Showing 15001 words to 18000 words out of 102653 words
Chapter 6 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt
za
ka jawa abun kunya, ka yiwa qanwarka fyadeee dan iskan to
wlh daga rana irin tayau ka gama haikewa ‘ya’yan jama’a.”
Ya juya a zafafe sai ga shi ya janyo wani qaton faskare,
Laure ta riqe tana
fadar. A,a don Allh kayi haquri Malam karka kashe shi.”
Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi
gawarsa cikin gidannan inya so nima a kashi yayi kukan
kura gamida yin kansa da faskaren
Wooooohoho jama,a wai ya abin yakene mu kubiyo ni donjin
yaddah wannan taqaddama zataci gaba da kayawaaaaaa
[1/17, 7:49 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼♂@lh@ji🙆🏼♂: [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 11*
ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana
fadar. a a dan Allah ka yi hakuri Malam kar ka kashe shi.” °
Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi
gawa'rsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.”
Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi’u da duka kamar Wani
zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin hankali su
suka hana Rabi'u komai saidai kare kansa da yake, sai da
yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike ya yi
waje
Hayaniyar su ce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta
tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake
faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana
dukan Rabi’u ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta
motsa
‘ Rabi’u ya ruga malam ya bi shi har
, “Sai na kashe ka la’anan nan Allah, Allah ya isa tsakanina
da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin *gidan nan, kai
cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka
munafukin Allah.”
Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa ‘yan zummokaransa
ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, “Ka san inda dare
ya yi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa
ka hadu da mummunan hatsarin da za a kasa gane ka,
Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah ya yi maka
wanda . ya fi shi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta,
Allah ya daga maka hakali ya hana nutsuwa a duk inda ka
ke”
Laure ta fito tana fadar, “Don Allah Malam ka shigo gida
haka nan tun'da dai ka kore shi ka ga har ‘ mutane sun fara
taruwa.” '
Malam Bala ya dawo gidan ya ci gaba da 'zazzaga masifa
tamkar wanda ba ya cikin hankalin shi, Saude dai na kallon
su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata
mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba
Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana
neman Rabi’u can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar
gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya
hada kan shi da gwiwa da ‘yan kullin tsummokaransa a
gaban shi.
Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake
tana kiran sunan shi, Rabi’u ya yi saurin dagowa yana
kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da
hawaYe, ya yi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. '
Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da 'wani irin
kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi’u
ya samu da kyar ya iya tsaida nasa
kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba
tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba.
“Saude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Ki yi
hakuni na san Ubang‘iji na sane da mu ba mancewa ya yi
da mu ba, kuma shi ya san yanda zai yi da mu, tashin
hankalina Saude a yanzu daya ne ' yanda zan tafi in bar ki
ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki
fuskanta bayan bana nan, ban sani ba.”
Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, ‘Dole zan
tafi', dole zan bar garin nan Saude ki yi hakuri ki rungumi
rayuwa a duk yanda ta zo miki kar ki yarda ki sabawa
Ubangiji a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0
kishiyar hakan. Na ‘ san insha Allahu Ubangiji ba zai bar
rayuwarki ta lalace ba." ‘
Yasa'hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi ‘yan, dari
biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya
raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, “Ga. wannanki riqe
a hannunki kiyi amfani dasu insha Allahu zaki rinqa samun
aikena a duk inda na shiga a fadin
duniyar nan.”
Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar,
“Allah ya hada fuskokin mu da alheri."
Saude ta yi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin
kuka mai daga hankali.
“Don Allah kada ka tafi ka bar ni Yaya wallahi mutuwa zan
yi idan ka tafi Wayyo Yayana!” Ta qara fashewa da wani
gunjin kukan.
Rabi’u ya dafa ta yana kallon idanuwanta kafin ya ce, “Ki yi
haquri Saude ni kaina ba dan na so ba zan tafi inbarkiba,da
zaiyiwu da dole dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne
tunda ke macece amma na
yi miki alkawarin duk inda make a duniya ina tare
da.... Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda
kukan da ya kwace masa shi ma. Ya zame hannayenta
daga jikinsa yana fadar, “In har kina sona da gaske Saude
kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida ni na tafl sai
wata rana.”
Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar
hawayen da ke zuba daga idanuwanshi kamar an kunna
famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka tun
iya karfinta. Rabi’u na jin ta amma bai waiwayo ba saboda
yanda yake jin zuciyarshi na
Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba
jama’a da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda
Saude ta duka ba ta sake tashi a gun ba, tun tana kukanta
iya karfinta har muryarta ta disashe. ~
Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga
gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana,
amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana' kuka, ba ta
ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina’ tana dagowa ta
ga Inna Laure, ta mike ta ‘ kwasa da gudu ta nufi hanyar
gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ' Tana shiga cikin gidan ma
nan ma Malam ya dora mata da na shi dukan yana zaginta
tare da yi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu
alamun ' tausayawa“ a fuskarta ita ma ta hau zaginta tana
fadin
* “’Yar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna
tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.”
Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu
tsummokaran kayan ‘Yar Baba wadanda ta gama da su ta
watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada
mata yanda za ta sanya sannan ta ‘ dora mata tallar
wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta tice daga gidan tana
matsar kwallah.
Haka ta je tallar ta dawo ba taci komai ba, sai kukan da
take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki
alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wurin ranar
yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za ta ga Yayanta
amma k0 mai kama da shi bata gani ba haka ta karaci
yawon tallar ta ta dawo da yamma likis.
Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman
kujera ‘yar tsugunne taya ni gulma suna
hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da
baki tana fadar.
“Kin gan ta nan fa dillalliya, wan: ai aikatau ga wannan ai
tallar cc kawai ta dacc da ita.”
Dillaliya ta ce, “Haba dai a ganin ki dai, amma in da ni ce da
wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai."
Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna
Laure cinikinta ta mike ta wucc dakinta.
Tana jin Inna Laure na fadar, “Hmm! Dillaliya kenan ai ni
duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, to shi kuwa k0
miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi
don har na fara tunanin in zuba masa shinkafar Bera a
abinci ‘ya ci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe.
Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na 'ga yarinyar jinin ya
zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai da na
shiga daki na yi ta dariyar qeta yanda na ga Malam na
sharar ‘yar kwalla.”
I
Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo
diilaliya na fadin
“Ke wai ba zaki saro gyada ki soya mata ta rinqa zama
kofar gida ba na ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za
ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da daddare.”
Laure ta ce “Ai k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje
‘Yar Kutungu da kaina in siyo mai kyau
in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata
Akwai ki da bada shawara mai kyau.
Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuquki
wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da
mai lallashin ta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda
rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa
Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta
yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata
a. duniya, ba su da kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta
sake rushewa da wani sabon kukan lokacin da ta tuna da
lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan
kwalliya. *
Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan ya ga ta shiga
damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen
nata, ga shi yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya
ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan
za ‘
tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shi ba
yanzu, wala ya mutu k0 ya yi rai. Shin k0 yana a wane hali
yanzun ma?
“Wai k0 ba da ke nake ba ne Saude kina ji ina ta faman
kiran ki?”
Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta
goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi
Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, “’Yar iska duk uban
me kike ina kiran ki kin yi min shiru?”
Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da
suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki
tana fadin.
“Ke dai kya kai su in kaya ne wuce ki ki dora mini sanwar
tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki
wanke mini su.”
Saude ta yi saurin dagowa ta kalle ta, Laure ta ce,
“Bakallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin
isa.”
Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta
taba yin wanki ba, don kayanta ma kale daya ne, duk wani
wankin gidan Rabi’u ne ke yinsa. To ta inn ma za ta fara?
Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan
ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan
Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama
aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga
mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman
numfarfashi.
Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al’amura sun
karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar
gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu
hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare.
Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar
kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun
girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara
dagulewa take tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum
a wurinta jiya ta fi yau.
Tun tafiyar Rabi’u bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara
samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara
biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan rashinsa
wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta
ta kwanta ta yi barci, qunci da wahalhalun rayuwa sun yi
mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin
rayuwar da take ciki.
Musamman abubuwan da ‘Yar Baba ke mata ya na
damunta, ko'dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a
lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma ‘Yar Baba na
da shekara sha biyar, amma tafi Saude garin jiki, saboda ita
irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan
gaBoBin nan.
Don ita Saude ‘yar siririya ce sosai, kamar a hure ta 'ta fadi,
sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa ‘Yar Baba gajeriya ce
mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da wadatar na
shanu, ba laifi 'ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci
da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware
ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya.
‘Yar Baba har tafi mahaifiyarta wurin‘rashin mutunci da
rashin tausayi ga gadara da ' rashin kunya da tsinannan
surutu, kamar aku, ga shi' Inna Laure da Malam Bala sun
dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka
samu yana kanta.
Shi yasa ‘Yar Baba ta tashi da kwalliya ‘yar gayu ce sosai,
suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na
fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma
idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau.
Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana
gab kawowa kofar gidansu ta hango wata qaramar mota
Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a
lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da
wasu ‘yan uwa masu 'mashin' ma balle mota
Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon
motar, ta zo daf da ita ne ta ga an bude an fito. ‘Yar Baba
ce da wani saurayi suka fito daga
gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan
ledojin nan na shopping.
Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke
Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side ga su
daban-daban, wato wari da wari, wani ya fi wani. Hakan
yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya
takalman duk sun sha faci da Leda.
Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu
tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin
na fadar, ‘Wannan kuma wace ce?”
‘Yar Baba tabe fuska kafin ta ce “’Yar talla ce gidanmu take
tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?”
Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce “A’a, haka kawai amma
dai gaskiya kazama ce, wallahi bakijiba data wuceni
harzuciyata saida ta tashi. "
Daidai nan Saude ta shige cikin gidan tana jin zuciyarta na
mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin
tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta sannan ta dauki
abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne
ke bi yabe
yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna
ta soma cin dumaman tuwon.
‘Yar Baba ta shigo niki~niki da ledoji Inna Laure da ke
zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar.
“Oyoyo! Ga ‘yata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka
farauto mana
‘Yar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye
ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin mayafinta mai
kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna,
gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo
waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta
k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take.
Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala-
kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace,
daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na
manyan mata.
Bakin Laure ya Ki rufuwa‘ta dubi ,‘Yar Baba taha fadar,
“Wannan kuma ina ki ka same shi ‘Yar Baba, dan wane ne a
garin nan?”
‘Yar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace,
“Wallahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi
na dawo daga makaranta.”
Laure ta rafka guda kafin ta ce, “Da kyau ‘yata tauraruwa
cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki
dan anan dai haihuwa ta yi rana, Ki dai tsaya ki nutsu ki
dage ki shake mana wuyan duk wanda ki
Kikeso in ja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa
daurin huhun goro
‘Yar Baba ta sa dariya tana fadar, “Kai shi yasa nake son ki
Laure.” ‘
Ta mike tsaye tana fadar, “Hmm! Gaskiya wani abu na ci
min tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar
mini da aji a gaban samarina.”
Laure ta zaro ido “Wace yarinyar?”
‘Yar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, ‘Yo wace ce in ban
da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta
wallahi da ta wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya
nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali
ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar
matalauta.”
Laure ta ce, “Ai waccan mai kama da igiyar shanyar ni
kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni
za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.”
‘Yar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune
kamar mai rawar taBa-kaka.
Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu
sunada bakinda ’zasu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa
sanin kayanta a duniya kala uku ne sumana Laure ne data
gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai
da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun
wanka k0
na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta
siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi
wanki tadiba aciki tayi wanka.
Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man
shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata
shekaru uku kenan da suka wuce da ‘yan kwanaki. Ta
mayar da ‘yar kwallar da ta ciko mata ido ta ci gaba da cin
tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata
tsaye a qahon zuciya.
Da rana Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa
bokitin alalarta a gaba tana kallon jama’a na ta kai wa da
kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take
yana faman tsangala kafa da shanyayyan hannunsa guda
can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda
ya shanye
Saude ta Kara hade fuska dan a duniya idan akwai wanda
ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijo dan a
Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani
qarami. Yaro
Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana
' faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta
daukc kanta ta ci gaba da kallon wani waje. Garba
ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. “sannu
da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?” Saude ta jiyo muryar
nan kamar an kunna injin
markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana
Lol i relly feel unhappy for rabiu
[1/17, 7:54 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/19, 5:11 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
*CHAPTER 12*
kallon shi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk ya yi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a