Showing 9001 words to 12000 words out of 27538 words

Chapter 4 - ALLURA TA TONO GARMA BOOK COMPLETE .txt

Unknown   

05 Jan 2025

1793

a haka" murmushi Aneeserh tayi tace " 'yanmata stop deceiving your self frankly speaking you are in love dan haka zan taimaka miki da addu'a Allah ya had'aki da lucky guy d'innan da ya sace miki zuciya " murmushi Ayusha tayi tace "ni na dad'e da gano cewa kina da mental problem so na miki uzuri lets go "











Fitowa sukayi daga hall Aneeserh ta rakata bakin gate ta tari Napep bcoz na cikin school d'in is occupied with people, sallama sukayi da junan su sannan suka rabu.








A b'angaren Fahad kuwa yana fitowa daga Fatie Shema estate ya karkata akallar motar shi zuwa hanyar da zata kai shi main road na 'Yar_adua University, agogon hanunshi ya duba yaga time 3: 45pm waje ya Samu yayi parking a kusa da wani masallaci, alwala yayi yai sallan la'asar yana mai addu'an Allah ya had'ashi da pretty d'insa.








4:05pm sharp ya fito daga masallacin motarsa ya nufa gaggawa saboda kar ya makara wajen neman pretty, tuk'i yake a nutse zuciyar sa na mararin kallon ta yana zuwa dai -dai da wajen wani road division d'aga idon da zai yi ya kalli right caraf yayi arbada da side view d'in ta, kokwanto yake kamar ita kamar ba ita ba, bai yi aune ba yaga ta karkato da fuskarta zuwa side d'in da yake, ba shiri ya karkata akalar motarsa daga left zuwa right dan ya cimma su amma unfortunately sun mishi nisa, wani wawan tsaki yaja yace "pretty me yasa zaki min haka, kin san baza ki bari muyi magana ba me yasa zaki bayyana gare ni, dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta, ki tsamo zuciya ta daga kogin son ki " haka dai yayi ta sumbatun sa shi kadai kamar wani tab'ab'b'e, da yaga babu sarki sai Allah sai ya hak'ura ya koma gida.










A b'angaren Ayusha kuwa tana zaune cikin Napep tana ta sak'a da warwara ta yadda za'ayi ta had'u da wannan guy d'in, ji kamar wani abu ta mitsine ta, da sauri ta dawo daga duniyar tunani juyawan da zata tayi arba da kyakkyawar fuskarsa yana k'ok'arin juya kan motar sa da sauri tace da mai Napep d'in "Malam yi sauri ka k'ara speed uzurin gaggawa ya taso min" shi ko kamar jira yake da sauri ya zaburi Napep a 90.








Yana sauk'e ta a k'ofar gida ta zaro 1K ta bashi ta nufi k'ofar shiga gida "Hajiya tsaya ga can jinki " "No ma rik'e na barma" "Godiya nake ranki shi dad'e Allah ya saka miki da alkgairi" "Ameen" tace sannan ta shige gida.










As usual Mum & Dad ta tarar a folo gaishe su tayi ta nufi upstairs Mum ce ta dakatar da ita "Auta dawo nan, akwai maganar da muke son yi da ke yanzu" dawo wa tayi ta samu guri ta zauna a k'asa.










Dad ne ya fara magana kamar haka "haba Autar Mum &Dad me ke damunki ne kwana biyu naga kin canza, idan wani abu kike da buk'ata ai sai ki sanar mana ba kisa kanki a damuwa ba, ke kanki kin sani farin cikin ki shine namu babu abin da zaki nema mu kasa miki face yafi k'arfin mu, saboda haka feel free ki fad'i buk'atarki in shaa Allahu zamu miki gwargwadon iyakar mu" k'ak'alo murmushin dole tayi tace " babu abunda nake buk'ata Dad, kawai dai boko ne ke gara ni, assignment sun min yawa ga thesis dake gaban mu that's all" "Ayusha yaushe kika fara b'oye mana damuwar ki, wannan maganar da kika fad'a ba gaskiya bace, ni na haifeki nafi kowa sanin halinki saboda haka fito fili ki fad'i mana damuwar ki"cewar Mummy kenan.








Shiru tayi for some seconds sannan ta sauk'e ajiyar zuciya tace "Mum & Dad ina alfahari daku kun kasance nagartattun iyaye masu kula da sauk'e nayin da Allah ya d'aura musu, na gode sosai da kulawar ku gareni Allah ya barmin ku, ina so ku kwantar da hankalin ku, ku yarda cewa babu abinda ke damuna face boko stress kun manta 300level nake yanzu komai k'ara zafi yake"










To shi kenan "Auta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" "Ameen thumma Ameen iyayen k'warai " zama tayi suka sha hira da iyayen ta har dare suna tare, da lokacin bacci yayi tayi sallama dasu ta nufi makwanci ta sai bacci ya gagara tunanin shi ya sake dawo mata, wani zazzafan hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta.




Zuciyar ta ce ta fara tariyo mata abinda ya faru d'azu take tace "Ayusha why!!! me yasa zakiyi haka, ke da kike nemansa ruwa a jallo ki bashi hak'uri amma zaki guje masa, kina da tabbacin zaki sake had'uwa dashi nan gaba!?" sai ta fashe da kuka "wayyo ni Shatu na cuci kaina idan na mutu da hakkin mutumin nan me zan cewa mahalicci na, na tabbata cin mutuncin da nai masa ne ke addabar zuciya ta da zaran na bashi hak'uri komai zaiyi normal.










```to masu karatu Ayusha dai ta kasa amincewa tana son Fahad all what she knows is that tana bashi hak'uri shike nan zata ci gaba da normal life nata. Shin haka abin yake ko yaya ina,idan kuma akwai wani solution da kuke gani Ayusha zata bi tunanin Fahad ya bar zuciyar ta ta ko da basu had'u ba to sai ku bata ina jiran comments naku kafin nayi typing next page NA BARKU LAFIYA taku har kullum```












*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*




® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*










*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*


*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*




*_Kindness Indeed Is Kindness I will never ever forget you in My life, you are more than a friend to me, My love for you is parmanent no wala-wala no algus I really appreciate your kindness, love,care and concern, you always put me in the right part when I'm wrong, you make sure i succeed before we depart i really miss you My Mentor HANEEFAH USMAN the whole page is your's������i heart you Beb❤ keep on rocking dear you rock even in the heart of your enemies LONG LIVE MY HANNEE_*












36-40








Babu abin da kunnuwan ta ke d'auko mata sai sautin zazzak'ar muryar sa me kama da busan sarewa a sa'ilin da yake ce mata "pretty wait!!!" a fili ta furta kalmar "OMG!!,wallahi ni d'in nan banza ce me yasa na wulak'anta shi ban tsaya na saurare shi ba, to wai ma ina ruwa na dashi ne da zan tsaya ina tunanin shi may be ma ya manta da existence d'ina yana can yana harkokin gaban sa ya barni da tunani!" tana ta tunane-tunen sa har sarkin iya sata ya sace ta, a b'angaren Fahad ma haka abin yake tunda ya shiga d'aki ya watsa ruwa ya haye gado bai sake sanin halin da yake ciki ba dan ya tafi duniyar tunanin pretty bai samu ya rintsa ba har asuba.












Tunda bacci yayi awon gaba da ita bata farka ba sai 6:30 a firgice ta tashi tana salati, tana ganin time tace "ya salaam!!!, yau nice na makara banyi sallar asuba a kan lokaci ba" da sauri ta sauk'o ta nufi toilet ta d'auro alwala ta gabatar sallah da azkar sannan ta fad'a toilet tayi wanka, a gaggauce ta shirya cikin wani material gown rose pink, light make up tayi sannan ta d'auko milk veil tai rolling takalmi da jaka ma milk sannan ta feshe jikinta da designer perfume na FARASHA ta fito daga d'akin ta nufi wajen Mummy.










Tana shiga d'akin Mummy taga wayam da alama bata ciki so direct kitchen ta nufa ta taradda ita tana had'a musu breakfast, " Morning sweet Momma da fatan kin tashi lafiya!" "lafiya lau Auta,har kin fito, to maza je ku gaisa da Daddyn ki a falo kiyi break" "Mum ni fa bana jin zan ma iya cin abincin nan ba yau nayi latti sosai" tana gama fad'in haka tayi saurin ficewa daga kitchen d'in dan tasan halin Mummy yanzu zata sata a gaba tace sai tace and ita kwata-kwata ma bata buk'atar cin komai.







A falo ta iske Dad d'urk'usawa tayi har k'asa tace "Morning Dad da fatan ka tashi lafiya" "lafiya na lau Auta an shirya boko kenan, yana da kyau a dinga bada himma, Allah ya miki albarka, ya sanya albarka a rayuwar ki ya baki sa'an abinda kika je nema" "Ameen Thumma Ameen Sweet Papa, ni zan wuce school" "ki tsaya muyi breakfast sai nayi dropping naki tun da ba motor a hannunki" "A'a dadi ka bari zan tafi a NAPEP coz idan na tsaya break zanyi latti" "ok ba damuwa ga 5k ki rik'e a hannunki ko zaki buk'aci wani abu" "No Dad ka bar shi akwai kud'i a hannu na wanda mijin Anty Zee ya bani jiya" "to shi kenan Auta a dawo lafiya Allah ya kare" " Ameen"








Tana fita k'ofar gida ta samu NAPEP ta shiga, a cikin gida kuwa Mum & Dad na breakfast Daddy ya kalli Mummy yace "Fatima wai baki fahimci wani changes a tattare da Auta ba ne?, naga yau d'in a bai-bai take" "wallahi Alhaji rigani furtawa kayi amma tun jiya da daddare na fahimci hakan,amma koma miye ne anjima idan ta dawo sai mu tambaye ta" "to shi kenan Allah ya kaimu anjiman dan ni sam bana son ganin Auta ta cikin damuwa" haka dai sukayi ta tattauna wa game da batun Ayusha.












Tana shiga school ta k'ira Aneeserh a waya, ringing biyu yayi tayi picking "Hello K'awata wai kina ina ne tun d'azu ina ta trying layinki ban samu ba yanzu har Mr Patrick yayi lecture baki nan" "wallahi yau makara nayi ban tashi da wuri ba yanzu haka na shigo school d'in kina ina" "ok ki zo ina zaune a bayan library" "ok to ganin nan zuwa"








Tana zuwa bayan Library ta hango Aneeserh a zaune waje ta samu kusa da ita ta zauna sannan suka gaisa kallo d'aya Aneeserh tai mata ta gane tana cikin damuwa sassauta murya k'asa tayi sannan tace "k'awata me ke damun ki dan naga damuwa k'arara a fuskar ki" "ba komai kawai dai bana jin dad'i ne" " Hmm... K'awata kenan to ai baki san wani abu ba duk wanda yasan ki a jiya ya ganki yau ya san kina cikin damuwa balle kuma ni da muke tare da ke kullum ya za'ayi dan naga changes a tattare da ke na kasa fahimta kawai Malama ki fad'a min matsalar idan da taumakon da zan iya sai nayi" shiru tayi na d'an wani lokaci sannan daga baya ta sauk'e wani dogon ajiyan zuciya sannan tace "jiya bayan mun sauk'e a hostel mun juyo", nan dai ta zayyane mata labarin Fahad hatta baccin da ta kasa saboda shi bata b'oye mata ba daga bisani tace
"wallahi ni babban damuwa ta ma shine bai wuci ina zan ganshi na bashi hak'uri ba" Aneeserh tayi shiru tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata in sha Allahu Allah zai bayyana miki shi and also na fahimci cewa zuciyar ki tana k'ok'arin fad'awa tarkon so ko ma in ce ta fad'a ciki tsundum" "lalle yarinyar nan baki da hankali dan nace miki ina son ganin shi na bashi hak'uri sai kice na kamu!!! ce miki akayi na shirya yin soyayya yanzu" " ko kuma kece babbar mara hankali ba yaya kike k'ok'arin hana zuciyar ki a bin da take so, Ayusha ki saurare ni da kyau kin san dai na girmeki a k'alla na baki shekara d'aya me kyau so wajen hankalin ma da bambanci,ke da kanki kin san na fiki sanin me duniya take ciki must especially ma ta b'angaren soyayyah!!" tana gama fad'in haka ta tuntsire da dariya dundu Ayusha ta d'aka mata sannan tace "shegiya yar iska ai dama anan kika fi k'wari ko Romeo and Juliet haka suka ganki suka barki " sosa wurin dundun tayi tace "Allah ya isa daga fad'an gaskiya sai ki dake ni" haka dai sukayi ta shirmen su har next period yayi suka koma lecture hall.










A b'an garen Fahad kuwa tun bayan da ya idar da sallan asuba ya kwanta bai farka ba sai 12:pm shima da k'yar ya iya tashi yayi wanka yaje gaida Mum a falo ya sameta tana kallo waje ya samu ya zauna sannan yace "ina kwana Mum, da fatan kina lafiya" tun da ya shigo falon take kallon shi har zuwa lokacin da yake gaisheta bata sauk'e idonta a kan sa ba har ta amsa masa da "lafiya My Son, sai yanzu ka tashi daga baccin Abban ku ya bar sallahu cewa idan kayi ka biya office ka same shi " "ok" shine kad'ai abinda ya fad'a ya mik'e tsaye sannan yace "Mum ni na tafi amma dan Allah kimin addu'a Allah ya had'ani da pretty na bata hak'uri" murmushi tayi tace "dawo ka zauna My Son akwai wata muhimmiyar magana da zamuyi da kai"










Waje ya samu ya zauna yana kallon ta sai da ta tabbata yayi paying attention nashi sosai sannan ta ce " yi maka addu'a ya zama wajibi a gareni My Son, amma dan Allah ina so ka nutsu ka kwantar da hankalin ka idan Allah yayi zaka had'u da pretty ka bata hak'uri zaku had'u dan haka ka cire damuwa a ranka ka dawo normal yadda kowa ya sanka daga jiya zuwa yau duk kabi ka susuce ka sukurkuce, ko breakfast bakayi ba ka kama hanya zaka fita kuma na tabbata idan ka fita ma ba abincin zaka nema ba kuma kasan matsalar da kake fama da ita, dan haka bari na d'auko maka d'umanen ka na jiya" shiru yayi yana kallonta dan yasan tunda ta zaunar dashi to sai yaci abincin.








Tashi tayi ta shiga kitchen ta d'auko masa abincin ba tayi tsammanin zai ci na kirki ba saboda yanayin damuwar da ke bayyane k'arara a fuskar shi amma ga mamakin ta sai taga ya cinye tas.








"Yawwa ko kai fa da kaci abin cin ai zaka fi samun kuzari a jikin ka" "wallahi Mum yarinyar nan A ce a girki Allah yasa pretty ma ta iya girki haka" "Ameen My Son, yanzu dai ka tashi ka tafi wajen Abban naku" " ok Mum sai na dawo" "to a dawo lafiya Allah ya had'a ka da pretty" "Ameen Sweetheart" ya fad'a yana dariya sannan ya fice.






Bin shi tayi da ido tana mamakin yadda akayi d'anta ya sukurkuce one time " ya Allah ka bayyana mishi wannan yarinyar idan har alheri ce a rayuwarshi" ta fad'a a fili.







Yana fitowa daga gida ya shiga motor Mai gadi ya bud'e masa gate ya kama hanyar office d'in Abba, a zuciyar sa sai sak'a da warwaran hanyar da zai bi yaga pretty yake, "ya zama dole ina barin wajen Abba na shiga Yar-adua neman pretty na" wanna shine kalmar da yake ta maimai tawa har ya isa office d'in.










Yana zuwa ya tarad da Abba da wasu bak'i seat ya samu ya zauna sannan ya gai da su a ladabce da fara'arsu suka amsa mishi sannan Abba yace "Fahad har ka iso kenan, to ya ka baro mutanen gidan" "lafiyan su lau Abba" d'aya daga cikin mutanen ne yace "au Alhaji Umar kana nufin Fahad d'an wajen ka ne ya zama haka" Abba yace "k'warai kuwa" "ikon Allah gaskiya girman d'an mutum ba wuya nifa rabona dashi ina jin tun yana secondary, Masha Allah" Abba yace "lalle kun dad'e baku had'u ba, Fahad wannan fa Alhaji Nafi'u ne Abban Su Muneer,wan can kuma baka san shi ba abokin mu ne Alhaji Hussain daga Niger yazo" Fahad ya sunkuyar da kai k'asa "Allah Sarki Abba sannu da zuwa ya Niger d'in da fatan ka barota lafiya, Abba ya gida ya su Muneer shima mun dad'e bamu had'u ba"







Alhaji Nafi'u yace "Muneer lafiyan shi lau yana India next month zai kammala masters nashi ya dawo" "Masha Allah" cewar Fahad sannan Alhaji Hussain yace "Niger lafiya lau take, yaushe zaka kawo mana ziyara" murmushi yayi yace "next week zan koma school amma in shaa Allahu ida na dawo next year zan je, domin akwai friends d'ina da nake son kai wa ziyara can" "Masha Allah ai ziyara na da kyau sosai" Abban Muneer yace "kai yanzu a ina kake karatu ka kammala degree d'in ne ko yanzu kake yi" Murmushi Abba yayi yace "ai yaron naka da zafin shi ya taho ya gama Degree &Masters nashi yanzu haka yana PHD a U.K next year in sha Allah zai gama" "wow!!! lalle yaron nawa babba ne wani course yake studying" "International relationship" cewar Abba gaba d'ayansu suka ce "gaskiya abu yayi kyau Allah yayi Albarka" "Ameen" ya amsa musu dashi sannan Abba yace "dama ba komai bane yasa nai k'iranka,illa ina so kaje ka gano min sabon gidan da na siya last week a FATI SHEMA ESTATE ka gano irin gyara-gyaren da ya dace ayi sai ka sanar dani" " ok Abba in shaa Allahu yanzu zan je" "yayi kyau Allah yayi albarka,yauwa ina fatan ka fara shirye-yen komawa school d'in dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login