Showing 27001 words to 27538 words out of 27538 words

Chapter 10 - ALLURA TA TONO GARMA BOOK COMPLETE .txt

Unknown   

05 Jan 2025

1791

neman da nake miki ma dan in baki hak'uri ne dan gane da buga miki motor da nayi yanzu da ki hak'ura da kar ki hak'ura duk d'aya a waje na" sai ya tafi ya bar ta a wajen .






Da zaran ya farka daga mafarkin sai ya tashi ya d'auro alwala ya gabatar da sallah yana kuka yana rok'on Allah ya masa zab'in da ya dace, idan gari ya waye kuma ya k'ira Mummy ya fad'a mata labarin da mafarki da yayi sai tayi ta mishi nasiha da addu'a wani sa'in har kuka yake mata a wayan.








Ana cikin haka ranar Sunday da yamma bayan sallar la'asar yana zaune a kan sallaya yana tilawar Al-Qur'ani mai girma, Suratul Maryam yake karantawa,sai yaji wayar sa tayi ringing bai d'aga ba sai da ya k'arasar da Ayar da yake.










Abokin sa Shareeef ne ya k'ira "Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu" shine abin da yace da yake gaskiya shi ba kasafai zai d'aga waya yace "Hello" ba tare da ya fara sallama ba.
*_(Yana da kyau yan uwa musulmai idan zamu amsa waya mu fara da sallama domin wani lokacin bamu san wane ne zai k'ira mu ba,bamu san dame yazo ba, yazo da mugun nufi ne ko sab'anin haka wannan sallamar da zamu fara gabatarwa kafin Hello na iya zame mana garkuwa da kariya a garemu ALLAH YASA MU DACE)_*






"Wa'alaikumussalam,Aboki na ina ka shiga haka ina ta kira bakayi picking da wuri ba,to ka fito ka bud'e min k'ofa gani a k'ofar gidan ka dan nasan kana gida ba inda kake zuwa kamar matar kulle" "to gani nan zuwa Suda sarkin magana idan ka fara magana no comma no full stop"










Yana gama fad'an haka ya kashe wayan dan yasan halin Shareef da surutu ba k'aramin aikin sa bane ya rike shi da magana a wayar ya hana shi bud'e k'ofar da wuri.








*_Kafin ya k'arasa bakin k'ofa naji an k'ira sallan magrib a 9ja shine na barsu na taho nayi sallah so ku jira in na idar sai naci gaba da d'ebo muku rahoto da fatan masu karatu kuma idan lokacin da kuke karantawa yayi dai-dai da na sallah zaku ajiye kuje kuyi domin sallah gaba take komai, labarin yana nan a inda yake babu inda zai je amma Sallah idan ya wuce ya wuce kenan sai dai na gobe ga me rabon gani daga ni har ku bamu da tabbacin cewa zamu samu na Goben_.*
*_Allah ya bamu ikon kiyaye sallah a kan lokaci wannan itace tunatar wan da nake so na mana ayau kuma Alhamdulillah nasan zai tunatar da wasu Allah ya bamu ikon tsira ranar alk'iyama,Bissalam NICE DAI HAR KULLUM_*












*RØØKÍÊY D BÊST✍��*






*ROOKIEY D BEST*
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)




WHATSAPP NO:
+2349030159301

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login