Showing 33001 words to 36000 words out of 102653 words

Chapter 12 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt

18 Dec 2024

5925

kafin ya ce,
“Waye kika ajiye ya yi serving din. "
Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai
ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, “Na ce
waye zai zuzzuba abincin?”
. Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, “Yanzu zan zuba.”
Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan
ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa.
Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da
takaici ya ce, “Yanzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin
tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali
mts!’ Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din,
sannan ya soma sha.
Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba
masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta‘ ce,
“Abincin kamar yaya za a zuba?”
Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka
mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki
plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da
miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da
kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa,
wato~ papper chicking, sai
gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora
saman plate, wato sandwich.
Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba
masa farfesun naman a plate din sai ta debi
yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman
ta rufe.
“Bai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali
har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka
tilastawa sai ya kalle ta ya ce, “Tashi kawo mini morning
fresh
‘Yan hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani
abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a
dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? ‘
Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan
ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya
tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to
k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan
qashi a kasa. ‘
Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko
‘yar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi,
ta durkusa tare da fadar, “Ga ta.”
Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani
mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu
ya ja tsaki mts! Yana fadar. ‘
“Ke jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba
ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta
shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?”
Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, “Kai Allah dai ya
wadaran dakikin mutum stuppid girl ni
Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.”
Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka ciko da
hawaye muryarta na rawa tace, “Ka yi hakuri don Allah. ”
Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki
“Mts!” ‘
Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta
cikeda tsanarta ya ce, “Ki fadawa Madam, ina da meeting
yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa
gobe komai kr nan mu hadu ta network.”
Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a
tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo
kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji
ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka
cire ni daga' wannan rayuwar qangin“ bautar da rashin
galihu.’ A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya,
sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta
share ’hawayenta.
Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa
yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda
yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike
ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar
ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko’ina ta yi
turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC

a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can
Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren
wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da.
kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a
sanyaye ta ce “YallaBa‘i ya ce“A fadawa Madam ba zai
dawo ba sai gobe
Aunty ta ce, “To ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.”
Saude ta dan yi jim cike da tsoro.
Aunty ta katse mata tunanin da fadar, “Kije mana Saudat
tunanin me ki keyi haka?”
Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan
ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na
farko kenan da ta fara hawa saman. ‘ Haka kawai ta tsinci
gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya
dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai
ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni’imar da Ubangiji
ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama‘
har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo
hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara
matsawa tare da yin wata sallamar.
Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata
dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi
tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa
tantance ta, ta ji saukar
wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu.
Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta
ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, “You
are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo
ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi
ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?”
Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take,
hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta
ce “Ki yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi
tafiya sai zuwa gobe da yamma za..
‘So What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni
duk inda nake ki fada mini, iye?’ Ta ja wani dogon tsaki mts!
Kafin ta ce, “Da alla gate out on my parlour’ Ta sake kwatsa
mata tsawa, “I say
gate out k0 ba kya jine?” saude ta zabura ta mike ta bi
hanyar da take nuna
mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana
fadar, ‘Stupld kawai.’ Sannan
ta juya ta koma ciki abin ta.
Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada
kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo
Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta
samu kanta a ciki me cike da qaskanci
da wulaqanci ni Saude? Kuka take ‘sosai bata da mai
lallashinta. Rayuwa kenan.
,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,,
Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da
rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da
bambanci, ’sauqin‘ ta ma tun a gida ta riga ta saba da
wahala.
Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara
falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya,
wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. ‘
Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan
wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin
‘yan kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun
masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan
kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce
abinsa yana fadar.
“Ki biyo ni da robar ruwa mai sanyi.”
Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye
lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda
tare da kofi guda daya tabi bayansa
A qaton filin wasan‘ dake gefen lambun gidanta“ same shi
yana ta faman tika kwallo shi daya, duk
ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta
hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _
raya mata wasu abubuwa da dama cike tàke da mamakin
Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi
masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum
ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum
irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa
na fadar.
“Wai ke k0 kurma ce ne?’
Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta
durkusa‘ gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, “Ga ni.”
Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, “Hankalin ki yana ina
ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki
ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali?
Tunanin me ki ke’?” ‘
' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif‘ta ta ya‘wuce yana
sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da
tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta
dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba.
Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake
gaban na’urar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa,
Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, “Don
Allah don Annabi
YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba
zan Kara ba.”
nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya
dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi
mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba
abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike
da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan.
‘ Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala
ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko’ina
sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen
falukan da kujerun‘
Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran
wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake.
Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi
biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai
kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa
ba yabo ba fallasa yace “Kije ki sanar da kuku yau ina da
baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk
abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba
ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba.
Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da
sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a
falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe
ta zauna.
Ya‘yi wayarsa ya gama sannan ya matso inda
~ take ya‘ mika mata wani key yana fadar, “Karbi
wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan
sauke bakin nawa.”
Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita
kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun
ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne
in ba wanda ya saba ba.
’don ko wancan karan da za ta shigo falon nasa ’anty ce ta“
bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin
* .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta
~samu ta bude kofar sannan ta shiga.
Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji
kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani
dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka «san odar
waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye
gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba
wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta
goge ko’ina da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba
dayansu “tayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala
sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da
turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin.
gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya
falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni’ima. .
” Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi
saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, “Sannu da fitowa
YallaBai an kammala.” Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana
bin falon da
kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya
burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa,
tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba
sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum.
Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi
gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba.
Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito
yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa.
Ba tare da ya qaraso inda take ba ya ja. ya tsaya
hannayensa zube cikin aljihu, cikin sanyayyar muryarsa ya
ce, “Akwai katon din lemma da , robobin ruwa da aka kawo
suna cikin‘ kanta, za mu shiga meeting karfe sha daya, kin
ga yanzu Saura minti goma ina so sha daya da rabi ki
dauko lemu da ,ruwa kizo ki jajjera a gaban kowacce
kujera, lemo daya robar ruwa guda. Akwai meat pie an
nadeshi guda biyu cikin tissue sai ki ajiyewa kowacce kujera
guda'a gaban teburinta. Ina fatan kin gane?”
‘ Saude. Ta daga masa kai alamar eh ya ce “Okey, kuma
idan za ki shiga ban da surutu, ban ce ki yi wa kowa
magana ba da akwai kayan da zaki karba ki canza.’ Oya
ban san wasting din time je ki.” ‘ ‘ Saude ta lallaBa ta mike
ta fice abin ta tana jinjina girman wadannan bakin a
wurinsa.
Tana shiga'Aunty ta miko mata leda ta karba ta nufi ciki, ta
watso ruwa ta flto. A tsaitsaye ta shirya duk da yanzu ta
dan nutsu ta shafa hoda da dan mai
‘a labbanta, ta sawa idanuwanta kwalli, tunda ta lura bakin
kunya ne za a yi, ta zazzage kayan daga ledar Suit ne irin
na jikinta, amma na yanzu wando ne da siket ba, kuma
bakake neba sai rigar.cikin ce mai kalar jini,‘ harda belt irin
ta mata. Mamaki ya. kama Saude shin k0 sun manta ita
diyar Musulmai ce ba arniya ba?
Taja ta zauna gefen gadon tana mamakin yanda za ta ratsa
mutanen nan da wadannan kayan, ta dafe kai tana jin
tamkar ta zabga da gudu. Bugun agogon dakin yasa ta yi
saurin dago kai qarfe sha daya daidai ta buga, Saude ta yi
saurin miqewa ta saka kayan wanda suka zauna mata a jiki
cif da cif tamkar
dama an auna ta, ta saka bakin takalmin kayan sawuciki
bakake marasa tudu
Ta janyo karamar himarta ta saka, wadda take ganin ta yi
mata qankanta nesa ba kusa ba,
bayan da ta Karasa ta fice da hanzarinta, tana faman rawar
jiki, sai kace angon kare
Karfe sha daya da rabi daidai ta dauki katon din lemo guda
da katan din faro tan nufi falon taron wanda take jiyo sautin
magana sama-sama a yi da
Hausa a yi da Turanci.
Saude na shiga ta ji tamkar ta zabga da gudu, saboda
yanda ta ga mutane sun kai ashirin Turawa bakar fata, shi
kuwa uban gayyar yana zaune a kujerar da ke tsakiyarsu,
da abun magana a gefen teburinsa, tsoro ya kama ta abin
ka da bagidajen mutum ta samu ta yi ta maza, ta shiga
zabga sallama, babu wanda ya amsa a cikinsu, mamaki ya
kama ta to su kuma wadannan wane irin mutanene da ba su
amsa sallama? Ta sa kai ta shiga tana faman muzurai
kamar wata marar gaskiya. ‘
Ta durkusa “Ina kwananku?" Babu wanda ya . kalli inda take
ma balle ya san abin da‘ take hankalinsu na kan jawabin
Dr., wani irin abu ya yi wa Saude tsaye a Kahon zuciya, don
ita a ganinta su ma sun yi niyar ci mata fuska ne. Don haka
ta shiga jera ruwa da lemon kamar yanda ya fada mata, ta
koma ta Kara dauko wasu sannan ta qarasa jerawa ta
koma ta dauko meat pie din su ma ta jejjera. Tana gamawa
ta tsaya gaban Dr. wanda ke dan rubuce‘ rubuce a saman
wani Karamin littafl, sannan ta dan rissina.
YallaBai a kawo maka abincin ka nan ko sai ka
fito zakaci Wani irin kunya da haushi da takaici suka taruma
Dr Ahmad ya ji tamkar qasa ta tsage ya shiga ciki. Jin ya
yi. shiru yasa Saude tunanin k0 bai ji bane ta sake
maimaitawa. “Yallabai nan za a kawo ma abincin ko,,,,,,,,
Tunkafin ta karasa rufe baki Dr. Ahmad ya rufe matashi
da’wani zazzafan marin daya rudarda ita, ya nuna mata
hanya.
‘get out stupid girl Bace' min da gani bagidajiya kawai.”
Saude ta dafe kunci cike da kaduwa ta juya simisimi ta fice
Tana fitowa daga falon tamkar wadda aka zungura ta fashe
da kuka mai ban tausayi, ta kifa kanta akan kujera tana
kukan ta babu mai lallashinta, ita kanta bata san tsawon
lokacin da ta dauka ba sai dai ta jiyo motsin mutane alamar
za a tito.
Ta zabura ta boye: bayan kujera tana jin su sàida suka
gama fita gaba daya, sannan ta fito cike da tsoro. Kai da _
ganinta kasan tana‘cikin tashin hankali dan bata san irin
hukuncin da zai yanke mata ba yau, duk da bata ga
laifinda‘tayi’masa ba, ammata lura ya dau zafi da * ita ta
qara fashewa da kuka Ya Allah Ka fidda ni tausayin kanta
ya kama ta.
Ita dai batayi sa,ar zuwa duniya ba tunda tazo batasan
masoyanta ba duk inda ta shiga da.
[1/24, 10:13 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*


*CHAPTER 17*


masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya
taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna
mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so
ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da
take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma
kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta
hadu da Hamid dibta kuIlum addu’arta kenan musamman
idan ta zo kwanciya bacci.
“Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka
Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne
ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi
Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi
hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya
tsaya cak yana kallonta ya ma rasa
me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa
lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa
da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan
abinci a gun «
Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata ‘yar
siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa,
wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar
farar fatar da hutu ya jika, hankalin
Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~
‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana
kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba
Na rantse da Allah ” ya runtse.idanuwansa ba tare da yace
da ita komie ba “ta rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan
abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login