Showing 33001 words to 36000 words out of 47407 words
Chapter 12 - GONAR SHARRI BOOK 1 COMPLETE by Billy S Fari And Hajja ce.pdf
ita tabar wajen tana
dariya.
Tuwon shinkafa ne da miyar agushi wacce tasha tantakwashin naman rago da man shanu,
Ayusher takawo masa agabansa tayi masa saving da kanta yaci suna ɗan taɓa fira, dan suna
ɗaukar gidan su Ayusher ɗin tamkar gidansu kasancewar da mahaifinta da mahaifinsa uwa
ɗaya uba ɗaya suke, kuma duk da rashin wadatarsu sosai basu taɓa nuna ƙyanƙyami ko kuma
ƙyamarsu ba idan sun zo gidan. Hakan yasa Irfaan ya saki jiki ya ɗan ci abincin kaɗan yace ya
koshi saboda da gaske yakeyi akoshe yake, kawai baya son yiwa Umma gardama ne yaki ci taji
ba daɗi.
Kwashe kayan Ayusher ta sake yi sannan ta dawo ta tadda shi har ya miƙe yana yiwa Umma
sallama tana yimasa godiya haɗe da sanya masa albarka shi da Yayan nasa, ta kuma ce idan
yaje yayi masu godiya sosai wajen Alhaji Sha'aban da Hajiya. Har zaure Ayusher ta rakashi
kafin tace,
"Toh Ya Irfaan Allah ya kiyaye ya tsare hanya, ina gaida su Hajiya."
"Amin 'yan matana, amma sakonki kije da kanki." Ya faɗa cike da son sanya ta magana,
"Kai Ya Irfaan! Nice fa?" Ta faɗa tana langaɓe kai.
"Eh ai nasan ke ɗin ce, kin girma tubarkallah kamar ba ƴar yarinyar da nake goyawa ba, ina
zuwa zan sanar da Yaya yazo ayi magana da Kawu abani aurenki in huta da hadiyar yawu."
Irfaan ya faɗa cike da tsokana yana murmushi. Ayusher tasa tafin hannayenta ta rufe fuskarta
haɗe da barin wajen aguje dan ba ƙaramar kunya kalaman nasa suka sakar mata ba. Irfaan
yasa dariya yana kallonta har ta shige ciki sannan ya juya yafice daga cikin gidan. A bakin ƙofar
gidan sukayi karo da Kawu Ibrahim wanda har bakon nasa ya tafi zai shigo gidan. Irfaan ya ɗan
rissina yana cemasa zai wuce.
"Toh ka gaida mahaifiyar taku sosai Nagode Allah yai maku albarka." Kawu Ibrahim yafaɗa yana
miƙa masa hannu suka sake yin musabiha sannan Irfaan ya shiga motarsa ya tayar ya wuce.
__________
Cikin sati ɗaya duka kayan da Hajja Maimoon tayi odar suka iso tasa aka kawo mata su har
gida aka baje su a nan tsakiyar palourn ƙasa ta watsesu ɗaya bayan ɗaya tana lissafa komai ta
gani idan ya iso dai-dai kafin akai su shago. Suhaila ke taimaka mata wajen haɗa lissafin yayin
da Suhana da Jannat ke gyara mata kayan suna haɗa su waje ɗaya. Bayan tagama haɗa
komai tace kowacensu ta zaɓi abinda takeso kafin akwashi kayan anjima akai shago. Jauhar
dake rakuɓe gefe taji kamar itama abata damar ɗaukar abunda take so da ta ɗauki wata ƴar
ƙaramar jaka data hango mai kyau data burgeta, fannin dogayen riguna da ƙananan kaya ne
kawai bata damu dasu ba balle har taga abinda ya burgeta, haka ma takalma da mayafan
kala-kala da turarukkan ƙamshi irin masu tsadar nan na waje duk hankalinta bai kai wajen ba,
kyan jakar ne ya sake janta bayansu Suhaila sun zazzaɓi abubuwan da suke so tace.
"Mommy dan Allah na ɗauki waccan jakar..?"
Kafin taƙarasa rufe baki Hajja Maimoon ta jefeta da wani kwali da aka cire cikin wata jakar cikin
ɓacin rai a tsawace tace,
"Me na gaya maki akan ganin yaran nan da abu kisa ran kema zaki mallaki irinsa, su sa'aninki
ne ko an faɗa maki matsayinku ɗaya dasu? Tukuna ma bance kidena kirana Mommyn nan ba
amma kika sake? rainani kikayi ko Jauhar?" Yadda ta dire maganar cikin wani karaji tana yowa
kanta yasa Jauhar ɗin miƙewa da gudu tabar palourn ta zagaya ta can bayan kitchen.
"Ƙaramar mara kunyar yarinya da ki tsaya na nuna maki banbancin dake tsakanin waɗanda
keda gatan mahaifi dake da baki da wata daraja ko gata awajen ubanki tunda har yakasa zuwa
ya ɗaukeki agabana, shashasha kawai. Wannan da kike ganinsu, su ɗin ƴaƴan so ne kuma ƴan
gatan iyayensu gaba da baya masu mutunci da daraja, kefa? Wane so iyayen naki keyi maki
balle kisa ran zaki samu gatantawa irin tasu?" Hajja Maimoon ta ƙare maganar tana haɗa zufa
saboda tsabar masifa duk da sanyin A.c dake tashi acikin palourn. Kallo Suhana da jikinta duk
ya mutu ta bi Hajja Maimoon dashi ganin irin masifar da data balbali Jauhar da ita da irin
maganganun da take faffaɗa mata tamkar mai yi da sa'arta, shin ina iyayen Jauhar ne? Me
suka yiwa Mommy haka data tsani ƴarsu bata sonta? Shin basu san halin da take ciki bane ko
a'a da baza su zo su ɗauketa ba takoma hannunsu?. Tambayar data jefawa kanta kenan da a
ƴan kwanakin nan take yawan yiwa kanta amma tarasa wanda zai amsa mata su, cikin sanyin
murya tace,
"Mommy dan Allah kibata tunda tana.." Kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda Hajja Maimoon
ta fizgo kai tana kallonta sai dai ta sadda kanta ƙasa tana cewa.
"Sorry Mommy." Sannan tabar wajen. Suhaila da Jannat ko ɗauke kai sukayi suka kwashi
kayan su suka haye sama dan ko ajininsu.
Daɓas Hajja Maimoon tafaɗa kan kujerar tana ɗage kanta da taji ya soma yi mata wani irin
ciwo, wai yaushe tayi sanyin da har Jauhar tafara tunanin amfani da kayan kyale-kyali a
rayuwarta? Yaushe mafarkanta suka nuna mata irin wannan rana zata taɓa zo mata bayan ita
ɗin ba kowa bace acikin gidan? Lallai dole ta sake tashi tsaye ta nuna mata wutsiyar raƙumi tayi
nesa da ƙasa. Da wannan tunanin ta jingina ajikin kujera haɗe da lumshe idanuwanta suka rufe
tana laluben ko meye mafita.
Jauhar na zuwa bayan kitchen ta zube ƙasa ta haɗe kai da giwowinta waje ɗaya ta saka wani
irin kuka jin kalaman da Hajja Maimoon ke jifanta dasu tana mai dana sanin tambayarta abinda
take da yakinin cewa koda zata mutu bazata taɓa samu ba a wajenta. Gashi ta tada mata da
fami a zuciyarta na son sanin inda iyayenta suka shiga suka barta a hannun matar da tafi
ƙaunar mutuwa da ita. Shin kodai da gaske mahaifinta baya sonta shiyasa yabarta babu wata
kulawa balle gata kamar yadda kowane ɗa ke samu agun iyayensa? Da haka bacci mai nauyi
ya ɗauke ta awajen har akayi sallar la'asar ba tare data sani ba.
_Bayan kwana biyu_
Hajja Maimoon ce da tuni ta manta da abunda yafaru dan har an kwashe mata kayanta an kai
mata shago angyara komai kamar yadda taba yaran da zasu riƙa tayata kula da shagon umurni,
tana sakkowa daga upstairs cikin wata irin shiga ta alfarma su Suhaila na biye da ita sai ƙamshi
suke zubawa kai da ka gansu kasan mutane ne masu alfarma. Fitowar Daddy kawai suke jira
su wuce wajen gagarumin bikin data gayyaci kawayenta da mutanen arziki na buɗe katafaren
shagon nata data sawa suna 'SUJASU COLLECTION' wanda tuni mutane sun hallara su kaɗai
ake jira.
Da ɗan hanzari Dady yafito daga part ɗin nasa yana saƙala agogon hannunsa taƙarasa
wajensa ta karɓa ta sanya masa. Zaman hular kansa ta gyara masa ya fito cas abunsa tamkar
bai isa aje su Suhaila ba sai wani sheki yakeyi yana zuba nashi ƙamshin. Murmushi ta saki tana
cewa.
"Ya Habiby anya zan yarda kaje wajen nan kuwa? Kaga kyan da kayi kuwa?" Side ɗinta ya kalla
inda yaransa ke tsaye ta bayanta sun sha kyau suma kafin ya maido kallonsa gareta yace.
"Asalin kyan ai kece kikayi sai wani sheƙi kikeyi Mommyn Jannat." Ya yi maganar yana ɗaga
mata gira, hakan yasa ta saki dariya tana gyara sarkarta ta gwal dake wuyanta da mayafinta
tace,
"Allah Ya Habiby?" Yace,
"Eh mana muje kinsan mu ake jira." Yayi gaba Jannat ta ruga ta riƙe masa hannu, Hajja
Maimoon kuwa ɗakin Jauhar ta leƙa ta ganta kwance, wani mugun takaici ya taso mata tasa
ƙafa ta kai mata shuri tana cewa.
"Waya baki izinin zuwa ki kwanta? Tukunna ma wa kike so ya kula da gidan kafin mudawo?"
Jauhar da zafin shurin da Hajja Maimoon tayi mata ya shiga jikinta ta tashi zaune tana shafa
wajen tace.
"Kiyi haƙuri naga na kammala komai shine na ɗan kwanta." Da wani irin fushi tace da ita,
"Dallah rufamun baki kifice ki zauna daga bakin ƙofa kafin mudawo, kuma karki sake mudawo
mu tadda wani abu ya ɓata a gidan nan, idan har haka ta faru sai na lahira ya fiki jin daɗi." Tana
kaiwa nan ta juya tafice daga ɗakin. Jauhar tamiƙe a kasalance ta biyo bayanta ta zauna daga
bakin ƙofar shiga cikin gidan dan tuni motarsu tafice daga gidan. Baba Bello maigadi ta hango
yana kicaniyar rufe gate da a yanzu keyi masa nauyi musamman wajen rufewa duk da
kasancewar gate ɗin mai tayu ne da turashi kawai akeyi saboda manyan ta data cin masa. Da
gudu ta taso ta dafa masa suka ƙarara rufe gate ɗin tana cewa.
"Sannu Baba Bello." Ya amsa mata da cewa.
"Yawwa Jauhar ba dake aka tafi ba?" Zaro idanuwa tayi tana rufe bakinta haɗe da cewa.
"Baba Bello karufa mani asiri kar Hajiya taji ta datse maka harshe! Ina ni ina zuwa irin wannan
taron manya na masu kuɗi?." Murmushi Baba Bello yai haɗe da cewa.
"Jauhar kenan! Ai wannan ba halin Hajiya bane balle ta aikata akaina, kece dai nake mamakin
irin takurawa da tsangwamar da takeyi maki, na kuma rasa dalilin da yasa bazata sallameki ba
ta sauya wata mai aikin, ko kina yimata wani laifi da bata so ne?" Cikin sauri Jauhar tace,
"A'a Baba Bello ni ko dana tashi wajenta cikin wannan hantarar da takura na ganni, bansan
laifin dana yimata ba take tsangwama min haka tun ina ƙanƙanuwata." Ya tausaya mata
musamman yadda yaga tana shirin yin kuka yace.
"Kiyita hakuri komai zai wuce in sha Allahu." Ya faɗa cike da tausayinta dan ba wanda bai san
kalar ukubar da take fuskanta wajen Hajja Maimoon ɗin ba.
SUJASU COLLECTION
Tunda sukaje wajan ya sake ɗinkewa, manyan mata ne da ƴan gayu masu ji da kansu ta tara.
Ganin yadda aka cika dan batayi zaton za'a zo har haka ba, ya sanya taji wani irin girman kai ya
sake shigarta. Suka gaggaisa da kaɗan daga cikin bakin kafin cikin isa da tinƙaho Hajja
Maimoon ɗin tayi nasarar buɗe katafaren shagon nata da taimakon Alhaji Sha'aban dake
gefenta tare da ƴaƴansa, sai kuma Hajiya da Irfaan da Maryam da suma sun samu hallarta
wajen taron duk da Hajja Maimoon ɗin bata so hakan ba. Murna aka shiga tayata ana tafi da
hannuwa kafin mutane su shiga cikin shagon su zazzagaya suna yaba kyan kayan da aka zuba
a ciki da tsadar su, ba abunda ya tafi da zuciyar Alhaji Sha'aban Sada sai yadda ta tsara
shagon da kuma sunan data saka mashi wato (SUJASU COLLECTION) dake ɗauke da farkon
sunayen 'ƴaƴan nasa wato Suhaila, Jannat da kuma Suhana. Daga ciki kuma kowane ɓangare
tayi amfani da sunayen yaran inda ɓangaren takalma da handbags aka rubuta 'Suhana shoe's
and bags fashion design'. A ɓangaren jallabiyoyi da mayafai kuma aka rubuta, 'Jannat Italy and
Arabian gowns.' Ɓangaren turarukka kuma nan aka sa 'Suhaila perfumes'. Hatta Hajiya wannan
abun da Hajja Maimoon tayi ya matuƙar burgeta sosai dan tsakaninta da jikokin nata tasan
soyayya takeyi masu ta gaskiya ba cuta ba cutarwa. Hakan yasa nan take tafitar da kuɗi ta sayi
wani turare mai kyau da tsada tana cewa.
"Nice zan fara saka albarka a wannan shagon naki Maimunatu Allah ya sanya alkhairi ya buɗa
maki kasuwa kuma yasa albarka aciki." Hajja Maimoon tayi dariya cike da makirci ganin Alhaji
Sha'aban Sada na tsaye wajen tace,
"A'a Hajiya ai bama karɓi kuɗinki ba duk wannan addu'a da kikayi mana da sanya albarka ai ta
ishe mu." Ta ɗauki turaren hadda wani takara ta miƙawa Maryam tace ta riƙewa Hajiyan. A
kasan zuciyarta kuwa tsine mata takeyi yafi dubu tana hango asarar da taja mata ta makudan
kudaɗen da zata karɓar a turarukkan dan Exclusive turarene na manyan mata da Hajiyoyi.
Kamar Alhaji Sha'aban yasan meke ranta yace,
"Nima dai bazan fita ba ban sanya na saka albarka ta ba, saboda haka Maryam keda su
Suhana ku shiga ku zaɓo duk abinda kuke so." Duk irin yadda taji yace zai siya, sai da taji har
lokacin ranta bai sakko ba na daga kyautar da ta yiwa Hajiya. Kaya suka ɗakko masu kyau da
tsada musamman Maryam dan su Suhaila turarukka kawai suka ɗauka, da yake akwai kuɗin
komai a rubuce Alhaji Sha'aban baice uffan ba yaje yai making payments duka har na
turarukkan da aka sanyawa Hajiyarsa. Haka kuwa akayi Irfaan yaje yayi payment sannan ya
cire kudinsa ya zagaya ya ɗakko dogayen riguna guda biyu da hand bag da takalmi ɗaya da
turare yaje wajen Hajja Maimoon ya ajiye yana cewa,
"Tunda babu irin namu kayan na maza bari muma musa albarka musayawa kannenmu." Ba
kunya Hajja Maimoon tayi dariya ta karɓi kuɗin tana mikawa cikin yaranta ayi payment tare da
cewa,
"Thanks Irfaan, haka muke so na gida su riƙa supporting kasuwancin mu." Dan a tsammaninta
Maryam ya siyawa kayan. Baice komai ba ya koma gefe har sai da Hajiya tace a maida ita gida
saboda lokacin ɗora abincin sadaka ya yi, duk da akwai masu yi takan bada umarnin yin wasu
abubuwan.
Sai da kowa ya watse a shagon sai ɗaiɗaiku masu zuwa sayayya sannan Alhaji Sha'aban Sada
ya kwashi yaransa suka wuce gida, haka ma Hajiya dasu Maryam Irfaan ya kasu suka wuce
gida. Yana ajiyesu ya juyo ya nufi gidan Yayan nasa da ledar kayan daya siya...
#A heart touching story
#Gonar Sharri..
#Hajja ce
#Billy s Fari
#Ƴan Tagwaye
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
*GONAR SHARRI*
Billy S Fari & Hajja ce
*IDANIYAR RUWA*
(Mai wuyar toshewa)
Ayusher Muhd & Jeeddah Aliyu
*WATA ALAƘA*
Zee Bawa & Stylish bch
*BISHIYAR TSIYA*
(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)
Umm Ashgar & Sadiya Dan.
*TSARIN ALLAH*
(Ba mai iya canzawa)
Asmy b Aliyu & Nana Diso
*ZAI IYA BIYAN*
GUDA 1 akan 500
GUDA 2 akan 800
GUDA 3 akan 1200
GUDA 4 akan 1600
GUDA 5 akan 2000
*BANK ACCOUNT*
8098456130
Opay digital services
Shaidar biya
07040402435
08098456130
*KATIN MTN*
07065283730
Shaidar biya ta lambar.
[8/1, 9:34 PM] Billy S Fari: *GONAR SHARRI...!*
*ƳAN TAGWAYE BIYAR*
(Batch C)
NA
*BILLY S FARI*
Da
*HAJJA CE*
Arewabooks@billysfari
Page 13..
Yana ƙoƙarin tura kan motarsa cikin gidan, yayin da Alhaji Sha'aban Sada na kawowa zai fita
campany dan yana ajiye su Suhaila aka kirasa aka ce yayi baƙi masu matukar muhimmanci.
Reverse Irfaan ɗin yai har sai da Yayan nashi ya fito zai wuce sukayi clashing Alhaji Sha'aban
Sada ya tsaya ya sauke glass ɗin gefensa yana cewa.
"Yauwa Irfaan ka zauna da yaran nan haka baƙi zasu zo yiwa Hajiya Maimoon murna kafin
nadawo ba jimawa zanyi ba, bana son barinsu gidan su kaɗai kasan yanayin rayuwar yanzu sai
a hankali sam bani da wata natsuwa akan barinsu cikin gidan ba wani babba. Kaga Baba Bello
shekaru sun miƙa balle nasa ran babu wata matsala idan na barsu tare." Irfaan dake riƙe da
steering motarsa yana sauraren Yayan nasa yace.
"Shikenan Yaya babu damuwa sai ka dawo." Horn Alhaji Sha'aban Sada yai masa alamar
amsawa yana maida glass ɗin motarsa ya wuce shi kuma Irfaan ya tura hancin tasa motar ya
shiga ciki ya samu waje yayi parking. Tsaye ya yi yana kallon yadda Baba Bello mai gadi keta
ƙoƙarin rufe gate ɗin har Allah ya taimake sa ya rufe yana faman sauke numfashi ɗaya bayan
ɗaya sai kace wanda yayi wani aikin wahala, dan gate ɗin turoshi kawai za'a yi ya rufe kansa ba
tare da ansha wahala ba. Kai Irfaan ya girgiza cike da tausayinshi yana sake fahimtar maganar
da Yayan nasa ya gama yimasa yanzu akan tsufan Baba Bellon da yake tunanin sam bazai iya
bawa yaransa kulawar data dace ba idan buƙatar hakan ta taso. Har ya nufi cikin gidan sai ya
tuna da saƙon daya kawo shi gidan, dan haka ya koma ya buɗe motar ya ɗakko sannan ya
wuce ciki.
Sallama yai abakin ƙofar shiga palourn haɗe dayin tsaye yana kallon Jauhar dake goge-goge,
kammala girkinta kenan na dare tafito tana sake gyara gidan dan hakan al'adarta ce kullum safe
da maraice sai ta share ko'ina kuma ta goge duk wani abu dake cikin parlorn. Kallo yabi palourn
dashi yaga ba kowa sai ita kaɗai dake faman aiki. Wata sallamar ya sakeyi dan da alama bata ji
ta farkon ba da yayi tare da ƙarasa shiga cikin palourn ya faɗa kan ɗayar kujerar yana cewa.
"Sannu da aiki Jauhar duk ina yaran gidan ne?" Jauhar da jin muryar sallamarsa tasa ta juyowa
riƙe da ƙyallen da take goge-gogen tace,
"Sunu da zuwa Uncle, Ina wuni?" Tayi maganar tana sinne kanta ƙasa cike da jin kunyarsa
tunowa da kayan da ya siyo mata kwanaki.
"Lafiya ƙalau Jauhar, kin dai warke ko?" Ta sunkuyar da kai tana faɗin,
"Eh." Tafaɗa tana ajiye ƙyallen da take goge-gogen dashi ta nufi kitchen dan takawo masa ruwa.
Dakatar da ita yai yana tashi zaune daga ɗan kishingiɗa da yai a jikin kujerar yace.
"Zo Jauhar ina zaki je?"
"Ruwa zan kawo maka." Ta bashi amsa ba tare data bari sun haɗa idanuwa ba duk da yadda
yake kallonta, shi har ga Allah mamakin yadda suke iya cin abincin da Jauhar ke girka masu
yakeyi saboda yanayin kayan jikinta da zai iya rantsewa tana kwana bakwai bata wankesu ba
balle kuma ayi batun sauyawa. Ya sauke wani nauyayyar numfashi tare da ɗaukar ledar dake
gefen ƙafafuwansa yana