Showing 48001 words to 51000 words out of 102653 words
Chapter 17 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt
her did Is my Saudat
' Da sauri ta maida hankalinta kan Saudat, ta sake juyowa tana kallon shi tana fadar, “Are you sure?” '
Ya yi wani takaitaccen murmushi yana fadar, yes am sure my sis.’ "
Ta yi wani tsallen murna ta dafo Saudat tana fadar “Wow my bross wallahi na ji dadi sosai, Saudat ‘ sannu da zuwa mu shigo don Allah.’ ‘ “* Saude dai kallon su kawai take tana dafeda . kafadarta har cikin falon, tsararran gaske wanda ya ji kayan alatu na more rayuwa iri-iri Da kanta ta zaunar da ita tana fadar. ‘Zauna nan my sis, da me dame ki ke so a kawo miki yanzu, tun daga snacks, lemo abinci, fruits, duk komi ki fada don wallahi naji dadin zuwanki my bross na gode fa.” Murmushi kawai ya yi mata, ta Kara jawo Saude a jikinta ‘Na ce don Allah ki saki jikinki munfa riga
Mun zama daya yanzu dan na san nan ba da dadewa ba ' zaki shigo cikinmu haka ne? ”
Saude da ke jin manganun tamkar saukar markade ta yi tamaza ta daga mata kai. Faridat ta ce ‘Gud ai dana sani.’ Ta dubi Dr kai kuma fa yaya me ka keso k0 , ,
duk kun bani zabi? Ya ce a a karki wahalar da kan ki dan yanzu haka gidan Uncle B za muje daga nan za mu wuce gidansu Dad, don haka kl kawo mana lemo kawai
Faridat ta bata fuska ta hau diredire tana fadar, wallahi ban yarda ba Allah
Dr. ya yi wata qasaitacciyar dariya kafin ya cc, ‘Wai ke har yau ba za ki girma ba k0 kin manta ke ki ka aje Affan da Ummy ta?”
Dariya ta yi ta juya ta bi wata hanya cikin falon nata, tana fita Saudat ta yi saurin kallonsa tana shirin yin magana ya yi saurin daga mata hannu alamar ta yi shiru, a dole ta ja bakinta ta tsuke
Gaba daya falon ya dauki shiru sai dai kukan A.C da talabijin din da ke ta faman haukanta ita kadai. Ba tafi minti goma ba sai ga ta ta dawo dauke da wani qaton tire ta ajiye saman tebur, lemukan kwali ne guda hudu sai kofuna masu kyau sai robobin Faro biyu, sai fruits kala-kala sai wani tangaran din da aka zuba dambun mama a ciki, sai daya plate din hadaddan chips din dankalin turawa ne. Farida ta dube su.
“Don Allah kuba ni minti goma zuwa sha biyar k0 dan wani abu ne marar nauyi in girka muku.”
Dr ya ce‘Kin san Allah sauri muke wannan ma is okay. ” Ya tashi ya matso inda Saude take zaune da
muryarshi qasa-qasa yace, ‘Tunanin me ki ke Madam”? Kallonshi kawai ta yi ba ta tanka ba.
Faridat ta yi murmushi tana fadar, ‘Wallahi Yaya '
ka yi zabe: kuma mai kunya, amma Bufullatana ceko?”* Murmushi ya yi tare da fadar, ‘Bana san sa ido fa.’ . Ta yi dariya tana fadar, ‘Ai dan Safwan baya nan ne “ wallahi daka sha tsiya, ya tafi ya dauko su Affan daga makaranta, amma don Allah yaushe za ku dawo don . gaskiya ni dai wannan zuwan ba nawa bane
Dr. yace‘Sai ki tambayi Madam din dan in gobe ta ce in dawo da ita kin san zan iya.”
Farida ta yi. saurin riko hannun Saudat tana fadar, ‘Don Allah don Annabi ki taimaka Anty Saudat ki dawo kin ga dai ni yanzu qanwar ki ce
Yanda ta yi maganar ya tilastawa Saudat yin dariyar da ba ta shirya ba, har da Kyakyatawa a haka Farida ta ja ta jikinta har ta samu ta saki jikinta da ita sosai kamar sun dade da haduwa, kasancewar Farida mai shegen surutu ga barkwancin tsiya da iya bada labari.
Inda suka bambanta da Dr kenan ita tafi shi Magana shi kuma bai da magana sosai; amma kamar su daya kamar an tsaga kara, har wajen tsawon kana ganin su ka ga ‘yan gida ‘daya. .. ~ Da wayo da wayo sai Dr ya yi da gaske sannan suka samu suka bar gidan Farida, ta hadowa Saudat ~ kayayyaki cike da wata qatuwar jaka mai girma Kirkinta ya bawa Saudat mamamki, kwata-kwata ba ruwanta da Jin kai k0 miskilanci irin na Dr
Suna cikin mota sun dau hanya Saude ta dube shi da alamun damuwa karara a fuskana tace
' “Zuciyata na cikin duhu kuma a cike take da
sarkakarkun al’amura masu rikitarwa ina cikin rudani ’ don Allah ka fidda zuciyata cikin duhun da take ciki ka fada min me yasa kai wa ‘yar uwarka Karya a kaina, k0 shi ma hakan duk yana cikin taimakon nawa‘ne?"
Dr. ya yi wani? murmushi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, ‘Kamar kin sani duk yana ciki, kuma daga yau deel din namu zai Kare da fatan kin gane?’ Ba‘ta ce
masa komai ba ta yi shiru zuciyarta na kaiwa da , kawowa
Katon gate ne ta ga sun tinkara katafaren gaske ‘ mai kama da‘ qofar shiga gari.. Saude ta saki hanci da ido tana kallon gate din yayin da shi kuma yake faman horn, masu gadi biyu ne suka bude kofar Sannan suka ‘shiga katafarea gidan ya sauke gilas din motar: yana ; gaisawa da masu gadin sannan ya wuce.
Kai tsaye Katuwar rumfar da aka tanada dan ajiye , motoci ya nufa ya faka motar tsakanin motecin da su kai jerin gwano a cikin rumfar Dr. ya bude motar yana . kallon Saude ya ce,’ ‘Yau ga ki har gidansu YallaBan
ki, da fatan kin yi farin ciki.” . Kallon shi kawai ta yi ta juya ta bude murfin motar ' ta fito, shi ma ya fito yana fadar “A’a ba ki yi farin cikin ba kenan? Lallai yarinya aiko zaki fadawa Momy Ya yi gaba ta bi bayansa
Ma’aikatan gidan da ke ta faman aikace-aikacens
u, , ‘ mai ban ruwa nayi mai aske fulawoyi suna ganinsu .suka nufo su suka zube suna kwasar gaisuwa, ita dai ' Saude ta gaza amsawa duk kunya ma ta ishe ta, yanda suke ta faman kiranta da Hajiya, a zuciyarta ta ce Allah Sarki ai duk mu ne dan ta san da sun san wacc ’ce ita da ba su gaishe ta ba. ' Suna wucewa Dr. ya dube ta ba walwala'a fuskarsa ya ce, ‘Duk wanda ya gaida ke ki rinKa amsawa, don za su dauka wulaqanci gare ki. ’
Ba ta ce masa komai ba ta ga sun nufl wata Katuwar kofa ya tura suka shiga cikin katafaren falon. Ne
Babu kowa a cikin falon sai ‘yan aiki guda biyo suna ta faman goge-goge suna shigowa suka zube suna kwasar gaisuwa, Dr. ya nunawa Saude wurin zama * sannan ya nufl wata kofa, ‘yan aikin kuma suka fice suka bar Saude na ta faman zazzare namujiya a cikin
falon. . Tsawon mintinan da suka kai goma
, sannan ya tito hannun shi sarke dana wata magidanciyar mace dan ba za a kira ta da tsohuwa ba, saboda a qalla shekarunta ba zasu wuce arba’in da _ ‘yan kai ba. Tun kafin su qaraso Saude ta yi saurin‘
saukowa Kasa daga saman kujerar da take sama, matar
ta wage baki har hakoranta suka bayyana wanda aka likawa hakorin Makka, ta ture Dr. wanda ke rabe da . kafadarta ta riqo Saude tana fadar. ‘
“ ‘Kai ni sakar ni ka ji tunda baka gaji'ya sannun ki da zuwa Saudatu zauna nan kinji
Ta zauna tare da ita saman kujera, tana amsa gaisuwar da Saude ke mata cikin sarkewar murya
Momy ta dubi Dr. tana fadar, ‘Kai sai ka cemin amaryar taka Bafullatana ce gaskiya nayi murna saki jikin ki Saudat mu gaisa ki dauke ni tamkar
mahaifiyarki kinji ko?’ Kai kawai ta daga mata
Momy ta yi murmushi cike da jin dadi tana fadar,
' ‘Allah Sarki je ka kira Dad dinka na san yana Bangarensa yana jiran ka Dr ya mike da zumudinsa ya fice.
Yau dai Saude ta ga ikon Allah ta ga inda soyayyar da da mahaifa take yanda suka rinka nan nan da ita tamkar zasu goya ta don Dad din na zuwa Dr cewa ya yi sai an yi siyan baki
* Kamar wasa dattijon yace ‘Au! Kace gaisuwa da neman iri ku ka zo.’
Dr, ya ce, “Eh Dad ba komai
“dad yace To amaryar taka za ta je Saudiyya?"
Dr yace eh
“Za ta Dady ” ~ yace
‘To an biya, mata.” *
Dr ya ce, ‘Ai bai isaba Dad wallahi inafa son ta da yawa
" Dad ya ce, ‘To ka hau sama ka dauko mata makullin
Motar da nayi niyyar yi mata takwuici.” ; musamman sbd ita nasa aka kawo motar daga london jiyannan kuma aka iso da ita maza jeka dauko mata makullin a sama
Lol jama,a asha karatu lfy
[1/28, 12:05 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼♂@lh@ji🙆🏼♂: [1/28, 12:10 PM] I love my mum: *YAR TALL*
*CHAPTER 21*
Dr yayi wani tsallen murna yana fadin kai thank u very much dad ya sumbaceshi kamar wani yaro momy tace “tunda dad dinka kadai ya siyi bakin don sai ta zage ta yi magana har sai mun ce ya isa haka.
Dr. ya ce, ‘Wlh A a Saura ke Momy.”
Dariya suka sa masa Momy ta ce ‘Ai kyauta ta tsakanina da ita ne babu mai ji bare ya gani.”
~ Dad ya ce, ‘Ai kuma bamu yarda da wannan wayon ba mu gani a qasa.”
Momy ta ce, ‘Ai tsakanin ‘ya da uwa babu mai shiga don ni yanzu na bar maka wannan da baya girma yau na dawo nan. "
Dad ya ce ‘Ba komai ai dama tare muke koya kaya kace my son?“ Dr. ya ce ‘Ai k0 dai Dad fada mata mu dai mu
gani a qasa ; Hajiya ta ce, ‘Hummm! Kan ku ake ji "Ta janyo
hannun Saude tana saka mata wani zobe tare da abun hannunsa, sannan ta bude sarkar ta sanya mata da kanta ta cire mayafinta tasa mata yan kunnanyen
Masu shegen kyau. * Dr ya kaure da tafi‘ yana fadar ‘Kai Mamy
gaskiya baki ya siyu." Dad ya ce, ‘Sai ku taso muje mu yi lunch
Gaba daya ba musu duka suka mike hannun momy sarqe dana Saudat, Dad kuwa yana dafe da kafadar Dr suka nuf1 dinning area
A tare suka ci suka sha ana ta barkwanci basu suka bar gidan ba sai bayan sallar Magariba. Zuwa Saudat. gidansu Dr. Ahmad yau ya Kara mata darasi a rayuwa iyayensa sun nuna mata qauna tamkar zasu goya ta abin daya karayar mata da zuciya wanda ya sa ta kuka mai cin zuciya
‘ Dr Ahmad da ke tuqi ya dago ya kalle ta kadan sai a lokacin ya lura da kukan da take ya maida kan shi saman. titi muryarshi a sanyaye ya ce, “Kukan me ki ke kuma?”
Tamkar bazata tankamasaba, saidatayi dakyar ta iya tsayar da kukan nata kafin ta ce, ‘Dole ne inyi kuka Yallabai ta yanda kai , wa iyayenka qarya don kawai ka cimma wata manufa ta ‘ ka, ni dama na sani tun fakro ka tsane ni kana san ka ‘kore ni amma ka rasa hanyar da zaka bi kar Hajiya ta bata ranta, amma ni da ka bi ta ni ba sai kabi ta wannan hanyar ba ta nuna kana sona ba, don hanya ce ta tarwatsa rayuwata wallahi, idan daga nan ka sauke ni ba za ka qara ganina a gidanka ba har abadan ‘ abada" ‘
Ta qarasa maganar tare da qara rushewa da wani sabon kukan ‘
Dr ya taka birki tare da sauka daga saman Iitin ya . koma gefe ya_faka motar ya kunna fitilar dake cikin
Motar ya jirkito yana kallonta gaba daya ya tattara duk _ wata nutsuwarsa a kanta, cikin sanyin muryarsa ya kira Sunanta.
“Saude kenan wallahi tallahi tunda nake ban taba tunanin tarwatsa rayuwarki ba kullum fatana shine in ga rayuwarki ta inganta dubi idanuwana Saudat kalleni don Allah.’ Ya fada. tare da riKo hannunta wanda ya tilasta mata kallon nasa.
Tayi saurin sauke idanuwanta saboda wani irin kwarjinin dayi mata ga alamun damuwa nan bayyane kwayar idanunsa Dr yaci gaba da fadin
“Ki kalle ni sosai Saudat idan har kin san abin da ake nufi da. so to zuciyata na dauke da dumbin soyayyarki da qaunarki', kuma duk abin da ki ka ji ina fada da gaske nake a shirye nake da auren ki a kowane
Yanayi.” Saude ta yi saurin dagowa a razane tana kallon shi,
tsabar rudu da kadauwar da ta yi ya yi bala’in firgitar da ita, a nutse yake kallonta ba tare da ya sake magana ba cak kukan Saude ya tsaya ta soma magana tana kallon tsabar idanuwansa, cike da kaduwa ga muryar har ta soma: disashewa saboda kukan da ta yi cikin sarqakKiyar murya ta soma fadar.
“Dan Allah don Annabi ka rufa mini asiri kar ka Sake furta wannan kalmar wadda za ta. zamo makamin rugujewar rayuwata wallahi ka fi qarfina ta kowace
fuska, kai ba sa an aurena bane karkama klsake fada" don Allah don Annabi."
Dr. ya lumshe idanuwansa ya harde a tsanakke ya soma magana ‘Ba kya sona kenan Saude Juyo ki kalle ni ki fada mini ba kya sona, fadi kawai
Saude ta ji tamkar yana buga lugudan tashin hankali a zuciyarta ta runtse idanuwanta tana jin tamkar zuciyarta za ta yi bindiga.
Dr. ya sassauta murya tamkar mai shirin‘fashewa da kuka ya ce ‘Saudat wallahi ina son ki, so kuma irin na gaskiya wanda babu wasa a cikinsa, kuma wallahi a shirye nake da na fuskanci kowace 'irin jarabawa ce a kanki, ki amince min don Allah inamai tabbar miki ba za ki yi nadamar damqa mini zuciyarki ba. ’
Shi yasa na fara kai ki wurin“ iyayena kafin in furta abin da ke zuciyata,‘ duk da ba su san wace ce ke ba, amma abun zai zo da sauki don gari na wayewa gobe zan mai da ke Katsina idan kuma kin amince na nemi auren ki ’
Cikin kuka Saude ta ce ‘Ta yaya zan mince in je fa rayuwata cikin matsala? Wace ce ni da zan iya kishi da matarka? ‘Yar wace ce ni a qasar nan da zan so miji kamar ka? Yallabai kafi karfina kai ba sa an aurena ba ne wallahi.’
Dr ya ce‘Ni ba wannan na tambayeki ba Saudat ' shi aure sa a da sa a ne? Wa ya fada miki? Ai shi aure cancanta ce kawai, Kuma da ki ke maganar kishi da Asma, wace ce ita, ta isa ta hana abin da Allah ya“
Qaddara. Saude nina ganki kuma nace ina so kuma mutum ko aljan bai isa ya. hana ni sonki ba har sai idan kece kika
ce ba kya sona, kuma insha Allahu na san ba za ki fada
ba, haka ne?”
Ya yi maganar tare da matsar yatsun hannunta wadanda ke cikin hannunsa, Saude ta runtse idonta tana jin wani abu na yi mata kai komo a zuciya. To k0 shi ne son? Ta tambayi kanta.
Dr. ya girgiza ta tare da fadar, ‘Bude idon ki Saudat ki kalli masoyin ki ki furta abin da ke ‘ zuciyarki, shin kina sona za ki aure ni?”
Shiru ya ratsa wurin ta kasa cewa uffan. Dr. cikin sarkewar murya ya ce, ‘Don Allah ki yi magana ki ce wani abu, please Saudat. ”
Kunya da nauyinsa suka dabaibaye ta ta samu ta duke da qyar kafin ta iya magana cikin wata likitacciyar murya ta ce, ‘To ka sake ni in fada.”
‘ Da sauri ya saki hannun nata yana fadar, ‘Na saki fadi."
Saudat ta dan yi jim tana tunanin abin da zai iya Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar muryana ta soma magana.
“Yallabai ni ba sonka ne ba na yi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen da ta same ka ballantana makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ce cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa ko ya yake.’
Cikin farin ciki Dr. ya ce, ‘Haba Saudat ai matukar ina “ciki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai
dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a ‘ zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.’
Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, ‘tasa tafin hannu ta rufe fuskarta, Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasa mota hanya suka cigaba da tafiya
» tare da waninsu ya sake magana ba.
Horn din da ta ji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso Cinna hancin motar cikin gate din gidan ya yi daidai da bugawar zuciyar Sanue dif zuciyar ta ** tsaya da aiki a take.
Ina ga k0 Asma ce za ta fito, Saude ta ji muryar Dr na fada wanda ba ta ma fahimtar me yake fada ba saboda tsabar rudu da kaduwa da take ciki.
Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr ya ji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso.
. Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare da ya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar
“Saukar yaushe My dear.”
,, Turus ya ja ya tsaya saboda k0 kallon shi ba ta yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr ya yi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura ta yi matukar ’ 'firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa a ‘ sanyaye yabi bayan ta
Tana qarasawa gaban motar ta ja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, ‘Bani key da motar." Ta fada cike da gadara.
Dr. ya ja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko’in kula ya ce, ‘Ba zan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?”
Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki ta ce, ‘ba zaka bayar ba ni ka ke fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zan yi mamaki ba tunda ka dauki ‘yar iska kun flta kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole za ka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. .
Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da