Showing 12001 words to 15000 words out of 28816 words
Chapter 5 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt
hannunsa ,a firgice ya dago ganin motar data nufo Aunty gadan gadan zata bigeta da azabatattar kara yake fadin"Mom,Mom,Mo..........".
Still ta juyo tana kallonsa fuskarta dauke da farin ciki najin abunda take burin jira tsawan shekaru waiyau itace Farooq ya kira da Mom murmushi tare da hawaye ta sakesu lokaci d'aya,shikam nuni yake mata ta kauce taki, iya karfinsa ya rugo ya janyota ,motar ta bige iccen dake wurin.
"Mom kullun kekemin fada na rika lura da hanya amma yau gashi kin tsaya waya da an bigeki kinyi tunanin halin dazan shiga nida Uncle" cewar Farooq,karbar wayar hannunta yayi ya rike mata hannu suka shiga mota,driver yaja sukayi Gida.
Murmushi dauke a fuskarta tace"My Son accident shiya jawo Mani abunda nakesonji tsawan shekaru".
Kallonta kawai yayi ya juya,suna isa Gida ,a parlo suka iske Amrah shiko ansa gaesuwarta beyiba ya shige dakinshi,Mom Ce ta iso wurin ta cike da fara'a.
Kuyi hakuri da wannan pls ,insha Allah inna samu hali zakujini da dare.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
*MAJIDADIN KAINUWA*
Pls
Vote
Comments
Share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
66โพ70
"A'a my Daughter yaushe kika shigo mun fita da yayan naki" cewar Mom.
Dariya Amrah tayi ta duka har k'asa ta gaishe da Mom sannan tace"a'a mom babu komai ban dade da shigowa ba ae".
"Sannu da zuwa y'a Umman taki?" Mom ta jefo mata tambaya.
Cikin sakin fuska tace"Umma na gida ,tace na gaisheki ma".
Fitowar Lafi mai aiki yasa Mom kallonta tana fadin"ladi ki had'amun abincin Farooq na kai masa yanzu".
Cikin girmamawa ladi ta amsa da "to" tayi kitchen donyin aekin da aka sakata.
"La Momy wai ke da kanki zaki kaiwa Yaya abincin gani a zaune,ki barshi bari naje a had'a Momy" cewar Amrah.
Dariya Mom tayi tace"ah lallai yau kice na huta,kinga in masu aeki suka kai yarda aka aje,haka ake daukowa kam".
Dariya kawai Amrah tayi ta wuce kitchen ta iske Ladi karbar aekin tayi ta hada komai a tray ta dauka lokacin data fito Mom bata parlo don haka kai tsaye ta nufi d'akin Farooq inda zuciyarta ke tsananta bugawa dukta tsorace ,knocking ta farayi amma shiru ba amsa.
Tsuka yaja ,yana kwance duka jikinsa yana kallon sama dara daran idanuwansa ya lumshe yana k'ara jin karan buga kofar na shiga har cikin kansa,murya cunkushe dason sanin waye yasa yace"yes come in".
Jiki sanyaye ta tura kofan d'akin ta shiga ,kallo d'aya yayi mata ya kawar dakai gefe ba tare da yace komaiba cikin zuciyarsa yace lallai ma wannan yarinyar zata kawo masa abinci,kuma ma har bedroom dinsa.
Jin maganarta kusa dashi yasashi saurin mikewa zaune yana aeka mata da mugun kallo.
Dakewa tayi tace"Yaya Farooq ga abincin ka nan ,inji Mom ,bari na zuba maka"cewar Amrah .
Wani wawan kallo ya mata,hakan yasa tayi saurin kawar da idanuwanta daga cikin nashi,murya cunkushe yace"u can go,and ya kamata kisan mata basa shigomin d'aki".
Ganin yayi maganar babu wasa,yasa ta mike jiki a sanyaye ta fito.
Shiko Farooq mamaki ne kawai ya cikashi na wannan yarinyar lallaima tanason rainashi dole yayi maganinta ,yanda koda an turota dakinsa bazata kuma gigin shiga ba.
**************
Abdul ne zaune a parlonshi ga kwalbar wine yana sha mikewa yayi tsaye yana karewa abokanansa kallo cikin d'aga murya yace"lallai wannan yarinyar ta tabka babban kuskure a rayuwa ,harni zata wulak'anta,to hukunci mafi sauki shine a baza yara duk inda take a kawoman ita,amma kafin nan dole gobe na had'u da ita school itama zata gane kuranta ne".
Dariyar mugunta suka sheke da ita bash yace"aeni namaga dauriyarka wallahi kwana nawa amma ka tsaya baka nunawa wannan yarinyar darasi ba inda koda sunanka taji saita russuna".
Murmushi kawai yayi ,ya juya tare dajan budurwarsa yayi ciki da ita.
(Ana wata ga wata fa๐ค๐คko meye hukuncin da Abduol zaiwa Zeenart ).
********
Cikin daran ranar Papi da Abba sukayi magana akan auran Ameer da Zeenat sosai Abba yaji dadin karamcin da Papi yayi mashi,anan suka yanke nan da one week zasu saka ranar bikinsu.cike da farin ciki suka rabu da juna da kuma k'ara girmama abotarsu,sannan Abba yace"tohm d'an naka yace ace zaizo gobe insha Allah sai a fad'awa Zeenat din".
"A'a ba komai ae gidansu ne ko yaushe ya shirya baya buk'atar neman izinin kowa kawai yazo" cewar Papi.
Sun jima suna fira kafin suka rabu kowa yayi gida wajen iyalanshi.
Zeenat ko ganin kwanciya bata yi mata,kuma bataso iyayenta su fahimci halin da take ciki yasa ta mike ta soma duba magani,paracetamol ta sha sannan ta saka dogon riga na rover,jin ana knocking kofar d'akin yasa tayi kokarin daidaita natsuwarta tazo ta bud'e kofar,dama Amma tayi zato kuma ita din Ce.
"Kizo Papinki na kira" daga haka ta juya ta wuce.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta wuce d'akin Papi,a zaune ta samesu bayan ta gaeshesa ta duka k'asa tare da fad'in" Papi gani"
"Yauwa Mama na,dama Ameer ne yace,ace miki zaizo gobe saiku fara shiri". Cewar Papi.
Murmushin karfin hali tayi sannan tace" to Papi ba damuwa,ae shima gidansu ne ko bani ,Allah ya kaimu lafiya".Zeenat ta fad'a cike da dakewar zuci.
Albarka Papi yaita saka mata,sannan ta mike tana juyawa wasu zafafan hawaye suka soma zarya akan kyakyawar fuskarta.
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.
Pls
Comments
Vote
Share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
71โพ75
Kai tsaye d'akinta ta shiga, fad'awa tayi akan bed dinta kuka ne ke kokarin kub'uce mata tayi saurin toshe bakinta ,yayinda hawaye kebin gefen kyakyawar fuskarta,ba zato ba tsammani taji an dafata wata iriyar mumunar fad'uwar gaba ya ziyarceta ta juyo a firgice,wata iriyar nannauyar ajiyar juziya ta saki sakamakon ganin fuskar Amrah Wanda a zatonta tasa Amma Ce.
K'ura mata ido Amrah tayi cike da damuwa da kuma son ta gano yanayin da kawar tata take ciki,don harga Allah takejin damuwar amininyar tata ,murya cunkushe tace"Baby meke damunki?,wacce iriyar damuwace tasa kika shiga wannan halin kinga ko yadda kika koma?".
Faahewa ta kumayi da kuka ta fad'a jikin Amrah ,riketa tayi sosai tare da bubbuga bayanta(like my aminiyas ๐คชlol)
Saida tayi mai isarta sannan ta dago jajayen idanuwanta tana kallon Amrah cikin tushewar murya a dishe ta soma magana kamar maison koyon magana tace"Baby Papi yazomin da zance mafi girma a gurina,Papi yana so na auri yaron abokinshi,ke in takai ce maki harsun gama magana daga jiya zuwa yau,dukdadai Ameer shiya ganni yanaso"ta karashe maganar fuskarta fal damuwa.
Dariya sosai ta kub'ucewa Amrah ,kwab'e fuska tayi tana zuba mata harara,ganin abun ba zai k'are ba yasa tajuya mata baya,kunshe dariyar da takeyi tayi tare da saita kanta tace"sorry Baby yanayin da kikayi maganan ne ya bani dariya,amma bazan sake ba ".
Banza tayi mata ,janyo ta tayi suna fuskantar juna tace"ni tambayarki zanyi ,Allah yasa dai kin ansawa Papi?".
Jinjina kai tayi almar eh.
Murmushi Amrah ta saki tare da fadin"Alhmdllh,kinyi kokari ,Baby ki fahimceni bawai ina dariya ne ba don ban damu da halin da kike ciki ba ,a'a kisani cewa farin cikinmu yana tafiya tarene kuma da bakin cikinmu,bazan b'oye makiba a gaskiya naji dadin abunda Papi yayi d'ari bisa d'ari,rayuwa tafiya take ,kwanakinmu karewa suke,tabbas nasan matsalarki amma har tsawan wanne lokaci kikeso ki d'auka wurin jiran Shureim?,Wanda baki da tabbacin shin yana raye,tunda a gabanki aka bigeshi,in yana da rai shin kina tunanin beyi aureba kokuwa be manta dakeba,kada kiji zafin kalamai na,nima nayi haka ne don nemawa rayuwarki mafita,tosu iyayen namu zasu tusaki gaba ne suyita kallo ga masuso sun fito,mafitarki d'aya Baby ki karbi zabin iayayenki hannu bibbiyu bazaki taba dana sani ba,sannan ki tashi tsaye kiyita gayawa Allah damuwarki n tabbatar zaifi maki wannan kukan da zakiyi tayi,gara hawayen su zuba a prayer mat dinki inaga zaifi".
Hannu tasa tare da goge hawayen idonta tabbas zancen Amrah gaskiya ne to amma ya zatayi da soyayyar Shureim da tayi mata katutu a zuciya batabar wuri ko kadan ba,akowanne lokaci kara yad'uwa takeyi a cikin zuciyarta.
Kallonta ta mayar ga Amrah Wanda itama din ita take kallo cikin sanyayyar murya ta soma magana"Baby bawai na kasa daukar shawararki bane,a'a nima inaso nayi haka,saidai cire soyayyar Yaya Shureim a raina tamkar raba gangar jikina da ranta ne,ko kinsan cewa ina rayuwa ne dominshi,duk wani minti na rayuwa idan nayishi ban tunashiba to tabbas bana cikin hayyacina,nayi rayuwa dominshi kuma zan mutu dominshi,SO 'DAYA ne kuma n Riga na bashi inda ya dace kuma bana dana Sani,zuciyata bata tare dani,zan auri Yaya Ameer badon soyayya ba saidon biyayya ga iyaye,ki tayani da addu'a Baby".
Rungume juna sukayi cike da kaunar juna.
(Yah Allah ka bamu kawa ta gari,Ameen).
********
Yau ta kama ranar da Ameer zaizo gidansu Zeenat,sosai ita da Amrah suka tsaya sukayi masa girki na gani na fad'a,cikin kankanin lokaci suka hada komai da zasu buk'ata,a dakin baki nan suka shirya komai,kafin suka hawo sama,phone dinta kirar Samsung ta soma ruri tare da neman agaji,number ne ya bayyana jikin screen din,kallon wayan take da mamaki dondoi ta tabbatar bata da Wanda zai kirata balle a irin wannan lokacin,jiki ba kwari ta dauka sallama dauke a bakinta.
Jin muryar tata yayi har a cikin kwalwar kansa, sosai siririyar muryar tata ta kawatashi,amsa sallaman yayi tare da fad'in"ranki shi dade my wife to be,sunana Ameer".
Wata iriyar zabura tayi a tsorace ko kad'an bata tab'a tunanin wani zai kirata da sunana wife ba,dakewa tayi murya kasan mak'oshi ta furta"ina wuni".
"Lafiya lau,my Angel ina fatan kin shirya zuwan mijin naki"?ya karashe maganar cike da zolaya.
Murmushi kawai tayi ,ta furta" sure".
"OK on my way" cewar Ameer.
"Allah ya kawoka lafiya" bata jira cewarsa ba ta kashe wayar ,jugum tayi tare da dafe kanta da duka hannayenta biyu.
Turo kofar Amrah tayi da sauri tare da fadin"Baby zanje home ,Umma na jirana zatamin aeka,amma banji dadi ba na rashin ganin mijinmu ba".
Murmushi ta sakar mata tace"Baby yanzu ni kadai zan tarbeshi,gaskiya kunya nikeji ni".zeenat ta karashe maganar da yanayin shagwab'a.
Dariya Amrah ta soma tana fadin"kajimin Baby,to inda auran akayi dani zakiyi zaman gidan mijin?,garama ki mike asha soyayya ki bada kai bori yahau Mrs Ameer,ni kinga tafiyata"ta karashe maganar tana sab'ar gyalenta ,ganin Zeenat zata rukota yasata fita da sauri taja kofan ,kai tsaye Amma taje tayiwa Sallama sannan ta wuce gida.
Mintina kad'an Lami mai aeki ta soma knocking kofar dakin .
D'an tsaki taja a dakile tace"come in".
Cikin nutsuwa ta shigo d'akin har k'asa ta duka sannan tace"Aunty zeena bak'in sun iso ,an saukar dasu".
"OK zaki iya tafiya ina zuwa" ta fad'a a takaice.
Mikewa Lami tayi ta fice.
Saida ta mike naga kwalliyarta ,Riga da siket ne na material red sai pattern din brown dinkin yayi matukar yi mata kyau sosai,simple makeup ne a fuskarta amma ta haska abunka da farin fata,gyale brown ta yafa ta kuma feshe jikinta da turare sannan ta fito ,kai tsaye d'akin da aka saukar dasu ta dosa,saidai kuma me ta nemi natsuwarta ta rasa ga tsanin fad'uwan gaba dake damunta soma karanto innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai takeyi har tazo kofar dakin,jiki sanyaye ta shiga bakinta dauke da sallama .
Amsa sallamar Ameer yayi,tunda ta shigo ya kafeta da idanuwa har ta zauna nesa dasu,shigo gogan naku kansa a k'asa be dagoba ballan tana yace wani abu.
"Sannunku da zuwa ya hanya?".
" lafiya lau,Alhmdllh yah muka sameku"cewar Ameer.
"Alhmdllh lpy " kawai ta iya fad'a.
Mikewa tayi tare da zuba masu drinks a cup tace"bismillah"tun d'azu bakusha komai ba.
Sai a sannan Farooq ya d'ago kyawawan idanuwansa ya dube tare da fad'in"na gode Mrs Ameer".
Wata iriyar zubawa tsikar jikinta tayi sanadiyar had'uwar da idanuwansu sukayi,da kyar ta samu ta koma mazauninta tana maida numfashi da kyar da kyar.
Shikam Ameer kurbar drink din yayi sannan yace"kamar yadda kika sani sunana Ameer Jabir,a gaskiya tun ranar dana fara ganinki a mall naji na kamu da sonki sbd natsuwarki da kuma hankalinki donko a shigarki mutum zai fahimci kin fito daga gidan mutumci ne,tun daga lokacin kuma kikaimin sata, duk inda nake tunaninki ban kuma San ina zan sameki ba".
Zaro ido tayi hankalinta tashe ta dafe kirji baki na rawa tace"Sata kuma,mena sata".
Yanayin yanda tayi magana ya bashi dariya ,saida yayi mai isarsa sannan yace"satar zuciyata mana,shine na biyoki na karba".
Sai lokacin Farooq yayi murmushi yace"itama bata tsira ba kenan".
Zeenat kam karkarfar ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi donta lura Ameer din akwai barkwanci.
"Tun daga lokacin nasa aka bincikomin komai na dangane dake,saida nazo neman izini na gane cewa ashe y'ar gida Ce,Zeenat banaso ki duba dangan takarmu ,karki matsawa kanki,babu dole nafiso ki soni don Allah badon alfarmar zumuncinmu ba,ki nutsu ki bani amsa".Ameer ya karashe maganar.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe๐คฒ๐ป
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Vote
Comment
Share
Maji dadin kainuwa
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
81โพ85
This page iz dedicated to Kainuwa writer's association
Da sallama Amrah ta shiga room din mahaifiyarta ,jefar da bag dinta tayi tare da fad'in "ashh na gaji da yawa".
Harara Umma ta zabga mata sannan tace"ba dole ki gaji ba,kina can kina taya wata gyaran mijinta ke ko ko oho tunda baki kishin kanki ko".
Ko kad'an bataji dadin maganar Umman tata ba ,basarwa tayi tare da fad'in" Umma kin kirani".
"Eh ba dole ba,na kiraki ne ki fad'amun wanda kike so,don ba zuba ido zanyi ba ,wannan yarinyar tayi aure ta barki ba"cewar Umma.
" oh Umma,meyasa kikeson canza hali bayan ba haka kike ba,kina matukar son Zeena ada,Umma ko kin manta aure lokaci ne"ta jefo mata tambaya.
Harara Umma ta gallah mata tace"to sannu wacce ta yankewa wa'azi cibi,Ce maki nayi yanzu ban sonta?, kawai aure ne bana so tayi ta barki ,kina yawan bin gidanta".
Murmushi kawai Amrah tayi sannan tace"nikam Umma mutum d'aya na gani na bawa SO 'DAYA,yafimin komai gani d'aya na kamu da sonsa, ba kowa bane Umma daya wuce Yaya Farooq saidai shi kwatakwata hankalin sa baya kaina ,na lura yana dajin kai,Umma a matsayinki na uwa kuma mai sona farin cikina d'aya ki bani shawarar ya zanyi ya soni"ta karashe maganar a raunane.
"Alhmdllh,Allah na gode maka,ashe har yanzu zan had'a zuriya da Hajiya Halima,ki kwanatar da hankalinki anyi an gama ,babu abunda zai gagara" Umma ta karashe maganar da zallar farin ciki.
Dariya Ce ta sub'ucewa Amrah ,rungume Umma tayi cike da tsantsar farin ciki.
********
2weeks later.
Yanzu kam ba laifi Zeena ta saki ranta,domin Ameer yana da saurin sabo ga barkwanci uwa uba yadda yake tarairayarta kullun yana cikin kiranta da bata kulawa ta musamman,tabbas tasan ba son Ameer takeba amma babu tsanarsa a ranta ga wani girmansa da take gani ,yana da k'ima a idanuwanta lallai shid'in mutumin kirki ne ta yarda da wannan baya da halin mazan zamani.
Cikin sauri ta fito sanye cikin White gown ta matukar yi mata kyau veil black da jaka da shoe ta saka tayi matukar kyau sosai dukda babu tarkacan makeup a fuskarta ,hannunta rike yake da handouts, cikin sauri ta shige motarta ta cillata akan titi a guje don sosai tayi latti yau,Zeenat kenan matashiyar yarinya.
Cike da fara'a yake shirinshi lokaci zuwa lokaci yana sakin k'ayataccen murmushi yayi kyau sosai cikin shigarsa ta kananun kaya.
Zuba masa ido bash yayi ganin irin yanayin farin cikin da yake ciki kasa jurewa yayi saida yace"my friend waiyau me ya kawo wannan farin cikin kodai ta samu ne?"Bash yayi tambaya.
Daure igiyar takalminsa yake sai da ya nisa sannan yace"ranar daukar fansa kashi na d'aya",yana fad'an haka ya mike tare da zurar key din motarsa.shima bash din binsa kawai yayi suka wuce scul kai tsaye ,cikin minti kalilan suka isa, kai tsaye capteria suka nufa don yana da tabbacin dole su had'u anan.
A gajiye likis suka fito lecture,shafa ciki Amrah tayi tare da fadin "ashhh wallahi yunwa nikeji sosai,muje muci abinci".
" kamar kinsan mezance kenan ,balle na hango twin sis tana zuwa,lecture din yau dukta kwashe mana abinda mukaci"Manal ta fad'a da muryar tausayi.
"Amma wallahi Ku raggaye ne,duka awarmu nawa, acici kawai daku" zeenat ta fad'a tanayin gaba.
Tare suka tafi harda Minal,kowa abinda zaici ya fad'a,Zeena lemu kawai ta buk'ata,fira kawai sukeyi ,ko kad'an bataga Abduol a cikin wurin ba,shikam taku yayi har zuwa inda take yad'an rangwafo tare da fad'in "am really sorry my Friend, ki yafemin abunda nayi miki pls".
Had'e fuska tayi kamar an saukar mata da mutuwa,ganin haka yasa yayi saurin yin baya tare da sakar mata murmushi,chair dinshi ya koma yana kare mata kallo.
" kunga ni Ku sameni a mota,bazan iya jurar zama wuri da irin wadannan mutanan a wuri ba"Zeena bata jira cewarsu ba tayi gaba.
Wani d'alibi dake bayanta ya kwashe da dariya tare da fad'in "call me a pool".
Ras gabanta ya fad'i,duka wurin suka dauka da ihun" call me a pool".
Kafin kice me,sun zagayeta,tuni idanuwanta suka ciko da hawaye,kallon tuhuma take aekawa Abduol dashi,shigo dage kafad'a yayi tare da murmushi ya fice yabar wurin.
Da gudu itama ta fito tana kuka sosai kamar zata sike,ko ganin gabanta batayi.
Fitowarsa kenan daga mota,jin abu yayi ya fado mashi,jin tana kuka kamar zata sike yasa