Showing 3001 words to 6000 words out of 102653 words
Chapter 2 - YAR TALLAH Book Complete Document by Jamila .txt
kwallar data tarar masa muryarsa a sanyaye yace
Kiyi haquri kije insha allahu zan samar miki takalmin da zaki dinga sakawa dakin dawo kinji?
Ta daga masa kai ya miqa mata kofin garin ta karba ta shanye ta miqa masa kofin
Ya amsa ya karbi tiren ya dora mata ta tafi
Yana tsaye yana kallonta harta bace
Sannan ya juya ya koma gida
Laure ta watsa masa harara tace ni naci uwar zariyama ballentana bita zaizai
Bai tanka mataba ya duqa yaci gaba da wankinsa harya gama
Ya shanya wankin sannan ya nufi kofar dakinta ya durkusa daga waje
Inna na gama ina alalata
Inna laure ta dago daga kwancen da take saman katifa ita da yarta
Ta watsa masa wani kallo tace abincima wato har kaso biyu zaka dinga ci kenan
Koba dazun na giftaka naga naga kanacin garin kwaki ba? Dallah ni tashi ka bani wuri ta doka masa tsawa
Rabiu ya miqe tamkar almajiri ya nufi bakin rigiya ya janyo ruwa guga guda yayi alwala ya nufi dakinsu yayi sallar asuba da azahar a hade
Sannan ya kwanta nanfa gajiyar daya kwaso ta rufeshi
Saude tasha yawon tallarta harta godema allah amman alalar ko rabi bata samu ta saida ba nanfa idonta ya ciko da hawaye ta soma bin jama,a tana hadasu da Allah su siya
Danladi ya tabo abokinsa ilu kai baba yarinyar canfa tana cikin matsi ina yawan ganinta a cikin tasharnan anya ba zamu far matAba kuwa?
Ilu yace nimafa na dade ina wannan tunanin to amman abinda ke tsoratani yarinyar karamace sosai karkaje ka balloma kanka ruwa
Danladi yace kaiko da mugun baki kake idan zakaxo muje mu fasa kawai kaxo muje malam
Mu jata kangon alhaji sani
Ilu yace kuma hakanefa to taro mana ita ni bari naje na duba mana wurin na tabbatar da tsaro
Ya dire daga kan teburin da yake ya nufi gurinda saude take duqe gaban wani direban j.5 tana zazzage masa alala a kwano ilu ya iso waje yace ke yarinya idan kin gama sayar masa kikaima wancan gashi can zai siya tace to ta miqama direban alalan ya karba ya somaci ita kuma ta rabe gefe tana jiransa ya gama ya bata kudin da kwanon ta qara gaba
Direban ya soma ci gaya dago sai yaga ta kura masa ido ji take dama bakinta yakekai alalar sbd tsabar yunwar dake cinta
Direban yadan daga murya yan mata ya kike kallona ko na miki ne ?
Saude tayi saurin dauke kanta yayi daria yaci gaba da cin alalarsa
Karen matar dake can gefe yace sai oga baka tambayeta ko tana ciki bane
Yace kai share wannan bata inda ke mata dadiba
Karen motar ya sake bushewa da daria yace sai oga allah yabar mana kai
Baice masa komaiba ya qarasa cinye alalar ya wurga mata robar ta zabura ta miqe gamida saka kwanon cikin tiren ta qarasa inda yake domin karban kudin ya kura mata ido yaya akayine?
Tace kudin zaka bani
Ta nawace?
Saude ta numfasa kafin tace ta murtala daya da gomace
Yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya dubeta
Yace yanxu idan na baki wadannan kudin zaki barni nayi lalata dake
Saude ta zaro ido tana kallonsa
Ya sake maimaita mata a karo na biyu
Idonta ya ciko da kwalla alamar zatayi kuka
Yace a,a meye abin kuka yanmata karbi kudinki kisan inda kikai kuma karna sake ganin kafarki ta tako inda nake
Idankuwa ba hakaba saina turmusheki
A wurinnan ya miqa mata kudin karbi ki wuce tasa hannu zata amsa hannunta na rawa ya hada hannun da kudin ya riqe yana dariyar mugunta
Meye sunanki yan mata?
Ta janye hannunta jikinta na rawa tabar wurin a hanzarce har tana tafka tuntube wani dan kamasho da yawo giftawa ta wurin ya tintsire da daria yana fadin dan baba kabar iya shege kabi Allah kaji
Ya miqe yana fadin kai garba mufa duniya gaba muka bata ba baya ba
Garba yace shegen sama kura taga biri
Allah ya kauda abin kunya
Yace ba aminba mu abin kunya binta muke tana guduwa Allah ka hadamu da abin kunya duk inda yake
Duk wurin sukasa ihu ana sai oga allah yabar mana kai
Ikon allah mai tsaida wando ba zariya saude dai bata sake bi ta kansu ba ta nufi inda danladi ke zaune saman teburin cikin tasha tace kaika aika a kawo maka alala ko?
Yace eh zubomin ta murtala biyu
Dadi ya kama saude don tasan daga wannan ta siyar tana murna ta zuba masa tasa masa mai da yaji
Ya zauna ya harde gamida lashe alalannen tas yana lashe baki
Saude na zaune tana kallonsa yana gamawa ya dubeta
Kinada canjin naira dubu?
Saude ta waro ido ita tunda takema bata taba riqe naira dubunba ballentana harta samo canjinta
Ta girgiza masa kai alamar a,a
Yace to ya za,ai kenan ko kuma xo muje na samo canjin saina baki kudinki
Ta mike ta tattara kayan ta bishi
Suka soma tafiya ganin suna shirin fita daga tashar yasa ta dubeshi tace
Ina kuma zamuje?
Yace ban gane ina zamujeba canji zan nema in baki kudinki
Saude tadanyi shiru maganar yayanta ya dinga dawo mata cikin kunne tamkar yanxu yake gaya mata
Saude ki kula banda aje tallah ki tafi samo canji banda kuma kibar mutum ya tafi samun canji shi kadai
Kuma karki sake ki yarda wani ya jaki zuwa wani guri koda kuwa nan da canne
Saude ta dubeshi a,a gaskia nidai kazo muje cikin tashar a samu canjin kaban kudina don yayana ya hanani bin wani
Ya hade rai jini da yar iskan yarinya sai kuma akacemiki kowa dan iskane. To karki bini ki karbi kudinki zauna
Ya wuce zai tafi hankalin saude ya tashi tasan kan kudinnan yau inna laure kashetane kawai ba zatayi ba tayi saurin riqo rigarsa tasa kuka
Nidai wlh saika bani kudina
Ya juya a fusace ya danna mata wani mugun zaki ke dan ubanki bazaki sakeniba? Ta qara cacimo rigarsa nidai wlh saika bani kudina idan naje gida a haka dukana za,ayi
Haushi ya kama danladi yasa hannu ya dauketa da wani wawan marin dayasa saidata kife. Ya juya zai wuce wani magidanci ya kwaso a guje yana kiran
Tsaya nan danladi karka sake ka matsa mugu mai kai mata?
Yayi saurin juyowa jin muryar ogansa
Gabansa ya fadi yai saurin juyowa yace wlh oga yar iskan yarinyace wai dan uwar yarinyarnan waini zata tsare nace
Nace taje ta samo canjin dubu tace babu nace muje na samo na bata taqi yarda toya takeso nayi da itane oga ?
Ya tallabo saude gamida fadin yanxu don rashin imani wannan yar qaramar yarinyar zakaima irin wannan marin?
Yanxu wannan yarinyar fisabilillahi meta sani?
Ya zaburo cikin irin muryar yan shaye shayennan yace oga zaginafa tayi yace idan ta zageka kai yanxu zagi nawa kai mata a gabana ko kunyata bakajiba
Yi hakuri yarinya kinji allah ya saka miki bani dubun na canja muku
Yadan sosa qeya a,a ai gurin ilu zan amso dubun na samo canjin mutumin ya girgiza kai yana fadin allah ya shiryeka ya zaro kudi cikin aljihu ya kalli saude. Kudin naki har nawane?
Cikin muryar kuka tace murtala biyu da goma ne
Ya girgiza kai ya bata sannan ya kalleshi na ranta maka ka samo canjin ka kawomin kudina
Dan ladi ya turo baki yana dan harare harare ya wuce kamar zaikai duka
Mutumin ya dubi saude yace wuce ki tafi kinji allah zai saka miki yace ai harda laifin iyayenku mata dake turoku tallah cikin maza basu san da irin mazan da zaku hadu ba don ko cikin masallaci zakukai tallah sbd tsoron allah sai an samu mutanen banza ballentana cikin tasha inda yayan banza ke taruwa wadanda daman can lalatattu ne ya za,ai ace bazai,ai barnaba fisabilillahi balle ke yarinya qarama
Wuce kije allah yayi miki sakayyah
Haka saude ta wuce gida jiki na rawa da yamma lis don tuni rana ta fadi a lungun gidansu ta hadu da rabiu cikin taron jama,a wai ana duban wata
Saude ta lallaba ta janyo hannun rigarsa yayi saurin juyowa yana kallonta yayi murmushi tana fadar
Tun daga nesa na hangoka duk ka keresu tsawo
Rabiu ya dungureta yana daria yace ke kuma sarkin sharri ko?
Daria itama tayi tana fadin anga watanne yaya?
Yace a,a munadai dubawane amman munasaran za,a ganshi kedai ki zauna da niyyar azumi gobe
Tace ai nima tsayawa xanyi yaya ka dagani inga watan
Yayi murmushi yana fadin so kike yau inna laure tayi kujera dake kenan ko? Ya riqo hannunta
Yace wuce mu tafi kinga har yara su fara tsokanarki
Saude ta juya taga dandazon yaran daketa tsalle suna waqa
Yar tallah qazama yar tallah bata wanka yar tallah bata wanki yar tallah bata sallah yar tallah saidai yawon tallah
Ta dago idonta cike da kwalla ta kalli yayanta tace aidai yaya ina sallah ko?
Kai kawai ya daga mata sbd yaddah abin ke sukarsa a zuciya ya daura hannunsa saman kuncinta inda shatin yatsu suka kwanta wurin yayi jajir abinka da jar fata
Muryarsa na rawa yace waya mareki haka saude?
Muryarta na rawa ta shafa wurin tace wanine ya mareni a tasha yaya wai don naqi binsa ya samo canJi
Rabiu yaja numfashi ai gara dabaki bishiba saude shida allah
Sai a lokacin ya lura da jinin daya kwanta a idonta yAja hannunta suka tafi yanajin zuciyarsa na suya fiye da radadin marin da taji
Suna shiga cikin gidan inna laure dake duqe bakin rariya tana tsane gero ta dago ganin kwanikan duk sun baci da qasa
Jar ubannan kai badai barin alalar kikaimin yauba ?
Saude tace a,a na saida wanine ya mareni harna fadi waidon naqi binsa ya samo canji
Inna laure ta daka mata tsawa ke gafara can munafuka tantiriya idan yace ki bishi ya samo canji to sai meye ?
Koyana iskanci dai ai bazaiyi da keba a balla qashi ko,a karya qafa bani kudina ni ki wuce
Saude ta warwaro kudin a habar zani ta miqa mata. Ta karba gamida kirgawa taga sun cika cas ta ninkesu ta soke akai
Rabiu ya dubeta dauki gora kije kiyi alwala kiyi sallah
Inna laure ta zaburo bazatayi
Maza ga kudi kije ki siyo icce ki daura sanwar tuwo kai kuma ka tattara kayan tallar ka wanke
Idon saude ya ciko da kwalla ta kafama yayan nata ido
Laure ta zaburo mata to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin
Ko ubankima bai isa ya hanaki yin tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba kokuwa sai naxo nayi miki dukan kawo wuqa?????
[1/8, 4:43 PM] I love my mum: ππDAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100ππ
[12:17PM, 02/02/2017] ππΌββ@lh@jiππΌββ: [1/8, 4:44 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
*CHAPTER 5*
Tace to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin don ko ubanki bai isa ya hana kiyi tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba ko kuwa?
Anan muka tsaya
Rabiu ya turata alamar taje ta karba
Laure ta maka mata rankwashi akai wanda yasata fasa wata uwar qara sbd azaba
Ta wurga mata kudin tana fadin munafuka nafa alamar watarana sai kin nemi kifi karfina a cikin gidannan
Dole saina gyara miki zama ta haureta da qafa
Zaki tashi ko sainaxo na casaki? Yar iska kawai lau yayyar banza kawai
Saude ta yinkura ta tashi gamida ficewa tana kuka
Rabiu ya rakata da idanu yana tausayin kansa rayuwarsu na bashi tausayi
A ganinshi babu yaran da suka taba samun kansu cikin halin kunci kaman yanda shi da qanwarsa ke ciki yanxu. Yace ya allah gamu gareka
Laure ta wurga masa murfin kwano ya zabura gamida dawowa hayyacinsa yayi gaba yana tattara kwanukan
Laure tace daka barta ta tafi kaita tunani ai gara ka bita can kuyita
Kwakwale kwakwalenku dan iskan banza da wofi kawai
Maganar ta soki rabiu yai saurin wuceta sbd yaddah maganar ta daki zuciyarsa matuqa ji yake kamar bata taba masa abinda ya qona masa zuciya irin na yau din ba
Saude ta dawo daga siyo iccen ta zauna ta hura wuta gamida daura ruwan tuwo a lokacin har ta fara sarewa da wahala a jikin murhun ta soma jinyar qafafuwanta ta samu daqar ta kammala tuwon da miyar kuka a bakin murhun taci tata ta miqe tayi alwala ta shige dan akurkin dakinsu domin jero sallolin da batayiba
Washegari aka tashi da azumi don haka saude ta samu sauqin wahalar sosai
Dukda aikace aikacen gidan da tayi itada yayanta bata wata sha wahala ba
Saida azahar inna laure tasata dauki markaden tiya uku aka kai markade aka markado shi ta sake daukoshi akai ji take tamkar wuyanta zai karye sbd nauyi
Data kawo markadenma qin sauke mata tayi ta barta dashi akai
Saude tasa kuka don allah kiyi haquri ki saukemin inna kaina zai karye
Laure dake zaune tana kwadon zogale ta dubeta a harzuqe kin fara ko? Wato nabar kwadon zogalen naxo na sauke miki sbd inajin tsoronki ko?
Ta maida kai taci gaba da kwadonta tana fadin bankadaddiyar yarinya masifaffiya
Iklima dake kwance gefenta tace laure bani ruwa insha karya azuminnan zanyi bazan iya kai azuminnan ba
Laure tace a,a ko aike kikasa kanki tuntuni nake fadin ki ajiye ki ajiye kikaqi waike sai kinyi.
Ta miqe gamida dibo mata ruwan cikin randa mai sanyi ta kawo mata ta miqe tasha iya shanta tayi wurgi da modar
Laure tace a!a mai makon ki bani in mayar sai kiyi wurgi da ita
Iklima tayi tsaki ta janyo kwanon kwadon dake gabanta ta soma ci
Laure taja kwafa sannan ta miqe ta dauko modar ta mayar sai a lokacin ta nufi saude data dafe wuyanta da takeji tamkar zai karye
Laure tace shin zaki tace ko na tace? Donna lura wuyanki ya isa yanka
Saude ta wuce ta nufi rijiya sannan ta dibo ruwan ta taceshi tas tana
Tana gamawa rabiu ya dawo daga markaden qosai
Da alamar shima a gajiye yake
Laure ta dubi saude maxa ki hadamin wuta ki hadamin kaskon suya ki hadamin murfi biyu dayan murhun kuma ki dora ruwan koko
Ba yaddah ta iya haka taci gaba da hada hadar hada wuta babu ko tausayawa
Laure ta soya kosai sannan ta sheqa koko cikin bokiti
Qarfe shida tace su dauka sukai makarantar malam hadi tasan almajirai zasu siya
Rabiu ya dauki kokon ita kuma
Saude ya dora mata kosan
Laure ta kwala musu kira suka dawo
Tace kuma ban yarda da ku daukarmin ko kayan sile ba kuje ku dawo kayan buda bakinku nanan zan ajiye muku suka amsa da to sannan suka fice
Cikin ikon allah kuwa suna zuwa ana kiran sallah
Alhaji bashir wani tsohon mai kudine a cikin layin yaxo zai shiga masallaci ya tsaya wurinsu ya zaro dari biyar ya miqawa rabiu yace ya kirga kosan da kokon ya bada sadaka,,,dadi ya cikasu shi kuma ya shige masallaci abinsa
Rabiu ya kirga kayan gaba daya na dari hudu da hamsinne
Yayima almajiran wurin sadaka da koko da qosan
Ana gama sallar alhajin ya fito rabiu ya fada masa ko kayan nawane yace tosu riqe canjin
Sannan yace musu kullun su rinqayin sadaka da koko da qosan zai rinqa biya
Ya zaro wata dari biyar din ya basu rabiu ya amsa cikin ladabi suka cika da murna
Alhaji bashir din yace kuma ku dinga diba kunaci kunji?suka amsa da to sannan ya wuce abinsa
Suma suka wuce gida rabiu ya canja kudin ya dauki canjin yankan da suka rage yaba laure sauran kudinta dadi ya cikata za,a ringa siyan kayana kenan kaga babu bandaro (kwantai) kenan ta dubi
Saude jiki maza ki dauko muku koko suka tsugunna a tsakiyar gidan tamkar almajirai sukasha sannan saude ta miqe ta dauko musu sanwar dimamen daya rage tun na sahur sukaci suka koshi duk da kuwa miyar kukar tayi tsami ta lalace amman a haka suka cinye tuwon tas. Gaskiane da hausawa sukace da babu kwara ba dadi
Sun gamaci suka tafi sallar asham a masallaci suna dawowa su duka suka kwanta a gajiye kamar matattu
Qarfe uku na dare laure ta tashesu wai su tashi susa sanwar tuwon saidawa na asuba
Saude tasa kuka saboda bacci da gajiya dake cinta
Laure ta haskata da cocila au kukama kika tsayayi kenan ni inanan ina jiranki?
To malam zoka gani da idonka saude na zagina
Malam bala ya zaburo tamkar shayayye
Zagi kuma laure wani irin zagi ba dadin ji?ya hankade labulen dakin ke ba magana ake miki ba yar jakar ubannan shine kika zauna kinama mutane kuka
Idanda uwarkice ta dawo daga lahira ta sanyaki aikin ai bazakiyi kukanba ko?
Fitonan inji wanda kike zagi
Saude tahau rantse rantse abinka da yarinta kuma ta rikice sai fadi take wallahi baba karya take ban zageta ba na rantse da allah ban zageta ba
Malam yace shin zaki fito ko saina shigo dakin?
Rabiu yace kayi haquri don allah baba wallahi bata zageta ba
Malam yace au karya tayi mata kenan?
Ta zabura ta boye bayan rabiu tana kuka tana bashi haQuri amman bai sauraretaba yasa hannu ya fisgota daga bayan nasa ya jata a qasa kiyyyyyyyy
Har waje ya janyo igiyar guga ya shiga laftarta ta ko ina bugu bana hankali ba baya ko duban inda zai doka sai ihu take tana roqonsa
Rabiu ya duqar da kansa qasa baya ko iya motsi hawayene kawai masu zafi dake diga daga idanunsa
Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato
[1/8, 4:44 PM] I love my mum: ππDAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100ππ
[1/9, 9:55 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
*CHAPTER 6*
Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan
kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya
wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo
ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen
numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon
siyarwan don lokacin sahur ya gabato
Anan muka tsaya
Rabiu ya miqe ya rarrafa wajenta gamida jawota jikinsa
yana sharar hawaye baisan sanda wani irin kuka maiban
tausayi ya kubce masa ba saida yai mai isarsa sannan
Ya janyeta ya tafi hura wutan tuwon don daman ya iya
tuwon duk da ba sosai ba don tun yana yaronsa inna laure
ke sanyashi kafin saude tayi kwari amman abinda ba
aikinkaba har saude data girma daga baya taxo ta fishi
iyawa
Saidai yau haka ya zage bakin kokarinsa yayi tuwon da
miya laure ta murmula musu naira biyar biyar ta zuba
tuwon a baho miyar a bokiti gamida basu fitila
Rabiu ya dauki kwanon tuwon akai kana ya dauki na miyan
a hannu yace saude ta koma ta kwanta shi zaije ya siyar
har bakin tasha yaje dukda rashin kyan