Showing 6001 words to 9000 words out of 27538 words
Ayusha na shiga ciki ta nufi toilet ta d'oro alwala tayi sallah, bayan ta idar da sallah Anty Zainab ta shigo fuskar ta d'auke da murmushi tace "sorry Ayusha tunda kika zo bamu zauna sosai ba yau nice a kitchen shi kuma babansu baya cin abincin mai aiki, so ban samu na d'aura girkin da wuri ba har magrib tayi, yanzu na gama abinci,Allah-Allah nake kar yazo ya samu ban gama ba"
"wallahi ba komai Anty, miyan me zakiyi na shiga na miki tunda nayi sallan" "la ki bar shi kawai kar na wahalar dake, nasan baki dad'e da dawowa daga school ba, gajiya bai gama barin ki ba, so idan na idar nayi kawai miyan alayyaho ne bai da wahala na gama yanka komai da na idar zan had'a" "walahi yau da wuri na dawo so bari naje nayi kawai" "to shi kenan Allah yayi albarka"
"Ameen"
Ayusha kitchen d'in taga komai neat kamar ba girki ake a ciki ba, murmushi tayi a fili tace "Aunty Zee kenan gidan tsafta da gayu wai a hakan girki take amma komai tsaf dashi, ni kitchen d'in ne ma ya birgeni komai orange" Bayan ta gama sumbatun ta ta nufi gas ta kunna, tukunya ta d'aura ta zuba mai ta soya da albasa, da yake man gyad'a ne soyuwan sama-sama tai masa, sannan ta d'auko sulallen nama ta zuba, shima ta d'an razana shi sannan ta zuba ruwan sulale kad'an ta sa taruhu da spices ta rufe tukunyar, kafin tukunyar ta tafasa ta wanke kwanu kan da tayi using bayan taga wankewa ta bud'e ta zuba Alayyaho da albasa mai tarin yawa ta d'auko sardine guda biyu ta bud'e ta zuba ciki ta rufe.
A take kitchen d'in ya turnik'e da k'amshi nan take ta kuma d'auraye sauran kayan aikin,5 minutes kacal allayahon yayi ta sauk'e, wasu zafafan warmers ta hango a gefe take ta nufi inda suke ta d'auko k'aramin ta juye miyan a ciki sannan ta mai da shi inda ta d'auko, bud'e babban tayi taga wani irin abinci Anty Zee ta girka, tana bud'ewa taci karo da had'add'en cous-cous anyi ganishing nashi da carrots & peace gashi yayi wasar-wasar gwanin ban sha'awa,rufewa tayi ta k'ara tattare komai sannan ta nufi fridge ta bud'e fruits ta gani a ciki sai yoghurt .
Banana ta d'auko ta b'are guda shida ta yanka su dai-dai misali sannan ta d'auko yoghurt roba biyu,banana ta fara sawa a blander sannan ta zuba yoghurt d'in a cikin tai blending, sai da ta tabbata ya nik'u sannan ta tace da rariya cikin bowl ganin yayi yadda take so yasa ta juye a Jug ta maida fridge, sannan ta dawo ta sake saftace kitchen d'in ta d'auki abincin ta shiga da shi ciki tana shiga parlor ta nufi dinning area ta shirya komai tsaf sannan ta wuce ciki wajen Anty Zee.
Tana shiga ta taradda Anty Zee ta idar da sallan isha tana lazimi toilet ta shiga ta sake d'auro alwala ta tada sallah.
Bayan ta idar da sallah Anty Zee tace "sannu da k'ok'ari 'yata na je naga miyan ki sai yayi dad'i in yanzu haka falon ya turnik'e da k'amshin d'adi,Allah dai yayi albarka d'iyar arziki, badan kina da lectures gobe ba da kin kwana gobe ki tafi" "karki damu Anty in shaa Allah upper week zanzo nayi weekend anan" da sauri tace "why not next week Ayusha" murmushi tayi tace "wallahi next week ina da visitor,Aneeserh zata zo min weekend" "okay, wace Ayusha kuma?" " baza ki santa ba Anty wata course mate d'ita ce takan zo tai mana weekend a gida" "to why not kuzo tare" "Hmm.....ai Mummy baza ta bari ba tana son zama da Aneeserh sosai so ki bari upper d'in in shaa Allahu zan zo" "to shi kenan ba komai Allah ya kaimu" "Ameen"
Kamar daga sama suka ji ance "Hajia Zainabu Abu mai dad'in tuwa, yau kuma wani daddad'an kikai mana ne tun daga bak'in gate k'amshin girkin ki ya bigi hanci na murmushi tayi tace "Alhaji kenan kai kullum baka rabo da zolaya to yau ba ni na girka abincin ba d'iyar ka ce ta girka" sai a sannan ya lura da mutum a d'akin kallon farko da ya mata yaji bugun zuciya take yaji gabanshi yayi mummunar fad'uwa take ya fara furta kalmar "innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, Allahumma ajirni fii nusibatihi wa aklifni khairan minha" sannan ya tattaro dukkanin nutsuwar sa yace "Hajjaju wace ce wan nan d'in ban wayeta ba wallahi" murmushi Anty Zee tayi tace "baza ka gane ta ba ai d'iyata Ayusha ce yar wajen Aminiyata" "Oh!!! kina nufin wannan Ayusha 'yar wajen Hajiya Fatima ce?" "kwarai kuwa" "Allah mai ikon wallahi ko a hanya na ganta bazan shaida ta ba, yarinyar da take k'arama bata da wajen zuwa hutu sai nan,idan ban manta ba rabonta da gidannan tun tana da shekara takwas" "kwarai kuwa Alhaji coz yanzu haka tana da 10yrs which means shekararta goma bata zo ba"
Shiru Ayusha tayi tana sauraron su sai da suka gama lissafe-lissafen su ta tsugunna har k'asa tace "Abba ina yini" "lafiya lau Ayusha, ya kike ya bayan rabuwa, yanzu kina JSS nawa" murmushi tayi tace "300level nake" da sauri yace "ikon Allah girman d'an mutum ba wuya ni ina miki batun JS ashe ke har kin shiga jami'a, to Allah ya taimaka Allah yayi jagora" "Ameen"
Aunty Zee tace "gaskiya yallab'ai ka ragewa d'iya ta classa dayawa yarinya da a 16yrs tayi candy" "sorry Hajjaju, a min afuwa naga alama so kike ki hana ni cin girkin d'iyar ki shiyasa kike son maida gobe tomorrow" "ina ni ina hana ka kwasar gara, yakamata muje muci saboda dare nayi Ayusha zata tafi gida kuma ba motor a hannun ta" "au dama ba kwana ta kawo mana ba, shi ke nan muje muci in yaso sai na kaita dan bai kamata a barta ta tafi ita kad'ai ba" gaba d'ayansu suka d'unguma sukayi falo don yin dunner.
```Nima Rakiya na kwashi tsumman legs d'ina na basu waje domin k'amshin miyan Ayusha ya tsuma ni dayake daukan rahoto nazo ba kwad'ayi ba and nasan muddin Ayusha ta hangoni zatamin bismillah lols�� na barku lafiya dearies kuci gaba da bibiyar labarin akwai disaster a next page ```
[14:53, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*QUOTE: Doing Good for a good done to you is simply repayment, whereas doing good for an evil done to you is a tremendous virtue. _THIS PAGE IS SPECIAL IT ALSO GOES TO MY SPECIAL ONE Auwal Shanu (MY ROSE��)_*
31-35
Alhaji ne a gaba Aunty Zee da Ayusha na biye dashi a baya suna isa dining Alhaji ya zauna sannan Anty Zee ta zauna, Alhaji ya kalleta yace "Hajjaju ya banga d'iyar tamu ba ko kunya take ji ba zata iya cin abinci a gaba na ba" "Hmm!! in dai Ayusha ce zata iya amma fa tare muka fito da ita daga d'aki, bari kawai nayi serving naka sai naje wajen ta muci tare" mik'ewa tayi ta fara serving nashi sai ga Ayushu ta fito daga kitchen ta shigo da tire a hannun ta me d'auke da Jug & cups.
Anty Zee tace "Ayusha ke dama kitchen kika shiga har mun fara tunanin ko kunya kike ji baza ki iya cin abinci da Abban ku ba" murmushi tayi tace "ba haka bane dazu da na gama girkin na had'a wani local drink shine nasa shi a fridge dan yayi sanyi " da sauri Alhaji yace gaskiya "Ayusha kina ji da iyayen nan naki har wani drink kika yi preserving that's good Allah ya miki albarka" "Ameen" tace sannan taci ci gaba da serving nasu.
suna cikin ci Alhaji yace "Hajiaya a ina zan samu irin cous-cous na shuka saboda b'aci wan rana kar a zo wata rana a rasa a kasuwa, na godewa Allah da yasa na shuka Alayyaho tun tuni kin ga bani da case da wannan" Hajiya tace "Hak'k'un gaskiya ya kamata mu bin ciko irin amma ka d'an kurb'i lemon kad'an ko Allah zai sa a tuno inda za'a samu irin"
Alhaji dai bai ce ko k'ala ba ya d'auki cup ya kai baki bashi ya sauk'e wannan kofin ba sai da ya shanye lemon da ke ciki tass sannan yace "Hajjaju k'aro, wato a hausawa sunyi gaskiya da suka ce wanda ya bar gida gida ya bar shi, ni fa dama can nafi son natural drinks akan artificial, dan Allah Ayusha ki zo mana hutu kinga zaki taimakawa Hajjaju sosai wajen sarrafa drinks"
Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Anty Zee tace "lalle Ayusha yau kin ciri tuta tunda Abban Fahad yayi santin girkin ki, shi fa ba girkin ko wace mace bane yake birgeshi, saboda haka Alhaji a bamu tukwici" "an gama uwargida sarautar mata" haka dai suka d'an tab'a barkwan ci daga bisani Hajiya taja Ayusha ciki ta bata sak'on Mummy suka fito, a falo suka tarad da Alhaji, hannu yasa a aljihu ya ciro 20K ya bawa Hajia yace "ga tukwi cin d'iyar ki" hannu biyu tasa ta karb'a tai masa godiya sannan ta mik'awa Ayusha tace " ga tukwicin ki nan d'iyar kar ki kuskura kimin gardama dama" hannu biyu tasa ta karb'a sannan tace "na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya k'ara bud'i" yaji dad'in addu'ar da tai mishi so da sauri yace "Ameen, muje in kaiki da wuri kar dare yayi sosai"
"Gaskiya kam, yanzun nan ma Hajia Fatima ta k'irani nace da ita yanzu zata zo" cewar Anty Zee Kenna da sauri Alhaji ya suri makullin mota ya yi waje suka biyoshi a baya,Anty Zee da kanta ta bud'ewa Ayusha mota tace "na gode d'iyata, idan kin je kice da Aminiya ina gaisheta" "zata ji" Malam Iliya mai gadi ne yayi saurin bud'e gate saka makon hon din Fahad da yaji, yana shigowa su kuma suna fita hannu ya d'agawa Abba shima ya d'aga masa yayi ya shi ge.
Tun da suka fara tafiya babu wanda yace da d'an uwansa k'ala har suka isa gida, yana sauk'eta tace "na gode' yace "ba komai idan kin shiga ki gaida min iyayen naki"
Anty Zee na zaune a falon Fahad ya shigo sallama yayi ta amsa sannan ya samu waje ya zauna yace "Mum barkan ki da gida, wallahi yau d'innan some how nake jina na rasa me ke min dad'i wallahi" "dole kaji ka some how mana Fahad,tun safe ka fita baka dawo ba na tabbata yunwa da gajiya ne suka maka rubdugu" murmushi yayi yace "wallahi rabo na da abinci tun breakfast, kuma yanzu haka bana jin zan iya cin abinci wallahi" " subhanallah!!! me ke damun ka haka har ya hana ka cin abinci, kasan fa kana da chronic ulcer kuma sannin kanka ne Doctor ya hanaka wasa da cin abinci,dan haka bari na tashi na kawo maka kaci yanzu-yanzun nan a gaba na" tana gama fad'in haka ta nufi kitchen murmushi yayi yace "Mama na ta kaina bata tab'a barina na zauna da yunwa,Allah ya bar min ke tawan"
Afrah ce ta shigo falon,da gudu ta d'ane cinyar Fahad tana fad'in "Yaya sannu da zuwa,yau tun safe da ka fita baka dawo ba har Anty Mekyau tazo ta tafi" "yawwa Little,wace ce kuma Anty Mekyau?" a dai-dai lokacin Anty Zee ta shigo hannun ta d'auke da tire ta zubo mishi abincin a plate da jug &cup sai da ta ajiye tiren sannan tace "Afrah uwar surutu,ba fa kowa ce kyakkyar da take nufi ba illa k'anwar ka Ayusha yar gidan Hajiya Fatima" "oh!!! Mummy dama yarinyar tana duniya wallahi na ma manta da ita da yake mun dad'e bamu had'u ba" "ai idan ka ganta a hanya ma baka shaida ta ba dan ta girma ta zama 'yammata,yanzun nan Abban ku ya ya kaita gida, karma ka biye surutun Afrah ga abinci na kawo maka kaci"
Duk da cewa ba wani yunwa yake ji ba ya zama dole ya d'and'ana wannan domin kuwa tunda ta shigo da abincin k'amshin ya mamaye shi. jawo plate d'in yayi ya kalli Afrah yace "Little je ki d'auko spoon muci tare" "na k'oshi tun d'azu Anty Mekyau ta samun nawa naci" "gaskiya kina ji da wannan Antyn naki" Anty Zee dai shiru tayi tana kallon shi, tun yana d'eban abincin a hankali har ya fara rushing bai tsaya ba sai da ya cinye tas ya kora da drink sannan yace "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani mahaifiyar da tafi ko wace mace iya girki a duniya, Mummy tun da nake a duniya ban tab'a shan drink me dad'in wannan ba, Mum wannan miyan Zogale ne ko me? gaskiya idan da saura ki ajiye min na d'umame"
Dariya sosai Anty Zee tayi sannan tace "oh!! ni Zainabu Abu yau d'iyata ta sace min zuciyar d'a da uba da girki, Abban ku ma haka yayi ta santin abincin nan kai ma kazo kana buga naka santin" "Mum kina nufin ba kece kika girka abincin nan ba?" "cous-cous kawai na dafa sauran kuma Ayusha ce tayi" "wow!!! gaskiya tayi k'ok'ari sosai dama a ce yadda ta iya girkin nan haka pretty ma ta iya" "pretty kuma!!!,wace ita?," Anty Zee ta fad'a in shock domin tun da take da Fahad bana shekarar shi 30 amma bai tab'a mata zan cen budurwa ba"
Sosa kai ya fara yi yace " wallahi M..u..m d'azu ne na shiga University wajen Sa'eed shine accidentally na buga mata motar ta, to bata tsaya ta saurare ni ba tayi tafiyar ta shine abin yake ta damuna, ban san ina zan sake ganin ta ba"
Murmushi Mum tayi tace "kwantar da hankalin ka My Son in shaa Allahu zaka sake ganin pretty,ka bata hak'uri,ina ce daga ka bata hak'urin shike nan?" girgiza kai yayi yace "No! Mum ba shike nan ba" "OK! then what next!!!" ta fad'a tana kallonshi mik'ewa tsaye yace "good nyt Mum a bar zan cen kawai"yayi gaba a bin shi murmushi tayi a zuciyar ta tace "wato My Son ya fara fad'awa tarkon so, ya Allah ka bashi sa'an abin da yake nema, Allah ka bayyana mishi pretty"
Ayusha na shiga ciki ta tarar da Mum &,Dad a falo suna hira,da gudu ta fad'awa Dad tana fad'in "Oyoyo Sweet Papa yau nayi missing naka sosai, i hope kai ma kayi missing" "nayi missing naki sosai Auta, tun d'azu nake jin gidan some how saboda baki nan" "Allah sarki My Love yanzu kam na dawo zaka ji ka normal" "tabbas Auta na naji normal yanzu" dariya tayi tace "Alhamdulillah tunda kaji garau bara naje na kwashi gaisuwa wajen Sweet Momma na" "Hmm....dama kin rik'e gaisuwar ki tun da Daddyn ki kad'ai kika sani kuma kike missing" "haba Sweetheart baki gane bane shi fa Dad rabona dashi tun da na dawo daga school while ke kuma bamu wani dad'e da rabuwa haba Habibty kar kiyi fushi da Autar ki mana" "to shike nan Auta na karb'i uzurin ki, ya kika baro min Aminiyar tawa" lafiyan ta k'alau tana gaishe ki" nan dai Ayusha tai ta basu labarin gidan tare da kud'in da Abba ya bata, su Mummy harda d'aukan ta k'ira Anty Zee tai musu godiya.
10:00pm nayi Ayusha tai musu sallama ta haye d'akinta tana shiga ta rage kayan jikin ta ta fad'a wanka tai shirin kwanciya, tun da ta kwanta ta nemi bacci sama da k'asa yak'i zuwa babu abinda idanun ta ke hasko mata sai fuskarsa, kunnuwanta na d'auko mata sautin Zazzak'ar muryar sa me kama da busar sarewa a yayin da yake fad'in..............
```To fah masu karatu nawa kunnen ya kasa jiyo mana sautin muryar tasa kuyi min afuwan haka amma in shaa Allah zan ci gaba da bibbiyar Ayusha dan gano cewa wani me sa'an ne yayi tattaki ya ziyarci zuciyar ta a wannan daren ```
*ROOKIEY D BEST*
[14:53, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*_This page is for you FATTY AXLAND (Mrs Lameed'o) Happy Birthday to you my special friend WLLNP❤Hip��Hip��Hip��Hurray_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
41-45
Tunda suka shiga lecture ba abin da take ganewa, attention d'inta complete ya karkata ga tunanin guy d'in da ya buga mata mota, burin ta shine ta ganshi ta bashi hak'uri ko ta samu relief.
Kamar daga sama taji an tab'a ta ance "Baby in love tashi mu tafi kowa ya watse ya barmu" a firgice ta juyo ta juyo da kallon ta ga Aneeserh sannan ta sauk'e wani zazzafan ajiyan zuciya tace "wallahi har kin bani tsoro" ta kalli hall d'in wayam sannan ta sake cewa "yaushe aka watse aka barmu mu kad'ai" " dama ina zaki sani kin tsunduma cikin kogin so" mik'ewa Ayusha tayi tace "kin ga malama bana son sharri, kefa dama baki iya samun abu ba daga baki labari sai ki canza akalar zancen, dan haka bana so zancen ya tsaya