Showing 66001 words to 69000 words out of 102653 words
Chapter 23 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt
Haushi ya kama ni jin ikirarin da Umma ke yi, cikin takaici tunanin yadda za a iya hana ni auren Bala lallai kau ba a isa ba, kin ji fa
.. wauta da sakarci.
Ashe abin da ba mu sani ba Baba yana cab kai tsaye gidan su Bala ya nufa ya yi sa’a ya iske mahaifinsa zaune saman tabarma a qofar gida suka gaisa, Baba ya ce “Da ma jiya na z0 ba ka nan, to da ma ba wata magana bace ' maganar danka ne Bala, nasan ba ka san abin da dake faruwa ba. ,
Bukatata a nan ni dai daya ce, don Allah ka aika a kira makwaftanka guda biyu suzo‘ yanzu ina son mu daura auren Mariya ‘yata da danka Bala ammafa kayi haquri nazomaka da magana haka gagab, akwai abin da na
hango mana ne wanda da ni da kai duka ba zamu ji dadinsa ba, don na san ba kasan danka na zuwa wurin yata ba, kamar yadda ni ma ban > san tana fitowa ‘wurinsa' ba, amma yanzu tunda
Dan na gani da idona to mafi alkhairin abin shine a ' " halasta musu juna tun kafin su aikata abinda bai kamata ba Malam Maimmaki 'ya 'zuba a fuskarshi idanunsa cike da mamaki kafin yace ‘Wallahl tallahi ban san abin da ke farawa, amma don Allah ka yi haquri, ka masa hankalinka mu ‘zo mu yi abin nan a tsanake Bala dai danka ne, kuma Mariya ma yata ce Baba ya ce, “A’a Malam kar mu‘yi haka da kai, ka taimaka min don Allah don Annabi ka kira makwaftanka su zama shaidu in sauke nauyin da ke kaina Malam Maitumaki ya ce, “A‘a ai gaggawa aikin shaidan né, kuma aure dole sauda’ sadaki”.Baba ya ce “Ga Wannan naira dubu biyar ce na biya masa ‘ Malam Mai tumaki Ya bude baki zai yi magana Baba ya tsaida shi da hannu yana fadar, “Don Allah kar ‘ka ce komai ka yi fatan alkhairi kawai": yace To “Allah ya saka da alkhairi Babaya ce:“Amin"
Daga nan aka aika kiran makwabtansu :
' biyu suka hadu da Baba da Kawu Ummaru da mahaifin Bala aka daura mana aura a kan ‘sadaki naira dubu biyar sannan kowa ya watsé. ’
Baba ya dawo gida a lokacin ina daki ina tisa buhun kayana a gaba na rafsa -uban tagumi, na ji an Kwallo min kira, na kwaso da sauri na fito jin murya Baba. ..
Ina zuwa na ganshi tsaye a tsakar gida, tun kafin in Karaso ya ce, “Kama koma ki dauko hijabinki ki fito mu tafi
Na danyi jim ina kalonsa ya dan daga murya, “Na ce kizo mu je k0?”
Na juya da sauri na koma daki na dauko ‘gyalena na fito, Umma ta dube shi tana fadar, “Inazakada ita Malam ?”
Ba tare da ya dube ta ba ya ce, . “Gidanta”' Umma ta ce, “Ban fahince ka ba Malam”.
Ya wai go yana kallonta kafin ya ce “Gidan aurenta zan kai ta an d’aura aurenta ‘ ~ ' yanzu ita da Bala, ga ma sadakinta
'* Ya mika min kudin
~ Dukda tsaurin idona da tashen balagar tauntsayen dake kaina saidanaji gabanaya fadi namika hannu dakyar nakarbi kudinda ya mikomin na saurara abinkamar almara, Umma tahau Sallalalami hardakwallanta tana
fadar
Yau na shiga uku ni Binta, yanzu Malam bintakan maganarkayi kadauramata auren?" ‘ Baba ya watsa mata wani kallo kafin yace,"sokike ingirketa agidan ina kallonta taje ta jajibo mana abin kunya a gari k0 me?” , Umma ta qara rushewa da kuka, ‘Wayyo Allahna shi kenan ta faru ta Kare, kin samu abindakikeso,amma wallahi tallahiki sani bada yawunaba wannan aurenkuma wallahi kar ki sake ko a hanya ki nuna kin taba haduwa da mai kamannina, babu ni habu ke har abada”.
' Baba ya ce,"‘Ka ji zancen banza, ke da
zakiyi mata addu'a kuma saiki hauyimata mugun alkaba’i? ai ke da ita sai dai fatan
alkhairi yanzu tunda kin samu kin rabu da ita lafiya
, . Umma wadda takaici da bakin ciki ke cin zuciyarta ta duqa ta suri Zuwaira ta yi gaba tana fadar “Ai kuma sai dai ka yi da wani ba
dai Binta ba”
Ta yi gaba tana sharar kwallarta. .
Baba ya ce, “Ke taso mu je kinji”.
Ni kuwa na mike cike da farin. ciki da dokin yau na samu abin da nake so. Muna ' ,zuwa qofar gida muka hadu da Yaya Sani ya rako a guje ya ja ya tsaya kamar zai fada Wa Baba yana ta faman haki Baba ya dube shi. ‘
“Kai kuma lafiyarka?”
Yana faman shessheka ya hau fadar, “Wai da gaske Baba an daura wa Mariya aure
,da Bala?" Baba ya ce “Eh an daura mata, wani abu ne?" * Idon da na kura wa Yaya Sani yasa na tabbatar da duk‘wata lakka ta jikinsa ta tsaya da , idonsa ya ciko da kwalla, muryarsa a“ ‘ sanyaye ya ce, “Amma Baba bai kamata a. Bawa Bala auren Mariya ba, don bai biyo ta ‘ hanyar da ta dace ba wurin neman aurenta .
Baba. Mariya yarinya ce mai kwakwalwa da . haZaKa irinta gwamnati ke nema don daukar
dawainiyar karatunsu don taimaka wa yan uwansu mata, musamman a bangaren asibiti Baba Bala bai dace da Mariya ba don bai san muhinmancin karatun boko ba, asalima ba shi da abin gaba daya wuce . Baba ya nisa kafin ya ce, “Nafika sanin haka Sani, amma kada ka manta wacce ka ke
’ son ka yi yaqi don inganta rayuwar tata ba ta
san kana yi ba, ba ta da wannan‘ butin, ra’ayinta daya aure, shin me zai sa mu tauye. mata hakkin? Kana tunanin idan naKi aurar da ita Allah va zai kama ni ba? Wallahi Kin yi mata auren nan Sani sai ya zame min abin ' bibiya a gobe qiyama, shin ka ga laifina don na sauke amanarAllaha a kaina ?‘ "
Yaya Sani ya girgiza kai wanda hakan ya yi daidai da zubar tarin hawayen da suka Cika kwarmin idanuwansa, ya juya ya shige gida ba tare da ya ce min Kala ba, sai a lokacin zuciyata ta dan karye kadan na bi Baba muka ““tafi zarai-zarai daganisai shi, har zuwagidan
"“su Bala Kinji fa wata kai amarya a nan bahu .‘yan rakiya duk da a addinance hakan yana da
kyau.
Muna zuwa gidan su Bala Baba ya yi sallama da Babansa, ya mika masa ni. Mahaifinsa ya ce ai Bala yana ciki bari a kirawo shi yanzu ya dawo daga kasuwa. Ya shiga sai ga shi ya dawo shi da Balan, ya zube
gaban Baba yana faman godiya.
Baba yace, “Ya isa haka Bala, ai ba ni za ka gode mawa ba, ka gode wa Allah kawai, don'Shi Ya‘ ba ka Mariya, don haka ga ta nan amana a wurinka, ka sani idan ka zalunce ta k0 ka ha'ince ta don kana ganin kamar sadaka ce a wurinka sai Allah ya kama ka, ni dai nauyi ne da Allah ya dora min, kuma ba mutane ba kawai hattamala’iku sun shaida na sauke don haka na barku lafiya”.
Bala ya hau godiya shi da mahaifinsa, Baba ya juya ya yi tafiyarsa ya barmu, mahaifin Bala ma ya juyo kanmu ya yi mana nasiha sosai, sannan ya ce ya je ya gyara mana dakinsa mu zauna.
' Haka ya juya ya nufi cikin gidan, na bi Shi a baya ina kallon gidan don ban taBa shigowa ba saboda babu mace a cikin gidan,
mahaifiyar Bala tun yana dan shekara sha' ~biyar ta‘ rasu, kuma mahaifinsa bai Kara aure
‘ba saboda ya. tsufa sosau, girma ya kama shi,‘ ‘ ' don lokacin da aka haifi Bale. ma har ya cire rai . da haihuwar a duniya sai ga shi Allah ya azurta shi‘ da Bala, daga shi kuma bai sake ba ‘ Allah ya yi wa mahaiflyar tasa rasuwa.
‘ Gidan ginin kasa ne, amma bai sha jiki sosai ba, yana dauke da dakuna uku, daya na mahaifin Bala, daya na Balan, daya kuma na ajiye~ajiyensu, sai qaton tsakar gida shareren gaske wanda aka raba biyu ana kiwo a cikinsa, sai qaton iccen bedi a tsakiyar gidan mai malalan kasa don babu sumunti.
' Bala ya tura kyauren dakinsa ya juyo yana min alama da na shiga, kamar kar na shiga har sai da ya sake yi min magana sannan na daure na sa qafa na shiga cikin dakin, ba wani mai girma ba ne sosai, yana dauke da katifar maza wadda aka lullube da bargo sai dan karamin tebur wanda aka dora wata ‘yar qaramar talabijin da bidiyo a sama.
Shi ke nan abin da ke dakin, sai ‘yar hanga ta katako wadda aka sargafe kaya sannan
‘kafet din da ya mamaye dakin, wanda ya ci uwar quta. Kin san abinki da samari bazaki taba tabbatar da tsabtar saurayiba saikinga dakinsa lol
(gayu a. ganku a .titi kar a ganku a masaukinki
Saudat in takaice miki haka na zauna dakin nan na gyara shi tas-tas kamar ba shi ba, washegari Bala ya fita kasuwa ya yi mana siye-siye, tun daga kayan abinci har zuwa na sawa irin wanda za mu bukata. Da kayan shafa wanka, turaren wuta, sabbin labulaye, karamar radiyo, Saudat haka Bala ya dawo da kaya niqi-niki don a lokacin yana samun kudi sosai saboda tun daga Dandagoro har zuwa cikin unguwarmu babu wanda ke saida kayan koli sai shi, don haka yake samun kudi sosai.
Sannu a hankali lokaci ya shiga tafiya
Saudat ina ganin , soyayya, qauna da kulawa fiye da yadda ba ki zato, hatta mahaifinsa idan ya tafi kasuwa ya dawo da kunShin nama na.
A haka harna samu ciki, irin mai masifar laulayin nan kamar ba na kai ba, amma daga gidanmu babu wanda ya leko ya ga ya nake, da Bala ya je ma Yaya Sani wulakanci ya yi masa, don haka ya dawo gida cike da takaici, ya fada wa mahaifinsa shi ne shi kuma ya ba shi shawara da ya je ya dauko diyar
Qanwar mahaifiyarsa Laure wadda aurenta ya mutu ta ke zaune gida: ”
' Bala ya amince saboda jin jikin da ‘ nake, ban iya yi wa kaina komai bane 'haka ya tafi ya dauko min Laure, aka gyara mata dayan dakin ta zauna.
Laure ita ke kula dani, duk wata dawainiya tawa ita ke min, tana gefe tana kallonmu ni da mijina duk abin da nake so shi yakemin inamai ’ tabbatar miki babu abin da' zai hana a kawo‘
shi.
’ Idan kuwa na ce ina son abu jikinsa har rawa yake ya je ya samo min k0 a ina, da ya shigo ya rinka tambayar Laure ya nake, ya jikina da sauqi dai k0? Na ci abinci k0 ban ci ‘ ba? Idantaceban cibaba hakazai zauna yatusa ni agabayana rarrashi kamar zaiyi kuka har ya sai ya samu na ci, haka mahaifinsa idan ya tafi kasuwa siyo min wannan kawo min wannan, ke na ga gata da soyayya.
A haka Saudat ciki ya cika wata biyar na huta da laulayi a lokacin ne kuma naje gida ni
da. Bala, amma Umma k0 kallonmu ba ta yi ba ita da Yaya Sani suka watsar da mu a makar
gida sai Zuwira ce wadda ta fara taflya ta tattako ta maqalqale ni na rungume ta ina jin SOyayyarta a zuciyata donni a wautata” wai gani nake ita kadai ce ke sona, ba ta guje : niba, haka na qaraci zamana na tashi muka dawo “ gida ba mu ma tsaya Baba ya zoba . ‘
Wulakancin da aka yi mana ya yi wa Bala ciwo, haka ya yi ta maimaitawa ni dai Ina jinsa ban tanka ba, don idan da zai tona tawa .zuciyar na san da ya tabbatar tafi tasa hawa da jin zafi, ni a ganina k0 don kyau da sauyawar da na yi yasa Umma bata saurare muba don ta' tabbatar Bala yana sona sutturar kanta dana naje gidan tsadarta ta kau dubu goma a lokacin kuwa dubu goma ba nan ba ce, kayan ' dubu goma sai dai dan wane da wane, amma hakan bai sa Umma ta duba qokarinsa ba ni kaina ta san ai na canza don na yi dumurdumur da ni, haske na ya Kara. fitowa na zama kamar wata. baturiya saboda kyau, ba yadda muka iya dole nena share na manta, sai dai Bala ‘ bai .mance ba don duk lokacin da na ce masa zan' je gida sai ya ce ban 'zuwa ba yadda zan yi . a haka nazo na haihu, babu wanda yazo ta Bangarena
gidanmu, sai dai Babana daya zo har gida ya ga ' jariri ya yi masa addu‘a, ya bani ‘dubu biyu da niki niqin kaya sannan ya tafi, daga shikuwa k0 kare bai ce komai ba. ‘
Sai dai Laure ceke dawainiya da ni ita ke dora min sanwar ruwan zafi safe da yamma ’ta kwashe ta kai min kewaye ta yi wa jariri wanka, ta yi girkin abinci a gaskiya a lokacin ta yi dawainiya kodayake ta saba da wahala tunda a can gidansu wankau ta ke na kudi da surfani.
A kwana a tashi har na yaye Rabi’ u, ban Kara zuwa gida ba, a ganina tunda sun Kini ni ma na manta da ~su kin ji wauta fa, ' haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tamkar bani da ‘ iyaye a garin, saboda Bala ya bar min Laure ita ke min komai na hidimar gidana iyakata ni dai inwanka nida dana mutafi wurin maigida. ~ , Ashe abindaban saniba Laure tana nan tana jin haushinmu kamar ya kashe ta ni k0 sakaran ban taBa sani ba, don ban yi zaton za ta iya jin haushinmu ba, saboda yadda nake ' ‘ kyautata mata ni da maigidana.
. Lokaci na tafiya ban sake haihuwa ba a tsawon shekara bakwai a lokacin ne kuma
mahaifina ya rasu, to a nan ne na dan yi hankali na dauki dana muka tafi gidanmu na zauna a can har sai da aka yi sadakar uku duk yadda Ummana ke shasshare ni sai data tanka min duk da ba wata maganar arziki ba ce muka
yi, anagama sadaka na tattara na koma gidana, to a nan fa labari ya sauya don ban sani ba ashe na bar baya da qura, haka kawai na ga Laure na min wani kallo-kallo, ga shi shi kuma uban gayyar ya hau shasshare ni da na yi masa magana sai ya hau ni da fad'a dana yi laifl da ban yi ba duk daya wai an yi wa tuwo Barin miya.
Abin duniya duk ya dame ni ya ishe ni, ga shi ba ni da wanda zan fada wa matsala ta, a haka dai na yi ta hakuri ga shi a lokacin ban
san na samu cikinki ba, sai da laulayi ya matsa min, amma Bala ko a jikinsa ya watsar da mu ba-ya kula mu ni da dana balle abin da ke cikina.
Rayuwa duk ta dagule min, na zauna na zama wata kalar tausayi, kin san halin da mace ke shiga idan miji ya juya mata baya abin ba dadi, sai dai in qule daki in yi jugum.
Ban“ taBa mantawa da ran Wata laraba ba ina zaune a daki shiru ' Laure bata ,kawo mana abinci ba ga shi k0 abun karyawar ‘ da ta yi mana da safe, ban samu cinsa ba nan na’bar wa Rabi’u ya yi ta wasada shi ’har wurin uku na rana babu abinci babu dalilinsa‘ A dole na takarqare na mike na fice shiga kicin din, sai dai abin da na gani sai da ya so tarwatsa min zuciya, na na tsaya turus ina kallon Laure wadda ta zabga uban goho ta takarkare tana ta faman barbada magani a kwanon miyar Bala, ban tanka mata ba har sai ' da ta gama barbade-barbadenta tas! Ta kawo cokali ta jujjuya miyar ta maida ta rufe, ta mike tana boye maganin a habar zaninta. Muka yi ido hudu, a take jikinta ya hau rawa ‘ tana faman karkarwa can kuma ta ja tsaki ta rabA ta wuce ta barni tsaye da. mamaki a zuciya. ; Can na girgiza kai na dauki kwanon miyar na fito na zubar ’da ita, da ma miyar danyar kubewa ce na dawo na zauna da' kaina na takarkare na sake dora wata miyar' ta
busasshiyar kucewa na yi na gama na debi * nawa na ajiye masa nasa da kyar na samu na ;
tuttura abincin ama zuciyata tamkar za ta tarwatse.
Bayan la’asar Bala ya dawo. daga kasuwa tun kafin in fito kuma ta riga ni fitowa ta tare shi ta shimfida masa tabarma jikinta na rawa ta tafi ta kawo masa abincinsa da ruwan randa masu sanyi cikin kwanon sha.
A lokacin ni kuma na fito na tsaya daga bakin qofa ina kallon ikon Allah, Bala ya ja kwanon miya ke nan ya bude suka yi ido hudu da miyar busassiyar kubewa ya yi sa‘uriin dago kai yana kallon Laure.
“Wannan miyar kuma fa? Ba ni na ba da danyar' kuBewa ba nace a kawo miki ba, k0 ba a kawo ba?”
Laure ta karya kai cike da kisisima kafin tace, “To ai ‘yan ba ni na iya yau :su suka ' dauki miyar suka zubar suka shirya tasu ta musamman”.
Bala ya yi saurin dago kai yana kallona.
, “Ban gane kin zubar da miya ba, kan wane dalili?"
Jikina ya yi matukar yin sanyi ganinyadda ya zaburo min na daure na durqusa ‘ gabansa muryata a sanyaye :nace kayi
Mai gida bari nayi ban sani ba
Shi ya‘ sa na sake maka wata, amma ina neman
wata alfarma a taimaka a maido girkin gidan nan wurina”. .
. Bala ya zaburo, “Ke gafara can rufe min baki, ki dai ce wani mugun halin kika tsiro da shi, kuma wallahi ba zan dauka ba, ba ma zan laminta ba, tsabar almubazarannci kawai ki dauki abinci ki zubar saboda ba ke ke nemowa ba k0?”
Zuciyata ta kara ganin yadda Bala ya hau ya ke ta zuga min masifa haka, idona ya kawo kwalla na mike cikin kuka ina fadar, “Allah ya ba ka hakuri
Na juya na shige dakina na barsu. Ban san abin da suka kitSa ba, da zai fita ya . hankado labulen dakin ya leqo ya wurgo min dari daya, “Ga shi nan sai ki yi cefane a dafa taliya da daddawa, da ma nasan dan sauran na samab kike mawa, to ga shi nan sai ki dauka kiyita zubin adashe". ‘
Ya