat wahala. Ƙoƙarin
yadda za'a duba Jauhar kawai Irfaan keyi hakan yasa ran Hajja Maimoon sake ɓaci tayi saurin
ƙarasawa inda yake cikin fushi take faɗin.

"Irfaan hala ka manta wacce tayi sanadin fitowar mu ko? Naga gabaki É—aya hankalinka yana
kan wacce babu wata alaka tsakaninka da ita. Kaje kaji da Jannat ka tsaya nan wajan. Ni wani
lokacin sai na kasa gane manufarka akan Jauhar wallahi." Jin kalmarta na ƙarshe-ƙarshe yasa
Irfaan saurin kallanta ta jinjina masa kai alamar tabbatar da abinda yaji ta faÉ—a. Yaja É—an guntun
tsaki yadda ba zataji ba. Yana mamakin yadda take yi masa abubuwa bayan a girme ya girmeta
dan shi yana da talatin da uku ita kuma tana da talatin. Gudun ɓacin rai yasa shi juyawa ya yi
settling case É—in Jannat aka bata É—aki sannan ya koma kan Jauhar wacce fitowar Zain kenan
wata nurse tana nuna masa inda Jauhar take a kwance kan bancin dake ajiye a reciption.
Wajan ya ƙarasa tare da buɗe baki da kyar ya furta.

"HI." Jauhar dake kwance taji tsayuwar mutum a kanta ta buÉ—e idanunta da kyar suka sauka
akan ƙafafuwansa dake sanye cikin black cover shoe ta kasa ɗaga kai ta kalli fuskarsa saboda
yadda idanunta sukai mata nauyi. Durƙusawa ya yi saitin fuskarta tare da leƙawa suka yi ido

huɗu da juna. Da sauri ya miƙe tsaye ganin idanunta biyu yace.

"Tashi zaune." Jauhar ta shiga ƙoƙarin tashi amma ta kasa, sai dai tana karfafawa zuciyarta
guiwa tana ta kokawar miƙewa sanin cewa jiranta ake yi. Hannunta da take dafa bancin ne ya
goce tazo zata faÉ—i cikin sauri Zain yasa hannu zai taro ta Irfaan da isowarsa kenan ya tare ta.
Da sauri dukkan su suka kalli juna ido cikin ido kafin Irfaan ya juya yana taimaka mata ta zauna
sosai akan bancin, daga shi har Zain kallanta suka yi yadda albarkatun kirjinta da suka fara
tasowa suka tsaya a cikin rigarta wacce babu bra a jiki. Da sauri Irfaan ya kauda kansa Zain
rintsa ido wani mugun takaici yana taso masa tun daga can ƙasan ransa har zuwa saman
harshensa...

#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*

*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce

*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu

*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch

*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.

*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso

*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000

*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435 ko 08098456130

*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*

*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
     (Batch C)

*BILLY S FARI*💎
Da
*HAJJA CE*👈
Areewabooks@billysfari

Page 8..

Da kyar Irfaan ya iya buÉ—e idanunsa yana kallan gefe, shi kam shaf ya manta da zasu taho bai
yi tunanin É—auro mata hijab ba akai kawai suka taho, asali ma shi bai wani kula da yanayin da
take ba sai yanzu, kuma yanzun ma da ace babu wani a kusa da ita ya tabbatar ba wani lura zai
yi ba. Ya saba ganinta cikin riga da zani na atamfa rigar kuma burmemiya ce yanzu kuma wata
yaloluwar t-shirts ce hakan yasa abubuwan nata suka kusa tsone musu idanuwa lokaci É—aya
duk kuwa da cewa ba wani girma ne dasu ba kasancewar babu kwanciyar hankalin da zata
samu natsuwar da har zasu iya taso sosai, É—an tsaki ya ja tare da sake É—auke kansa gefe. Shi
kuwa Zain saboda yanayin aikinsu sun saba ganin ire-iren haka ga patient sai kawai ya maze
tare da buÉ—e idanunsa yana kallan fuskar Jauhar tare da don kaucewa kallonsa ga kirjin nata,
amma duk da haka da yake ido gulmammi ne sai da yaji sun sake sauka wajen, cikin sauri ya
sake kawar da idanuwan nasa daga wajan yana cewa.

"Zo muje naji meke damunki ko akwai taimakon da za'a iya yimaki kafin Dr ya ƙaraso." Ya faɗa
yana juyawa tare da shiga wani office dake nan kusa dasu. Ɗan ƙaramin tsaki Irfaan yaja ganin
Jauhar ɗin ta mike tabi bayansa sai faman durƙushewa take alamar tana jin jiki sosai. Kallon
inda su Hajja Maimoon suke tsaye ya yi cikin sa'a suka haÉ—a ido da Suhana ya kirata da
hannunsa. Kamar ba zataje ba sai ta daure taje lokacin har Jauhar ta shiga cikin office É—in.
Hannun Suhana yaja suka zauna akan bencin da Jauhar ta tashi ya kalleta sosai sai kawai
tasha jinin jikinta cewa akwai abinda tayi, mamakin irin kallan da yake binta dashi takeyi kafin
tace.

"Uncle menene?" Irfaan ya sauke numfashi tare da lasar lips É—insa da suka soma bushewa
yace.

"Yanzu abinda kukayi É—azun kun kyauta? A ina ko koyo zuciyar rashin son taimako? Allah yaji
ƙan Aunty yai mata rahama sam halinta ba haka yake ba" Jikin Suhana ne yai sanyi jin abinda
ya faÉ—a kafin ta amsa masa da.

"Amin Uncle." Tana sinne kai ƙasa, sake kallonta yai akaro na biyu tare da sauke numfashi
yace.

"Amin É—inki ba zatayi mata amfani ba Suhana, kawai ki amsa Mani tambayar da nayi maki." Duk
da tasan akan Jauhar yake zance da suka nuna ko oho da rashin son taimaka mata da zasu zo
asibiti, hakan bi hanata yin tunanin me yasa zai kawo zancen mahaifiyarsu acikin zancen ba?
hawaye taji ya tarar mata acikin idanuwa ta É—ago kai ta kalleshi tana cewa,
"Innalillahi saboda me zaka ce Amin É—ina ga mahaifiyata ba yada amfani Uncle? Wane laifi nayi
ne?" Cike da damuwa dake kwance akan fuskarsa ya riƙo hannunta haɗe da cewa.

"Saboda baku da hali mai kyau dukkan ku Suhana. Gabaki É—ayan ku babu wanda yake faranta
mata a nan duniya. Tana kwance a kabari abinda zai sanya ta farin ciki baifi a tashe ta ace tashi
kiga abinda Æ´aÆ´anki keyi aduniya mai kyau, amma na tabbata da wannan halin naku da kukeyi
Suhana da akwai hanyar da Aunty zata fito ta gaya muku ku gyara da tayi, amma babu hanya
sai dai kawai ta ganku ta kyale har zuwa lokacin da kukaje inda take." Hankalin Suhana ya fara
tashi dan gabaki É—aya taji cewa suna yin abinda bai kamata ba duk kuwa da cewar har yanzu
bata tunanin abinda sukayi É—azu É—in laifine. A gigice take kallansa tana jin tamkar ta fashe da
kuka take cewa.

"Dan Allah Uncle ka sanar dani me mukayi da har mahaifiyar mu baza tayi farin ciki damu ba?"
Ganin anzo gabar da yake jira yasan ya shi cewa.

"Wulakanta É—an Adam da nuna baya da daraja ta kowace fuska, wato Suhana Allah shi yasan
dalilin da ya yo É—an adam a mafifita darajar duka al'umma. Me yasa kuke yiwa Jauhar haka?
Kuna tunanin da tazo aiki gidan ku hakan yana nufin Allah baya sonta ne? Please Suhana kuyi
abinda Allah zai baku lada, kinga kece mai sauki a cikinsu, kece muke ganin kamar zaki É—akko
dabi'un mahaifiyarki amma wani lokacin sai ki karkace ki koma irin su, dan Allah ki riƙa tausayin
Jauhar, yarinya ce kamarku dake bukatar kulawa irinta uwa da uba kamar yadda kuke samu
amma tarasa saboda haka Allah ya tsaro rayuwarta zata kasance mata." Take hawaye suka
fara zubowa daga fuskarta tasa hannu tana sharewa, dama duk cikin su itace mai sauki kuma
batada weak point aduniya kamar na zancen mahaifiyarsu, dan haka maganar Irfaan ba
ƙaramin tasiri tayi a zuciyarta ba. Murya a sanyaye take kallonsa haɗe da cewa.

"Insha Allah Uncle na bari kuma daga yau na dena takurawa Jauhar saboda bana so Mami taji
haushinmu idan taga abinda mukeyi marasa kyau". Cikin ƙarfafa guiwa ya sakar mata

murmushi yana cewa.

"Insha Allah zatayi farin ciki dake Suhana duniya da lahira idan kikayi kokarin gyarawa. Kinga
yanzu tana ciki ita kaÉ—ai sai nurse ga jiki tana ji, ki shiga ko zata bukaci taimakonki kin ji ko?."
Ɗaya masa kai tayi haɗe da miƙewa a hankali ta nufi cikin office ɗin jiki duk babu daɗi. Zaune ta
tarar da Jauhar É—in akan kujera ta É—ora kanta saman table É—in da Zain ke rubutu bayan ya gama
gwada BP É—inta da kuma yi mata tambayoyi akan abubuwan da takeji. Shigowar ta Suhana
yasa shi É—an sakin murmushi, duk da shi É—in ba mai yawan hayaniya bane, zamowarsa nurse
kuma sai ya sake sashi kamewa musamman idan yana kan aiki kasancewar dole sai da
natsuwa a aikin nasu, duk da wani lokacin yakan zama mutum mai sakin fuska da kuma
barkwanci saboda ya ƙarfafawa marasa lafiyan da yake kulawa dasu guiwa.

"Ya akai? Ko so kike kiji abinda yake damun ƙawata?" Mamaki ya kama Suhana ta ɗan zaro
idanuwa tana kallonsa tace,

"Ƙawarka?" Yace,

"Eh mana muna sirri da ita kika shigo ko tare kuke?" Ya tambaya yana tsare Suhana da ido.
Lanƙwasa idanuwan nata tayi kafin tace

"Dama kasanta ne?" Yace,

"Eh yau muka ƙulla ƙawancen da ita gashi har allura ma zan yi mata." Jauhar dake jin abinda
suke cewa ta ɗago da kyar tare da zuba masa ido jin yace wai ita ƙawarsa ce. Gira ɗaya ya
É—age mata hakan yasa tayi saurin juyawa ta kalli Suhana taga ko ta ganshi. Suhana ce tayi
magana cikin kulawar da ta bawa Jauhar É—in mamaki take cewa.
"Sannu Jauhar kin ji abokin naki wai allura zai yimaki, meke damunki ne halan?" Mamaki yai
bala'in É—aure ta dan haka da kyar ta iya girgiza mata kai tana cewa.

"Ba komai." Zain dake jinsu yana miƙewa tsaye yake cewa.

"A'a fa ƙawata jininki ya hau sosai kuma kin ƙi sanar dani meke cikin ranki taya zaki ce babu
komai? Please ko zaki fadawa Yayar mu sai ta faÉ—a mani". Ya faÉ—a yana maida kallonsa ga
Suhana, kafin ta bashi amsa ya nuna Jauhar da hannu yana cewa Suhana.

"Ki É—an taimaka ki yafa mata É—an kwalinki tunda bata sako hijab ba tana Æ´an mata da ita."
Murmushi Suhana tayi tare da zaro É—ankwalin material É—in jikin nata ta É—orawa Jauhar akan
kafaÉ—unta. Kallansu ya yi tare da faÉ—in.

"Bari naje sai kun jira likita yazo muji wane irin taimako zai bata." Yaƙare zancen tare da ficewa
tun kafin su bashi amsa. Kai tsaye Zain ya dinga duba mararsa lafiyan da aka kawo har yazo
kan Jannat wacce ya tarar da ita kwance a kan gado Hajja Maimoon tana faman shafa bayanta

sai wani sake narkewa takeyi. Inda take ya ƙarasa yana sargafe hannayensa a kirjinsa. Jannat
ta É—ago kyawawan idanunta ta zuba akan na Zain, ganin yadda yake kare mata kallo ne yasa ta
turo baki tana cewa.

"Mommy kin ganshi ko?" Da sauri Zain ya ware ido yana cewa.

"Good girl, dama so nake naji kina magana ne ko bebiya ce sai na san ta inda zan fara dubaki.
Da alama ma lafiyarki ƙalau kawai raki ne irin naki dan ki tayarwa dasu Momynki hankali ko?"
Zabga masa harara Jannat tayi bata wani damu da girmansa ba tana sake shagwaɓewa cikin
jikin Mommy take cewa,
"Mommy ki masa magana wai cewa yai ƙarya nakeyi." Hajja Maimoon ta kamo hannayenta cike
da kulawa tace,

"Rabu dashi tsokanarki yake yi shima kansa in yasan aikinsa to tabbas yasan bakida lafiya"
Hajja Maimoon tayi maganar tana wani mammatsa hannun Jannat É—in a cikin nata. Cikin rashin
nuna damuwa da kalaman na Mommy Zain

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login