Showing 21001 words to 24000 words out of 28816 words

Chapter 8 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt

kuzarinshi ga wani abu dabai tab'a jin irinshi ba ya tokare masa zuciya,cikin kwarin gwaiwa ya mike suka fita daga gidan,hankalinsu gaba d'aya ya tashi ganin har lokacin babu alamun numfashi a jikinta kai tsaye wani private hospital suka kaita mafi kusa domin ceto rayuwarta,cikin hanzari aka shiga Emergency da ita.








Kai komo Farooq ya shiga yi,kwata kwata ya rasa natsuwarsa ga wata irin zufa da takeyi jin Iminat yake har cikin ransa soyayyarta da tausayinta kara nunkuwa sukeyi a cikin jinin jikinsa kamar yadda jini ke yawo a jikin d'an Adam haka Soyayyar Iminat ke zagaya duk wata gab'a da jijiya ta jikinsa.








" she will be alright kaji Buddy,zoka zauna"Ameer ya fad'a.






Kunyace ta kama Farooq yayi saurin zama yana fadin"tausayi ta bani Buddy ,ka duba ta fito gida lafiya sannan kuma yanzu sai suji wani lavari daban".






"Kama tunamin,bari na kirawo Momy na sanar musu" ya karashe maganar yana fiddo waya tare da kiran Momy ya fad'a mata meke faruwa.








"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Papi ,Zeena na asibiti fa,yarinyar data fita yanzu" ta karashe maganar a matukar tsorace.










Jin Zeena na asibiti ba jaramin d'aga hankalin Papi yayi ba amma saiya daure don kwantarwa da matarshi hankali yana fad'in"ke kada ki damu kanki, insha Allah komai zaiyi daidai,tashi ki fad'amun asibitin mu tafi kawai".




Jiki na kyarma haka suka fita zuwa asibitin Papi ke driving motar,cikin kankanin lokaci suka iso asibitin da aka kwatanta masu,kuma hakan yayi daidai da fitowar Dr daga Emergency farin gilashin dake idonsa ya cire yana fadin "Ku biyoni office". Daga fadin haka yayi gaba abunsa,Papi da Ameer suka bishi yayinda Momy tabi gadon da aka fiddo Zeena don canza mata daki.








Rubuce rubuce yayi sannan ya dago yace" ba wata matsala bace,kawai firgicine da tsoro yasa ta suma da kuma tayi gudu sosai tana buk'atar Hutu,saidai Ku kula da kiyaye ganin ko jin abunda zai firgitar da ita don zai iyayin daidai da bugawar zuciyarta Wanda hakan na iya sawa ta rasa ranta,amma yanzu an mata allura zata samu bacci insha Allah zata tashi lafiya lau".








"To Dr mun gode,don Allah ko zamu iya samun sallama" Papi ya fad'a.






"Eh ba matsala insha Allah, data tashi bacci shikenan,bari na rubuta maku" Dr ya fad'a yana rubuta masu takardar sallama.




A waje suka samu Farooq,saurin mikewa yayi yana fadin"Ameer ba wata matsala daiko".






Dagasa Papi yayi tare da fad'in"ba wata damuwa yanzuma gida zamuje".








Sai yanzu Farooq yake k'arewa Papi kallo tare da gane kamanninsa nada a tare dashi a fili,murmushi kawai yayi tare da fadin"to Alhmdllh".








Haka suka rankaya zuwa gida,Papi ne ya dakko Zeena tamkar gawa ko motsi batayi illar numfashin da take fitarwa a hancinta kawai zaisa ka gane tana da rai.








Suka kuwa daga nan komawa sukayi gidannan Farooq ya dakko motarshi sannan kowa ya wuce gida.






Da sallama ya shiga parlon gidansu ,dama bayaso ya samu kowa a ciki,ya koyi sa'a babu kowa a wurin sai Ladi mai aeki tana masa sannu amma ko kulata beyi ba ya wuce warsa d'akin shi ,wani irin zafi da zugi zuciyarsa take masa dukawa yayi kasa tare da dafe zuciya ,take maganganun Dr Nasir suka shiga dawo masa fil a rai,dafe kai yayi yana ambaton sunan Allah daya kawo mashi dauki,ya dade yana jiran had'uwarsa da Iminat yana matukar sonta ya rike alkawarinta ya zauna zaman jiranta na tsawan shekaru,saidai gashi yanzu tazo mashi a kurarran lokaci tazo a inda ya zama dole ya sadaukar da ita,tabbas wannan shi ake kira zanan kaddara ,tabbas Ameer yayi masa kyautatawa da dama Wanda ya zama dole ya boye sirrin dazai gano Zeenat itace Iminat dole ya samu lokaci ya hadu da ita, indai tana sonsa har yanzu to tayi masa wannan alfarmar.








*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karashe*








*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Pls
Vote
Comment
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*
*Maji dadin Kainuwa Ce* ✍🏻





*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
116♾120




"Ya kamata ki bada number dinsu a kirasu kinji kiyi hakuri komai zai daidai ta" Farooq ya karashe maganar yana fiddo da phone dinshi daga aljihu,a take ya kira gida ya kuma kiran Ameer ya fad'a masa,sannan yaba Manal wayan .






Hannu na kyarma ta karb'a wayan ta kira Momy tare da sanar mata,kafin ta bashi wayan.






"Innalillahi wa'innalaihir raju'un" Kalmar da Momy keta maimaitawa kenan.






"Lafiyanki kuwa Momy na meya faru kika tashi hankalinki haka" Shaheed ya tambaya.






"Ka dauko key muje asibiti yanza mota ta bige Yaya Minal".






Kamar saukar aradu haka yaji maganan Momy domin duk gidan Shaheed yafi shiri da Minal,gudun kada hankalin Momy ya kuma tashi yasa ya daidaita natsuwarsa ya dauki key tare da kama hannunta suka fice daga gidan.










Asibiti




" Buddy ina fatan bakaji ciwo ba"Ameer ya karashe maganan yana duduba jikin Farooq,da suka iso yanzu shida su Daddy.






"Sannu kaji Son ,komai lafiya lau ko" Momy ma ta jefo mashi tambaya.






Murmushi ya saki "ina lafiya Mom ,saidai wacce na bige tana emergency Mom taji ciwo sosai,kunga twin sis nata nan" ya karashe maganan yana nuna Manal da duk ta rasa natsuwarta burinta kawai taji halin da y'ar uwarta ke ciki.








"Allah sarki zonan y'ata ,ki kwantar da hankalinki insha Allah ba wata matsala"ta karashe maganan tare da janyo Manal jikinta sai lokacin Manal ta gaishesu,kuma a daidai lokacinne Shaheed da Momy suka iso wurin sallama dauke bakinsu.








Kallan kallo ne ya fara tashi tsakanin Momy da Farooq ga kuma Shaheed da yake gani kamar an tsaga kara a kamanninsu,mikewa yayi tsayi yana murza idanuwansa ya rasa a wacce duniya yake har abada bazai tab'a mance wannan muryan ba ballantana kuma mai fuskar baki na kyarma ya furta" Um....Ma.....Umma na"








Wasu zafafan hawaye ne suka soma bin fuskarta tabbas ita uwace data dauki tsawan shekaru tana jiran wannan rana kullun cikin mafarkinta take"Shureim zo gareni,Ashe zaka iya ganeni".






Jan kafarshi kawai yayi zuwa gabanta ya zube a kasa yayinda hawaye ke zubowa akan fuskarsa"Umma ko cikin shekara million zan iya ganeki ballanta y'an shekaru da basufi 20 ba".






Rungumeshi tayi tsam a jikinta tana fashewa da kuka.






Momy ma kukan ta saka ta jin farin cikin dawowar ahalin d'anta a cewarta ya daina damuwa kenan.






"Kuyi hakuri don Allah ,tunda abun farin ciki ne ya samu kuma kunga nan asibiti ne be kamata mu shiga hakkin wasu ba,mike kaji d'ana" Daddy ya fada yana kama hannun Shureim.






"Alhmadllh Allah mun gade maka,Yaya Shureim mun Dade da gane kai jininmu ne amma sai Momy tace wai kamane,Shaheed ga Yaya Shureim".Manal ta fad'a tana Jan Hannun Shureim ta hada nada Shaheed.




Rungume Juna sukayi dukansu suna zubar da kwallah,wani irin son junansu yake ratsasu da kewarsu yana tuna lokacin da yayi tare da Twins dinsa ,ashe jininsa ce ya buge yanzu.








Fitowar Dr Nasir ya maido hankalinsu duka jikinsu,har rige rige suke wurin fad'in Dr ina fatan tana lafiya.






Be basu ansa ba illah kallonsa daya maida ga Farooq " ka saukaka wa zuciyar ka pls mana".






Nuni yayi masa da yayi shuri,tuni ya gano mai yake nufi"waye mahaifin yarinyar muje office ".






" gani nan muje Dr"Dady ya fad'a.




Cike da mamaki yakebim Daddy da kallo.






Dafa kafad'arsa yayi "karka damu d'ana muje" kafin su wuce Office dinma aka fiddo Minal zuwa d'akin hutu tanata sharar bacci abunta ga kanta an nade da bandage da kuma hannun damanta,tuni suka rufa mata baya suna jera sannu dukda ba jinsu take ba.






Nuna Dr yayiwa Daddy daya zauna,sannan ya zauna.




Sai lokacin ya cire farin gilashin dake jikin idonshi ya Ce"to Alhmsllh Daddy babu wata matsala kawai buguwace yayi kuma mun dubata ,insha Allah data tashi daga bacci lafiya lau komai zai daidaita,ga magungunan da za'a siya nan"ya karashe maganan yana mika wa Daddy takardan magungunan.






"To Alhmdllh,Dr mun gode sosai ,bari naje na duba jikin nata"




Fita yayi yana kallon Farooq dake nufo kofar.




Tsaye tayi cak tare da kwallah ihu,"Shureim dama kana raye na shiga ukku no Aysha"ta karashe maganan tana kuka da tafa hannuwa.






Kallonta yayi cikin mamaki na ya akayi ta ganeshi,"Mama dama kuna garinnan"ya fad'a da niyar k'arasawa wurinta.






"Karma ka aekata wannan babban kuskuren na zuwa gaban Aysha ,domin bazan tab'a lamuntar hakanba ,kada ki sake ki kuskuren sake zuwa wajen zuri'ata ,Aysha kun rusamin farin cikina kun rarraba kan y'ay'ana kunsa sun tashi marayu " cikin sauri tazo taja hannun Farooq tana zubada kwallah"karka kuskura ka k'arasa gareta nazan tab'a lamuntar hakanba har abada".






"Na shiga ukku don Allah Ku yafemun ,kunga yanda komai ya canza".






Tsaki Momy taja tare dajan hannun Farooq ta koma d'akin da aka kwantar da Minal.










*ALK'ALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Pls
Vote
Comments
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*


*MAJI DADIN KAINUWA CE* ✍🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https:///kainuwawritersassociation
___________________________________
121♾125








Sai lokacin Daddy ya iso inda take yana kallonta da mamaki da alama dai itace matar kawun Farooq da yaji labari ,to tun yanzu Momy ta dauki fushi da ita inaga tasan yacce ta rike Farooq "kinga ki daina kukan nan yanzu ta riga da tayi fushi sosai amma ga adreshin gidana in yaso in an d'an kwana biyu ta natsu sai kuzo a sasanta komai nasan zata yake maku kada ki wani damu fatana kuyi nadama ta gaskiya ni kuma nayi maku alkawarin daidaita komai".






Karbar katin tayi tana kuka yana Kiran" na gode kwarai Alhaji Allah ya saka da mafificin alkhairi".




Da"Ameen "ya amsa ya shigo d'akin yana kara tambayarsu yamai jiki.






Hajiyace ta kira Ameer ya dauka yana fad'in" Hajiya ina zuwa aekam sai kin biyani tukaici zan baki wannan albishir d'in".






Murmushi Hajiya tayi"d'an nema ,abunda ka iya kenan ,to kazo yanzu ina d'ana Farooq?".




Kallon Farooq yayi yana masa kwalo yace"Hajiyata gwauro zakicemun zanfi fahimta dai".






"Kaniyarka Ameeru,maza kazo yanzu ina jira"daga haka ta kashe wayarta.




" zanje gida wurin Hajiya daga nan sai in taho da ita, Allah ya kara lafiya ".






" aekam da kabar Hajiya ta zauna gida ,inmun koma sai tazo dawainiyar tayi yawa ga girma kuma"Mom ta fad'a.






"Rufan asiri Momy na,kinaso tace don ba mu bane,zatace da gangan na boye mata shiyasa yau nakeso nayi mata abun kirki na fara mata albishir cewa munga danginmu muma" yacce yayi maganar yasa kowa dariya cikin d'akin .






"Abunda kasa gaba kenan,maza kaje ka kulamun da Hajiya ta" Farooq ya kare maganan yana tankad'a keyar Ameer,saida suka rungumi juna kamar kullun yacce suka saba in zasu rabu sannan Ameer ya fita daga asibitin.








Wayar Farooq ne yayi kara alamar shigowar sako,wayar ya Ciro ya duba da mamaki a ina ta samu number dinshi amma ya zama dole yaje d'in don shima yana buk'atar ganinta cikin lokacin nan,sallama yayi wa su Daddy yace zaije ya dawo yanzu ba jimawa saida ya shafi kan Minal da har yanzu take bacci sannan ya fita.






"Wanene kuma wannan Ameer d'in naga suna son juna da Shureim" Mom ta tambaya.






"Ae wannan da kika gani ko bacci baya rabasu wani lokacin,tunda Allah ya bamu Farooq muka wuce London suka had'u da Ameer,tun lokacin abotarsu take harta zama y'an uwan taka komai tare sukeyi sunsha sadaukar da rayuwarsu kan juna" Mom ta fad'a mata tana murmushi.






Itama murmushi tayi don harga Allah taji Ameer ya kwanta mata a rai taji tana sonshi.






**********




Da sallama Ameer ya shiga parlon yanayi yana rawar murna,Abba dake zaune yabishi da ido ya k'asa cewa komai donshi Al'amarin Ameer abun kallone wurinshi ya girma besan ya girma ba a cewarsu,da murna ya zauna kusa da Abba yana fadin"Abba na ina Hajiya ta?".






"In ka gama rawar ba,kai gaskiya Hajiya Halimatu(Mom) tana da d'a nan wurin wallahi" Hajiya ta fad'a tana safkowa daga bene.






"Tamkar da dubu ko Hajiyar Farooq,biyani kud'i. Albishir nasan zakifi kowa son wannan albishir d'in" ya fad'a tare da mika mata hannu alamar ta bashi






"Kajika da shirme first tell me before i give u d gift".




" OK Hajiya ta yau ranar farin cikinmu ne Buddy yaga Family dinsa a yau".ya karashe maganan yana washe white teeth nashi.




"Nakoji me ka fad'a Ameer kai Alhmdllh ,Allah ya karbi addu'armu dukda Farooq baya cikin maraici amma rashin iyalin gaskiya ba karamar damuwa bace garesa ba,yanzu sora Iminat datasa yarona zaman jiranta itama Allah yah bayya masa ita".


(Nikam nace yo Ae iminat ta dade da bayyana Hajiya amma ya sadaukar da ita kam).




Jin Ameer yayi kamar bazai amsaba sannan kuma dai yace " Ameen Hajiya ta.






Mikewa tayi tana fad'in"to bari na shirya sai muje ,ae yau kayi abun kirki Ameer ban tab'a zato ba".




Dariya kawai yayi yana mokewa"before ki shirya let me fresh up ".




Abba kam farin cikinshi yaki misaltuwa yace shima dashi za'a kan.




*********




Tunda ya taho ta tsura mashi ido ko kad'an ta kasa dauke idonta gareshi ,lokutan baya kawai take tunawa lokacin tana yarinya yacce yake kula da ita,tabbas yau taga tsantsar ramar da yayi ga damuwa shimfide fall akan fuskarshi har ya iso gabanta sannan ta dukar da kanta k'asa wasu zafafan hawaye na gangaro.




Har cikin ranshi yaji kukan nata amma ya basar tare da fadin"why ,always cikin kuka zaki zauna Imi?" Ya tambaya.






Saurin d'agowa tayi tana kallonsa jin sunan daya kirata dashi kuma ta Dade tana k'ara son jin sunan a bakinsa murya na rawa tace"Yaya Shureim ka damu da kuka na ,da damuwata ne?".






Yasan tambayar da zata masa dama kenan kallonta yayi yana jin wani mugun sonta na k'ara zagaye dukkan jinin jikinsa,Allah ya sani dauriya kawai yakeyi"Imi u know I love u,amma inaso ki taimakeni na cika abokantakarmu ,soyayyarki fansace ga abotanmu tabbas na jiraki na tsawan shekaru amma yanzu kinmun nisa ,pls ki bani hadin kai kiso Ameer da zuciya d'aya kuma shima yana matuk'ar sonki kece rayuwarsa,sannan ina rok'onki ko bayan raina kada ko tab'a bari ya gane kece Imibat,don Allah kimun wannan indai har gobe ina a matsayina dana sani"ya had'a hannayensa duka biyu alamar roko.






Kallonsa takeyi cikin mamaki ga hawaye shabe Shabe a fuskarta tuni zuciyarta ta fara bugawa da sauri"why destiny always me,I can't take it any more,shin soyayyarka zaka sadaukar ga abota,selfishness "girgiza kai tayi hankalinta na kuma kara tashi ,ganin da tayi ya sunkuyar da kanshi k'asa ya ki kulata.hannu tasa ta dago fuskarsa tana kuma fad'in" look at my eyes ,kullun tunda muka rabu suke marararin kuma ganinka suke zubar da hawaye zuciyata ta kasa karbar soyayyar wani dukdon rike alkwarinka,tabbas indai Ameer son gaskiya yake maka kuma yasan labarinka shimai iya cika maka burinka ne,amma wannan shine tukaicin da zan samu daga dakon soyayyar shekaru,meyasa ban mutu kafin wannan ranar bama"kuka ne yaci karfinta ta durkushe wurin.




Shima duk'awar yayi lokacin har zuciyarsa ta fara masa wani azababban ciwo,"please karki mun haka,ki share hawayenki domin ganinsu yana tab'amun zuciya".






"Hawaye,na tabbata duk duniya ba Wanda ya kaika son ganin hawayena,but am sorry zan maka abunda kakeso domin ka tabbatar har abada kana raina,zan Auri Ameer kuma zan zauna dashi amma Ku fara hak'ar kabarin sakani don tabbas soyayyarka ita zata zamo ajalina" da gudu ta fice daga wurin ,yana kiranta amma ta shareshi ta wucewarta ta fad'a mota rta ikon Allah kawai ya kaita gidansu Amrah.






Farooq kam tarine ya sarkeshi yana saka hannu a baki sai jini ya fara fita,a matukar razane yakebin hannunsa da kallo,a lokacin kuma wayarsa ta fara ringing sunan Buddy ya fito radai a screen din,saurin dauraye hannunsa da bakinsa yayi ya daga wayar cikin dakiya yace"hello Buddy".




"Where are u man,tun daxu munzo da hajiyafa Minal harta farka".




" kai Alhmdllh ,I will be on my way"be jira cewarsa ba ya kashe wayan ya shiga mota.






Allah ka gafartawa iyayenmu ,kayi mana kyakyawan karshe.






*ALK'ALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Pls
Vote
Comments
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*


*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* ✍🏻




*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
126♾130




Bakinshi ya goge ya tada motarahi tare da barin wurin kai tsaye hanyar aaibitin ya nufa cikin k'ank'anin lokaci ya isa iskesu yayi sunata had'a kaya don tuni Minal ta mike ras abunta ciwukane kawai da aka dorata kan drugs akayi discharging nasu zuwa gida, Farooq ya dauki Manal ,Minal da Shureim,yayinda Ameer ya dauki su Momy ,Daddy kuwa suka wuce da Abba,kai tsaye gidansu Manal suka wuce,da kallo Kawai Farooq kebin gidan, ganin gidan da mahaifiyarsa ke rayuwa da y'an uwansa ba wani nisa zuwa gidansu amma be sani ba,shiya taimakawa Manal zuwa cikin gidan ya zaunar da ita a saman chair,hannunsa ta rike tana kallonsa hawaye na safkowa daga idanuwanta don duk taji abunda ya faru,fad'awa tayi jikinsa tana rusa Kuka,shafa bayanta yakeyi a hankali dayi mata alama tayi shiru,a hankali ta furta"Yayana I miss u so much".
Murmushi yayi shima yace "I miss u too my Dear", daidai nan iyayen nasu suka shigo gidan,tare da zama suna tattauna abubuwan da suka faru bayan rabuwa,sosai Mom taji tausayin Shureim da irin rayuwar wahalar da yasha,nan Mom ta isa gaban Farooq tace" Farooq ka zauna tare da Momynka nasan kuna buk'atar kasancewa da juna".






"A'a Shureim zai biku ,innayi haka banyi adalci ba ,naji dadi da abunda kuka mani bani da abunda zan biyaku,kuma ke kinga ba yaro wurinki nabar maki Shureim".






Murmushi hajiya tayi tace" eh zai zauna da Momynshi amma yaukam ya zauna wurinki ya kula da yarin Yar nan Allah ya bata lafiya".




Sun dade gidan kafin Ameer ya daukesu suka wuce gida.




Yaukam farin cikin Farooq be musaltuwa gashi gaban Momynshi,babu abunada sukeyi sai labarin bayan rabuwa sukeyi wani Momy tayi kuka amma tabbas har ranta takejin Son Hajiya sadiya ga yanda ta rike mata amana jin rasuwar mijinta takeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login