Showing 18001 words to 21000 words out of 27538 words
sannan wani hali Fahad yake ciki. TAKU HAR KULLUM dai_*
*_RØØKÏÊY D BEST_*
[14:55, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
71-75
Suna fita waje suka tarar da Mallam Ayuba mai gadi a tsaye a kanshi, kin kimarshi sukayi da Dad suka sashi a motor Aunty Zee a gefen shi Mum a gaba Dad na driving, Mum ta kalli Aneeserh tace "ki koma ki kula da k'awarki sai mun dawo" "to Mummy a dawo lafiya" "Allah yasa"
Dad ne ya kalli Aunty Zee yace "Zainabu wani asibiti zamu je!? " cikin muryar kuka tace "Autopedic, a can file d'insa yake" "ok"
Aneeserh na shiga ciki ta tarar Ayusha ta fito daga toilet da alama alwala tayi, kallon ta tayi taga gaba d'aya one time ta canza ta birkice ta susuce take taji tausayin ta ya k'ara kamata tace "k'awata alwala kikayi ne, wallahi baki ga halinda bawan Allah nan yake da kin tausaya mishi sai kin ganshi very unconscious wallahi"
Tsaki Ayusha taja tace "to ina ruwana da unconsciousness nashi idan ya gadama ya mutu ma ba damuwata bane,nima ku barni naji da abinda ke damuna!!" tana gama fad'in haka ta wuce ta d'auko sallaya ta shimfid'a ta zira hijab ta fara sallah.
Girgiza kai Aneeserh tayi tace "Allah ta kyauta" ta wuce ta d'oro alwala ta gabatar da nata sallan, bayan ta idar tace da Ayusha "k'awata na tabbata da kin ganshi sai kin tausaya mishi" "dakata!!! nifa bana so kina min maganan tsohon najadun nan, me yasa ni baza ku tausaya min ba sai shi, wallahi tallahi na tsane shi duniya wa lahira shine mutum na farko da yake k'ok'arin ruguza farin ciki na, tun da na taso a rayuwa ta Dad bai tab'a d'aura hannun shi a jikina da sunan duka ba amma a sanadiyar shi har mari na yayi,ina da wanda nake so a zuciyata amma zuwan mutumin ciki rayuwa ta na shirin rabani da abin k'auna ta abin alfahari na wanda nake fatan kasancewa dashi har abada" sai ta fashe da kuka "mai yasa bazan tsaneshi ba, saboda shi Mummy &Dad suka tafi suka barni ba tare da sun yi la'akari da abinda zai biyo baya ba"
Kuka ne yaci k'arfin ta tayi shiru, Aneeserh ta matso kusa da ita tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata na fahimce ki sosai, amma yaushe kika fara soyayya bamu sani ba, sannan wane ne shi saurayin naki a ina yake?"
"Na fara soyayya ba tare da ni kaina na san hakan ba sai yanzu, ban san sunan wanda nake so ba, kuma san komai game dashi ba all what i know about him is Love!!! in fact bai ma san inayi ba amma ni dai ina son shi, k'awata ki taimaka ki nemo min shi wallahi i can't live without him"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un!!! wannan wani soyayya ne k'awata, ta inna zamu fara nemanshi tunda bamu da details akan shi!" "ni dai kawai ki nemo min shi idan kina so nayi alfahari dake a matsayin jajirtacciyar k'awa" "to shike nan, Allah ya shige mana gaba" "Ameen"
Haka dai suka zauna sukayi ta tattauna batun ko zasu samu solution amma shiru, daga baya Aneeserh ta tashi ta shiga kitchen ta girka musu abinci ta zuba wanda za'a kai asibiti.
*_AUTOPEDIC HOSPITAL KATSINA_*
Suna shiga nurses suka zo da wheelchair suka d'auke shi sai emergency room, sun ci sa'a Doctor Sa'ad ne on duty so bai sha wani wahalan binciken me ke damun shi ba, treating nashi yayi based on physical observation.
Bayan an shiga dashi ciki Anty Zee ta k'ira sauran matan a waya ta sanar dasu halin da suke ciki, Mummy & Dad ne suke controlling nata domin gaba d'aya tayi loosing hope a kan Alhaji sai faman sumbatu take kamar zararriya.
*_30 MINUTES LETTER_*
Doctor Sa'ad ne ya fito rai a b'ace daga emergency, wata nurse na biye dashi da files a hannun ta ko k'ala bai ce musu ba ya wuce office Nurse ta kallesu tace "kune patient relatives da aka kai Emergency yanzu ko"
"Eh mune" cewar Dad "Ok!!!Doctor na son ganin ku a office" da sauri suka nufi office d'in doctor Sa'ad, suna shiga suka samu seat suka zazzauna.
Doctor Sa'ad ya kalle su da kyau yace "Alhaji me yasa kuka bari ya shiga cikin matsananciyar damuwa haka, wallahi badan kunyi gaggawar kawo shi asibiti ba da sai ta Allah kawai yanzu haka mun samu munyi resolving case d'in amma sai mun kai shi ICU (Intensive Care Unit) domin tabbatar da k'wak'awaran bincike a zuciyar sa and also ina shawartar ku da ku nemo masa abinda yake so wanda rashin sa yayi coursing ciwon, domin ganin abin a kusa dashi na iya taimakawa wajen samun lafiyar shi"
Dad yace "ba komai in shaa Allahu za'a nemo masa abin, yanzu ya jikin nasa" "jiki Alhamdulillah, yanzu haka mun masa allura da zata taimaka wajen dai-dai ta bugun zuciyar sa, so zai iya kai wa kamar kwana uku bai farka ba, amma in shaa Allahu da zaran ya farka za'a ga changes and idan so samu ne yana farkawa yaga wannan abin a kusa dashi" " ba komai Doctor in shaa Allahu za'ayi yadda kace"
*_5: 30pm_*
Aneeserh ta kammala komai tace wa Ayusha ta tashi ta shirya su tafi asibiti wajen su mu, tsaki taja tace "kin ga Malama ni fa karki takurawa rayuwa ta, tun d'azu kike damuna da abinda bai shafeni ba, dole ne sai munje tare ki tafi ke kad'ai mana ai ke ba bak'uwar garin bace"
Murmushi Aneeserh tayi tace "Allah ya huci zuciyar ki Mr's Unknown, kinga tafiya na barki lafiya" "Allah raka taki gona ba Mr's unknown ba komai ma ki k'irani"
A dai-dai ta sahu Aneeserh ta shiga ya kai ta asibitin, bata wani sha wahalan neman su ba bcoz a reception ta hango Dad a zaune, bayan sun gaisa yayyi allocating nata zuwa inda su Mum suke, bayan sallan Magrib suka tattara suka dawo gida.
Tun da Aneeserh ta tafi Ayusha take kuka sai da aka k'ira sallan magrib ta hak'ura ta tashi tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta d'auko Al-Qur'ani me girma ta fara karantawa ko zata samu waraka cikin zuciyar ta, tana cikin karatun taji shigowar su amma ta manna musu ta ci gaba abinta.
Sun iso gida ana sallan isha so Dad na parking mota ya wuce masallaci, Mum da Aneeserh suka shige ciki, ganin tana karatu yasa Mum bata kulata ba ta wuce nata d'akin dan tayi nata sallan haka abin yake a wajen Aneeserh ma ban d'aki ta shiga ya d'oro alwala.
Bayan ta idar da karatun ta tashi ta gabatar da sallan, tana cikin sallah Mum ta shigo tace da Aneeserh "idan Auta ta idar kuzo ku same mu a falo Abban ku na son ganinku!!!" bayan ta idar tayi addu'o inta sannan suka d'unguma zuwa falo, waje suka samu suka zana a k'asa yau ba hawa cinya domin sunyi fad'a da Dad......kallon ta yayi sosai shi kanshi ta bashi tausayi lokaci d'aya ta sauya kamar ba ita ba, yace "Auta ya jikin naki, da fatan kin ji garau yanzu" "Jiki Alhamdulillah" "Masha Allah haka ake so, dama ba komai bane yasa na k'iraki illah.... "
*_A dai-dai lokacin alk'alamina ya fad'i k'k'asa!!! Afuwan masu karatu manage with this little page, kuci gaba da bibiyata in shaa Allahu zakzaku gane inda labarin ya dosa.._*
*RØØKÏÊY KÆXS*
[14:55, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
76-80
"Dama ba komai bane yasa na k'ira ki illah ina so mu tattauna wata muhimmiyar magana dake, sannan in rok'i wata alfarma a gareki" shiru tayi tana kallon Dad a zuciyar ta kuwa cewa take "kowace irin alfarma kake buk'ata zan maka Dad amma banda na Auren Alhaji Umar " sannan tayi ajiyar zuciya tace "ina jinka Dad".
"Yauwa D'iyar kirki, maganar da nake so muyi dake game da cutar da ke damun Alhaji Umar ce, dazu ya fad'i anan yana ta aman jini da muka je asibiti likitoci sun tabbatar mana da cewa yana d'auke da ciwon zuciya, kuma ciwon ya kamu da ita a dalinlin sonki ne, yanzu haka yana kwance shame-shame rai a hannun Allah baya iya ko motsi, ana kyautata zaton nan da kwana uku zai farfad'o in shaa Allah, sannan sun ce idan so samu ne ana so yana farfad'owa ya fara ganin abinda yake so a kusa dashi, shine nake neman alfarma a gareki dan Allah dan Annabi Mamana ki amince muje asibiti ya farfad'o a gabanki, sannan ki dubi girman Allah ki amince da soyayyar shi ko dan ki ceto ranshi, amma ki je kiyi shawara kafin nan da kwana ukun ni bazan miki dole ba, duk hukuncin da kika yanke dai-dai ne amma ki sani amincewa da soyayyar shi tamkar kin ceto ran iyalan shi daga fad'awa maraici ne, tashi ki tafi Allah ya miki Albarka"
Maganganun Daddy sun matuk'ar kashe mata jiki amma fa hakan baya nufin ta zubda makaman yak'in ta, domin baza ta tab'a yarda ta auri wanda bata so ba, a hankali ta mik'e ta nufi d'akin ta Aneeserh ma ta mik'e da niyar binta Mummy tace "Aneeserh dawo bamu gama da ke ba".
Dawowa tayi ta gyara zama sannan Mum tace " ni haifi Ayusha sannan nafi kowa sanin halinta, tana da taurin kai da kafiya sosai, idan muka ce zamu mata ta k'arfin tsiya to abin zai fi haka b'aci, dan haka muna so ki taimaka wajen bata shawara ko Allah zai sa a dace, kin je asibiti kinga halin da mutumin nan ke ciki amimcewar Ayusha ne kawai zai dawo dashi hayyacin shi, kinga yana da kyau kema ki bada gudummawa wajen ceto rayuwar shi" ta k'arashe maganar tana zubda hawaye.
"Ku kwantar da hankalinki Mum&Dad in shaa Allahu nayi alk'awarin shawo kan Ayusha ta amince, zan jure duk wani wulak'anci da zata min dan na cimma buri na"
Dad yace "idan kikayi haka kin tabbatar mana da cewa ke 'yar halak ce, saboda haka daga yanzu aikin ki zai fara Allah ya miki albarka ya baki nasara"
"Ameen thumma Ameen Dad, bari na shiga na sameta duk yadda mukayi da ita I will let you know" "ok d'iyar albarka Allah ya bada sa'a" inji Mummy.
Aneeserh na shiga ta tarar da ita ta had'a kai da gwiwa sai kuka take, da sauri ta k'arasa wajen ta tana fad'in "Subhanallah!!!, haba k'awata bai kamata ki tada hankalin ki akan k'addarar da Allah ya sauk'ar miki ba, addu'a ya kamata kiyi Allah yasa hakan shine mafi alheri" "kar kiyiwa k'addara sharri domin wannan ba k'addara bane son zuciya ne, me yasa Mum &Dad suka canza sun kasa fahimtar halin da nake ciki, abin da ke damun Alhaji Umar shi ke damuna, idan har bazai iya hak'ura da soyayyata ba nima bazan tab'a iya hak'ura da son wanda nake k'auna ba amma gaba d'ayan ku daga ke har su kun kasa fahimtar hakan, to ki sani idan ma aiko ki sukayi ki koma ki sanar dasu cewa nayi making decision ban amince da shi ba kuma bazan tab'a amincewa da shi ba" tana gama fad'an haka ta fad'a kan gado ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro"
"Ayusha bazan tab'a mamakin fitowar wad'annan kalaman daga bakin ba, domin duk wanda soyayya ta rufe masa ido babu abinda bazai iya aikatawa ba... amma ina so kiyi saurin dawowa hayyacin ki k'awata ki sani fa shi bawan Allan da kike hauka a kanshi ma bai san kina yi ba, baki da tabbacin zaki sake ganin shi a rayuwa idan har Allah ya k'addara had'uwar ku dashi ma baki da tabbacin zai so ki ya aure ki"
"Ai dama banyi dan yasan inayi ba kuma da kike cewa bai zama lalle ya soni ba ban kai ya soni ba? ko kina nufin bani da qualities d'in macen da ya dace a aura ne!!! wallahi Aneeserh kin bani mamaki ban tab'a tsammanin haka daga gareki ba, Mum &Dad sun juya min baya kema haka" sai ta k'ara fashewa da kuka.
Matsowa bakin gadon Aneeserh tayi sannan tace "k'awata ina so ki fahimci wani abu guda d'aya idan kika ce mun juya miki baya sai Allah ma ya tambaya ki, muna k'ok'arin mu nuna miki hanyar da ta dace ne, ki tuna fa tunda kike a rayuwarki baki tab'a neman wani abu wajen iyayen ki kin rasa ba, duk wani abu da suka san zai saki farin ciki shi suke miki sannan suna gudun duk wani abu da zai b'ata miki mai yasa a karo na farko baza ki faranta musu rai ba, kar ki manta Ayusha Dad da bakin sa yace yana so ki mishi alfarma while kin san yana da right d'in da zai iya d'aura miki aure da duk wanda yake so ko kina so ko ba kya so, and another thing da nake so ki sani shine faranta musu rai dai-dai yake da faranta ran mahaliccin ki sannan b'ata musu ma dai-dai yake da b'ata masa ki tuna da hadinsin manzon Allah ( S. A. W) da yake cewa *_"Ridallahi fii Ridal Walidaini Wa Sukhd'ullahi fii Sukhd'ul walidaini "(Yarda Allah yana tare da yardar iyaye kuma fushin Allah yana tare da fushin iyaye)_* saboda haka k'awata ina mai shawartar ki da kiyi gaggawan dawowa hayyacin ki, ki farantawa iyayenki ko kya samu tabaraki a rayuwa"
"Baza ki gane bane K'awata, wallahi dai-dai da na second d'aya ban jin zan iya k'aunar Alhaji Umar, domin shi mutum ne mai son kansa da yawa, budurwar zuciya gareshi, kar ki manta Anty Zee aminiyar Mummy ce tun yarinta tare suka tashi komai nasu tare sukeyi har sukayi aure basu daina zumunci ba, Anty Zee ta kasance mace yar k'walisa da gayu ga addini da ibada uwa uba ga san mutane d'anta d'aya a duniya Fahad daga shi bata sake haihuwan wani ba, Allah yayi ta da son jama'a hakan yasa ta d'auko cousin sister nata Muneerah ta dawo wajen ta da zama, Muneerah na primary 3 ta dawo wajen ta da zama tana gama secondary school tsabar rashin adalci da son zuciya irin na Alhaji Umar ya aure ta, babu kunya kuma ya ajiyeta a gidan take abin da ta ga dama domin Muneerah bata da kunya sannan bata da mutuci ko kad'an"
Daya ke Allah ba azzalumin nawansa bane shekarar Muneerah uku ya auro Rahma, Rahma k'anwar kishiyar Maman Muneerah ce suna zuwa gidan tare da k'anne ta har Allah yasa ya k'yallaro ta ya auro ta sannan ni ma yanzu yace zai aureni, inaa wallahi sai dai ya mutu ya bar duniyar gaba d'aya amma bazan tab'a yarda na aure shi ba, mu uku Iyayen mu suka haifa, Anty Khadeeja da Anty Fareedah sai ni Auta duk kansu auren soyayyah sukayi me yasa sai ni da nake autar su za'a min auren dole a rasa ma wanda za'a aura min ma sai tsoho sa'an Babana mai 55years a d'oron k'asa inaa wallahi da sake sai dai Mum & Dad su tsane ni su daina sona kwata-kwata amma bazan tab'a yadda na aure sa ba" sai ta k'ara fashewa da sabon kuka.
```Wasa Farin girki This is just the beginning of the story kuci gaba da bina dan ganin yadda labarin zai kasance na barku lafiya masoyana ```
*RØØKÎÊY D BEST✍��*
[14:56, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
81-85
Sake matsowa kusa da ita Ayusha tayi tace "ki kwantar da hankalin ki K'awata na fahimce ki sosai da sosai amma ina so ki sani Mum & Dad baza su tab'a cutar dake ba a rayuwa wannan zab'in da suka miki shine dai-dai a wajen su nasan zakiyi tunanin cewa dan ba ni ce cikin wannan situation d'in ba yasa nake fad'in haka, to ki sani ko da nice iyayena suka nemin alfarmar nan a guna zan musu duk da cewa they are not responsible parents basu yi deserving a musu hakan ba amma domin samun rabauta wajen ubangiji zan amince musu" kuka ne yaci k'arfin ta yasa ta yin shiru.
D'ago jajeyen idon ta Ayusha tayi sannan tace "what do you mean by they are not responsible, Aneeserh iyayen naki kike fad'awa haka, bai kamata damuwa ta tasa