Showing 12001 words to 15000 words out of 27538 words
ko?" "Ameen Abba na gama komai" "yayi kyau" sallama ya musu ya bar office d'in.
Direct FATI SHEMA ESTATE ya wuce bayan ya duba yana yin gidan da komai da za'a buk'ata sannan ya kama hanyar Umar Musa Yar'adua University.
```masu karatu kuci gaba da bibiyar yar Mutan yobe dan ganin me zai faru a gaba da fatan Allura ta tono garma na baku feelings.
Na barku lafiya ni ce dai har kullum```
[14:53, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Wannan Shafin naki ne FEEDO DEEDO YAR-FICIKA My Aminiya A.K.A Mosoyiyar amma fa a daa bcoz yanzu kin zama 'yar AIR (Lols)Allah ya barmu tare, Allah ya nuna mama ranar Aurenku da Ahmadie muje KT mu kwashi shoki_*
51-55
Alhaji ne yayi ta maza ya fara magana kamar haka " dama ba komai ke damuna ba illa...." sai kuma yayi shiru "illa me?, dan Allah ka daure kayi magana mana" "Hmm!!! bawai maganan bane bana so abin da zai je ya dawo nake gudu" "kar ka damu in sha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi, saboda haka feel free and say out your mind " "emm... to dama de tun ranar da na fara kallon ta Allah ya dasa min k'aunar ta a raina, da tunanin ta nake kwana dashi nake nake tashi, duk hanyar da zanbi naga na yak'i zuciya ta nayi amma abin ya gagara dan Allah dan Annabi ki taimaka min na same ta wallahi idan ban mallake ta ba komai zai iya faruwa" yana kai wa nan ya fashe da kuka.
Da sauri ta matsa kusa dashi sannan ta rungumo shi jikin ta tana bubbuga bayan shi kamar wani k'aramin yaro sannan tace "ka kwantar da hankalin ka My Love kai kanka kasan bani da wata matsala akan kishiya, fatana shine Allah yasa sauran matan naka su yarda" wani sassanyan ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Alhamdulillah! amincewar ki kawai nake nema Hajjaju sauran nasu mai sauk'i ne"
"To amma me yasa kafi buk'atar amincewa ta fiye da na sauran matan?, ina so ka sani dukan mu matan ka ne matsayin mu d'aya ne a wajen ka so suma suna da hak'k'in ka sanar dasu" "haka ne amma kusancin da ke tsakanin ki da ita nake dubawa shi yasa nafi bid'ar taimakon ki"
"Hmm!!! kusanci ya wuce Wanda ke tsakani na da Muneerah amma ka rufe ido ka aureta to yanzu me zai sa na tada hankali dan zaka auri wata" "Hajjaju kenan dan Allah ki daina tuna abinda ya faru a baya"
"Abban Fahad kenan ai tuna baya ya zama dole, ehm! wai ni wace kake son aura ne haka da kake cewa akwai kusanci tsakani na da ita?"
Take yaji wani wawan fad'uwan gaba saboda yasan yanzu game d'in zai fara" "kai fa nake tambaya kamin shiru?" ta sake jefo masa wata tambayar unexpected , dakewa yayi yai ta maza a zuciyar sa ya k'udirta cewa ya zama dole yayi jahadi ya fad'a mata ko ma wace ce !!! sai da ya gama tattaro nutsuwar sa baki d'aya sannan yace "d'iyar ki AYUSHA 'yar Hajia Fateema nake so,kin ga idan nayi haka na raya sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam" ni Rukayyatuwa nace "Sunnah me k'arfi ma kuwa"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, Alhaji me kake so ka zama a duniya, yanzu budurwar zuciyar taka har takai ka son d'iyar cikin ka, no wanda kake ta kwana-kwana ashe kasan me ka tab'uka tsabar idon ka ya rufe zuciyar ka ta k'ek'ashe ka kasa tuna matsayin Ayusha a waje na, to idan ka manta bari na tuna maka Ayusha 'ya ce wajen Aminiyata da muka tashi tun muna yara saboda haka idan kai baka d'auke ta a matsayin 'ya ba ni 'ya take a guna kuma kai ma ya zama dole ka yarda da hakan, ko da yake bazan yi mamaki ba tunda ka Auri Muneerah waye baza ka aura ba, ina so kasan wani abu guda nasan tunda ka furta kana sonta ban isa na fidda maka ita daga zuciyarka ba amma ka sani k'arshen zamana da kai yazo, saboda bazan tab'a iya had'a shimfid'ar aure da d'iyar ciki na ba, ina!!! wallahi never,over my dead body" tana gama fad'in haka ta fashe da kuka sannan ta mik'e ta nufi hanyar fita.
Tana zuwa bakin k'ofa yayi saurin zuwa ya sha gabanta, zuba gwiwowin sa yayi a k'asa ya dafa k'afafun ta da hannayen sa sannan yace "Hajia dan girman Allah kiyi hak'uri ki fahimce ni, wallahi banyi hakan da niyar CIN AMANA KO CIN ZARAFI a gareki ba illa dan zuciyata ta samu sukuni daga tarkon da ta afka, nima ba yin kaina bane, kin san shi SO ba ruwansa da cancanta, ba ruwansa da dangantaka,please kiyi hak'uri ki taimaka ki cetoni, ki fidda ni cikin halin da nake ciki, wallahi tallahi ba yin kaina bane" sai ya fashe da kuka, bangaje shi tayi tace "dakata malam ni fa ban hanaka auran abinda zuciyar ka ke so ba, idan ka ga dama ba Ayusha ba ka had'ada Hafsat da Maryam ma ka auro ba damuwata bane amma ka sani ni Zainab bazan iya zama da kai a matsayin miji ba, mai budurwar zuciya kawai mtswww...." ta fice ta barshi a d'akin.
Tunda ta shiga d'akin take ta faman Safah da Marwa, can ta tuna ashe fa ta manta wayan ta a d'akin shi da sauri ta nufi hanyar d'akin nasa domin tana da buk'atar wayan a kusa da ita, tana shiga d'akin ta tarar dashi kwance shame-shame a k'asa dak'yar yake numfashi, da sauri ta nufi inda yake "na shiga uku Alhaji lafiya!!! , me ya sameka" a dai-dai lokacin ta k'arasa wajen da yake kwance, wani nishi me k'arfi taji ya sake sai numfashin sa ya d'auke d'if!!! wani mahaukacin k'ara ta saki "wayyo Allah jama'a kuzo ku taimakeni Alhaji ya mutu" da gudu mutanen gidan suka hallara, basu tsaya wata -wata sukayi rushing nashi zuwa AUTOPEDIC HOSPITAL dake nan katsina.
```TAKU HAR KULLUM```
*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Wannan Shafin naku ne_!!!*
*_AYUSHA ILIASU MUSA (the eloquent writer of 'YAR BOKO very Interested and Educative Novel) & AMEERAH AMNOOR (Saraku for life)na gode sosai da gudunmawar da kuke bani Allah ya bar zumunci (AMEEN) ina k'aunar ku har cikin raina irin SOSAI d'innan��_*
55-60
Suna zuwa asibiti aka shiga dashi emergency room, likitoci biyu ne a kanshi, take nan suka shiga bashi taimakon gaggawa. Hajia Zee da sauran kishiyoyin ta na zaune a reception sun shiga cikin matsanan cin tashin hakali, kallo d'aya zaka musu su baka tausayi most especially ita da tafi kowa sanin mene ne musabbabin abin, tambayar ta suke me ya sameshi amma ta kasa basu amsar komai saboda tasan zafin kishin Muneerah yanzu sai ta fara musu hauka a asibiti shiyasa suna tambayar ma tace "yanzu bata wannan muke ba, fatan mu dai Allah ya bashi lafiya sai muyi maganar daga baya".
*_BAYAN HOUR D'AYA_*
Dr' Sa'ad ne ya fito biye dashi wata nurse ce hannun ta d'auke da file, yana k'arasowa suka nufi wajen shi at once suka jefo mishi tambaya "Likita ya jikin nashi, ya farfad'o ne?" "Ku biyo ni office mayi magana can"
Suna shiga suka samu waje suka zauna, rubutu yayi a hospital card nashi sannan yace dasu "Hajiya ku kwantar da hankalinku in shaa Allahu zai samu lafiya, dama yana da Asthma ne?" "Eh! Doctor yana dashi " "ok, Allah ya basa lafiya, asthma d'insa ce ta tace due to wani abu na b'acin rai da ya sameshi and bai samu yasha magani ba har k'arfin numfashins sa ya d'auke so hakan yayi leading to doguwar suma, yanzu haka Dr. Ahmad na gudanar da wasu bincike a kansa in shaa Allahu zai farfad'o any moment from now, so ga wannan kuje pharmacy ku siyo da sauri magani ne da allurai, dan yana farkawa za'a mishi alluran "
Da sauri Anty ta k'arba tace mun gode Doctor, sannan suka fice daga office d'in zuwa siyan magani, tana zuwa pharmacy aka duba bubu ko d'aya daga cikin so da sauri ta k'ira driver a waya yazo ya sameta su shiga gari ne, ko minti uku batayi da k'iranshi ba ya zo suka tafi.Sun je a k'allah chemist uku basu samu ba sai a na hud'un suka samu complete.
Ko 30 minutes basuyi da fita ba alhaji ya farfad'o a dai-dai lokacin Hajia Muneerah da Hajia Rahma sun shigo, "Hajia dan Allah dan Annabi ki barni na aureta, wallahi nayi alk'awarin yin adalci a tsakanin ku" kalmar da ta fara fitowa daga bakin shi kenan.
"Tabd'i jam!!! wallahi sai dai ka mutu baka aureta ba, wato dama ciwon SO ne ya kwantar da kai anan duk muka bi muka tada hankalin mu to wallahi baka isa ba" "haba Muneera me yasa sam baki da tausayi ne, ki dubi halin da bawan Allan nan yake ciki amma kizo ki titsiye shi da masifa da wanne zai ji da ciwon da ke jikin shi ko da masifar ki"
"Ai dama ke ba hankali ne dake ba Rahma!!! ko da yake kin ci amanata kin aure min miji ai baza ki damu ba dan yace zai k'ara aure" " dakata!!! malam kar ki nemi ki wuce gona da iri dan na auri mijin ki sai me, ke d'in ba mijin wata kika aure ba, idan abin kunyar ne ma ai daga gindin ku ya fara fitowa mtsww!!!"
Suna cikin hayaniyar Anty Zee ta shigo d'akin idonta bai sauk'a a ko ina ba sai kan Allahi da yake ta fitar da wani irin numfashi yana kakarin amai, da sauri ta bankad'e su ta nufi wajen shi tana "innalillahi wa'inna ilaihi raj'un!!!"a dai-dai lokacin ya fara amai, wani ihu Anty Zee ta saki "wayyo Allah na shiga uku!!! shi kenan kun k'arasa shi aman jini fa ya keyi" wani mugun tsaki Muneerah ta saki sannan tace "idan k'arasawan ne ma sai dai in ke zaki k'arashi tun da kin k'i amince mishi ya aure wacca yake so, wallahi ki sani duk abinda ya samu mujina to kiyi kuka da kanki" tana gama fad'in haka ta fita ta nufi office d'in Doctor Sa'ad da gudu.
Abin bai bawa Anty Zee mamaki ba saboda ta dad'e da fahimtar cewa Muneerah, jaka ce bata hankali, a kan kishi babu abinda bazata iya yi ba.Ita ko Rahma nufowa tayi wurin Anty Zee ta taimaka mata suka d'aga Alhaji dan har ya gangaro daga kan gadon.
Doctor Sa'ad ne zaune a office Muneerah ta shigo da gudu Doc!! Doc!! please we need your help Alhaji zai mutu kazo da sauri ka taimake shi kar ya mutu" kawai sai ta fashe da kuka "Sorry Madam,you don't need to cry addu'ar ki yafi buk'ata by now , so muje in ganshi"
Suna shiga suka tarar Doctor Ahmad yazo joining nashi Sa'ad yayi suka bashi duk wata kulawa da ya dace, alluran da aka siyo Sa'ad ya mishi sannan ya umarce su da su biyo su office d'in doctor Ahmad.
Suna shiga suka basu wajen zama, bayan sun zauna Doctor Ahmad ya fara magana kamar haka "da farko ina so na sanar daku cutar da ke damun mijin ku tare da hanyoyin da za'a bi a shawo kan matsalan, idan har kuna son lafiyar mijin ku ya inganta to sai kun taimaka masa, kun k'arfafa masa gwiwa wajen ganin ya samu abin da yake so, mijin ku ya kamu da Heart Attack wanda akafi sani da ciwon zuciya sakamakon mummunan b'acin rai da ya shiga game da wani abu wanda mu nan bamu sani ba sai ku matansa, rashin wannan abin na iya zama barazana ga rayuwarsa"
Doctor Sa'ad kuma ne yace "kamar yadda d'an uwana ya muku bayani zan d'aura nawa akai, mutanen da suke d'auke da irin wannan cutar suna buk'atar kulawa ta musamman, lallab'asu ake kamar k'ananan yara, a guji duk wani abinda zai b'ata musu rai saboda lafiyan su idan ba haka ba komai zai iya faruwa Allah ma ya rufa asiri" gaba d'ayansu suka amsa da "Ameen" Doctor Ahmad yace "kuma dan Allah kar a taru a wajen shi dayawa idan da hali ma mutum d'aya ya zauna a wajen shi" "shi kenan Doctor in shaa Allahu zamu kiyaye duk abinda kuka ce bi'izinillahi rabbi zai samu abinda ya keso"
Tun da ta fara maganar Muneerah ta zuba mata eyes jira take takai aya ita kuma ta d'aura daga inda ta tsaya, Anty Zee na rufe baki tace "Ai nasan ke abin bazai tab'a damunki ba, so dole kice zai samu abinda yake so tunda ba ke za'ayi wa kishiyar ba" "to ke da kike tada jijiyoyin wuyan ke za'a yiwa kishiyar?" cewar Rahma kenan.
Doctor Sa'ad yace "dan Allah Hajiya kuyi hak'uri ya isa haka, yanzu da lafiyar shi zaku ji ko da batun kishiya" ya nuna Muneerah yace "ke d'in ba yanzu kika zo waje na kina kuka in taimaka miki baki son Alhaji ya mutu ba?, amma gashi kece me tada zaune tsaye, abinda nake so ki sani shine kiyaye lafiyar shi a hunnun ku take sai ki zab'a ko, ki barshi ya samu abinda yake so ko kuma rayuwar shi ta k'are a haka, dan naga alama ke ce me matsalan" yana gama fad'ar haka yayi ficewar sa suma fitowar sukayi daga office d'in suka nufi wajen Alhaji, bacci yake sosai amma kana ganin shi kasan yana fama da jiki.
Misalin k'arfe biyar da rabi ya farka, Anty Zee da Rahma ne suka taimaka masa ya zauna, "sannu Alhaji, ya jikin da fatan ka fara jin k'arfin jikin ka" atare suka fad'i hakan, shiru yayi yana kallon su d'aya bayan d'aya "ina Muneerah take" ya fad'a a hankali bud'e k'ofar d'akin da akayi ne yasa su yin shiru basu bashi amsa ba.
Da sauri ta k'araso wajen shi tana fad'in "ka kwantar da hankalin ka mijina in shaa Allahu zaka samu abinda kake so dukanmu mun amince ka k auri wacca kake so, ko ba haka ba Anty" da k'yar Anty Zee ta iya d'aga kai ta amsa mata alamar eh!!! haka dai sukayi ta kwantar masa da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya a haka dare tayi suka tattara suka koma gida suka barshi da Anty Zee.
Washe gari y'an dubiya sukayi ta zuwa dubashi cikin su harda Mummyn Ayusha da Dad, satin su d'aya a asibiti aka sallame su suka koma gida, kulawa sosai yake samu wajen matan sa a haka har ya wartsake ya dawo normal kamar bashi ne yayi jinya ba.
*_BAYAN SATI BIYU_*
*_5: 00pm_*
Alhaji Umar na zaune a d'aki yana sana'ar tasa wato tunani, Hajia Zee ta shigo d'auke da tea flask da fara'ar ta ta k'araso gurin shi ta ajiye flask d'in a kan center table,mug ta d'auko ta tsiyaya mishi sannan tace "Alhaji ga ruwan zafin nan ka sha" shiru taji yayi bai amsa ba, ajiye mug d'in tayi a gefe ta d'aura hannu ta a saman nashi tace "haba Abban Fahad, dan Allah yaushe zaka daina tunanin nan haka tunda muka dawo daga asibiti nace zan je na sanar da iyayen Ayusha abinda ake ciki ka hana, kuma kai banga kayi yink'urin yin wani abu a kai ba gaskiya ni kam bazan iya jurar ganin ka a irin wannan halin ba saboda haka in shaa Allahu gobe zanje gidansu na sanar da iyayenta halin da ake ciki"
"Kina da tabbacin cewa yarinyar da iyayenta zasu yarda? " shine tambayar da ya jefo mata "kwarai kuwa tun da na amince in shaa Allahu suma baza su k'i amincewa ba dama abinda zai hanasu amincewa saboda ni ne" "to naji, idan iyayen ta sun amince yarinyar kuma fa?" "kar ka tada hankalin ka akan wannan Ayusha kamilar yarinya ce, mai tarbiyya da bin umarnin iyaye matuk'ar iyayenta suka yarda da kai to itama zata yarda domin a duniya bata tab'a bijirewa umarnin su, idan kana tunanin cewa ko tana da wani saurayi ne a'a mahaifiyar ta ta shaida min har yanzu bata fara soyayyah ba"
"Madallah da matar k'warai irinki, Hajiya Zainab Allah ya saka miki da alkhairi yasa ki gama da duniya lafiya, da ace duka mata zasuyi koyi da irin kyawawan halinki da mata dayawa baza su shiga wuta ba"
```Masu karatu ku jimin Alhaji da sweet mouth... Lols
Sai mun had'u a next page dan gani badak'alar da za'a kwasa
Bissalam
Nice har kullum```
*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION &