Showing 3001 words to 6000 words out of 28816 words

Chapter 2 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt

taimakonmu".




"Ah sosai ma, ae bazamuce komai ba, sai Allah ya biya da haka ake masu kudi da mu mabarata mun huta"Sani ya fada cikin doki.




Haka suke firan jefi jefi har SHUREIM yayiwa sani sallama ya wuce gida.




Sauri takeyi da duban lokaci tasan tabbas SHUREIM na jiranta bayan gidansu lokacin aekinsa ya kusa farawa, tsaki taja hakan yayi daidai da isowar driver da gudu ya fito a motan yana bata hakuri tare da bude mata, batace komaiba ta shiga yaja motar Kai tsaye bayan tabkeken gidansu SHUREIM yayi parking, balle murfin motar tayi ta fito da sauri tahau waige waige, tasan kullun anan take samunshi tsaye yana jiranta, abun kamar wasa ko ina ta duba baya nan idanuwanta harsun ciko da kwallah ta juya zata koma Mota.




Dariya ta kwace masa yana zaune akan iccen dake rife da ganyaye, daga Kai tayi Sama tana binsa da kallo, dirowa yayi tare da kama kunnensa alamun tayi hakuri, binsa tayi da gudu, suka shiga zagaye wurin ta kasa kamasa gajiya tayi ta zauna, ganin hakan yasa ya kuma sakar mata murmushi yazo kusa da ita ya zauna yana maida numfashi.




Kallonta yayi yace"am so sorry Dear, na gwadaki ne naga ya zakiyi".






Dukan wasa ta masa ta dora kanta akan kafadarsa tace"to ae ka gani, ka kusa sakani kuka".






Dagota yayi ya kura mata ido, kusan minti biyu suna kallon juna ido cikin ido, ajiyar zuciya SHUREIM ya sauke ya kauda idanuwansa tare da goge guntun hawayen da suka zubo masa yace"IMINAT".


Kallonsa tayi tace"na'am Yaya SHUREIM".




Kama hannuwanta yayi duka biyu yace"ina so kimin alkawari zaki rayu dani harna mutu, kuma kiyi min alkawari bazaki auri kowa ba duk daran dadewa zaki jirani na girma na samo kudi na aureki, ki soni kinji, ni ina sonki"








Dukar da kanta tayi kasa ta rufe fuskarta da duka hannayenta murmushi dauke kan fuskarta tace"nayi alkawari Yaya SHUREIM".








Murmushi yayi ya dauko wasu abun hannu masu kyau ya saka mata a hannu yace"ki aje wannan, duk daran dadewa zan zo duk inda kike kinji Kanwata"






Janye hannunta tayi wai ita kunya ta ruga da gudu saida tazo daidai shiga tace" I love u too yaya SHUREIM zan jiraka"sannan ta shige Mota tana dariya, har motarsu ta bace basubar dagawa juna hannu ba. Sai lokacin ya shiga gida cike da kewar IMINAT, wani mugun birki ya taka take jikinsa ya soma bari ganin Mama na huci rike da zabgegiyar bulala a hannunta daka masa tsawa tayi tace"zo nan dan uwarka, dan iska ni zaka wulakanta na hada maka wanki ka barsa ka tafi yawo? ".






Baki na rawa yace"Mama na rokeki kimin hakuri zan maki yanzu"




Be rife bakiba yaji an tankadashi zuwa gareta, Abdul ne kuma ya bishi da dariyar mugunta.






Wata irin shaka Mama tawa SHUREIM tahau zabgarsa da dorunar hannunta, ihu yake saki abunka da ba sabanba duk duka sai fatar jikinsa ta daye tayi jawur, bata kojin tausayinsa haka ta shiga zabgarsa saida ta masa lulus ta farfashe masa jiki sannan tabarsa yashe kasa yana nishin wahala jikinsa duk jini, Kada kan Abdul tayi sukayi cikin gidan tana huci.








IMINAT kuwa cike da farin ciki suka shiga gida, cikin parlinsu ta kutsa Kai ta ruga ta dare cinyar Amma tana mata sannu da gida, shafa kan y'ar tata tayi tace"yauwa Mamana sannu da dawowa".




"Amma Papi be dawoba kuwa? "IMINAT ta fada.




"Gani, ko harna makara ban dawo bane"Papi ya fada.




Rugawa IMINAT tayi ya rungume abarsa sannan yace"Albushirinku ga takardar transfer ta fito zuwa America insha Allah company dinmu sun turani can".




Wani irin washe baki Amma tayi tana fadin"Allah mun gode maka yau kuma daga kaduna sai America Kai Alhmdllh".






IMINAT kuwa bata ida daskarewa ba saida taji yace yau da yamma jirginmu zai tashi, SHUREIM kawai take tunawa.






Kallonta Papi yayi yace"baki murna habibty zamu bar kasar".




Murmushi ta kakaro tace"congratulation Papi"tare da rungumarsa.


Jan jikinta tayi tayi dakinta saurin canza Uniform dinta tayi ta dauki paper tayi rubutu jiki, fakaitar idon iyayenta tayi ta fita da gudu Kai tsaye kasan bishiyarnan taje tana haki.






Kallonta sani yayi ya mike zunbur yace"lafiya dai ko IMINAT waya biyoki? ".




Cikin haki tace"babu kowa, Sani kakaiwa Yaya SHUREIM wannan yanzu don Allah". Ta fada tana bashi takardar nan.




Karba yayi zai tsaya surutu ta katseshi da fadin "ba lokaci please ka Kai masa yanzu yanzu ni na koma gida". Juyawa tayi tabi hanya da gudu ta koma gida ta fada kan bed tana haki.








Shiko Sani ya dauka wani abunne ya kwallah da gudu sai gidansu SHUREIM, kasancewar mai gadin gidan ya sansa yasa yabarshi ya shiga, kwance magashiyan ya iske SHUREIM a katifa a razane ya karasa garesa.




"No banason tambaya lafiyata lau, mekaxo yi? ".




Yasan halin SHUREIM sarai shiyasa yaja bakinsa yayi shiru yace"gaji inji IMINAT".






Hannunsa har kyarma yake wurin karbar takardar ya warfare ya soma karantawa.






Yaya SHUREIM ka fito please inaso na ganka a hanya yanzu, don zamu koma America da zama.
Ur wife IMINAT.




Ae kafin kice mai ya arce ana kare Sani ma rufa masa baya yayi, a guje suka nufi titi daidai inda yasan zai ganta ya tsaya tare da waige waige.








*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻




Yawan comment yawan typing




Pls share it


Sharhi nikeso ba sticker ba, ta hakan zaisa na gane labarin n isa inda nakeso
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*







*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https:///kainuwawritersassociation
___________________________________


26♾30.




Kai tsaye gida suka nufa dashi, wani irin tankameman gida ne harta wajensa abun kallo ne, ko ina ka juya masu tsaron gidanne kama daga police daidai sauransu, parking space suka nufa, bayan sunyi parking sannan suka fito ma'ae katane birjik a gidan sai faman gaeshesu suke, Masha Allah shine abunda na fada dana ga parlon da suka shiga fadar tsaruwansa ma kyauyancine dukdai wani abu na more rayuwa yaji a gidan.




Kai tsaye stairs suka hau wani madaidaicin daki suka shiga tare da SHUREIM, a daya daga cikin chairs na bedroom din Alhaji Ismail ya zauna tare da dora SHUREIM akan cinyarsa, HJY Halimatu kuwa kai tsaye toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka, ita da kanta tawa SHUREIM wanka, kallonta kawai yake yana hawaye don Momynshi kawai yake gani a fuskarta, hakuri kawai take basa har suka fito, ta shiryashi cikin kaya masu kyau, tea mai kauri ta bashi yasha sannan ta balli maganinsa ta bashi yasha, kwantar dashi tayi a bed tare da lillibesa shafa kansa takeyi har bacci ya daukesa, sai lokacin ta tashi ta nufi sakin mai gidan nata Wanda ya dade da fita.






Zaune yake a bed tana shigowa suka sakarwa juna murmushi, kai tsaye bisa cinyar sa tayiwa kanta mazauni, rungumarta yayi sosai a jikinsa sannan yace"habeebty ya kike gani game da yaron nan, ya kike tunani idan yana da Mama kamarki, da kuma baba irina, yaro karami yana yawo a titi beda tabbacin samun abunda zaici ko inda zai kwanta balle kuma slipars a kafarsa".






Guntun hawayen idonta ta share tace"hubby Allah be bamu haihuwa ba, inaso ka tambayi taron nan ya zauna tare damu, ina sonshi a gaskiya iyayensa basu kyauta ba".




"Karki damu yanzu zai samu iyaye, zanyi magana dashi gobe"Ismail ya fada.






Next day




SHUREIM be farka ba sai wajen 9 kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka, ya fito daure da towel, zaune ya iske Halimatu ta kawo masa kayan dazai saka, murmushi ta sakar masa, kai tsaye wurin ta ya nufa yace"ina kwana Aunty".




Shafa kansa tayi sannan ta amsa da" lafiya lau, ka shirya kazo kasa muna jiranka".




Da "to"ya amsa sannan ya karbi kayan hannunta ya shirya tsab, sannan ya nufi down stairs.




Zaune Ismail yake a dining yana kurbar tea, kai tsaye wurinsa SHUREIM ya nufa ya gaeshesa, zaunar dashi yayi ya bashi fresh milk yana sha saida ya shanye tas, sannan yake kallon ismail tace"thank u uncle".




Ismail kallon matarsa yayi, ido ta kashe masa alamar ya tambayesa, daga mata kai yayi sannan ya dubi SHUREIM yace"SHUREIM inama ace zaka zauna tare damu kaga bamu da yaro da munji dadi".




Dariyace ta subucewa SHUREIM yana kallon Ismail sannan yace"Uncle zan zauna, nima ina sonku".




Da gudu Halimatu tazo ta rungumi SHUREIM tana kuka tare da gode masa, dukansu biyu ya hada ya rungume cike daso da kauna.






Nan take ya Kira inspector, nan akayi rubuce rubucen komai aka basu SHUREIM, wurin saka sunane yace FAROOQ yakeso a dole suka rubuta masa haka, kuma suma sukaci gaba da kiransa da FAROOQ.




Wanene Alhaji Ismail.




Alhaji Ismail babban dan shiyasa ne ya rike matakai da dama gashi dan kasuwa ya Tara dukiya wacce besan adadinsa ba mutum ne mai tsananin kirki da karamci gason talakawa, matarsa d'aya hajiya Halima sun dade dayin aure saidai, Allah be basu haihuwa ba, dukansu yan Asalin garin Zaria ne.
*******
"Ina fada maka yau kwananshi hudu baya gidannan, kuma an duba duk inda ya dace babu Wanda ya gansa"Mama ta fada.






"To shine me, aeni garama, shege mai zubin mayu daya gudu, kinga yanzu mu keda dukiya, don haka gidansu dake Abuja zamu koma mu kara more rayuwa"Kawu ya fada.






Washe baki Mama tayi tace"to Masha Allah shiko yaje ya karata".




Tafawa sukayi tare da shekewar mugunta, cikin satin suka koma gidan Daddy dake abuja, suka saka murja da Abdul makaranta mafi tsada, jin dadin rayuwarsu kawai sukeyi.




Yanzu kam FAROOQ ya ware ya zama dan gida, ya koma dan gayunsa hankalinsa ya kwanta, yana da kokari sosai don haka Aunty(halimatu) zata wuce dashi London ya ida karatu acan.




Wurin ya tsaru iya tsaruwa birthday party ne kawar hajiya Halima ta hada nan na hango Uncle da Aunty da FAROOQ sunciyo ado sunzo wurin, sosai aka rarbesu, gift ya bawa yaron, swimming pool ya ruga ya fara kwalla Kira"Aunty, Aunty look at me".




Bude baki tayi tana dubansa yayinda shi kuma ya fada cikin ruwan yana sweming, basu suka dawo gidaba sai dare, saida ta tabbatar ya kwanta sannan taje tayi shirin bacci, sai lokacin ta nemi bacci ta rasa ta fara zubar da hawaye cike da kuncin zuciya.






Dafata Uncle yayi yace"Meke damunki kiyi hakuri".




"Ka duba duk yawan al-ummar dake wurin amma FAROOQ ya kirani da Aunty, kowa sai yasan ba d'ana bane, inaso ya kirani da Momy koda so d'aya ne a rayuwa".






Tausayi ta basa sosai ya rungumeta yace"kiyi hakuri, Kada kuma ki sake ya gane bakyajin dadin Auntyn da yake kirani one day one time zai kiraki da Momy".




Kara rungumesa tayi murmushi dauke a fuskarta, haka bacci ya daukesu.






Read and share pls.




*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*




21♾25




*بسم الله الرحمن الرحيم*




*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍ ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________








Tsaye take ta jingina jikinta jikin Amma ji takeyi zuciyarta babu dadi, sha kanta Papi yayi yace"ko baki farin ciki da tafiyar nan? ".




Murmushi kawai tayi, suka juya suka shiga Mota don sun gama komai har Dan'uwansa ya Kira Wanda zai dawo gidan da zama, driver yaja motar Kai tsaye airport suka nufa.




Tunda Motar dake bawa su SHUREIM kudi ta diso wurin Sani ya wangale baki yace"duba can ga samun kudi kuma ga ganin IMINAT".


SHUREIM kuwa don takaici ko kulasa beyi ba, zuciyarsa sai halbawa takeyi, saida motar tazo daidai inda suke sannan danja ta tsayar dasu, bakin glass din motar aka shiga saukewa har yakai zuwa kasa, hannunta ta ziro mai dauke da awarwaron hannun daya saka mata, take ta fiddo fuskarta ta kofar tana masa alama daya karba, ido ya zaro cike da mamaki baki na rawa yace"IMINAT".




Murmushi ta masa ta kuma miko masa hannunta, rugowa yayi zuwa gareta saidai kash kafin hannunsa ya rike nata tuni danja ta basu damar wucewa, kuma take driver yaja ya tafi, kudin dake hannunta ta watso masu tarin yawa, ta fada bisa cinyar Papi tana kuka, lallashinta suka shigayi.




SHUREIM kuwa bin motar ya somayi akan titi yana zubar da hawaye ko hanya baya gani ga fita daga hayyacinsa dukya rude, gam naji motar ta bada, yayinda SHUREIM yayi sama ya fado bisa kan motar ya kuma gangarowa zuwa kasan titin tim haka ya fado kanshi ya bugu da titin ya fado a sume, tuni jini ya wanke masa fuskarsa ko motsi bayayi.hakan yayi daidai da ihun da IMINAT ta saki tare da mak'alk'alle Papi tana kiran sunan SHUREIM.






Wata irin razana tayi tare da taka burki ta zaro idanuwanta, matashiyar matace da bazata wuce shekara 32 kyakyawa daka ganta kasan hutu ya ratsata musamman idan kaga irin kayan dake jikinta da gwalagwalan zabban dake hannunta, tuni mutane sun cika wurin, b'alle murfun motar tayi ta fito da gudu tare da rungumar SHUREIM tana wani irin kuka mai cin rai, Mota tayi dashi da gudu tare da wasu matasan maza guda biyu, figan Motar tayi da gudu ta nufi hospital.


Sani kam tsabar rudu zabgawa yayi da gudu besan ina zai dosa ba saboda tsabar rudu.




Sun isa airport lafiya, driver bai tafiba saida yaga tafiyarsu sannan ya koma cike da kewar Amma da Papi saboda mutanan arziki ne. Tuni jirginsu ya lula sararin samaniya, har lokacin IMINAT ajiyar zuciya take har bacci barawo ya dauketa.




Karfe 9:00 daidai na daran garin suka isa America, Kai tsaye akwai driver an turo daukarsu yayi Kai tsaye ya wuce dasu gidan da aka umurta ya kaisu, gidane madaidaici ya hadu akwai parlo a kasa da kitchen da toilet sai kahau stairs daki ukku ne ko wanne da toilet a ciki Kai gidan ya tsaru, companyn da Papi zaiwa aeki baya da nisa sosai da gidan, daki suka zab'arwa IMINAT sannan Amma ta kwantar da ita kasancewar har lokacin tana bacci, masu aekin gidan Amma ta Tara su hudu ta masu bayanin yadda takeson komai, suma part dinsu na daga cikin gate. Saida su Amma sukayi wanka sannan sukayi Dinner suka kwanta har lokacin IMINAT bata tashi ba.




Nigeria


Kai tsaye likitoci suka karbi SHUREIM tare da yan sanda EMERGENCY suka nufa dashi inda suka shiga taimakonsa na gaggawa, cikin ikon Allah suka tsaida jinin dake zuba daga kansa, ba wata matsala bace take sukayi masa allurar bacci suka kaisa dakin hutu.






Tsaye matar take jikin dakin da aka kwantar da SHUREIM fuskarta tayi sharkab da hawaye, dukta hargitse, cikin sauri ya rikota wani mutum ne da bazai wuce shekara 45 ba, shima kyakyawa dashi, da sauri ta rungumesa tana fadin" Hubby"hakan yasa na gane shine mijinta.




"Shishi kiyi shiru, gani nazo, komai zai tafi daidai". Mutumin ya fada


"Hubby ina tuki ya fado bansan da yaro ba na bigeshi pls kaje ka dubaman yana lafiya ko".


"Ok kiyi shiru". Be jira cewarta ba ya nufi inda yaga Dr da yan sandan nan, hannu ya basu suka gaisa sannan yace shine mijin wadda ta bige yaron"




Kallonsa Dr yayi yace"to Alhmdllh ba wata matsala akanne kawai yaji ciwo, na masa allurar bacci zai iya farkawa ko wanne lokaci insha Allah, saidai matsala d'aya an nemi Wanda yasan yaron ba'a samu ba, kowa yana cewa yaron yana barane a titi beda kowa".


A razana Isma'il ya dago yana duban Dr din yace"kana nufin beda kowa yawo yake a titi".


Inspector Jafar yace"kwarai kuwa shine abunda bincikenmu ya bada, beda kowa bara yake akan titi kuma shi ba almajiri bane"




Tuni tausayin yaron ya kama Alhaji Isma'il, yace"zanyi tunani akan case din, bari na duba yaron".




Daidai zai shiga ya tsaya kallon yaron, zaune yake yana kalle kalle allurar ta sakeshi, tan garas yake saidai bandage da aka daura masa akai, shiga ciki yayi da murmushi ya kama hannun SHUREIM.


"Yaya Aunty, tana lafiya daiko? "SHUREIM ya fada.




"Tana lafiya lau, nine mijinta, muje ka ganta ko? ". Alhaji Ismail ya fada.




Mikewa SHUREIM yayi, rike masa hannu yayi har zuwa wajen Hajiya Halimatu, tana dagowa taga SHUREIM saita saki murmushi tare da hawayen farin ciki rungumesa tayi tace"am so so sorry Dear".




"Ba komai Aunty nine na fado maki ae"cewar SHUREIM.




Saida suka danyi rubuce rubuce sannan aka basu shi suje gida kafin su yanke shawarar data dace nanda 2days zasu dawo, kasancewar kowa yasan Ahaji Ismail babban mutum ne ansan da zamansa.




Shin ya rayuwar SHUREIM zata kasance, wazai rikesa?.




Ya rayuwar IMINAT zata kaya lokacin da babu SHUREIM a tare da ita.




Wanne irin haji Momy take dasu Manal?.




Kudai kuci gaba da bina donjin ya zata kaya, labarine mai sarkakiya, soyayya da tsantsar tausayi.




Yawan comment yawan typing.


Read and share please.




Banason sticker a novel dina, sharhi nikeso donna gane sakon na isa gareku.






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*







*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
31♾35


America.


Zaune IMINAT take da uniform a jikinta hakan yasa na gane cewa tana cikin School ne,ita kadaice a wurin idanuwanta suna kallon kasa,wata kyakyawar yarinyace ta nufota itama ba zata wuce sa'arta ba,zama tayi tare da dafa kafadan ta tace"Sannu sister tun a class ina maki magana bakiji ba".




Murmushi IMINAT tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login