Showing 96001 words to 99000 words out of 102653 words
Chapter 33 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt
watsa mata babu komai a cikinsa bayan
tsagwaron tsana da ‘ qiyayya, Saudat ta taho
dakin tare da murda Kofar falon
maigidan ta shiga da sallamarta. ~
Yana kwance saman gado daga shi sai short ‘
niker riga a jikinsa, ya dora ipad saman ’ kirjinsa
yana lallatsawa, yana ganinta ya ture ipad din
tare da miqewa tsaye ya rifito ta yana fadar, “Kun
hade da Asmako? Allah yasadai bata miki irin
haukan nataba?” ~
Saudat ta girgiza masa kai cikin sanyin jikinta.
Ya shafi fuskarta yana fadar, “Allah har gabana
ya
fadi". ‘ Ya zaunar da ita saman gadon shi kuma
ya zauna a Kasa yana fadar, “Jiya na dawo na
sameki
kina ta bacci, kin yi adalci kenan mijinki yana kan
'hanya amma har ki iya runtsawa ba tare: da kin
kira ni kin ji ko na isa lafiya ba? Kai Saudat anya
kin damu dani kuwa?”
Saudat ta langwabe kai tana fadar, “Allah fa na
kira ka ta Ki shiga
Ya kada kafada tare da fadar “Allah ya sa da
gaske ki ke”.
Ta dan yi murmushi tare da fadar “Ni na zata fa
zanzo in sameka kana shirin tafiya
ne
Ya girgiza mata kai, “Jirgin Karfe hudu ai zan bi
na yamma, k0 kayan ma da zan yi tafiyar dasu
ban hada ba”
Ya langwaBe kai, “Allah ji nake tun yanzu harna.
fara missing dinki my baby bacin karatunki da ba
abin da zai hana na tafi tare da ke”; ‘
Saudat ta lumshe ido ta bude saboda yadda
maganar tasa ta yi mata dadi, ta mike tana fadar,
“Bari na hada maka kayan” Ya ce “Yauwa tawan,
da kuwa kin kyauta” Saudat ta nufl bedroom
dinsa inda ta samu duk ya wargaje shi komai ya
yi watsawatsa Ta girgiza kai cike da takaicin
yadda har ya iya rikita dakin baccin nasa haka.
Ta kada kai, ta soma gyara masa tare da mayar
da komai a muhallinsa, ta cire bedsheet dinsa
ta canza masa sabo, ta gyara dakin ya dawo
yadda ya kamata, ta dauko boner ta zuba turaren
wuta ta jona a
dakin. Nan da nan ya soma. fitar da wani
sanyayyen kamshi *
Ta nufa wurin ma adanar kayansa da takalma
‘ (walk and closed) budadde mai girman gaske,
an jera komai a indayadace, Saudat batayi
mamakin ' yawan kayan nasa ba k0 daga yadda
ta lura bata taba ganin ya maimaita kaya ba. Ta
dauki wani jakar kaya ’ trolley bag ta zuge ta ta
soma shirya masa kayan a ciki komai set ta kce
hadamasa‘ don ta fahinci maigidan nata ya yarda
da tomarch.
Asma kuwa da kyar ta iya kai kanta bangarenta
saboda bacin rai da zafin kishi, kuka ta ke sosai,
tabbas Ahmad ya wulaqantata, ya qaskantar da
ita, wai yau ita ce ya hada kishi da ‘yar aikinta,
‘yar * matsiyata, yarinyar da ta ke gani daKiKiya,
mara ~ ilimi, kuma ‘YAR TALLA! 'Tabbas Ahmad
ba qaramin wulakantata ya yiba a idon duniya,
wai a ce kamarta mijinta ya auro ‘yar aikinta,
wannan wane irin cin fuska ne?
Ta suri makullin motanta ta fice dAga gidan tana
faman shar barkwalla tamkar za ta tashi sama
haka 'ta ke tuqin don haka cikin Kankanin lokaci
ta iso
‘Ministcr’ Quarters, maigadi na bude mata qaton
gate
. din gidan ta kutsa motarta, bata tsaya gyara
fakin ba _ ta tsaida motar ta flce a guje ta nufi
cikin gidan
Hajiya Zakiya ita ce mahaifiyar Asma, ita ke
nan tilo Allah ya basu mahaifinta kuma bai yi ’
shekara da rasuwa ba. sakamakon hadarin jirgin
da ya, _ rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa
qasar Uganda bayan shekara biyu da ‘yan
watanni da auren Asma Allah ya yi masa rasuwa.
Asma ta shigo falon mahaifiyar tata wadda ke
tsaye a gaban dinning table tana jera kulolin
abincin rana ita da ‘yar aikinta, Asma ta fada jikin
Umman tata ta rungume ta tana kuka mai daga
hankali.
Hankalin Hajiya Za'kiya ya yi matukar tashi, ta
ruKo ta tana fadar, “Ke Asma lafiyarki? Me ya
faru ne? Yau na shiga uku ni Zakiya
Ta bambare ta daga jikinta tareda janta cikin
falon ta zaunar da ita kan kujera, ta dauko ruwan
tambulan mai sanyi ta mikamata, "‘Karbi ki sha
don Allah zuciyarki ta yi sanyi’
Ta karBi ruwan ta soma sha, Hajiya Zakiya ta
juya kan mai aikinta a fusace 'tana ‘fadar, “To ke
kuma uban me ki ke jira ki ka yi mana tsaye a
ka?”
‘Yar dattijuwar ta rusuna, “ yi hakuri Hajiya”.
Sannan ta juya ta yi gaba jiki na rawa. Hajiya
Zakiya ta raka ta da harara kafin ta maida
kallonta a kan ‘yar tata ‘wadda ta kurbi ruwan ta
hadiye da kyar tamkar ta kurbi madaci‘ _
Hajiya Zakiya ta dafo tana, Fadar me ya
farune?” Asma ta sa bayan hannu tana goge
hawayenta
_‘ Cikin ‘muryar kuka ta soma fadar, .
umma wlh zuciyata tarwatsewa zatayi bazan iya
a gidan Ahmad ba, baqin ciki kashe ni zai yi ldan
:naci gaba
‘ da zama a gidansa, Umma 'Ahmad ya
wulakanta ni,
ya tozarta ni na rantse da Allah na hakura da
aurensa, ba -. dan bazan iya zaman Kaskanci ba.
..”
Kuka ya ci qarfinta tamkar wadda aka aiko wa da
sakon muntuwa. Hajiya Zakiya ta ja tsaki kafin ta
ce “Amma wallahi Asma kina bani kunya, yanzu
ke ba abin kunya bane a zo a iske ki kina kuka a
kan da namiji da, kyanki da yarinyarki da komai
ke k0 ni da make tsohuwa ba zan iya tsayawa
namiji ya ci kashi a kaina ba tare da na nuna
masa bambanci tsakanin ruwa da hawaye ba.
Haba sma Ahmad din banza da zaki zauna yana
wulakata ki a banza tun lokacin da ya bijiro
da‘maganaar zai auri ‘yar aikin gidanki na ba ki
shawara ki .bar masa gidansa inyaso ya biyo ki
da takardarki amma sai kayi kunnen uwar shegu
dani, ke ga ki mai miji, yo namijin banza kayan
amai ma don zuciya ta ki tashi ba za ki barshi
ba? Yo namijin me Allah na tuba? Ke kin san k0
sakinki Ahmad ya yi ba za 'a kwashe kwanaki ba
tare da maza sun soma
’ go slow a kanki ba. Ki duba yadda Allah ya yi
miki "” baiwarkyau, haba Asma sai ka ce ba ki
duba madubi, ga maza nan birjik a gari sai kalar
wanda ya yi miki amma ki maqalewa namiji guda
kamar gam, sai ka
Ce ba Asmar da ke cudanya da maza ba a kan
lamarin
siyasa, haba don Allah don Annabi ki rabu da
yawonan. nan, ya sake ki haka nan k0 dole ne za
ki zauna
namiji yana qaskantar da ke ya bata miki suna a
gari
don kawai ya lura kina sonsa, ba ki iya rabuwa
da shi kamar wadda aka yi wa asiri, haba don
Allah don Annabi Asma ki guntile ,wannan
Kaskantaccen auren naki don ban ga amfaninsa
ba. . .”
Asma ta zame daga rikon da Hajiyartata tayi ‘
mata ta kwasa da gudu ta yi Bangarenta wanda
ta yi rayuwar ‘yan matancinta a cikinsa.
Hajiya Zakiya ta raka ta da idanu cike da takaici
idan akwai abin da ta tsana bai wuce Bacin ran
‘yar tata ba, k0 kadan ta tsani abin da zai Bata
wa ‘yartata, ta ja tsaki ta dauko wayarta a gefen
kujera ta danna wa sirinkinta kira. A lokacin yana
zaune kusa da Saudat suna cin abincin rana, ya
dauko wayar ya rusuna tamkar yana gabanta, ya
soma gaishe ta.
Hajiya Zakiya ta dakatar da shi ta hanyat fadar,
Dakata ba gaisuwarka nake nema ba, ka gane ina
gida ina jiranka ka iske ni da takardar sakin Asma
‘ yanzu-yanzun nan”.
Ba ta saurari abin da zai fada ba ta datse wayar,
ta bar Ahmad riqe da kan wayar.
Saudat ta zuba masa ‘ido ganin yadda ya yi
Kasaqe idonta na kanshi kafin ta ce “LafIya dai
k0?"
Ya yi saurin dawowa cikin nutsuwarsa ya ci
gaba da cin abincin tare da fadar “No.lafiya lau
ba komai"
Ganin yadda ya saki jiki ya ci gaba da cin abincin
shi yasa. Saudat ta saki jiki ta ci gaba da cin _
nata abincin ita ma.
Suna kammalawa bandaki yanufa ya watso ruwa
ya shirya cikin‘ qananan kayansa ya nufi .
Bangaren Saudat ya same ta a kicin ita da
Mansura tana ganinsa ta saki yankan 'alayyahun
da ta ke ta nufe shi, tana fadar, “Ba dai tun
yanzu xaka tafi ba?”
Ya daga mata gira alamar eh, ta langwabe kai, ‘
“Kai don Allah duka yanzu fa qarfe biyu, kaida
kace jirgin karfe hudu za ka bi?” ‘
Ya riko hannunta yana fadar, “Akwai inda nake so
na dan biya shi ya sanya. amman zakimin rakiya
k0?,,
Jikin Saudat ya yi sanyi qalau, ba yadda ta iya
haka ta bi shi suka nufi harabar gidan inda
direbansa ke sa masa jakarsa a mota, sai masu
tsaronsa har uku suna tsaitsaye a bakin'motar.
Ya riko hannunta yana fadar, “To Madam sai na
dawo, ki kula min da kanki, _ akwai kudi na nan
na ajiye miki a bed side drower dinki, daga gobe
za ki fara zuwa makaranta dircba zai rinka kai ki,
don Allah ki maida hankali ban da shiririta, ban
da biye wa tarkacen kawaye kinji?”
Saudat ta daga masa kai alamar eh don‘ta san
tana bude baki kuka ne zai kwace mata, Dr; ya
lakace mata hanci ya fada. mota yana mata
dariyar Karfin hali, don ya lura ta yi matukar
kuluwa, shi kansa ba don ya so zai tafi ya barta
ba, don "a yanzu Saudat ta -'
ida zama wani Bangare na rayuwarsa wanda ba
zai iya rayuwa in ba tare da ita ba Ya soma daga
mata hannu lokacin da direba
ya ja shi.
» Saudat ba ta iya motsawa ba, tana tsaye har
suka fice tajuya ta nufi cikin gidan tana sharar
kwalla
girkinda ba a karasada ita yauba kenan tana
~dakin 'baccinta ta fada kan gadonta ta
qudundune
tamkar mara lafiya. '
' Dr Ahmad bai bar Nigeria ba sai da ya biya ta
gidan su Asma, sai dai abin da Hajiyar ta yi masa
ba qaramin kuntata masa zuciya ya yi ba, tunda
ya durKushe a qasa bai iya dagowa ba, yana
saurarenta ta inda ta ke,shiga ba ta nan ta ke fita
ba. Shi dai bai 'iya tankamata ba har sai da ta
gaji' don kanta ta yi shiru sannan ya soma
magana kansa a qasa.
‘ “A yi haquri don Allah Hajiya, abu ne wanda
Allah ya riga ya qaddara Sai ya faru babu
makawa sai ya faru, amma aurena da Sauclat
wani mukaddari ne na Allah wanda ba mu isa mu
guje masa ba, amma Wallahi ba don ba ni son
Asma ba, duk da komai ya faru badasa hannunta
ba amma ni ban riqe ta da komai ba, aurena wani
mukaddari ne daga Allah, wanda,,,,
‘ “Saurara min haka Malam, ai tun kafin a haife
ka na san wannan guntun wa’azin, tunda da ma
budurwar zuciyarka ta ja ka izuwa ga kisisinar:
‘yar . aikin gidanka har ka aure ta ai dole xakake
fadar komai muqaddari' ne. Sai dai abin da nake
bukata a yanzu
.kawai ka rubuta takardar Asma ka ba ta: amma
aure dakai tagama kodakuwa kaine autan maza
banda rufewar ido k0 meye abin naci a tattare da
kai? Yo a tauna qashi k0 a karya haKori?’ ’
Ahmad ya mike tsaye ba tare da ya saurari
umarnin hakan daga gare taba, ya zura hannu
cikin aljhu ya zaro bandir din‘ yan dubu-dubu har
guda ‘ biyar, wato na naira dubu dari biyar kamar
yadda ya ba wa Saudat ya ajiye a kan kafet yana
fadar, “Ga wannan a ba ta Hajiya ta ‘yi maneji
kafin na dawo, amma ni bazan saki matata ba
tunda’ har yanzu ina sonta”. Bai tsaya sauraren
abin da zatacevaya fice abinsa ya barta tana
faman kumfar baki
,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,, ,,,,,,,
Al’ amarin rayuwa ke nan, a kWana a tsahi
babu wuya wurin Allah, Saudat ta kwashe “Sati
hud'u
tana. zuwa makarantar boko da islamiyya, cikm
ikon
Allah kuma duk abin da aka koya mata saita
dauke
shi kasancewarta mai budaddiyar Kwakwakwa
don hatta
tukin motar da ta ke zuwa koyo cikin sati guda
’ta
' kware don haka a sati na uku ta fara hawa titi
ita * daya, yanzu haka ita ke tuka kanta ta je
makaranta ta
, dawo gida
Saudat ta Kara gogewa tai
‘ wani fresh tamkar ba ‘YAR TALLA ba fatar"
jikinta
yayi wani luwai luWai har ‘yar qiba ta yi Wadda
ta
da yanayin jikinta, ga wata wayewa data qara
samu ta musamman. ,
» ‘ A yanzu haka Saudat ta ita rubutun 1Hausa,
Turanci ne dai take dan daddagirawa Hausa kam
ta yi matuqar iya ta, don har karanta littafan
Hausa ta ke na Mambuta dabamdaban, ‘ abin da
ya Kara bude kwakwalwarta da Kara
wayarmata da kai, ta qara samun experience din
yadda za ta kula da kanta da shi kansa maigidan
kenan
Yau asabar ce ta yi daidai da cikar DR Ahmad
sati hudu da tafiya kuma itace ranar isowarsa
cikin ikon Allah, don haka tunda ta tashi daga
islamiyya Karfe sha biyu da rabi ta dan wuce
wurin gyaran jikida kunshida kitso ba ita tabar
wurin ba sai qarfe hudu na yamma, don haka
tana dawowa‘ gidan kicin ta nufa don hada abin
da zata. ma maigidan kamar yaddata sanarda
Mansura tana son girkamasa dambun shinkafa
tareda pizza
da kuma alkubus cake, potatoes chicken
sai lemun‘karas tareda Creamy mango. Duk
wannan zaBi nena Saudat don a yanZu
itake bada umarnin komaima kondan Ayanzu.
takwarene don har littafan girkin tana
. Za ki dauko Barzazziyar shinkafarki ki bakace
ta, ki cire garin sai ki zuba wa ‘shinkafar ruwa ki
tsiyaye ruwan ki sa hannu ki matse, don ‘yan
ruwan da suka yi saura su tsiyaye tsaf. Sannan
ki zuba ' Barjinki a madambaci ki rufe ki batta ta
turaru minti" goma zuwa sha biyar, sai ki sauke
ki zuba a mara mai dan fadi ki barbaje shi sosai.
*
Sai ki kawo mangyad'a mai dan yawa ki zuba
ki jajjaga attarugu ki zuba ki yanka albasa
qanana, ki
Sai .ki kawo dafaffiyar hantarki wadda kika .‘
yanka gutsin~gutsin ki zuba kisa garin kurkur
cokali " guda sai kisa magi da gishiri da curry
tare da thyme dadan garin citta da tafarnuwa sai
ki juya sosai . sannan ki maida a madambaci ki
rufe ki barsu su
turaru minti goma zuwa sha biyar, sai ki sauke.
Ki zuba a farantin maigida ki kawo dafaffen
kwanki ki
Bare, ki ‘masa yankan fadi, sai ki jejjera a saman
abincin. Ni ma haka na ga Saudat din ta yi, sai
na ga ta sa wani faranti ta rufe Sannan na ga ta
dauko kwano mai fadi ta kalli Mansura. ' ’ “Yanzu
kuma zan hada Pizza”. Ga yadda na ga ta yi.
PIZZA
lol
Saudat na idarwa ta fice daga kicin din ta nufi
babgarenta don magruba ta kawo jiki, don haka
tana shiga ruwa ta watso .wa jikinta ta dauro
alwala ta gabatar da salla, sannan ta nuifi gaban
madubi ta ja stool ta zauna, kwalliya sosai ta yi
irin wadda ba ta san ta iya ta ba, ta mike ta nufi
kan gadonta ta dauki sabuwar atamfarta cikin
wadanda ta kai wa ‘yar islamiyyarsu ta dinko
mata.
Tana cikin fesa turaren cool water ta ji wayarta
ta soma rurin neman agaji, ta yi sauri ta nufi kan
bed side drawer dinta ta dauki wayar, ganin
sunan da ya fltO a kan madubin baro-Bare ya sa
ta yi saurin shafar kore da dan' yatsanta, sannan
ta kara wayar a kunnenta cikin tsananin doki ta
ce, “Yallabai
‘ har kun iso?”
Daga can ta ji ya karya murya yana fadar.“Wayyo
tamyau, don Allah ki gafarce ni, na iso, amma
ba zan samu isowa ba yau, za mu yi meeting a
majalissa” '
Ai Saudat ba ta san lokacin da ta datse kiran .
ba, saboda takaici ta wullar da wayar a kan gado
cike da Bacin rai, don ganinta idan ya yi mata
haka bai mata adalci ba. Ta ja tsaki tare da
mikewa da niyyar ta cire kayanta, ta ji an turo
kofa tare da sallama.
Ai bata san lokacin da ta wuntsira ta nufe shi ba,
shi kuwa ya bude hannayensa ta fada cikin
jikinsa.
“Madam kin yi kyau, kin Kara girma, wallahi
kamar musanya min ke aka yi”.
Ta sa dariyar farin ciki, “Mu je YallaBai ka ci
abincin da na shirya maka sai ka yi wanka ka
huta”.
Bai musa mata ba ya miketa riko hannunsa
tamkar wani qaramin yaro ,suka fice, har dinning
area, ta ja mass. kujera ya zauna sannan ita ma
ta zauna. Duk abin da ta girka sai da ta zuba ta
tura masa, babu abin da bai ci ya yi santiba
Wayarsa dake kan tebur ta soma‘ruri ya mika
hannu ya dauka, ganin sunan Momy ya sa shi
saurin dauka ya kara a kunne, “Hello Momy ina
wuni, eh ga
ta ma”.
Ya kara wa Saudat wayar a kunne, muryar Momy
dinta ce ta ji tana fadar, “Hello Saudat,
albishirinki? Yau na ga yayanki Rabi u, an ganshi
yanzu haka yana zaune a falona“
Ai Saudat ba ta san lokacin da ta fasa wata uwar
Kara ba, ta saki wayar cikin tsabar kaduwa ta
soma fadar, “YallaBai an ga Yaya Rabi’u, wayyo
Allah na bari in dauko mayafina mu tafi
Dr. ya waro ido, “Muje ina Saudat? Ba ki san k0
Karfe nawa ba ne yanzu? Takwas saura fa".
Saudat ta marairaice masa, “Don Allah ka zo mu
je, wallahi ba zan iya runtsawa ba yau in ban
ganshi ba, k0 ka sa direba don Allah ya kai ni”.
Dr. ya dan yi kasaKe yana kallonta, yadda duk ta
firgice lokaci guda a take kuma sai ya ji
tausayinta ya kama shi, tabbas ta yi kewar yayan
nata, za ta iya ma shiga kowane irin hali. Ya
sauke kansa daga kallonta ya mike ya suri
wayoyinsa da ke kan teburin, ya ce, “Dauko
mayafinki kizo muje”.
Sai kuma tausayinsa ya kama ta, k0 awa 'daya
bai yi da dawowa daga wata tafiyar ba, sai dai ba
yadda za ta yi, tana son ganin yayan nata a
yanzu fiye da komai. Ta juya ta dauko mayafinta
kalar atamfar ta dauko wayarta da jakar takalman
kafarta ta tattara kudaden da Dr. ya ba ta wanda
ko dubu hamsin ba ta taBa a cikinsu ba ta zuba a
jakar, sannan ta fito. Yana nan tsaye inda ta bar
shi yana jiranta. Yana ganin ta flto ya yi gaba ta
biyo shi a baya, sabuwar motarsa ya shiga. ‘
Saudat ta dube shi, “Ba direba zai kai mu ba
Yallabai?”
Ya ce, “A’a mu je kawai na tuqa mu, zamu fi
sauri”, , ' Ba ta sake tankawa ba ta zagaya
kujerar da ke gcfen direba ta bude ta zauna, ta
samu ya kwantar mata da kujera, don haka ta
kwanta sosai, shi kuma ya yi wa motar key suka
fice daga gidan suka hau hanyar Katsina, inda
suke sauraren karatun alkur’ani mai girm wanda
Dr. ya kunna musu a motar, hakan yasa kowane
ya nutsu yana saurare sai ‘yar maganar da ba a
rasa ba. Ba karamin gudu ne Dr. Ahmad , yake
sharawa ba a kan titi, don Karfe goma da minti
talatin ta yi musu a cikin Katsina a gidan su
Saudat.
Tun kafin ya ida tsayawa Saudat ta Balle murfin
Kofar ta fito a guje, ta nufi cikin gidan tana
Kwalla wa Yaya Rabi’u kira. Tana shigowa ' falon
tana wurwurga idanu, can hango shi cikin
doguwar kujera yana shan fan-milk, Saudat ta
fasa wata uwar Kara ta kwatsa a guje ta fada
jikinsa ta
kankume shi tana ihun dariya. , * Shi kansa
dariyar yake yana ambaton sunanta ‘ tare da
Kokarin dago ta don ganin yadda ta koma amma
taKi sakinsa, su Nabil da Nabila ma ‘suka rufa
mata baya suka rungume ta suna murnar ganinta.
’ . Momy dai dariya kawai ta ke musu zuciyarta
dauke da matuqar farin ciki da shaukin ganin
sanyin idaniyar nata 'Dr ya yi sallama ya shigo
falon rike da jakar Saudat da wayarta ya durkusa
agaban Momy yana
gaishe ta cike da girmamawa, Saudat ta zame
daga jikin yayan nata tana kallonsa, kuka ta ke
sosai shi kansa sai da kwallar ta zubo masa cikin
karfin hali ya soma share mata hawayen yana
fadar, “Ya isa haka Saudat, ba kuka za mu yiba,
sai mu gode