Showing 54001 words to 57000 words out of 102653 words

Chapter 19 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt

18 Dec 2024

5927

manyan rumfuna a kakkafe a kofar gidan da ' ‘yan tsirarun mutane a ciki.
Saude ta dafe kirji, ‘Wayyo Allah na k0 dai Baba ne ya rasu?”
Dr ya yi saurin kallon Kofar gidan kafin ya ce
"A a ba mutuwa ba ce, dan ga hunhun goro can a gefe’ « Saude ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce, ‘Ina Jin ko‘ yar Baba aka daurawa aure yau.’ *
" Dr; ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali kafin ya ce, ‘Watakila, ki shiga ki gani sai‘ki min sallama da Baban.
Saude ta amsa da to tare da bude murfin motar ta fice.
Tun kafin ta fito dama hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kan hadaddiyar motar ta Dr wadda ta dauke illahirin hankaiinsu, duk da ba za ka ; iya ganin wanda ke ciki ba saboda bakin gilas din da ‘ke gare ta
Saude na fitowa daga motar kallo ya koma kanta, sai ka ce ba mutum ‘yar uwarsu ba, mutanen dake zazzaune a rumfar ba za su wuce goma ba tun daga nesa ta dan gane mutum uku mahaifinta neda ‘ kuma qannansa guda biyu, sauran kuwa ba ta san k0 su waye ba * .
Saude ta qaraso ta durqusa har kasa ta gaishe ' su, tamkar za su kwanta mata suke amsawa, saboda ’ tsabar girmamawa; amma ban da mahaifinta wanda ya Kara kafe ta da idanuwansa muryarsa a sanyaye yace, “Wace ce wannan kamar Saude?”
Saude ta ce, ‘Ni ce Baba.”
innalillahi ’Yanzu Saude ke ce ki ka koma haka? Ina Dillaliyar da suka tafl _ ; dauko ki dazu?” . Gaban Saude ya fadi cikin sanyin jikinta ta ce, = “Ai kobasu kai ga zuwa ba, Allah yasa dai lafiya?“
Malam Bala ya ce, ‘Yanzu dai tashi ki shiga Ciki u ’ Kawu Isiya ya ce ‘Wai wace Saudan ce ka ke fada ban fa game ba?”
Malam Bala ya ce, ‘Saude dai wadda aka tura a dauko a can Habuja amarya ita.” ‘
Kawu Hamisu ya ce, ‘To wancan mai motar fa da ya kawo ta?”
Ba ta saurari abin da ya ce masu ba ta yi cikin gidan abin ta da sallamarta, mutane ne ke ta kujibakujibarsu an cika tsakar gidan nasu‘makil da mata, an girke manyan tukwane da murahu Sai faman tuKin ' tuwo da sanwar miyé ake, kana gani k0 ba a fada maka ba ka san hidima ake.
Sude ta gaishe su sannan ta wuce dakin Inna Laure wanda shi ma yake ciké da jama’a, duk gungun matan ~ da Saude ta gani kafin ta gaishe su su sun gaishe ta, ana fadar sannu da zuwa Hajiya, ba ta damu ba don a‘ lokacin burinta kawai ta ji hidimar me aka a gidan nasu. ' '
Ta "samu ta kutsa dakin Laure ta gaishe da jama’ar sannah ta wuce har bakin’ gadonta inda take zaune ita ~ da ‘Yar Baba an ‘sha ankon shadda an kashe dauri sai faman zufa ake. ‘
Saude "ta~ qaraso har bakin gadon inda Inna Laure inna laure ce ta fara fadar ‘Sannu da zuwa Hajiya kar dai ince. harda ke aka taho kun ji Saqon bazata haka, sai aka ce muku an daurawa yarinya aure yau din nan.’ .
,Saude ta . durkushe a bakin gadon muryarta a sanyaye ta soma fadar, ‘Bikin wa ake Inna Laure?" ‘ . Gaban Laure ya yi wata masifaffiyar faduwa ’wanda ya ja mata wata muguwar zabura daga ita har ‘ ‘Yar Baban. Inna Laure ta mike tsaye tana gyara daurin zani tana fadar.
“Me nake gani haka me zan gani Saude ke ce ki ka koma tsohuwar karuwa haka? Innalillahi wa’inna ‘ ilaihir raji’nn! Jama’a ku taya ni figa yan uwar kishiya ta zama zakara. Saude mu za ki zubarwa da mutunci a gari mu za ki jawa abun kunya abun fada, wayyo ni . ' Allah naga ta kaina ‘ .Sai ta fashe da kuka ta fadi qasa. Sumammiya jama,a sukayo kanta suna fadin a taimko da ruwa laure tayi dogon suma
‘Yar Baba ta kalli Saude sama da qasa ta
watsar ta ja wani uban tsaki tana fadar, ‘Aikin banza ai
. dai dadin abun da ba a san. asalin balbela ba da sai
ta ce daga Masar take, kuma duk rigar qadangare bai
isa ya zama kada ba a Kadangaren nan dai na shi zai
zauna. .
Idan kina jin dadi ne kin tafi birni kin goge to babu
, abin da gogewar ta ki zata ‘ta Kare domin yau dinnan
za a wuce gidan Garba Gurgu don tuni an daura auren, ‘
ki da shi a safiyar yau kuma wallahi tallahi wani abu
‘ idan ya samu mahaiflyata sai na dauki fansa a kanki
munafuka kawai.’ . ‘ Tunda ‘Yar Baba ta furta daurin auren nata Saude
ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da gurnan,ji
take numfashinta na wani sam -samA kamar zai dauke.
Ta rushe' da wani irin kuka mai daga hakali, ta zabura ta yo waje a guje tamkar marar hankli ta tsallake mutanen da ke waje da gudunta tana jin mahaifinta na kwala mata kira, amma ba ta tsaya ba
Dr Ahmad wanda ya gaji da zaman motar ya fito ya jiggina da motar yana latselatsen wayarsa ya ganta
Ta fallo a; guje hankalinsa ya yi masifar tashi ya nufe ta yana qokarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunji kuka
ya rikice cikin tsananin rudani' ya riko ta yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne, ki fada min?’
Sande ta. Qara rushewa da wani kukan ba tare da ta saurara ba‘ ta shiga qakarin fadar, ‘Na mutu.. na mutu... na lalace... YallaBai.., an daura min aure yau..’
‘innalillahi wa ’inna ilaihirrajiun
Abin da Dr. Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar.
« ALHAMDULILLAHI
Wohoho jama nasan da yawanku kunyi missing din laure to mun dawo qauye ya abin zai kasancene da DR AHMAD wai INA YAYAN SAUDE SHINE MASOYIN SAUDE HAMID FUSHI YAYI YA HAQURA DA ITA KO YAYA SHIN WA ME ZAI FARUNE IDAN SU DILLALIYA DA ASMA AKA HADU YA AUREN SAUDE DA GARBA GURGU ZAI KASANCE wadannan amsoshin tambayoyin naku na cikin YAR TALLA BOOK3 WANDA ZAMU FARA GOBE AMMAN IDAN NAGA COMMENT SOSAI
NAKU HAR KULLUM ADMIN DBOY👍🏻☝🏻
[1/28, 12:10 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 10:24 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

BOOK 3


*CHAPTER 22*


Saude ta sulale qasa tana wani
gunji mai kama da. gurnani ji ta ke numfashinta na
sama‘sama
kamar zai dauke, ta rushe da Wani irin kuka mai daga
hankali, ta zabura ta yo waje tamkar marar hankali ta
tSallake mutanen dake waje da gudunta. Tana jin
mahaifinta na Kwalla
mara kira, amma ba ta tsaya ba Dr wanda ya gaji da zama
a motar ya fito ya jingina da motar yana lallatsa wayarsa ya
ganta ta fito a guje,hankalinsa ya yi ‘ masifar tashi ya nufe
ta yana KoKarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani
irin gunjin kuka. Dr ya rikice cikin tsananin rudani ya rike ta
yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne? ki
fada min." Saude ta Kara rushewa da wani kukan ba ‘ tare
data :saurara ba ta shiga qokarin fadar, “Na mutu... .“mutu
, na lalace. yallaBai * an d‘aura min aure da Garba .
“Innalillahi wa" inna ilaihi raji ’"un Abin‘
da Dr Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa
kansa saman motar gabad'aya
ya ma rasa a wace duniya yake
Malam bala ya qaraso da hazarinsa yana fadar keko
wannan diya allah ya wadaran halinki yanxu sbd dibar
albarka shine zaki kwaso a guje kina ihu kamar wata tabin
iska shin ba,a gaya miki yanxu muryarki al,aura baceba
iyee?
Sauce najin abinda ya fada ta sake rushewa da kuka tana
fadar wayyo allah na shiga uku na lalace malam bala ya
dauki sallallami kafin yace anya saude da hakalinki kuwa
yanxu budewar idon taki taki har takai kiyo waje kina
kururuwa? To maza tashi ki shiga ciki mutuniyar banza
mara mutunci zaki tashi ki wuce ko saina jefeki
Saude ta tashi da sauri ganin yana niyyar jefeta da wani
hogen daya rarumo ta fada cikin gida tana kuka sai a
lokacin Dr ya dago idanuwansa da suka kada sukai jajir
cikin dasashshiyar murya yace kayi haquri baba don allah
inason magana dakai
Malam bala yace Ohoo daman kaine mai hure mata
kunnen?
, . Dr. ya girgiza masa .kai, yana jin zuciyarsa tamkar zata
ballo ta fito ya ce,‘ “K0 daya ni dai ne wanda ta ke aiki a '
gidana, inda aka kai ta aiki" Malam Bala ya ce “Auho, to
bismillsh
mu shiga daga soro ai ban fahinta ba, mu shiga in kira
maka innar tasu ku gaisa'Ba musu Dr. ya bi shi~suka shiga
cikin soron gidan, sannan Malam Bala ya shiga cikin gidan
ya sa Inna Lami qanwarsa uwa, daya uba daya ya ce ta kira
masa Laure ta taho kuma da tabarma Yana tsaye ta shiga
ta fito masa da tabarma tare da fadar, “Lauren tana zuwa" ‘
’ Malam Bala ya, juya ya dawo ya ‘ shimfida masa tabarma
suka zauna, Dr, ya dubi Malam Bala suka gaisa sosai cikin
girmamawa Sannan Dr ya qara gabatar da kansa Baba nine
wanda Saude ke aiki a gidana, na maido ta. ne saboda wani
muhimmin abu wanda maganar aurenta da ta sanar ds ni a
«yanzu ya tarwatsa komai amma Baba kayi haquri da abin
da zan fada maka a yanzu kai
_ masa kyakkyawan kalla da kuma, kyakkyawar ” . fahimta
Baba kai ka haifi Saudat ka fi kowa sonta, kafi kowa sanin
ciwonta, kuma amana ce a gare ku abin tambaya a gobe
kiyama idan ku ka cutar da ita ku ka wofintar da rayuwarta
wallahi sai Allah ya kama ku a kan hakan duk dakuwa
kukukahaife ta. ' Baba, Saudat tana da masu sonta da aure
a nan garin, da kuma ni kaina, sannan Saudat yarinya ce
qarama Baba bai kamata ku_ tankWare rayuwarta ku zaba
mata mijin da bai cancanta da ita ba don kawai saboda,
wani dalili naku ka yi haquri Baba na san kuna da hakkin
zaba mata mijin da ya yi muku, amma Baba’ zaba " mata
mijin da ya‘ dace da rayuwarta don Allah don Annabi Baba
ka dubu girman Allah ka yi wa rayuwar yarinyar nan
adalci ' Tunda Malam Bala ya sadda kansa bai dago ba,
komai yake tunani oho! Inna Lame ‘ wadda take labe a
tsaye hannunta dafe da kofa . tana sauraren duk bayanan
Dr. tace, “To muna godiya Alaramma, Allah ya biya. Sai a
tashi a tafi umma ta gaida assha, kuma abin da . :ka yiwa
"yarmu Allah ya sa ayi wa taka, mun . kai diya aiki ka hure
mata kunne ka lalatata ka
maida mana, ka iske kuma za a yi mata aure kana Kokarin
hanawa kai shaida, saboda dandin bai iske ka ba? To ta
fada mana komai, kuma ba abin da za muce maka sai mu
ce ka je Allah Ubangiji ya yi mana sakayya".
Dr Ahmad wanda ya ji maganganun tamkar: saukar
markade, ya dago da sauri yana kallonta cike da mamakin
maganganunta ya
Kasa cewa komai, su Malam Bala ne ya
Daga kai yana fad'a, “Ya Isa haka Laure, koma cikin gida
don Allah”
Inna Laure ta ce, “Ka bar ni da wannan‘ babbab shaidanin
mai munafurcin kashe aure ya maida mana diya karuwa,
kuma saboda rashin imani ya biyo ta har gida ya ce kar a yi
mata aure‘ tunda bai gaji da lalatar ba. Malam ka
kalli Saude sosai na rantse maka da Allah cikine daita”.
ldanuwan Malam suka yo warwaje * saboda tsabar dukan
da maganar tata tai masa a
Kirjinsa. Cikin rudu ya mike yana fadar“Laure ki shiga gida
haka wuce ki tafi” Ganin maganganun nata sun yi tasiri a
zuciyar Malam yasa ta juya tana matsar kwalla a
munafurce ta gefe tana kallonsa “
Malam ya dubi Dr. Ahmad zuciyarsa na huci yace “Malam
mun gode kwarai amma don Allah ina rokonka ka tashi ka
tafi don Allah”. .
Dr ya danne mamakin da ya cika masa zuciya, cikin qarfin
hali ya bude baki da niyyar yin magana.
Malam ya daga masa hannu cikin tsananin fushi ya ce.
“Babu abin da za ka fada don Allah don
Annabi ka tashi ka fita ko na samu zuciyata ta sassauta”.
‘ Dr. ya mike tsaye cikin halin jarumtaka,
don gabadaya zuciyarsa' rugurguza ‘ta ,ke
tamkar za ta Balle Kirjinsa ta fito fili. Ya danne
abin da ke yunkuro masa kafin ya iya Karfin
halin fadar “Ka yi hakuri Baba, wallahi tallahi na
rantse maka da Allah ban aikata abin da kuke zargina da
aikatawa,ba kuma na amince zan tafi amma don Allah ka
bani minti biyu in magana da Saudat a gabanka
Malam ya zabum masa “Kai Malam ka ga ka bar nan tun
muna shaida juna, don
wallahi Saude ba za ta sake fitowa ba sai idan za,a tafi da
ita dakinta, ka ji na gaya maka".
Dr Ahmad yaji tamkar anwatsa masa tafasassan ruwan zafi
mai qona zuciya. Ya lumshe idanuwansa yana jin tamkar
mala’ikan mutuwa ya taho ya zare masa ransa koya’ huta,
ya bude idanuwansa da kyar
‘wadanda suka ida rikicewa ba ka ganinkomai ‘ cikin shi sai
tsananin ja tamkar garwashin wuta.
Ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro ' gabadayan canjin da
suka yi masa saura, yasan bazasu haura dubu hamsin ba,
ya ajiye a kasa
' tare da fadar kayi hakuri a bata wannan canjin insha l
Allahu ko tana gidanta ne zan yi mata aike” Ya juya ya fice
yana kokarin dauke kWallar da ke neman~zuraro masa .
Malam ya duka ya dauki kwalin yana . faman juyawa a
hannunsa, Laure da ke labe tana jiran ta ji yadda zasu qare
ta zabura ta yo ' c'iki'n soron ta yi caraf da kudin tana fadar
yauwa "‘KaWo su nan Malam". ‘
Shi hatta ma ba shi tsoro ya sakar mata
~ ya tsaya yana kallonta, ta soke a zani tana . fadar
“Allah ya ga tsimurmular da muke muna ta fama da Tv
Stand ba kayan kallo yanZu k0 ka ga
wad‘annan sai a siyo ma ‘yar baba irin wannan talabijin din
wadda ake lika wa jikin bango da ‘ kafet din tsakiyar daki su
kadai ne dama ba a siya ba”
. Malam Bala ya ce“Haba Laure, yarinyar nan ita aka ba wa
kudin nan, kuma kina sane daga katifa da zanin gado da
labule babu abin da aka sai mata, yanzu wadannan ba ' sai
a Kara a sai wani abun ba?”
Inna Laure ta ce, “Haba Malam ka sani fa sarai irin
mutumin da ‘yarbaba ta aura, dan masu da shi fa dan gidan
hali, ne za su rike; mana ita da mutunci? Ita ko Saude Garba
ne fa ka sanni na sanka, kar ce ta san kar to mu wahalar da
:kanmu na me? Dakunan fa naji ‘yan jere na fadar daki daya
ne ya ware mata mai girma, to me za mu zuba a cikin daki
daya? Ai da ma
Dan gado ne da katifa toga katifar nan ko zuwa gaba ai:
idan Allah ya hore ai sai mu yi mata gadon k0 ya ka ce
Malam‘?" ’
Malam Bala ya ce, “Shikenan aje a yi k0 ma . ‘ me za a yi.
ni dai na rabu da yaran nan lafiya
nan da awa daya za a wuce da su gidan Yaya Maje”. . ‘
Laure ta amsa da, “An gama Malam ’Sannan ta juya ta nufl
cikin gidan ta bar shi yana kwashe tabarma.
Tunda Dr Ahmad ya fita ya fada , motarsa ya kifa kansa
saman sitiyarin motar bai sake dagowa ba,» duniyar
gabadaya «ta shiga juya masa, ya rinka jin tamkar ana sa
guduma ana sassaka masa kirji
Ya dauki tsawon lokaci a kife tamkar matacce jijiyoyin
kansa suka tattashi rado rado abunka ga jar fata, kamar an
zana su, wani irin ciwonkai mai zafi ya sauko masa, ya.
dagO‘ kansa da Kyar wanda ya ke jin ya yi masa bala’in
nauyi ya mika hannunsa a kwabar jikin .motar ya dauko biro
da takarda ya yi wani dan rubutu layi biyu ba tare da ya flta
ba, ya kira yaro cikin dasasshiyar muryarsa ya ce, “Ka san
Saude?" ‘ "‘
.Yaron yace, “Yar talla, wadda ku ka zo
yanzu tare? Dr». ya ce, ‘Ita don Allah karBi ka kai
mata, ka tabbatar ka ba ta hannunka da nata, kar fa ka ba
wa kowa kaji?” '
Yaron ya amsa da, “To". Sannan ya juya ya nufi gidan a
guje.
Dr. Ahmad ya maida murfin motar ya rufe ya yi mata key,
ya ja sannu a hankali ya bar unguwar.
Saude wadda tunda ta shigo gidan ta fada dakinta wanda
aka maida shi na zuba tsummokara ta zube a Kasa ba tare
da ta damu dadattin dayayiba, tashiga rusarkukamai ‘ tada
hankali ji ta ke gabadaya ta tsani rayuwar.
Yaron ya shigo tsakar gidan inda jama'a ke ta hidimarsu ya
tambaya, “Ina! Saude?”
Inna Lami ta nuna masa dakinta, yaron ya nufi dakin, ya
iske‘ ta kwance Kasa~ tana sharBar kuka, ya ce “Ga shi inji
mai mota a waje ya ce na kawo miki”.
Saude da ke kife tana kuka a dago da kanta a hanzarce
tana kallon yaron ta karBi takardar hannunta na kyarma
tana qokarin warwarewa kamar tasan abin da aka rubuta ta
zuba wa kyakkyawan rubutun ido wanda ta ke jin tamkar
shi ne ta ke gani, yaron ya juya ya tafi ya barta tana kallon
rubutun da ba zata iya karantawa ba, illar jahilci”. Ta fada
ta qara durkushewa ‘ta dukunkune takardar ta sake
Ta qara fashewa da wani sabon kuka mai ban tausayi..
Yaya Rabi’u ya fado mata a zuciya, ta tuna rayuwarta da
shi, da irin yadda yake rudewa idan ya ga hawayenta ya yi
ta rarrashinta, rayuwa ke nan, ga ta yau tana kuka ba ta da
wanda zai ce ki yi shiru balle har ya rarrasheta.
Yau ta yi' kuka kamar ikon Allah idanuwanta suka kumbura
suka yi luhu-luhu, ga bangaren kanta da ya dauki ciwo a
dole ta saurara da kukan saboda yadda ta ke jin kan nata
kamar zai rabe biyu.
Ta tashi zaune ta jingina da bango ta ‘ rafsa uban tagumi
tana tunani mai tarwatsa zuciya, Inna Lami ta tah0 dakin ta
turo mata robar tuwo wanda aka yaba wa miyar taushe ta '
ce, “Ga shi nan idan kin gaji da kukan ki dauka ki ci da
sauri, don yanzu za a wuce da ku gidan uban wanka”.
Ta wurgo mata bakar leda, “Ga wannan atamfar uban
wanka ceda takalma ‘yan Maradi da abaya wanda za ki
saka a tafi, maza don ba ke za a tsaya jira ba”.
Tana gama fada ta juya ta yi gaba abinta ta bar Saude na
bin ledar da tuwon da kallo, a
yanzu idanuwanta sun KeKashe babu abin da suke sai zogi
da radadi mai ciwo k0 motsin kirkibatayiba, har Inna. Lami
tadawota ~ dauki sallallami, “Wai Saude ya ki keso da
mune, kefa kawai akejira,karma kici tuwon
kanki kidaukikayan kisaka mushine ‘ matsalarmu”
Ta yi tsaki ta juya abinta.
Saude ta Ki motsawa daga inda ta ke don yadda ta ke ji.
zuciyarta k0 kashe ta za su yi ba za'ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login