Showing 21001 words to 24000 words out of 27538 words
ki fad'an kalaman da basu dace dasu ba, ki tuna fa ke kike min nasiha akan iyaye no matter what they do basu cancanci haka ba"
"Ayusha nasan abin da nake fad'a gaskiya ne so no need kiyi tunanin cewa ban kyauta musu ba, idan kika ji labarina zaki san cewa eh lalle basu dace su zama iyaye na ba shiyasa a ko da yaushe iyayenki suke birge ni rayuwar su tayi min A1".
"Ban fahimce ki ba k'awata" "yanzun nan zaki fahimce ni in shaa Allah, yaune rana ta farko da zan fara baki labari na so tari ina attempting fad'a miki sai naji kunya ta dabaibaye ni amma ya zama dole na sanar dake ko zaki d'auki darasi a ciki."
*_LABARIN ANEESERH_*
Da farko dai sunana Aneeserh Adam Muhammad, asalina yar jigawa ce a wani gari ana k'iranshi D'angyatin, Mahaifina ya kansan ce yana kasuwancin fata kuma Alhamdulillah yana samu sosai da sosai gidan mu babban gida ne me kyau da tsari, mahaifiyata Hajia Zainab ita ce uwargida sai kishiyoyin ta Maryam da Halima, mu goma sha biyar ne a wajen mahaifin mu kuma nice babba, mu bakwai wajen Mamar mu, sai biyar na Maryam uku na Halima"
Tun da na taso a rayuwata ban san menane parental love ba (soyayyar mahaifa) nayi k'uruciya ta cikin wahala da tashin hankali, bani da ikon yi komai a gidan mu mahaifiyata bata damu dani ba kamar ba ita ta haife ni ba, da nayi abun da bai kai ya kawo ba sai ta hau zagina a gaban k'anne na da kishiyoyin ta kamar "shegiya, mahaukaciya, jaka dabba mara hankali wacca bata san ciwon kanta ba, ke dai a haka zaki k'are".
Shiyasa daga kishiyoyin nata har k'annena basu ganin mutunci na yaro sai ya rufe ido ya zage ni son ransa ban isa na tanka ba, shima mahaifin mu ba damuwa yayi da yaja mu a jiki ba, abinci dai baya yanke mana a gidan nan sannan idan sallah ta zagayo zai mana d'inki amma fa sauran responsibilities d'in sai a slow ko wace mata ita take yiwa 'yay'anta banda mahaifiyar mu, gashi tana business sosai yadda bakya tsammani amma dai-dai da pant bata tab'a siya min ba.
K'awata na taso cikin tashin hankali yadda bakya tsammani domin tsakanina da mahaifiyata maganana mai dad'i baya shiga sannan kuma ta kafa min takun kumi ban isa na fita ko bakin k'ofa ba ko k'awaye na ne suka zo ban isa na raka su ba, gashi ni kuma Allah ya halicceni me farin jinin jama'a daga manya har yara idan na fita suna sona.
Bayan na gama primary school na tafi FGC Gwaram dake nan jigawa state, mahaifina yana min shopping na provision dai-dai gwargwado ya bani pocket money da yasan bazan buk'aci wani ba, to idan naje nakan siya inner waers da sauran necessary things d'in da bani dasu a wajen metron namu.
Tunda na shiga secondary school rayuwata ta fara canzawa domin na had'u da friends da yawa masu sona da k'aunata, idan mun zauna suna labari iyayen su sai dai nayi shiru domin bani da abinda zance me dadi game da nawa iyayen idan lokacin visiting yayi sai dai amin aike ko karen gidan mu bazan gani ba har visiting ya k'are.
A haka rayuwata taci gaba da tafiya har nakai SS1 a wannan lokacin na fara mallakan hankalin kaina girma yazo, domin a lokacin na ma fara period, ranar da na fara period nayi kuka sosai domin ban san wani abu game dashi ba wata k'awata mai suna Amma na samu na sanar da ita abinda ke faruwa tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata girma ne ya kamaki ai it's normal a wajen ko wace mace, kinga ni a gida na fara so ban wani sha wahalan neman Pad ba Mamana ce ta koya min komai sannan tamin nasiha sosai tace kar na kuskura na diga mu'amala da maza ko da kuwa yayyena ne ko hanuna namiji ya rik'e zanyi ciki da zan dawo ta had'oni da PAD shida dan haka muje na baki idan kin koma gida sai ki sanar da maman ki, nasan zata ji dad'i sosai " muka je ta bani pad ta koya min komai.
Tun daga wannan lokacin na fara siyan PAD da kud'ina har na kammala secondary mahaifiya ta bata tab'a attempting tambayana ko na fara period ko ban fara ba balle tayi k'ok'arin siyamin pad, inada 16years na kammala secondary school Samari da dama sun na kawo min hari duk wanda yace yana sona bana bashi fuska domin ina tsoron abinda zai je ya dawo, nayi applying ABU &BUK ban samu ba ina ji ina gani na cinye wannan shekarar a gida.
The next year wani Uncle d'ina ya sake biya min kud'i nayi jamb shine na samu admission anan 'YAR'ADUA UNIVERSITY KATSINA kafin na taho warning mai gamma iyayena suka min akan soyayya musamman ma mahaifiyata da tayi ta jifana da kalamai marasa dad'in ji akan maza wanda ko mak'iyinta akai wa baza taji dad'i ba.
A sheka da nazo Allah ya had'ani da ke da Mujaheed kun zamo wani babban jigo na rayuwata wanda bazan tab'a iya rayuwa ba tare da ku ba, Mujaheed ya dad'e yana takura min game da ya turo iyayen shi gidan mu nak'i amince mishi badan komai ba illah dan ban san ta yadda zan shawo kan al'amarin ba,Ayusha iyayen ki sun min komai a rayuwa sun maye min gurbin iyayena sun soni kamar d'iyar cikin su bani da abinda zan saka musu dashi sai addu'a saboda haka dan Allah dan Annabi ki daure ki amince da buk'atarsu albarkacin kasancewar su iyayen na gari"
Tana gama fad'in haka ta fashe da kuka Rungumota Ayusha tayi suka ci gaba da kukan su.
Sai da sukayi mai isarsu sannan Ayusha tace "lalle k'awata kinga jarabawar rayuwa Allah yasa k'arshen wahalar kenan in shaa Allah zanyi k'ok'ari naga na dai-daita tsakanin ki da iyayenki na dawo miki da farin cikin da kika rasa shekara da shekaru"
"K'awata na gode da kullawar ki gareni amma ki sani in da sabo na saba da halin iyayena sannan shawo kansu ba abu bane mai sauk'i domin kaf family d'in mu babu wanda bai san halin da nake ciki ba tun ina k'arama wasu ke k'ok'arin sulhuntamu amma abin yak'i so ni yanzu ba wannan bane a gaba na fata na ki amin ce da buk'atun iyayen ki domin sun kai a sadaukar musu"
"Aneeserh baza ki gane bane Mum &Dad are more than everything they deserve more than sacrifice from me, the fact is that bazan iya amimcewa da soyayyar tsohon nan ba na tsane yadda bakya tsammani"
"Ayusha me yasa kike da taurin kai ne, na san abin da ciwo amma yak'ar zuciyarki ya kamata kiyi bawai kibi umarnin ta ba, ki zauna kiyi nazari sosai a kan batun idan kina da hankali labari na da na baki ya isa ki k'ara tausayawa tare da k'aunar iyauenki" haka dai sukayi ta tattauna batun sai wajen 2: 00am sukayi bacci.
*_WASHE GARI DA SAFE_*
Sai misalin 10: 00am suka tashi daga bacci already Mum ta had'a musu breakfast, so had'uwa sukayi gaba d'ayan su sukayi break, ko a fuska Ayusha bata ga wani changes a wajen iyayen ta ba, bayan sun gama break tace da Mum & Dad zata shiga ciki ta kwanta domin baccin bai isheta ba.
Bayan ta shiga ciki Mum tace da Aneeserh "ya kuka k'are da ita jiya ne" "ke dai ki bari kawai Mum, wallahi ban tab'a sanin Ayusha na da taurin kai haka ba sai jiya duk yadda nayi da ita tak'i amincewa da batun yanzu haka ma bama magana na fita harkarta"
Dariya sosai ta basu sannan Dad yace "to in banda abinki d'iyata miye na gaba kuma keda kika ce zaki jure duk wani wulak'anci da zata miki sai ki b'ige da gaba"
"Baza ka gane bane Dad gaban ma wani salo ne ai" "ok sai yanzu naje ghana"
A kwana a tashi ba wuya, yau ta kasance saura kwana d'aya ranar da Doctor yace Alhaji zai farfad'o yayi, iyayen Ayusha sai zuba ido suke ko zata basu had'in kai zuwa wajen shi asibiti amma shiru ko alamu babu a wajenta, Aneeserh ma da take jiyo musu information tayi shiru.
*_RANAR FARFAD'OWAR ALHAJU_*
6: 00am Ayusha da Aneeserh suka tashi suka shiga kitchen suka had'a breakfast sukayi shirin zuwa school bayan sun gama suka zuba a flasks sukayi wa Mum & Dad sallama zasu tafi school dashi domin yau suna da visiting lecturer kuma zasu iya kaiwa yamma lis a can, tsabar takaici basu iya cewa dasu komai ba sai "Allah ya kiyaye hanya".
```To Masu karatu ku biyoni dan ganin me zai faru da Alhaji tunda Ayusha ta rufe ido ta kama gabanta tayi school ```
*RØØKÏÊY D BEST*
[14:56, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Assalamu Alaikum Masoya na nayi farin ciki sosai da na dinga cin karo da sak'wanninku tabbas idan ba makaranta barubuta, amma ina so ku fahimci wani abu guda d'aya idan muka ce a rayuwa duk abin da muke so sai mun samu to muna tare da wahala sannan akwai matsala babba domin wani abun ba alheri bane idan mun k'wallafa rai mun same shi daga baya za muzo muna da nasani dan haka dan Allah 'yan-uwana mu kiyaye mu rungumi duk k'addarar da ta zo mana hannu bibbiyu, saboda haka ina so duk abin da ya faru a littafin nan ku d'aukeshi a matsayin K'ADDARA da JARABAWA, Muje Zuwa. sannan wannan Shafin na sadaukar dashi ga duk wani masoyin ALLURA TA TONO GARMA����_*
91-95
Washe gari da safe bayan sun kammala komai na aikin gidan suka yi shirin school sannan suka had'u a dinning dan yin breakfast, Favorite food d'in Ayusha Mummy ta dafa wato D'an wake amma abin mamaki shine kowa yana cin abincin banda ita ta tsaya sai jujjuya fork take.
Dad ya dube ta da kyau yace "Auta lafiya bakya cin abincin, tunanin me kikeyi haka?" "ba komai" "da komai mana Auta,tunda kin kasa kai koda gudan d'anwake d'aya ne bakin ki, while kin san cewa saboda ke nayi d'an waken nan" "wallahi Mummy bana jin zan iya cin d'anwaken nan saboda gaba d'aya nayi loosing appetite d'ina, baki na ba taste wallah" Dad yace "Look Auta!!! har yanzu akwai sauran damuwa a tattare da ke so say out your mind ni kuma nayi miki alk'awari zan zame miki garkuwa na miki abinda kike so idan bai fi k'arfina ba"
Kallaman Dad sun matuk'ar kashe mata jiki har take jin ba zata iya gabatar musu da buk'arta ba amma wata zuciyar tace da ita "haba Ayusha this is the only opportunity left!!! wallahi idan kikayi wasa da wannan damar shike nan kin rasa Dream Guy d'inki har abada, you better do something to save your love, ki zab'i inda zaki samu farincikin rayuwar ki, me zakiyi da tsoho ai yaro sai yarinya "
D'aya zuciyar kuma tace "a gaskiya Ayusha idan kikayi haka baki kyautawa iyayen ki ba ki duba kiga irin damuwar da suka shiga yanzu sakamakon rashin cin abincin ki, har suna ikirarin komai kike buk'ata zasu miki, to idan ki sanar musu canjin ra'ayin da kikayi ya zasuyi feeling and da wani ido zasu kalli su Anty Zee while in public kika furta cewa kin amince da auren Alhaji Umar, ya kamata ki dawo hayyacin ki kisan me kikeyi domin dream guy d'in naki ma bai san da existence naki ba balle ya damu dake"
Bata gama deciding wace zuciya zata bi ba taji Mummy ta jefo mata tambaya a k'ufule "wai ke ba magana ake miki bane kikai banza da mutane Ayusha bana son sakarcin banza da wofi fa". wasu hot-hot tears ne suka fara gangarowa daga idon ta a hankali ta bud'i baki zatayi magana sai ta tsinci kanta a mai jin kunyar iyayen ta.
Dad yace "kinga Auta idan baza kiyi magana ba shikenan, amma ki sani barin damuwar taki a ciki ba shi zai magance miki ita ba. "Dad dama ba komai bane fa, tun jiya da muka baro asibiti nake ta tunanin halin da Uncle Umar yake ciki shine nake so idan mun tashi daga school mu biya mu duba shi"
A take Mum ta fara washe baki "dama wannan ne damuwarki kika tsaya kina wani kwane-kwane, ba komai idan kun tashi daga school d'in sai ku je" nazarin ta sosao Dad yayi sanna yace "kin tabbata abin da kika fad'a mana haka ne?" "Eh haka ne" "to shike nan Allah ya miki albarka ya baki ladan biyayyan da kika mana, shima Alhajin idan yaji sauk'i sai a fara zancen biki dan ba wani dogon lokaci za'a d'auka ba saboda yanayin da ake ciki"
Da k'yar da lallami suka shawo kanta taci abincin, bayan sun gama Dad ya basu kud'i yace su Siya fruits da drinks su kai asibitin.
Suna fita ta fashe da kuka Aneeserh tace "dan Allah K'awata ki kwantar da hankalin ki mana, naga alama kin kasa karb'ar k'addarar da ta zo miki, saboda haka ni zan koma ciki na sanar da Mum &Dad cewa kin janye maganar auren Alhaji Umar ai abin is understandable " tana gama fad'an haka ta juya da niyyar komawa gida da sauri Ayusha tasha gabanta "dan Allah kiyi hak'uri K'awata wallahi na kasa amincewa zuciyata ta so shi amma daga yanzu na miki alk'awarin zan amince dashi zan karb'e shi a matsayin hannu bibbiyu koda kuwa hakan na shirin barazana ga rayuwata ne saboda haka daga yanzu na sadaukar da soyayya Dream guy zuwa gare shi"
Rungumota Aneeserh tayi sukayi ta kuka san ransu sannan suka k'arasa car park Ayusha ta bata key ba musu ta karb'a da yake itama ta iya motan suka nufi boko, da yamma liss suka je asibiti, abubuwa da dama sun faru tsakani Ayusha da A. Umar tayi k'ok'arin danne tsanar sa a fili ta bashi kulawa ta musamman, ita ko Anty Zee sai nan-nan take da Ayusha kar abu kad'an ya faru tace ta faso domin tayi observing cewa dauriya kawai takeyi ba son shi takeyi ba, Allah ya taimaka Muneerah bata nan tun jiya da ta fice bata sake lek'ewo ba, Rahma ma tunda ta tafi da azahar bata dawo ba so abin ya zo da sauk'i, sai da sukayi Magrib sannan suka koma gida.
Kusan kullum Ayusha sai taje duba Alhaji Umar amma fa kullum da daddare bata bacci dream guy d'in ta ne ke zuwa mata a mafarki da kalamai masu rikitarwa tun tana damuwa har ya zama jiki.
Bayan sati d'aya aka sallami Alhaji Umar daga asibiti Alhamdulillah an samu improvement sosai domin ya dawo normal sai d'an abinda ba'a rasa ba, kwanan shi uku da sallama ya fara zuwa Zance, Ayusha in taje banda Uhm.. da ummm-ummm babu abinda take cewa har a tashi daga hiran idan ta dawo tayi ta kuka domin yanzu Aneeserh mai d'ebe mata kewar ma bata nan ta tattara ta koma school.
A kwana a tashi ba wuya har sun fara exams a lokacin ne aka. tsaida lokacin auren ta da Alhaji bayan ta gama exam's da two weeks, ba k'aramin tashin hankali Ayusha ta shiga ba da jin labarin auren, amma saboda tsananin tawakkali irin nata bata tab'a yarda Mum &Dad ko Aneeserh sun gane hakan ba, sannan bata da aikin yi cikin dare sai ibada, (karatun Al-Qur'ani mai girma, Nafilfili da Nagartattun addu'oi) tana sanar da ubangiji damuwar ta.
Ranar last paper sukayi sharing IV k'awayen ta mamaki suke domin sun san Ayusha bata son aure yanzu ita da take ikirarin sai tayi Masters da PHD sai gashi 300level d'in ma bata gama ba zata shiga daga ciki, da suka isheta da zolaye tace "kai ku k'yaleni lokaci na ne yayi, daa d'in ma yarinta ne ke damuna, yanzu da na girma ba gashi na rigaku kawo miji ba "
Sai suka kwashe da dariya suna tambayar ta event nawa za'ayi a bikin Sai tace dasu "ku kwantar da hankalinku 'yammata, bawani bidia zamuyi a bikin ba domin mijina Ustazu ne, walima ce ran Friday sai yini ran Saturday that's all, batun anko kuma ba siya zakuyi ba Daddy ya mana odar dogayen rugunan da zamu sa a walima shi kuma ango ya siyo mana atamfar