Showing 1 words to 3000 words out of 27538 words
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:+2349030159301
[14:47, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*
GODIYA
```Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai da ya bani ikon fara wannan littafin Allah ya bani ikon isar da sak'o me amfani kuskuren da ke ciki Allah ubangiji ya yafe min
SAK'O GAISUWA GA
Haneefah Usman
Jiddah Ja'o
Yar_ficika
Ramalurv
Kausar Lurv
Ummiey Big
Fatiey Azland
Amnoor
Meelart AHK
Ayusha Iliasu
Asy Khaleel
Billy Sarki
Sweery
Deejah Jahun
Deejah Wazeeri
Aunty Jiddah Musa
CwtJiddah
Mr's Fawwaz
Umma yahya
Mommy sulti
First Lady
Memxiey
Maryam Abdool
MSB
Duduwa PML
Wanna Littafin tukwici ne ga each and every member of ``` ```PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S Up! Up!! together we stand divided we fall ,we rock even in the heart of our enemies # one ❤ ```
1-5
SHIMFID'A
Jami'ar Umaru Musa Yar Adu'a Jami'a ce da ke d'auke da mutane daga sassan Nigeria daban-daban kama daga Gabashin Nigeria zuwa yammaci,kudanci da Arewaci.
a cikin d'aliban da ke wannan Jami'ar ya had'a da wasu Kyawawan 'yan mata guda biyu AYUSHA DA ANEESERH.
AYUSHA yarinya ce kyakkyawa ta ajin farko tana da shape me kyau me d'auke hankali,ba fara bace amma kuma baz'a a kirata bak'a ba tana da gashi har gadon baya sai dai matsalanta d'aya Allah bai hore mata yalwataccen dukiyar Fulani ba asalin ta yar garin katsina ce.
ANEESERH ma kyakyawa ce ta ajin farko bambancin su Ayusha kad'an ne ita fara ce sol sannan tana da wadataccen dukiyar fulani sai dai gashi ya mata yawa domin dakyar ake samun na parking.asalinta yar Jigawa ce wani gari da ake kira Dangyatin karatu ne ya kawota katsina har Allah ya had'ata da Ayusha suka fara k'awance ita a campus take zama sab'anin k'awarta da cikin gari.
*GUNDARIN LABARIN*
A nutse suke taku kamar basa son taka k'asa Aneesa ta dubi Aminiyarta tace " 'yan mata ya kamata mu d'aga k'afa fa dan wanna tafiyar tamu ba inda zata kaimu kuma kin san Mr Ojokolo ba mutunci gareshi yana riga mu shiga sai dai muji a slow last week ma bamu samu munyi attending lecture nasa ba"
"Hmmm!!k'awata kenan wallah baza ki gane bane, Yau tunda garin Allah ya waye nake jin jikina very week dak'yar na iya tashi na shirya har na samu na shigo school"
"subhanallah,me ke damun ki haka"
"Wallahi nima ban sani ba nasan dai yau am abnormal, zai yi wuya idan ba wani mummunan aika aika ke shirin faruwa dani ba" sai ta fashe da kuka.
Aneeserh tayi saurin rufe mata baki tana fad'in "please sistor ki daina fad'an haka falyak'ul khairan Auliyasmut (ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru) in shaa Allahu babu abinda zai faru dake sai alkhairi" itama sai ta fashe da kukan,waje suka samu suka zauna suka ci gaba da kukansu sai da sukayi me isarsu sannan suka bari a k'alla sun d'au minti talatin a zaune ba wacca tace da yar uwarta k'ala daga bisani Ayusha tai k'arfin hali tace "Sistor tashi mu tafi hostel tunda munyi missing period din idan yaso da yamma sai mutafi gida muyi weekend a can dama Mummy na complain wai kwana biyu kin daina zuwa"
Aneeserh zatayi magana tai saurin rufe mata baki " bana son jin unnecessary excuse naki dole sai kinyi weekend a gida"
Murmushi tai sannan tace "Al-masifatu your wish is my command" dariya sukayi gaba d'ayansu suka nufi hanyar hostel.
```A dai-dai lokacin alk'alamina ya tsaya for today ku biyoni gaba dan bibiyar labarin wad'an nan yammatan da fatan wannan soman tab'in ya k'ayatar da ku```
*ROOKIEY D BEST*
[14:48, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_A short_ REMINDER*
*_It is normal to see a boat floating on the water but to see water fill up inside the boat is considered dangerous, in that same way you can live in the heart❤of world but you must not let the world enter you heart_*
*_This page goes to my one & only Besty KABEER SKT thanks for the Love,care and un endless Support #1Lurv❤_*
6-10
Suna shiga hostel Ayusha tace "wallahi sistor yunwa nake ji yau ko breakfast banyi ba na fito"
Aneeserh tayi dariya tace " to dama ke wani cin abinci kikeyi yanzun ma dan dai yunwar ta rinjayeki ne amma breakfast baya daga tsarin ki"
"ke dai Kika jiyo,yanzu dai tashi ki dafa min indomie as usual" wani harara Aneeserh ta sakar mata " lalle baza kici indomie ba in dai ni zan dafa miki"
"Haba my chef kin san dai ban iya cin indomie kowa idan ba naki ba girkin ki daban yake a cikin mata you are the best among the equals"
da sauri ta mik'e tana dariya tace "wannan Ayushan kinfi k'arfin bil'adama idan kika sa naci a abu ko mutum baiyi niyya ba sai yayi"
Murmushi tayi tace "k'awata idan baki kula dani ba anan zai kula dani"
"dole kice haka munafukfuk ina gama dafa miki zaki fara min iskanci"
a haka da wasa da dariya suka dafa indomin bayan sunci sun huta sukayi sallan azahar Sanan Suka nufi library don yin karatu.
Misalin 3:45pm suka fito masallaci suka wuce don gabatar da sallan la'asar, bayan sun idar suka koma hostel Aneeserh ta d'auko duk abubuwan da tasan zata buk'ata sannan suka nufi student parking lodge suka dauki mota suka nufi gida.
5:45pm suka isa tun kafin su k'arasa k'ofa Ayusha ta fara suburbud'a hon da sauri Mallam Ayuba Mai gadi yazo ya bud'e get domin yasan halin uwar d'akin nasa idan ta dad'e bai zo ya bud'e ba zata sauke masa masifar guntun gajiyar school, shi kanshi yasan Ayusha tana da kirki ga ba rowa ko kadan bata k'yamar talaka ya rab'eta amma bata da hakuri ko kad'an sab'anin k'awarta Aneeserh bata fad'a ko hayaniya in fact she's totally cool.
Yana ganinsu tare ya fara washe baki "Hajjaju makkatu yau kece a gidan namu gaskiya kin bamu rani dayawa dazu fa kamar in ce da Hajia Shatu(haka yake kiran Ayusha) ta ce miki yaushe zaki kawo mana ziyara"
"Allah Sarki Baba nima nayi missing naku kwanannan Ina busy sosai shiyasa ban samu na lek'o ku ba"
"Ayyah barkanki da zuwa"
"Yawwa Baba"
Ayusha ta kallesu tace "Baba na Aneesha idan kun had'u baku san rabuwa dan surutu yanxu dai ayi hak'uri magarba ta doso anjima kwa cigaba da gaisawar" dariya sukayi dukkansu sannan suka shige ciki.
Tun daga falon k'asa suka fara cin karo da wani had'ad'd'en k'amshin girki na tashi hakan ya tabbatar musu da cewa Mummy na kitchen da sauri Ayusha ta haye sama da gudu tana fad'in "am home Mummy na i miss you today so much" ta fad'a jikin Mummy da sauri Mummy tayi hugging nata tana fad'in "miss you more darling, ya school I hope baki tattare da wata matsala ko damuwa"
"yeah! Mummy na bani da damuwan komai"
"Alhamdulillah haka nake son ji My Daughter"
Da sauri Ayusha tace "au na manta fa ashe nazo miki da surprise a k'asa,bani two minutes yanxu zan dawo" da sauri ta fice ta bar Mummy da tunanin wani irin surprise ne wannan.
bata gama tunani ba baji ana fad'in "Mummy close your eye's before i show the surprise" idan da sabo ta saba da shirmen Ayusha ta sani idan bata rufe idon ba ba nuna mata zatayi ba so she has no decision rather than to close her eye's.
Tana rufe idon taji ance "Mum open your eye's and see the surprise" tana bud'e idon ta gansu a tsaye suna mata dariya b'ata rai tayi tace"da nasan wannan na surprise d'in da ban rufe idona ba" rau rau sukayi da fuska abin tausayi a tare suka had'a baki wajen ce "Mummy why?"
hararan su tayi in a cool way ta Nina Aneeserh "sai yau Kika gadaman zuwa waje na to ku koma inda kuka fito nayi fushi da dukanku"
marairaicewa sukayi da face fad'in "we are sorry Mommah" Murmushi sannan tace dasu "your apology is accepted" da tsalle sukayi hugging nata suna fad'in "thanks for accepting our apology Mommah" murmushi tayi tace amma "next time" da sauri suka ce "better" tace " to maza kuje ku watsa ruwa a jikin ku ku huta domin nasan akwai gajiya a tattare daku"
"OK Mum" shine kad'ai abinda suka iya fad'a suka nufi ciki.
```Nima Rakiya a dai-dai lokacin na bisu d'akin ina ganin Ayusha ta shiga Toilet Aneeserh d'ora towel nace bari na basu waje letter naci gaba da d'auko muku rahoton.```
*ROOKIEY D BRST*
[14:50, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_MY SPECIALPAGE IT ALSO GOES TO MY SPECIAL ONE❤❤❤_*
*_A gift sent to me from Almighty, he showed me love lyk no other "LIKE A BLOOD BRO" his shoulders were alwaiz there for me to carry on when I was in a deep sorrow. he's someone i will cherish forever❤he care's so much about me and lend me a helping hands and never get tired of my endless demands._*
❤ *_WHO IS THIS ANGEL??? OF COURSE YOU ARE THE ONE���� UNCLE SULTAN MY PRIDE MY EVERYTHING IN LYF_* ❤
11-15
Ayusha na fitowa daga wanka tace da Aneeserh " 'yan mata sai a tashi a shiga a watsa ruwa, wai mutum idan ya shiga wanka sai kace me canza fata,wallahi idan na gama shirya wa baki fito ba sauk'a zanyi na barki tunda dama ke ba bak'uwar gidan bace"
"Mtswww!!! kin san ni ba bak'uwa bace zaki bi ki addabeni da mita,kuma da kike cewa ina dad'ewa a wanka ke d'in awa nawa kike d'auka kafin ki gama kwalliya lazy girl kawai" tana gama fad'in haka ta fad'a toilet da gudu dan tasan halin mutumiyar yanzu sai ta d'uma mata dundu dan ta tsani a ce mata lazy and she's lazy a reality.
Murmushi Ayusha tayi tace "karki damu 'yan mata zanyi cin tuwon kishiya ramako ne" taci gaba da shiryawanta, minti goma sha biyar kacal ta d'auka wajen shiryawa har zuwa wannan lokacin Aneeserh bata fito ba murmushi tayi ta sauk'a k'asa wajen Mummy. tana fita da minti biyu kacal Aneeserh ta fito tana murmushi "Oh su masifatu an sauk'a k'asa za'a je a sauk'ewa Mummy rigima" wato a gaskiya yanayin closeness d'in Ayusha da iyayenta na birgeta sau tari ta kanji dama ace itace take samun wannan kulawar daga wajen iyayenta da taji dad'in rayuwarta,take wasu zafafan hawaye suka fara gangarowa daga kumatunta.
Ayusha na isa falon k'asa ta taradda Mum & Dad na zaune suna hirarrakin sun irin na tsofaffin masoyan da suka shak'u da juna,da sauri ta k'arasa da gudu ta fad'a kan Daddy tana fad'in "Oyoyo Daddy na yau nayi missing naka a lot" had'e rai yad'anyi kad'an yace "gashi ni kuma banyi missing d'inki ba asali ma fushi nake dake" zaro ido waje tayi ta marairaice tace "yanxu Daddy da Autan naka kake fushi shi kenan" sai tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka shi abin ma dariya ya bashi yace "idan Auta tayi ba dai-dai ba sai a hukuntata, dan haka tashi daga jiki na, kuma na baki assignment ki binciko laifin da kikayi min daga wayewar safiya zuwa yanxu" shiru tayi na d'an wani lokaci tana tunanin irin laifin da ta aikata, a iya tunaninta dai tasan through out yau basu had'u da Dad ba to ko shi ne laifin da tayi? Yes!!! shi ne ma tasan yadda zata shawo kan Dad yanzu-yanzun nan.
Sauk'a tayi daga jikinshi ta zuba gwiwowinta a k'asa tana fad'in "dan Allah Sweetheart kayi hak'uri na gano laifin da na aikata kuma na tabbata girman laifin na can-can ci a hukuntani haka amma duk da haka ina neman rangwamen horon da ake shirin yimin, Dad wallahi ba intentionally na tafi ba tare da mun gaisa ba,sanin cewa jiya ka kwana da ciwon kai yasa da na shiga wajenka ban tashe ka munyi sallama ba sannan aka sake samun akasin na manta wayana a gida,yanzu shigowa na gidan ban fi 30 minutes ba Afuwan Daddyn Auta"
Murmushi yayi ya d'agota sama ya zaunar da ita kan cinyarshi sannan yace "shi yasa a kullum nake alfahari dake Auta a duk lokacin da kika b'ata min rai kina k'ok'arin tausasa ta da kalamai masu dad'i da zasu sanya ni cikin farin ciki Ina miki albishir cewa Daddyn ki ya sauk'o daga fushin da yake dake".
Murmushi tayi tace "that's why i am always proud of you my Dad Allah ya bar min kai har k'arshen rayuwata" a dai-dai lokacin Anerserh ta shigo falon tana ganin k'awarta kan cinya ta tuntsire da dariya tana fad'in " Daddy sannu da zuwa, k'atuwa a kan cinya ko kunya bata ji, wallahi Daddy ka sauk'e ta zata tsufar mana da kai" murmushi yayi yace " yauwa Aneeserh ai in da sabo na saba da shagwab'an Auta Ina ganin ita da ta daina hawa kan cinyata sai na Aurar da ta barwa 'ya'yanta,ina ga ma kwanan nan zan Aurar da ita" dariyar mugunta Aneeserh ta Saki domin ta sani sarai Ayusha babu abinda ta tsana a yanxu sama da aure domin ita a cewar ko ta gama university sai tayi masters da PHD zatayi aure,so da hazak'a tace "wallahi Daddy a mata auren ko zata shiryu" tana gama fad'in haka ta gudu bayan Mummy dan ta sani sarai ta taro match, take hawaye ya fara zuba a fuskar Ayusha sauk'a yayi daga cinyar Daddy taje gaban Mummy ta zube "Mummy dan Allah dan Annanbi karki bari Daddy yamin aure wallahi har yanxu ni k'arama ce duka-duka fah am just 18yrs,wallahi ni aure baya daga tsarina a yanzu har sai nayi PHD " sai ta fashe da kuka. gaba d'ayansu sai suka kwashe mata da dariya Mummy tace "dai na kuka Auta babu wanda zai miki aure yanzu, shima Daddyn naki wasa yake miki ba yanzu zai aurar dake ba sai lokacin da kika samu saurayin da kike so, amma Ina so ki sani shi aure lokaci ne idan lokacin mutum yayi ko ya shirya ko bai shirya ba sai yayi babbar sunna ce mai k'arfi,sunnar Annabinmu Muhammad Sallallahu Alaihi wa'alihi wasallam saboda haka kar na sake ji kince baki shirya aure yanxu ba".
Jikinta yayi matuk"ar yin sanyi sosai a sanyaye tace "na gode Mummy da kika tuna sar dani abinda ban gane ba in shaa Allahu daga yanxu na janye burina na cewa bazan yi aure yanxu ba amma Mummy Daddy bazai min auren dole ba ko" dariya abin ya basu Daddy ya kamo hannunta yace "zo nan Auta ni bazan tab'a miki Auren dole ba na baki dama ki kawo duk wanda kike so in dai ya cika sharud'an da addinin mu ya tsara shikenan" murmushi tayi tace "na gode Daddy na Allah ya barmin ku in rayu da ku" dariya Mummy tayi tace "Auta ko dai kin fara soyayya ne ban sani ba naga fuskarki d'auke da farin ciki mara misaltuwa" rufe ido tayi alamun kunya sannan tace "Daddy kaga matarka ko" murmushi yayi yace "a 'a Mummy karki takurawa Auta ta kuje can ku k'arata da d'iyarki" ya nuna Aneeserh.
Aneeserh da ke rakub'e a gefe tana ganin ikon Allah a zuciyarta tanaiwa iyayenta addu'ar "Allah ya shiryesu ya ganar dasu gaskiya su fara nunawa 'ya'yansu so da k'auna" kamar daga sama taji Mummy na cewa "ai d'iyata wayayya ce ko gobe ta kawo miji aurar da ita zanyi,ko ba haka ba Aneeserh" murmushin k'arfin hali tayi ta sukuyar da kai k'asa. Ayusha ta tuntsire da dariya tace "dama ai ita aure take so yanzu haka tanada saurayi" da sauri Mummy ta katseta da cewa "in fitsari banza ne kaza tayi mana" dalilin da yasa haka ta fahimci cewa Aneeserh ta shiga matsanan cin kunya sakamakon katob'arar da Ayusha tayi. Daddy ma ya fahimci hakan shiyasa ya mik'e yana fad'in "ni zan wuce masallaci naji kamar anata kiraye-kirayen sallah saboda haku kuma kuje kuyi" kai tsaye dak'in shi ya wuce ya d'oro alwala ya wuce masallaci,suma saman suka hanye dan gabatar da tasu sallar. daga nan kuma suka ci gaba da gudanar da activities d'insu ,iyayen Ayusha mutane ne masu mutunci,karamci da sannin hak'k'in d'an Adam yabawa da nutsuwar Aneeserh yasu su barin yarsu yin mu'amala da ita tun suna 100level suka so ta zauna a gidan amma tak'i coz she don't want to be a boarding to them,shiyasa once idan tazo weekend sai ta bari sun nemeta saboda tsaro.
Normally idan tazo weekend zata koma suna had'a ta shaa tara ya arziki to wanna karon ma haka, yau ta kama monday bayan