Showing 24001 words to 27000 words out of 27538 words

Chapter 9 - ALLURA TA TONO GARMA BOOK COMPLETE .txt

Unknown   

05 Jan 2025

1788

da zaku sa ranar d'aurin aure abinda zakuyi kawai d'inki ne fak'at!!!"










Nan fa 'yammata suka kacame da hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinshi daga masu cewa"gaskiya Dad da Ango sunyi sun rage mana wahala" "gaskiya an kwafsa mana da baza'ayi chasu ba" sai masu cewa "hakan ma yayi dai-dai ai, albarkar aure ake nema ba komai ba"








Bayan sun gama exam's da kwana biyu suka shiga raba anko daya yake friends d'in nasu basu da yawa basu wuce 20-25 ba a kwana 3 suka kammala komai domin AYUSHA ba wani gayya tayi niyyar yi ba suma wad'annan d'in dalilin da yasa ta basu I.V ba komai bane illa course mates nata ne da kunya suna tare ba'ayi grads ba suji labarin tayi aure ba invitation, da baza tayi inviting nasu ba.










Sun gama rabiya da kwana d'aya suka tattara suka nufi D'angyatin garin su Aneeserh tare da Mum & Dad, iyayen Ayusha sun sha wahala sosai wajen shawo kan iyayen Aneeserh akan abin da suke aikata mata, da farko iyayen ta rufa ido sukayi suka fara rashin mutunci "wai su babu wanda ya isa ya koya musu yadda zasu tafi da rayuwar iyalinsu, wato ma dan rashin mutunci ma k'ararsu ta kai ko? to daga yanzu sun soke university d'in ma zaman gida za tayi tunda bata san ciwon kanta ba" da yake Mum &Dad mutane ne wayayyu sun san yadda zasu bi da mutum duk irin bak'aken maganganun da suke fad'a musu bai sa sunyi fushi dasu ba, sai ma gyara zama da sukayi saka fara sanar da su illar abin da girman hak'k'in d'a akan iyayen sa.














Jikinsu yayi sanyi sosai sukayi ta kuka suna neman gafarar Aneeserh sannan suka ce ta sanar da Mujaheed idan ya shirya ya turo magabatan sa a d'aura musu aure rana d'aya da Ayusha, nan dai farin ciki ya dawo sabo"














Nan fa Dad ya nemi alfarma cewa idan iyayen Mujaheed sun amince da auren yana so a d'aura a katsina tunda can Aneeserh zata zauna, sannan batun kayan d'aki shi zai musu, Abban Aneeserh yace ya amince a d'aura auren a can amma shi zai musu komai da komai domin a karo ma farko ya faranta ran d'iyar sa.










Kowa ya amince da hakan domin Wannan alamu ne na cewa ya zubda makaman shi, Ayusha ce tayi wa Mujaheed waya ta sanar dashi abin farin cikin da ya faru, yayi murna sosai da daddare ya k'ira ta ya tabbatar mata da cewa gobe iyayen shi zasu zo, a daren suka sanar da iyayensu.










Kamar yadda Mujaheed ya fad'a hakan kuwa akayi domin iyayensa sun zo an tsaida maganar aure, washe gari Mum & Dad suka koma Katsina suka bar su Ayusha a D'angyatin domin Maman Aneeserh tace itama baza a barta a baya ba ita zata gyara 'yammatan ta in yaso ana sauran two days to bikin sai suje gaba d'ayan su.










Duk abinda aka sa masa rana sai yazo yau ta kasance ranar walimar Auren Ayusha da Aneeserh inda Angwaye da Amare da sauran 'yan uwa da abokan arziki suke farin cikin wannan ranar banda Ayusha domin ta so ace da dream guy d'in ta akeyi amma haka tayi ta managing rayuwar ta har zuwa ranar d'aurin Auren.












Ranar Saturday da misalin 10: 30 am aka shaida d'aurin auren ANEESERH da MUJAHEED, AYUSHA da ALHAJI UMAR muna musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa.










Lokacin da Ayusha taji an d'aura aure haukacewa ne kawai batayi ba domin dak'yar Aneeserh dak'awayen su suka shawo kanta domin tirewa tayi sai an warware auren Allah yaso duk Dramar da akeyi iyayen su basu sani ba so sunyi nasaran shawo kanta amma fa wunin ranar da ba a dad'in rai tayi ba.












Da dare yayi su Anty Zee 'yan d'aukar Amarya suka zo nan ma Ayusha tace bata san zance ba da yake normally amare nayin haka sai mutane basu fahimci komai ba, ana cikin show d'in dangin Mujaheed suka zo nan fa aiki ya dawo sabo da k'yar aka raba Ayusha da Aneeserh domin kowa cewa take ba zata tafi ba sai ta raka 'yar-uwarta sai da aka musu da gaske kafin suka rabu.










SARDAUNA ESTATE aka kai ANEESERH ita kuma AYUSHA G.R.A daren ranar da zazzab'i ta kwana duk wanda suka kwana a gidan ta basuyi baccin kirki ba domin ta matuk'ar tada musu hankali. Nidai RØØKÌÊY KÆXS nace Allah ya bada zaman Lafiya AYUSHMAR, ya kawo Zuria d'ayyaba.












Kuma ANEESMU ban barku a baya ba duk da cewa kuna k'aunar junanku hakan ba shi zai sa na kasa yi muku addu'a da fatan alkhairi ba.
















*_#TEAM FAHAD kuyi hak'uri da abinda ya faru nima ba da son raina Alhaji ya auri Ayusha ba amma ku sani mutum bai isa ya wuce k'addarar sa ba, kuyi duba ga Aneeserh a lokacin da batayi zato ba rayuwarta ta canza ta dawo dai-dai domin ta tsaya ta jajirce ta mik'a lamuran ta ga Allah. Dan haka kuyi hak'uri kuci gaba da bibiyata domin tsugunno bata k'are ba dan har yanzu ALLURA bata TONO GARMA ba._*
























*RØØKÎËY D BEST*
[14:56, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*




® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*




*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*


*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*


96-100












Washe gari da safe jikin Ayusha ya tsanan ta sosai dan haka ba'ayi wata-wata ba su Aunty Fareeda suka kaita ALHERI SPECIALIST HOSPITAL wani private hospital da ke nan G.R.A. suna zuwa basu tarar da mutane ba kasancewar asibitin private ne dan haka babu b'ata lokaci Doctor yayi diagnosing nata, bayan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce ya d'ago ya kalle ta da kyau sannan yace "ke ko 'yammata tunanin mai kike haka kina nema ki illata rayuwar ki,gaskiya tunani bai kamace ki ba at your young age" .








Duk da azababben ciwon kan da ke damun ta hakan bai hanata d'agowa ta galla mishi harare ba a zuciyar ta tana fad'in (lalle Doctor d'in nan ya raina min wayo, ina ruwan sa da shekaru na da zaina min kallon yarin ta, yana wani iyayi sai kace shi d'in wani babba ne Mtwss!!!" taja tsaki ashe ya fito fili bata sani ba.










Da sauri yace "sorry 'yammata na miki shishigi a lamarin ki ko" kafin tace wani abu Aunty Khadija ta shigo hannu ta rik'e da waya "Doctor sannu da aiki, Ayusha ga Mummy nan zakuyi magana a waya" bayan Ayusha ta karb'i wayan Doctor yace "Bismillah Anty ga waje ki zauna za muyi magana da ke,ku ne kuka kawo wannan patient d'in ko,dan naga kuna kama sosai hala SISTER d'inki ce ko dama ba wani abu bane illa ina so ku mata fad'a ta rage yawan tunani domin yana gab da ya mata mummunan illah" hospital card ya mik'a mata "ga wannan kuje pharmacy ku siyo Magani,Allura da Drip ne aka rubuta zamu bata gado domin za'a d'aura mata drip kuma condition d'in nata is not stable tana buk'atar hutu"








"Doctor bazai yiwu mu tafi da ita gida a sa mata a can bane,saboda Amarya ce jiya aka d'aura auren ta, kaga hankalin mutane zai tashi sosai idan suka ji an kwantar da ita anan" "eh to za'a iya sa mata a gidan ma amma dan Allah a keb'eta daga cikin mutane domin hayaniyar su na iya coursing wani ciwon, sannan tana buk'atar kulawar ku domin jinin ta ne ya hau sosai sakamakon wani b'accin rai ko damuwa da tasa a ranta so you need to counsel her because she is in risk at her young age"








"Innalilahi wa'ina ilaihi raji'un yaushe Ayusha ta kamu da hawan jini dama ni nasan ba son mijin nan take ba, tunda haka ne wallahi sai an raba auren nan" ta fad'a tana kuka a lokacin ne Aunty Fareeda ta shigo da Ayusha tace "Doctor ga patient d'in ka na dawo maka da ita wai hajijiya take ji sosai" kafin Doctor yayi magana Aunty Khadeeja tace "Ayusha yaushe kika fita bamu sani ba" "ai kina mik'a mata wayar ta fice ina kallon ta, dama zata ji hajijiya mana tana tattare da yunwa cikin ta ba komai ga zazzab'i da sauran su" cewar Doctor kenan.












Aunty Fareeda ta kuma cewa "Khadeeja mai ya same ki naga kamar kina kuka" "ba kama bane Aunty kuka nake Ayusha na d'auke da hawan jini saboda rashin adalcin da aka mata na aura mata wanda bata so, wallahi zanyi iya kacin bakin k'ok'ari na naga an raba auren nan" sai ta kuma fashewa da kuka.










"Yi shiru Khadeeja wannan ba maganar da zamu tattauna a nan bane saboda haka kiyi hak'uri yanzu ta lafiyar ta muke tukun idan mu koma gida zamu san me zamuyi a kai" Doctor ya tambaye su ko suna da wanda zai mata allura ya sa mata drip ne a gidan Anty Fareeda tace "muna dashi Doctor wannan da kake ganin ta ma Nurse ce so zatayi duk abin da ya dace" "OK!!! tunda haka ne ba damuwa kuje ku siyo sai tai mata abin da ya dace Allah ya bata lafiya" "Ameen Doc." suka fad'a a tare sannan suka fita da ita.






Suna fitowa daga office d'in Doctor suka nufi pharmacy, bayan sun gama da komai suka koma gidan Amarya suna isa suka ga gidan ya sake cika da mutane sai faman sannu ake musu, d'akin Ango aka kaita domin nan ne ba hayaniya.








Aunty Zara'u Cousin sister d'in su ce ta shigo musu da breakfast tana fad'in "sannun ku da dawowa, ga breakfast nan Aunty Zee ta aiko tun d'azu" "OK sannu da k'ok'ari K'awas had'awa Ayusha tea tasha, sai tasha magani a sa mata drip" cewar Anty Fareeda kenan.
"Ok to ba matsala Allah dai ya baki lafiya Amarsu ta Alhaji, wallahi yarinya ki kwantar da hankalin ki ki zauna da mijin ki lafiya" Aunty Zara'u gidan surutu kenan tana had'a tea tana suburbud'a zance bayan ta gama suka sa Ayusha a gaba sai da ta kusan shanye one cup sannan tasha magani Aunty Khady ta d'aura mata drip,a hankali ta samu bacci ya d'auke ta sannan suma suka samu sukayi breakfast.










Sun kai kusan minti talatin suna hirar duniya sannan Aunty Khadeeja tace "Sister har yanzu baki ce komai ba game da issue d'in Ayusha da na miki magana d'azu a asibiti ba, nifa gaskiya zan je gida na samu Daddy na mishi bayanin abin da ke faruwa domin wallahi ni bazan iya barin ta cikin halin nan ba"








"Matsala ta da ke gajen hak'uri wallahi, yaushe ma muka dawo gidan balle mu tattauna batun, maganar ki akan hanya take amma yanzu mu bari idan Ayusha ta tashi daga baccin sai muji labarin komai kafin musan matakin da zamu d'auka, kar muje mu yanke hukunci kuma ya zama tana son kayan ta" "haba Sister wani irin so kuma wallahi tallahi Ayusha ba Son shi take ba kawai dai an tursasata ne amma in banda k'addara me zatayi da tsoho sa'an baban ta ko ni da nake da 26yrs yamin tsufa balle Ayusha Sweet 18"













Murmushi Aunty Zara'u tayi tace "Deeja k'aya baki san na gida ba, idan banda abin ki akwai wanda ya isa ya wuce k'addarar sa ne? Allah ne kad'ai yasan dalilin had'a auren nan ki duba fa kiga yadda Mum suke da Aunty Zee amma gaba d'ayan su suka iya amincewa had'in nan cikin sauk'i ai wannan ma kad'ai ya ishe mu muyi accepting fact d'in dan haka ni a ganina raba auren nan ba shine mafita ba addu'a ya kamata mu bisu dashi dan bamu san me zai faru a gaba ba" "yawwa K'awas fad'a mata dai ko zata gane" cewar Aunty Fareeda kenan "babu abin da zan gane wallahi!!! baza ku gane rad'ad'in da take ji ba tunda ku ba auren dole aka muku ba ni dai gaskiya bazan..."






Bata k'arasa maganar ba Ayusha tayi saurin cewa "Dan Allah Aunty Khadija kiyi hak'uri kar a ra ba auren nan wallahi ina son shi na amin ce zan zauna dashi" kawai sai ta fashe da kuka.






Da sauri suka koma wajen ta suna lallashin ta "Ayusha karki yaudari kanki da wad'an nan kalaman da baza su miki amfanin komai ba, ni da ke da su duk mun san bakya son shi, to why not mu samo mafitar da zata sama mana kwanciyar hankali baki d'aya, dalilin da yasa kika ga na dage da hakan shine ni auren soyayya nayi nasan dad'in ta na san d'acin ta, idan kana son mutum no matter how hurting d'in ka da zai yi zaka iya resisting kayi controlling kanka albarkacin SO sai kiga zama yayi lasting forever, but idan baka son mutum baza ka iya jure komai ba no matter how little it is baza a je ko ina ba za'a fara facing problems, kin sani mijina barrister ne nasha ganin cases d'in aure k'iyaya a wajen shi and abin ba dad'in ji that's why bana so kema ki shiga irin wannan halin gashi matsalar kina da kishiyoyi ba d'aya ba ba biyu ba har uku, idan ita Anty Zee mun san tana da pure mind are we sure of the rest? dan haka maganin kar ayi ma kar a fara ne just accept the fact that bakya son shi wallahi you will see wonders" duk wannan bayanin Aunty Khady ke zizaro su.








Wasu Zafafan hawaye ne suka zubo daga idanun Ayusha tabbas tasan maganganun da Aunty Khady take fad'a gaskiya ne amma baza ta tab'a accepting ba tunda har yanzu bata san matsayin ta a wajen Dream guy ba,da ace ta san inda yake to wallahi babu abin da zai hanata d'aukan shawarar 'yar-uwar ta, kai!!! koda tasan inda yake ma baza ta kashe auren ta ba dan tayi alk'awarin sadaukar da farin cikin ta ga iyayen ta, "kinyi shiru Ayusha baki ce komai ba ko har yanzu kina kan bakan ki ne?"










"Tabbas Aunty maganar ki akan hanya take amma bazan iya rabuwa da Uncle Umar ba though ban tab'a jin ko da d'igon son shi a raina ba, nayi alk'awarin sadaukar da soyayyata gareshi domin farantawa iyaye na, nasan duk kan ku baku gane inda zance na ya dosa ba amma Yanzu zan warware muku zare da abawa"








Ido suka zuba mata suna kallon ta nan dai ta kwashe musu labarin abinda ya faru from A-Z hatta labarin Dream Guy bata b'oye musu ba, sannan ta k'ara da cewa "Dan Allah Sisters kuyi hak'uri mu yarda da k'addarar da ta same mu sannan kuyi min wata alfarma ko da wasa kar ku bari wani yasan ina da hawan jini nayi alk'awarin kula da kai na zan koma Ayushar da kuka sani , Mum & Dad idan suka san ina da hawan jini zasu shiga damuwa zasuyi zaton na kasa musu biyayya ne"




Maganganun Ayusha ya tsuma su sannan ta basu tausayi sosai kaf cikin su babu wacca bata zubar da hawaye ba amma basu da yadda suka iya da ita domin matacciyar soyayya takeyi ,wanda take so d'in ma bata san shi bata san komai game dashi ba kuma bata da tabbacin cewa yana son ta itama ko sun kashe auren ma a banzan domin Allah yafi mu sanin dalilin faruwar hakan.












Anty Khady tace "Allahu Akbar Kabeeran!!!,Alhamdulillah Allah shine abin godiya, na gode Allah da bai bari shed'an yayi tasiri a zuciya ta na aikata babban laifi ba Alhamdulillahi ala ni'imatullah" gaba d'ayan su suka amsa da "Allah shine abin godiya" nan da suka din ga jan Ayusha da labaran da zasu sakata nishad'i da walwala, sannu a hankali ta fara warewa kamar ba ita ba.








*_10:00am_*


K'arfe goma dai-dai taje tayi wanka ta can cad'a kwaliya ta sa kaya ta fito fes a Amaryar ta sak, san nan taje ta gaisa da mutane ta dawo d'akin Oga wajen Anties sunyi ta bata shawarwari masu inganci game da yadda zata tafi da rayuwar auren ta tun da ma gidan su ba d'aya da kishiyoyin ba.








*_Bari mu lek'a rayuwar FAHAD (Dream Guy)_*




Kamar yadda na fad'a muku a baya ya hak'ura ya fauwalawa Allah komai dangane da pretty yaci gaba da tafi da harkokokin shi dai-dai gwargwado amma a duk lokacin da ya keb'e shi kad'ai bashi da wani aiki sai tunanin ta da imagining irin rayuwar da za suyi da ita idan sunyi aure.










Wani abin mamaki shine a 'yan kwanakin nan yana yawan mafarki da ita tazo ta durk'u sa a gaban shi tana kuka tana fad'in "dan Allah dan annabi mijina ka taimakeni rayuwata tana cikin hatsari kai ne zab'i na kai ne farin ciki na,kai kad'ai ne zaka iya taimaka min a halin da nake ciki yanzu" shi kuma sai yaja mata dogon tsaki yana fad'in "tafi can malama ki nemi mijin ki bani ba, ni ba sa'anki bane na miki nisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login