Showing 15001 words to 18000 words out of 27538 words
CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
61-65
Haka dai Alhaji yayi ta kalallame Anty Zee da sweet mouth, ranar through out wuni yayi yana farin ciki hatta 'yan office nasu sun fahimci hakan, ko ina sai side talks ake domin rabonsu da suga farin ciki a fuskar sa tun lokacin da ya fara afkawa kogin so, kai hatta matan sa da 'yayan sa sai da abin ya dinga basu mamaki domin sun dad'e basu ga yana sakar musu fuska haka ba yau har zama yayi a falo akayi hira dashi kamar da.
Masu karatu kuji Alhaji da zak'ewa sai kace wanda aka ce mishi Ayusha da iyayen ta sun amince (Lols) .
Washe gari ya kama Sunday tun safe Anty Zee ta fara shirin tafiya misalin 10: 30am ta gama komai nata d'akin Alhaji ta nufa domin yi masa sallama, tana shiga ta tarar shima ya shirya tsaf cikin wani cuffee brown shaddar shi me d'aukan ido.
"Hajiya Hajjaju gidan sammako, wato fa ke da gaske kike sai kin nemowa angon naki mata , to masha Allahu haka ake so ke dai kici gaba da bada himma ladan ki na wajen Ubangiji"
Murmushi tayi sannan tace "Yaa Alhaj, sarkin dad'in baki, ni dai kabar fasa min kai na da yawa, irin wannan kwalliya haka sai kace me zuwa zance" shima murmushin yayi sannan yace "kai Hajjaju ta inda kika b'ullo kuma! to ni wajen d'aurin auren wani abokina ma zani, sai ma muje na sauk'eki tunda naji kince motar ki na gareji ko?" "eh wallahi tun jiya Bala Driver ya kai ta yanzu na k'irashi a waya yace ba'a gama gyaran ba so muje ka ajiye ni kawai sai yazo ya d'aukeni" " ok haka za'ayi Uwargida sarautar mata" "Hmmm... kaji dashi dai"
Murmushi yayi yace "Hajiya Zainab ikon Allah muje kar na makara sha d'aya da rabi ne d'aurin auren" fita sukayi daga d'akin suna fara'a, key d'in motar ya bata sannan yace "je ki jirani a mota bari nayi sallama dasu Muneerah" "ok" shine abinda tace ta karb'i key d'in ta wuce.
Bayan yayi sallama da sauran matan ya dawo mota suka fice daga gidan, hira suke sosai cikin ni shad'i kamar wasu saurayi da budurwa, suna cikin tafiya wayarsa tayi ringing, yace da Anty Zee "Hajjaju angon ne ma yake k'ira sa min wayar a hands free, muji dame yazo" "to"
Tana sawa Alhaji yace "Ango kasha k'amshi! ka jini shiru ban iso ba ko wallahi uwargida ce ta rik'e ni amma yanzun nan zan k'ara so" "aboki dama ka zauna a inda kake dan an ma fasa d'aura auren" "what!!!why!!! ya akayi haka ta faru " "kai dai ka bari kawai yanzu haka ma bana gari idan na dawo zamu tattauna batun" "to shikenan Allah ya dawo da kai lafiya yasa hakan shine mafi alkhairi" "Ameen"
Bayan ya gama wayan ya kalli Anty Zee yace "uwargida kin ji abin bak'in cikin da ya faru da abokina ko" "wallahi kuwa, Allah ya rufa asiri" "Ameen" haka dai suka ci gaba da hirar su har suka isa k'ofar gidan.
"To Hajjaju Allah ya bada sa'an abinda aka zo nema ina nan ina jiran feedback Hajiya ta" "Alhaji akwai wani hanzari ba gudu ba, me zai hana mu shiga tare, ina ganin abin zai fi zuwa mana da sauk'i" "yanzu ke a ganin ki hakan yayi" sosai ma, bari na shiga na sanar dasu zuwan ka " "your wish is my command ranki shidad'e" murmushi tayi ta sauk'a daga motar ta shiga gidan.
Da sallama ta shiga gidan a falon k'asa tayi kicib'is da Mum & Dad na breakfast a falo, da sauri Mum ta nufo ta tana fad'in "lalle yau munyi babbar bak'uwa gaskiya k'awata kin shammace ni yanzu nan fa nake cewa Abban Ayusha ya kamata anjima naje na dubo ku tunda aka sallame ku sau d'aya naje, ya me jikin to, ga waje ki zauna" "jiki Alhamdulillah, yanzu haka ma tare muke dashi yana waje" "Haba Abuwa ya zaki baro min aboki a waje sai kace wani bak'o, bari naje na taho dashi" cewar Daddy kenan, yana gama fad'an haka yayi waje.
Murmushi Anty Zee tayi tace wato mijin ki bazai daina cemin Abuwa ba ko? ko da yake nasan maganin sa" Mum tace "kun fi kusa me shiga zancen ku shi zai ji kunya"
Dad ne suka shuga tare da Alhaji Umar, zama sukayi a kan kujera bayan nan gaisuwa ya biyo baya, bayan an gama gaisawa Mummy ta kawo musu kayan motsa baki, sun kai 30 minutes suna hirar duniya domin sun dad'e basu had'u dukansu a waje d'aya ba.
Daga bisani Anty Zee tace "wai ni ina d'iyata ne tunda nazo fa ban ganta ba, kuma ko motsin ta banji ba" "laa Ayusha ai baza ki ganta yanzu tana can tana sana'ar baccin nata da yake jiya munyi dogon hira sosai Aneeserh ce ma ta iya fitowa ta had'a mana breakfast " cewar Mummy kenan.
"Yauwa ni kam ina so naga Aneeserh nan da nake ta jin labarin ta rannan da nace Daughter tazo min weekends ma cewa tayi inyi hak'uri sai Aneeserh ta tafi" Daddy yace "ai Aneeserh yarinyar kirki ce sosai"
"Allah sarki, yauwa tun d'azu mun tsaya surutu bamu samu mun tattauna abinda ya kawo mu ba" inji Anty Zee, Mummy tace "ai ni nasan ruwa baya tsamin banza yaushe rabon da kuzo gidannan tare to Allah yasa dai lafiya" "Anty Zee ce tace "lafiya lau sai alkhairi, wata muhimmiyar magana ce ta kawo mu, amma bamu san yadda zaku d'auki maganar ba"
Sannan taci gaba da cewa "Munzo neman wata alfarma ne a gurin ku da fatan baza ku kasa yi mana wannan alfarman ba" "wallahi k'awata kin bani kunya, ke kanki kin sani tun muna yara d'ayan mu baya tab'a neman abu wajen d'an uwansa ya rasa to me yasa yanzu zakiyi kokwanto wajen tambayata abu har ma kike k'iranshi da alfarma" "ba haka bane k'awata wannan karon abin yasha ban-ban, ni dai fatana ku amince da buk'atar mu"
"Kar ku ji komai Abuwa, tun kafin ki fad'i buk'atarki an amsa miki" inji Daddy, shi dai gogan namu shiru yayi yana kallon ikon Allah zuciyan sa sai dukan tara-tara yake da ya tuno kalaman uwargidan sa na jiya da daddare inda take cewa "ka kwantar da hankalin ka My Lurv nace maka muddin na gabatar musu da buk'ata ta zasu amince" take sai yaji relief domin yaga alamun nasara a tattare dasu.
Baiyi aune ba yaji tace "wato abin da yake tafe damu shine... " sai ta tsinci kanta da jin nauyin maganar, hankalin Alhaji yayi k'ololuwar tashi take ya fara auro irin halin da zai shiga idan ya rasa Ayusha.
"Ci gaba da magana mana Abuwa, lokaci na tafiya fa azahar ma ta gabato" cewar Daddy, Mummy tace "k'yale yar rainin hakali idan taga dama kar ta fad'a d'in" "kwantar da hankalin ki k'awata me kika ci na baka na zuba, yanzun nan zakiji komai , dama akan Ayusha ne tun ranar da Alhaji ya d'aura idonsa a kanta yaji duk duniya babu wanda yake so ya aura sama da ita, nasan zakuyi tunanin abubuwa da dama a kai na, to ni na yarda na amince da hakan shiyasa ma nayi masa jagora zuwa gareku!!!?
Dakata Zainabu, kina nufin d'an wajen ki Fahad ne yaga Ayusha ko kuma wa? " tambayar da Daddy ya jefo mata kenan, k'arfin hali tayi tace "ba Fahad nake nufi ba Alhaji Umar baban Fahad ne yaga Ayusha yake so" "wallahi tallahi k'awata kinyi asarar rayuwar ki, sai kace kin rako mata duniya yanzu ke tsabar dak'ik'anci ki rasa wa zaki zo nemawa aure sai mijin ki, auren ma na Ayusha ina hankalin ki da tunanin ki suka je, to idan ma mafarki kike to kiyi saurin farkawa dan wallahi tallahi bazan tab'a amincewa da wannan iskancin ba Mtwww!!! kai ma na dawo gareka babban munafiki wato buduwar zuciyar taka bata tashi sauk'a a kan kowa ba sai a kan d'iyata!!! to ka sani ko zaka mutu baza ka tab'a samun ta ba dan haka ka tashi ka tattare 'yanmatan k'afafun ka bar gidan nan tun kafin nayi maka rashin mutunci, tsohon najadu kawai" duk wannan bala'in Mummy ce keyi.....
Ajiyar zuciya me k'arfi Anty Zee tayi sannan tace "dan Allah dan Annabi k'awata ki kwantar da hankalin ki, ki saurari abinda zan fad'a miki" "baki da sauran kalaman da zan saurara daga gareki, kunya dai kin riga kin bani dan haka ki tashi ki bishi kuje wani wajen neman matar ba nan ba tunda de ke kare ya riga da ya lashe zuciyar ki"
Ba suyi aune ba sai ganin Alhaji Umar sukayi ya zube a k'asa yana fad'in "dan Allah dan Annabi ku taimaka ku ceto rayuwata daga halin da take ciki wallahi tallahi bazan tab'a iya rayuwa ba tare da Ayusha ba rasa Ayusha dai-dai yake da rasa rayuwata!!!" sai kawai ya fashe da kuka.
Mummy tsabar tak'aici ma kasa magana tayi, Allah sarki Daddy da yake shi namiji ne yasan ba k'aramin abu bane zai iya sa gawurtaccen namiji kaman wannan kuka, yace "tashi ka zauna Alhaji muyi magana"
A dai-dai lokacin suka jiyo ihun Aneeserh na fad'in "wayyo Allah na shiga uku Mummy kuzo ku taimakeni Ayusha ta.....!!!"
```Masu karatu kuyi manage da wannan sai mun had'u a next page dan ganin me ya samu Ayusha. Bissalam nice dai har kullum```
*ROOKIEY D BEST*
[14:55, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
66-70
Da gudu suka hau sama dan ganin halin da Ayusha take ciki, sun sameta a kwance shame-shame kamar gawa a take hankalin su yayi mugun tashi Dad yace "Aneeserh me ya same ta?" cikin kuka tace "wallahi nima ban sani ba dan muna zaune da ita tace bari taje ta gaishe ku, bayan ta fita ta dawo cikin wani yanayin da ban tab'a ganin ta ba fuskar ta d'auke da hawaye sannan ta rik'e kanta da hannun ta da sauri na nufi inda take sai gani nayi ta fad'i k'asa tana nishi numfashin ta na fita sama-sama lokaci d'aya ya d'auke" sai ta k'ara fashewa da kuka.
Dad yace "Tabbas taji maganar da muke tattaunawa da alama suma tayi" kafin ya rufe bakin shi Aunty Zee tayi saurin shiga toilet ta d'ebo ruwa ta watsa mata,Mommy na rik'e da ita sai tofa mata addu'a take, d'ago idon ta tayi sukayi four eyes da Alhaji dogon tsaki taja sannan ta nunashi da yatsa tace "wallahi idan na rasa 'yata kotu ce kad'ai zata rabani da kai"
Shi bai ma san tanayi ba balle yaji zafin maganganun ta, tunda ya shigo yaga Ayusha a wannan yanayin hankalin sa ya tashi zuciyar sa ta fara murd'a tana zugi da rad'ad'i.
Dogon ajiyar zuciya Ayusha ta saki wanda yayi dragging attention nasu cewa ta farfad'o "Alhamdulillah" shine kamar da ya fito daga bakin Dad, Mummy ta rugunmota jikin ta tana fad'in "sannu Auta, ina ne ke miki ciwo fad'amin kin ji d'iyata" shiru tayi tana binsu da kallon one by one tana k'ok'arin tuno wani abu da ya faru tana kai idon ta kan fuskar Alhaji ta fashe da kuka tana fad'in "me ya kawo ka d'akina ka fita ka bani guri natsane ka na tsani me k'aunar ka, wallahi ko maza sun k'are a duniya bazan tab'a auren ka ba i hate you!!! "
Aunty Zee ce tayi saurin matsowa kusa da ita ta, ta kamo hannun ta, zatayi magana kenan.. Ayusha tayi saurin dakatar da ita ta fincike hannun ta a jikin ta, Malama karki kuskura ki k'ara attempting tab'a ni domin a yanzu nafi tsanar ki fiye da kowa, na d'auke ki a matsayin uwa ashe ke ba haka kika d'auke ni ba Allah ya isa tsakani na da ke muguwa azzal... " bata k'arasa maganar ba Dad ya d'auke ta da wawan mari "Ayusha dama baki mutunci ban sani ba? tarbiyyar da muka baki kenan, to ki sani na yanke hukunci ko zaki mutu sai kin aure shi"
Rik'e k'uncin ta tayi tana kallon Dad tun da take a rayuwa bai tab'a sa hannu ya duke ta ba sai a dalilin Alhaji Umar a zuciyar ta tayi alk'awari to ko sama da k'asa zata had'e baza ta tab'a yarda ta aure shi ba, wani irin kuka ne ya yunk'uro ta tace "Dad yau nice ka mara saboda wannan mutumin" ta nuna Alhaji, sai kawai ta mik'e tsaye take jiri ya d'ebe ta ta fad'i ak'asa .
Mum da Aneeserh sukayi saurin d'agota suka d'aura ta kan gado, a take jikin ta ya d'au zafi ta fara karkarwa tace "Mum kaina zai fashe ciwo yake min d'auko bargo ki rufeni sanyi nake ji" da sauri Aneeserh ta jawo bargo ta rufe ta.
Anty Zee tace "na shiga uku na lalace ya zanyi da raina ni Abu Alhaji dan Allah kayi hak'uri ka janye maganar auren nan kaga halin da yarinyar nan ta shiga sanadiyyar mu idan wani abin ya sameta ma Allah bazai barmu haka ba"
Kasa magana Alhaji yayi saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga babu abinda idanun sa keyi sai zubda k'walla lura da halin da yake ciki yasa Dad ya rik'o hannun shi yace "kwantar da hankalin ka aboki na muje masallaci an k'ira sallah" ya kama shi suka fita waje.
Suna fita Aunty Zee ta k'araso gaban Mum ta zube "dan Allah dan annabi k'awata kiyi hak'uri da abin da ya faru, kar wannan abin ya zamo silar rushewar zumuncin mu ki sani bani da niyar cutar da Ayusha nayi haka ne dan na ceto Alhaji daga halin da ya ke ciki amma ki min afuwa daga yanzu komai zai dawo normal in shaa Allah" wani mugun kallo Mum ta watsa mata sannan tace "baki da abinda zaki ce min, tunda bakiyi la'akari da halin da yarinyar zata shiga ba saboda son zuciya ke dai burin ki kawai ki farantawa mijin ki rai ki b'ata na wasu"
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga idanunta tace "OMG!!! dan Allah K'awata ki fahimce ni, wallahi ban yi haka dan son zuciya ba illah dan ceton rai!" "Ceton rai kuma!!!? nifa ban gane ina kika dosa ba" cikin kuka Aunty Zee tace "ranar da Alhaji ya tunkare ni da batun Ayusha babu irin haukan da ban mishi ba,ji nayi a duniya ban tab'a tsanar wani d'an adam irishi ba, nayi dana sanin kasancewa tare dashi amma daga baya na tausaya mishi sakamakon halin da ya shiga dalilin k'in amince masa..." nan dai ta kwashe labarin abinda ya faru ta basu da irin shawarwarin da likita ya basu sannan ta k'ara da cewa "yanzu haka Allah ne kad'ai yasan halinda Alhaji yake cikin kamar yadda yace rasa Ayusha dai-dai yake da rasa ransa haka abin yake, dan Allah dan Annabi kin ga laifi na dan nayi k'okarin ceto shi"
Duk wannan labarin da Aunty Zee ke bayarwa a kunnen Ayusha da Aneeserh, Aneeserh ta tausaya mishi sosai, ita ko Ayusha ji tayi ta k'ara tsanar shi sannan ta k'ara k'udirta wa bazata tab'a yarda ta aure shi ba, Mummy ma tayi matuk'ar tausaya mishi sannan ta k'udiri niyar cewa in shaa Allahu zata shawo kan Ayusha ta amince ta aure shi domin yana buk'atar taimako, tana ganin abin ma zai zo mata da sauk'i tunda Ayusha bata da saurayi kuma tasan yanzu ma b'acin rai ne ya sata yin hauka dan bata tab'a bijirewa umarnin su.
Dafa kafad'ar Aunty Zee Mum tayi tace "ki kwantar da hankalinki k'awata yanzu na fahimce ki kuma na miki alk'awarin in shaa Allahu komai zai dai-daita" a dai-dai lokacin Dad ya shigo a gigice yace "Hajia mik'on makullin mota ta mu tafi asibiti yanzun nan mun fito daga masallaci Alhaji umaru ya fad'i yana ta aman jini"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, shike nan Alhaji ya mutu kawai!!! ,dama Doctor yace idan muka bari irin haka ta kuma faruwa zamu iya rasa shi" Dad yace "ki kwantar da hankalin ki Zainabu, bai mutu ba da ranshi addu'ar mu yafi buk'ata yanzu ku zo mu tafi asibitin"
Gaba d'ayansu suka fice daga d'akin Ayusha da kawai suka bari ko motsawa tak'i yi daga kan gadon.
*_kuci gaba da bibiya ta har yanzu da sauran rina a kaba, domin yanzu labarin ya fara.... mu had'u a shafi na gaba dan ganin ya zata kasance tsakanin Alhaji da Ayusha