Showing 3001 words to 6000 words out of 27538 words
sun tashi daga bacci sukayi sallah, wanka sannan suka shirya,d'akin Mummy suka nufa suka gaisheta sannan suka d'unguma wajen Daddy nan ma gaisuwar suka kwasa aka d'an tab'a barkwanci na minti biyar dayake Dad mutum ne me son barkwanci, ya bud'e side drower ya zato 20K ya bawa Aneeserh yana fad'in " 'yata ga wanna ba yawa kiyi managing" hannu biyu tasa ta k'arba tace "na gode Abba, Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i" "Ameen di'yar albarka" ya juyo da dubansa ga Auta yaga ta marairaice yace " ya akayi ne autar Babanta" k'ara shagwab'ewa tayi tace "Daddy ni baza a bani kud'in shaa mai ba" murmushi yayi yace "Auta kiji tsoron Allah jiya-jiyan nan fa kikayi full tank" sosa keya tayi tace "to a k'ara min pocket money Daddy" murmushi yayi yace "Auta dai ta rantse sai ta caje ni yau,any ga 5k nan ki rik'e" hannu biyu tasa ta karb'a tana godiya.
a gaggauce sukayi breakfast sukayi sallama da Mummy suka fita suna isa school direct lecture hall suka wuce.
A haka rayuwa taci gaba da tafiya har suka fara second semester exams,a ranar da suka gama Aneeserh ta wuce gidansu Ayusha kwanan su uku sannan ta tattara ta koma d'angyatin.
```To masu karatu Ku biyo Rakiya dan ganin inda ALLURA ZATA TONO GARMA....this is just the Beginning of the story. ```
*ROOKIEY DBEST*
[14:51, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_This page goes to MUFEEN , AREEF (MY SON) ,MAIMUNA (Maman Fatiey) & Fatiey❤❤❤na gode da K'aunar ku Allah ya barmu tare_*
16-20
Rayuwa taci gaba da tafiya yau fari gobe bak'i,a haka har suka gama hutun su suka dawo 300level new session,abubuwa da dama sun faru sai godiyar Allah. wata rana sun fito daga lecture Ayusha ta kalli Aneeserh tace "k'awata kin bamu rani da yawa fa rabon da kizo gida weekend yaka 3 weeks fa" "k'awata ban da sharri fa duka-duka rabona da gidan two weeks kuma in shaa Allah this coming weekend a gida zanyi" "yauwa ko ke fah wallahi Mum &Dad ma suna missing naki kin san ni kad'ai ce a gidan nai ta musu rigima" "shegiya ba k'atuwa dake baki dai na hawa kan cinya ba wallahi ya kamata kiyiwa kanki fad'a na tabbata ko yanzu aka aurar da ke tsaf zaki zauna a gidan miji amma tsabar iya shege kiyi ta abu kamar yarinyar da ba'a yaye ba" dundu Ayusha ta d'uma mata sannan tace "shegiya sai ki aurar dani ai,idan ke idon ki ya rufe da soyayyah ni nawa a bud'e yake so allow me to shana,ni da aure sai nai PHD"
"lalle baki da hankali k'awata har kin manta nasihan da Mummy ta miki akan aure ko, to wallahi ki nutsu ki farka daga nan nauyan baccin da kike aure shine mutunci d'iya mace saboda haka daga yanzu ki ma sanya aure cikin budget naki kafin grads" "Allahu akbar ya Al-sheik Allarammiya Aneeeserh matar Allaramma Mujaheed,any way naji magan ganunki may be Zan yi thinking a kai" " ke kika sani dai in kin ga dama kiyi dreaming ma"
Dariya Ayusha tayi tace "dreaming d'in ma zanyi kuma duk abinda na gani in my dreams zanyi believing dashi" dundu Aneeserh ta d'uma mata tace "shegiya jaka Allah yasa ki gano aure a kwana kusa Ameen" "Hegiya muguwa ba Ameen ba,sai dai na gano aurenki da Mujaheed, yauwa k'awata wai me ya faru ne kwana biyu bana jin d'uriyarki da Mujaheed ne ina fata ba sab'ani kuka samu ba" " eh to k'awata zan iya cewa mun samu misunderstanding dashi" "kamar ya fa!!!?" "kin san tun last year yake bina akan yana so ya tura magabatan sa gidan mu iyaye na su san dashi nace ba yanzu ba, shine shekaran jiya ya sake tayar min da zance wai a gidansu an takura mishi ya fitar da mata idan ba haka ba zasu bashi duk wacca suka ga dama nayi-nayi na fahintar dashi matsalan ya kasa fahimta ta ni yanzu i'm totally lost and i don't know how to fix it" tana gama fad'in haka sai ta fashe da kuka.
Da sauri Ayusha ta kamo ta, ta zaunar da ita kan wani resting chair itama ta zauna sannan ta sassauta murya tace "k'awata ki kwantar da hankalinki, komai yayi tsanani maganin sa Allah, ni banga laifin Mujaheed ba dan yace yana so ya turo magabatan sa ke ce fa nan kike min wa'azin aure,yanzu dai ba wannan ba ina so ki fad'amin mene ne damuwarki ni kuma na miki alk'awari in shaa Allahu sai zan taimaka miki wajen ganin kin cimma burinki" shiru tayi na d'an wani lokaci sannan tace "ki gafar ce ni k'awata,na san zaki iya yin komai dan ki sanya ni cikin farin ciki, bawai bana so na fad'a miki damuwa ta bane no I'm waiting for the right time,please ki gafar ce ni wallahi in time yayi zan sanar da ke"
Shiru Ayusha tayi tana observing nata daga bisani tace " ba komai k'awata Allah ya kaimu lokacin" jikin Aneeserh yayi matuk'ar yin sanyi jin kalaman k'awarta ita kanta tasan bata kyautawa Ayusha bata tab'a boye mata damuwanta ko ya yake amma ita dai-dai da lokaci d'aya bata tab'a fad'a mata na ta ba,ba komai wannan karon dai ya zama dole ta sanar da ita duk da tasan cewa babu taimakon da Ayusha zata iya, in shaa Allahu in tazo weekend zata sanar da ita komai.
Ayusha yarinya ce mai zurfin tunani da hangen nesa, ta dad'e da observing Aneeserh na facing problem and bata son kowa ya sani shi yasa batai insisting ta fad'a mata ba ta bar ta har zuwa lokacin da tayi niyar fad'a mata.suna a zaune a wajen wasu course mate's nasu suka zo sukayi joining nasu Fateema da Safiyyah sun dad'e suna hira daga bisani suka watse suka nufi parking lodge Ayusha ta d'auko mota tace da su Teema su tsaya tayi dropping nasu, ba musu suka shige motar a k'ofar hostel ta sauk'e Aneeserh sannan ta juyar da kan motar zuwa waje a dai-dai bak'in gate wani matashin saurayi wanda a k'alla zai kai 30yrs ya gobza mota, wani wawan birki taci ta tsaya,shi kuwa gogan zaune yake cikin motar sa ko kad'an bai da niyan fitowa rai b'ace ta fito daga nata motan ta k'araso tai masa knocking, a hankali ya bud'e k'ofar yana mai sauk'ar mata da mayatattun idanu wansa a kan ta kallon up and down tai masa sannan tace "Mallam kai makahon ina ne,ka buga min mota and you still have the gouts to seat kana nufin ni zan biyo ka" shiru yayi bai ce ko uffan ba har ta gama bal-ba-lin bala'in ta ta tafi.
Da sauri ya bud'e motar ya biyo ta a baya yana fad'in "pretty wait!!! dan Allah kar ki tafi ki barni" manna mishi bajon mahaukata tayi ta shiga mota.
Safiyyah ce ta kalleta tace "Beb i like your action,kin min dai-dai da baki saurareshi ba irin banzayen samarin nan ne da basu san me sukeyi ba" "Hmm!!! ni daman bani da lokacin shi ai yaci sa'a yau a Shatu nake wallahi da a Indo nake da yaga tsantsar wulak'anci" k'yalk'yalewa da dariya sukayi Teema tace "wallahi guy d'in A1 ya had'u over,wallahi ban gaji da kallon sa ba muka baro gun" wani dogon tsak'i Aysha taja sannan tace "ke wallahi banza ce a haka zaki k'are da kallon maza ina hud'uwar take anan, ni ban ma yadda yana da cikakken hankali ba domin abinda yayi mai hankali ba zai aikata ba" har suka isa inda zata sauk'e su basu dai na discussing issue d'inta, tana aje su ta pigi mota sai gida.
Tun daga nesa take ta faman buga mai gadi da kansa yasan yau ba lafiya duk lokacin da yaji tayi irin wannan hon d'in yasan akwai matsala,da sauri yazo ya bud'e mata gate ya doka mata kirarin da ya saba ko kallo bai ishe ta ba ta shige ciki.
a falon k'asa ta iske Mum & Dad daga musu hannu kawai tai ta haye sama baki suka sake suna kallonta, sai da ta kusa hayewa gaba d'aya Dad yayi gyaran murya yace "zo nan d'iyata,waya tab'a min haka kike cic-cin magani"
Da gudu ta sauk'o ta fad'a mishi sai ta fashe da kukan shagwab'a Daddy yayi murmushin su na manya yace "kukan ya isa haka Auta fad'a min damuwarki" nan ta kwashe mishi da duk abinda ya faru from A-Z bayan ta gama koro bayani yace "yanzu saboda d'an wannan abin kika tada hankalinki, ki godewa Allah ma da abin ya tsaya a kan motar yanzu haka wani mugun abin ya tare, sannan cin mutuncin da kika masa bai dace ba ba irin tarbiyyar da muka baki ba kenan saboda haka kar na sake jin kin ci mutuncin wani, bari na k'ira Nazeer electrition yazo ya tafi da motar garage" "na gode Daddy in shaa Allah bazan sake ba" "good, ko ke fa" tunda aka fara show d'in Mummy bata ce komai ba sai da aka gama sannan tace "duk abinda ya kamata na fad'a Abbanki ya fad'a saboda haka ki jiyaye" "to Mummy in shaa Allahu zan kiyaye" "yayi kyau Allah yai miki albarka, tunda yau kin dawo da wuri shiga ciki ki huta anjima zan aike ki gidan Hajiya Zainab zata baki sak'o ki kawo min"
"to Mummy bari na shiga cikin"
```To masu karatu anan na dakata for today kuci gaba da bina har zuwa lokacin da Allura zata tono garma```
*ROOKIEY D BEST*
[14:51, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Wannan shafin d'ungurugum d'inshi na sadaukar dashi ga k'awar Arziki FATEEMERH MUKTHAR D'AN-MALLAM (Yarmal) Amaryar December In Shaa Allah, Allah ya barku tare da Hubby❤❤❤yan LAKER'S Ku shirya akwai bikin bud'e madara @ KT lols��������_*
21-21
Misalin k'arfe biyar Ayusha ta shirya tsaf cikin wani maroon gawn me d'auke da milk Stone's a jiki simple make up tayi tai rolling kanta da milk vail ta d'auko milk jaka and shoe's ta sanya, wajen mirror ta nufa ta kalli kanta tsaf sannan ta murmusa tace "Masha Allah ashe ni d'in kyakkyawa ce" sannan ta fice daga d'akin, direct d'akin Mummy ta nufa.
Tana shiga d'akin Mummy ta kalleta tace "Wow My Daughter kin gan ki kuwa irin wannan kyau haka Masha Allah, Allah ya sa a fita a sa'a" murmushi tai tace " na gode Sweet Mum,amma ban gane sa'ar da kike nufi ba" murmshi Mum tayi tace "yaro man kaza ai nasan baza ki tab'a ganewa ba so a bar zance kawai coz idan nace zan tsaya miki explaining tym zai tafi" "ok,Mum bani da kirki wallahi, rabona da gidan Aunty Zainab har na manta, kullum tazo nan sai tamin gori amma a banza" "Hmm....ke kika jiyo dai ba kullum in nace miki kije ki gaishe ta sai kina kawo min wasu unnecessary excuses naki ba idan kin je kya mata bayani ai" murmushi Ayusha tayi tace "Aunty Zainab tawa ce nasan yadda zan shawo kanta, so yanzu fad'a min sak'on kar na makara kin sa ba mota a hannu na" "je ki d'auki keyn mota ta ki tafi da ita" "no Mummy bar shi kawai ban jin zan iya driving yanzu zan hau adai-daita kawai" "shikenan Auta, idan kin je kice ina gaishe ta, sannan ki ce da ita ya labarin sak'on nan ne na jita shiru bata motsi, idan sak'on ya samu ta baki ki kawo min, sannan dan Allah ki kula da kanki Auta".
"OK Mum in sha Allah zan kula" "good Allah yai Albarka" "Ameen Sweet Mum"
Da yake gidansu ba nisa da bakin titi tana fita ta samu NAPEP me NAPEP yace da ita "Hajia wani unguwa za'a kaiki" "SARDAUNA ESTATE zaka kaini San nan ni kad'ai zaka d'auka ban san gayya" "Angama Hajjaju in dai masu gidan rana na aiki to babu inda baza a kaiki ke kad'ai ba" tunda ta shiga ta manna mishi bata kula shi ba saboda taga alama yana da rawar kai.
Suna isa estate d'in yace "Hajiya ina muka nufa" directing nashi tayi zuwa k'ofar gidan Aunty Zainab tana sauk'a tace dashi nawa ne kud'in ka" "300 ne Hajjaju" 500 ta ciro a jaka ta bashi, ta juya zata tafi yace"Hajiya tsaya ki karb'i can jin ki" murmushi tayi tace "no ka bar shi kawai" "godiya nake Hajjaju Allah ya baki miji na gari me k'aunar ki" ta amsa mishi da "Ameen" ta wuce.
Knocking k'ofar falon tayi, wata yarinya yar kimanin 7yrs ce ta bud'e k'ofan tana ganin Ayusha tayi murmushi tace "sannu da zuwa Anty kyakkyawa" dariya tayi tace"yawwa Cutie coz kema kyakkyawar ce" dariya yarinyar tai tace "na gode Anty, wajen wa kika zo Mummy ko umma, ko Mami?" murmushi tayi tace " yammata kai ni wajen Mummy" kamo hannun Ayusha tayi tace "muje" suna shiga falon ta taradda da Amaryar su Anty Zee Fatima wacca suke k'ira Mami wani kallon raini ta fara watsa wa Ayusha "sannunki" shine kalmar da ta iya fitowa daga bakin Ayusha "ke kuma daga ina" shine abinda tace da ita manna mata Ayusha tayi ta shige ciki ba tare da ta tsaya bata amsa ba "iyeh, lalle wannan yarinyar tacacciyar mara mutunci ce ki tako har gidan nawa sannan ki kawo min iskanci, hmmm zaki gane baki da wayo" ita kad'ai take bambamin ta domin Ayusha bata san ma tana yi ba, falon Anty Zainab yarinyar ta kai ta sannan tace da ita "Anty zauna anan,bari na miki magana da ita tana kitchen" "OK 'yan mata" zama tayi kan kujera ta tsurawa falon idon tana kallo komai na falon d'os da shi gwanin ban sha'awa a zuciyar tana fad'in, " Anty Zainab sarkin gayu komai nata na 'yan gayu ne jibi falon ta kamar na sabuwar Amarya, Allah sarki rayuwa kamar ban zauna a gidan nan ba nida nake shafe wata da watan ni anan amma yanzu a k'alla na kai kimanin shekara goma ban zo ba, rayuwa kenan"
Tana cikin tunani taji an dafa ta ana fad'in "Aunty Me kyau ga ga drinks kisha Mummy na zuwa" firgita tayi tace "oh Cutie har kin bani tsoro" "Sorry Anty Mekyau nai ta sallama shiru baki amsa ba shine nace bari na dafa ki ko zaki jini" " oh!!! haka ne fah na shiga duniyar tuna ni ne" "tuna nin me Anty" "Ba komai Cutie" "to Anty wani drink zan mik'o miki HAPPY HOUR KO MULT" "bani Happy hour dan ban cika sha Maltina empty ba" Happy Hour ta tsiyaya mata a tumbler, sannan ta matso mata da center table gaban ta tace "Anty na zuba miki drink d'in gashi ki had'a da snack's" "wow Cutie wanna duk nawa ne ni kad'ai, thank you very much, amma bani kad'ai zan ci so kema d'auko cup kiyi joining d'ina" ba musu tace "to" ta wuce d'auko cup tare da Anty Zainab suka shigo tare tana shigowa tace "Lalle kam Anty Mekyau ,Afrah ta shigo ta same ni wai in zo Anty Mekyau tazo, na rasa gane wace ce Anty Mekyau ashe ke ta ke nufi, ko da yake bata san ki ba domin rabonki da gidannan tun kafin a auro mahaifiyar ta" zaro ido waje tayi tace "Amma ba yar matar da nagani a babban falo bane" "dariya Anty Zainab tayi tace "no mamarta bata nan ta fita unguwa ban ce ta dawo yanzu ba saboda bata dad'e da fita ba may be Sumayyah kika gani" "OK"
Nan dai suka shiga gaisawa da junan su Anty Zainab tai mata tatas sannan tace "nasan wannan zuwan ma ba zuwan kanki bane aiko ki akayi gobe nake shirin aika mata sak'on sai gashi kinzo" dariya tayi tace "kimin afuwa Aunty abubuwa ne yamin yawa shiyasa bana samun damar zuwa amma In Shaa Allah daga yanzu zan dinga zuwa ko dan Cutie ma" "a lalle wato kema da sunan da kika sa mata kenan to shike nan idan zakiyi aure zamu baki ita" gaba d'ayan su suka kwashe da dariya.k'iran sallan magrib akayi Aunty Zee tace "Ayusha shiga ciki kiyi sallah,naji an fara k'iran sallah" "to Aunty"
```Masu karatu kuyi hak'uri da wannan ku ci gaba da bibiyar Allura ta tono garma```
[14:52, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Wannan shafin naki ne HAUWA BASHIR ISA (MEKWI A.K.A EXCLUSIVE) The most shortest girl among the giant set of LAKER'S 2011 @ HIGSS lols������ ni kaina na san kin fi kowa K'aunar ALLURA TA TONO GARMA��i heart you Beb❤Allah ya barmu tare_*
*_NOTE:_*```Ku min Afuwa masu karatu nayi Making mistake wajen numbering page maimakon 21-25 nasa 21-21 so zan cigaba da 26-30 hope you will not be confused ❤ ```
26-30