Showing 18001 words to 21000 words out of 28816 words

Chapter 7 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt

*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)





*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
86♾90




Kallonsa takeyi idanuwanta taf da hawaye ga wani irin yanayi da take tsintar kanta duk lokacin data had'u da wannan lecturer din nasu zuciyarta na raya mata abubuwa da yawa a kansa amma ita kanta ta kasa fahimtar ko mainene ,sunkuyar da kanta k'asa tayi zuciyarta na mata kuna dajin ihun da students keyi a kanta da kiran call me a fool.










Girgiza kai Farooq yayi tare da cire mata paper din dake bayanta ,Yana kallonta kamar mai son gano wani abu cikin kakkausar murya yace"silent "take sukayi tsit kowa ya fara kama gabansa,hakan kuma yayi daidai da isowar su Amrah wurin,ras ras haka zuciyar Amrah ta buga saurin dafe kirjinta tayi tanajin zuciyarta na niyyar bugawa lokaci d'aya wani irin mugun kishi takeji na ganin Farooq rike da Zeena ,da sauri ta juya su Manal na kiranta amma taki sauraransu,to she bakinta takeyi gudun kada ihun da take shirin kurmawa ya fito fili bayan wata bishiya ta zauna tare da fashewa da kuka jin d'aci takeyi har cikin makoshinta ga zuciyarta data tsananta bugawa,Meye hadin My Farooq da Baba na?,tambayar da takeyiwa kanta kenan amma ba amsa.








" if ur ready zaki iya neman y'ancinki ki shigar da case dinnan ga hukumar makaranta,kodon soyayyar dake tsakaninki da Boddy na zan iya tsaya maki don neman y'ancinki"Farooq ya fad'a yana kallonta.








Share hawayen fuskarta tayi murya dishe tace"ba damuwa ,bana buk'atar ramuwa,kuma karka fad'a masa"tana zuwa nan ta jenye jikinta tayi mota,a mota tafiya kawai take amma ita kanta tasan ikon Allah ne kawai ya kaita gida bawai don tasan ina take dosa ba.








********


"Ae ba wannan ne matsalarba,domin ni kaina Amrah ta kwantamin a rai,saidai shifa Farooq akwai wacce yakeso tsawan shekaru da dama" Momy ta fad'a tana kallon Umma.








"Kikace,akwai wacce yake so?,to suna tare ne?,kaji ikon Allah" Umma ta fad'a a dabarbarce.








Jinjina kai Momy tayi tace"basa tare,amma itace a zuciyarsa,sai dai kuma ae komai bazai gagara ba ,bari Daddynshi ya dawo daga tafiya zan masa magana,zamu nemi amincewarsa".








Wata karkarfar ajiyar zuciya Umma ta sauke tare dajin wani sanyi na ratsata .




Yini d'aya cur anan gidan rayishi sunata tsare tsaren yadda Farooq zai amshi Amrah a matsayin matarsa.




A gurguje pls


3weeks later.




Babu laifi yanzu kam Zeenat tadan saki jikinta da Ameer bawai kuma donta fara sonshi ba a'a,saidon shi mutum ne mai barkwanci da Shiga rai gashi yana nuna kulawarsa akanta koda wanne lokaci cikin kula da ita yake,amma babban abunda ke damunta mamadin ta rage son Shureim sai ya kama kullun soyayyarsa kara nunkuwa takeyi a zuciyarta.








"Yaune last day,bana buk'atar korafi ,duk inda take inason a kawo man ita,bana buk'atar bacewar aeki" Abduol ya fadawa yaransa murya cunkushe.






Kallon juna sukayi tare da fad'in "OK sir"sannan suka fice don cika aekin da aka sakasu






*******


Lek'a mutanan dake shigowa da manyan jakukunan da akwatina sunayin gefan bak'i,sai yanzu hankalinta yayi matukar kara tashi juyowa tayi da sauri ta fad'a jikin Amrah tana fad'in" yanzu na rasa Yaya Shureim dina kenan,kina kallo bikina zasu saka yau,na shiga ukku na".






Saurin rife mata baki Amrah tayi tana fadin"meye haka kuma,ki daina tada hankalinki ,dama haka Allah ya rubuta ae".






"Why ,why Destiny always me"


Kallonta kawai Amrah tayi ganin dai da gaske ta soma fita hayyacinta yasa ta soma karanta "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"


A hankali Zeena ta soma binta tana maimaita duk wasu addu'o'in da Amrah keyi,a haka har wani nannauyan bacci yayi nasarar yin gaba da ita,gyara mata kwanciya Amrah tayi tare da lullub'eta.








************




"Kaji marar kunyan yaro,ni sakeni" hajiya ta fad'a tana ture Ameer daga jikinta.








Kallonsa kawai Farooq keyi ya rasa wanne irin so Ameer kewa Zeena duk yabi ya zare lokaci d'aya ba kaman yau d'aya kama ranar saka bikinsu ne,nisawa yayi yace"Allah ma yasa a saka Shekara a bikin".






Waro idanuwa Ameer yayi tare da fadin"Amma wallahi bakayiba,gwauro kawai ,ba bakinka ba,ni wallahi sati ukkun nanma da aka saka yamin yawa,akasa shekara ae mutuwa zanyi,kasan wacece Zeena wurina itad'in bugun zuciyatace kuma rayuwata ,ina matukar sonta zan iya sadaukar da komai nawa dominta ,harta raina".








Iya zallar gaskiya da tsantsar soyayya mai zafin gaske ita Farooq ke hangowa kwance a idanuwan Ameer,besan yaushe soyayya tawa Buddynshi wannan mugun kamun ba.






"Ohni Ameeru yaushe ka zama haka,bako kunya,niko kaga d'ana Farooq da kunyarsa ras a idanuwansa bayayin abunda kakeyi,kuma ni d'ana ba gwauro bane,kaga tafiyata ni wannan kalaman naka sai Momynku ita ta saba,ni kaga nayi gama".






Dariya suka tuntsure da ita ,yayinda Ameer ke kiran " Hajiya,Hajiyata my love".






"Ungo wannan kaci gidanku nace,yaro ya fetsare " Hajiya ta fad'a tare da yiwa Ameer dak'uwa.








Shiru Farooq yayi take kewar mahaifiyarsa ta dawo masa fall a rai ,bawai donya rasa gata ko rashin wadda zata maye masa gurbinta ba a'a ,sai don Uwa Uwa Ce,duk lokacin da Ameer yake tsokanar Hajiyarsa sai yaji inama yaga Mom d'inshi da twins sisters nashi,ya fad'a jikin Mom dinshi ya fad'a mata damuwarsa koda zaiji sanyi,sai dai yana sawa ranshi inda rai ashe da rabo.








Dafa hannunsa Ameer yayi "bana so kana damuwa irin haka,muci gaba da addu'a komai zaizo da sauki insha Allah,tashi muje kiran Momy kada taga mun jima".




Murmushi kawai Farooq yayi tare da mikewa suka nufi gidansu,a parlon Daddynsa nan ya samesu gaeshesu sukayi tare da zama a gabansu.






Gyaran murya Daddy yayi sannan yace" na kiraka ne Farooq saidon na Baja shawara,zama bayayi haka ba aure a matsayin da kake yanzu,mezai hana kayi aure,dukda nasan matsalarka amma in Allah yasa da rabo sai ka kara da wacce kakeso d'in ,tunda Allah be haramta maka ba".






Kamar saukar aradu haka Farooq yaji maganar Daddy na ratsa kunnuwansa,a firgice ya d'ago idanuwansa Wanda suka sauya launi lokaci d'aya yana kallon Daddy.






*ana wata ga wata*






Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe.








*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻






Vote
Comment
And share






Follow me an Facebook at Maryam Ismail (majidadin Kainuwa)
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)





*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook Maryam Ismail(maji dad'in Kainuwa)


101♾105.






Da wani irin fitinannan gudu ta iso cikin gidansu ko saita parking mota batayiba ta fito a guje,zubewa tayi akan carpet din tsakar d'akin wani irin d'acin zuciya takeji har cikin kwalwarta ,tuni hawaye ma sun daskare ta nemesu ta rasa jin numfashi na gagarar shak'a gareta yasa ta kwanta k'asan carpet din tana sauke ajiyar zuciya,bata wani jimaba wani b'arawon bacci ya saceta anan wurin,ga wani zazzafan zazzabi daya rufeta.








Bangaren su Zeena kuwa tafiya sukayi mai nisa kafin suka iso wani tankameman gidan gona dake wajen gari,ba jimawa suka shige cikin gat din gidan,ganin haka yasa Farooq fitowa a motarsa da sauri waige waige ya somayi da neman hanyar dazai shiga gidan,mafita d'ayace shine ya dira ta bangon bayan gidan,wayarsa ya cusa cikin aljihunsa ya d'are saman bangon gidan kafin ya dira,sosai gonar keda girma soma tafiya yayi dason gano ta ina sukayi wata razananniyar k'ara yaji ta doki dodon kunnenshi kuma muryar Zeenat Ce,ba shiri ya zunduma da gudu yana bin inda yake jiyo sautin k'arar tata.






Kokarin janta sukeyi zuwa gaban wani matashi daya juya baya yana sanye da bakaken kaya,daidai lokacin kuma Farooq ya iso wurin tare da labewa inda zai hango komai,damkar yalwataccen gashin kanta black yayi tare da kara ingizata gaba,tuni jijiyoyin kanta suka fito radau fuskarta tayi jawur abunka da farin mutum wurgar da ita yayi ta fad'a daidai saitin wannan mutumin ,hannunta tasa tare da tokare k'asa bata bari kanta ya ida isa k'asa ba,hankalinta tashe da sanin mezaiji ya dawo jin muryar wannan mutumin na fad'in"ohhhh nice job".








Koda bata d'agoba tasan ko wanene muryarsa kawai ta shaida mata hakan,cikin dakiya ta dago idanunta tare da mikewa tsaye suka shiga kallan kallo tskaninta da Abduol,dariya ya tuntsire da ita tare da soma zagayeta yana furta"y'an mata adon gari,gaskiya kin bani mamaki dahar kika bari wannan mazan suka iya dakkomin ke duk zafin kan".








Murmushi mai cike da kuna ta saki dakewa tayi ta juyo tana kallonshi ido cikin ido ta d'aga hannunta ta hada babban yatsanta dana tsakiya suka bada k'as k'as"idan bacci kakeyi gara ka farka Abduol,ashe kaidin matsoraci ne wlh kaban kunya daka rasa aikinyi sai nasawa a dakko maka Mace, idan zarra kake buk'ata kaje ka nuna karfin ikonka ga d'a namiji sannan kake cikakken jarumi,sannan ina gargadinka da tab'ani domin zaka taso wutar da zata konaka da kanka, rigimar da duk danginka bazasu iya tare maka ba"ta kareshi maganar tana zabga masa Uwar harara










Shu'umin murmushi ya saki "oh I see zanga iya ka ikon uban naki,ked'in y'ar uban wacece a garin Abuja,yanzu zanyi kaca kaca da rayuwarki naga abunda za'ayi,saidai kuma rashin tsoronki ya burgeni y'an mata" ya karashe maganar tare dason shafo gefan fuskarta,wani wawan mari ta sauke mashi akan kumatunsa.








A take zuciyarsa da komai na jikinsa ya tsaya cak,tunda yake duniya ko mahaifanshi basu tab'a dukanshi ba balle mari(yo Abduol iyayen da baka dauka da araja ba).




Hannuwansa duka biyu yasa tare da ingizata ta fad'i kasa dukawa yayi tare da shaketa ,yasa hannunsa d'aya a bayanta ya fizge zip din dake jikin rigarta ,wani karfine taji ya dirar mata ta hankade shi ta mike tare da soma gudu tana neman wurin boyo,yayinda su kuma suka take mata baya.






Saurin daukar wayarshi yayi da Ameer ke kira"eh muna ciki,ka diro kawai malam"be jira ansarsa ba ya latse wayar tare da fitowa kai tsaye ya tari gaban Zeena,ita kuwa zuwa lokacin ta jigata karfinta ya gama karewa fad'uwa tayi daidai saitin kafar Farooq.








Sai lokacin ya d'ago kyawawan idanuwansa domin kallon shugaban Wanda yasa aka daukota tun d'azu yakeso yaga fuskarahi be samu dama ba,a matukar razane tare da k'ara waro idanuwansa don tabbatarwa da kanshi cewa Abduol ne,saidai ya lura Abduol din hankalinsa baya jikinsa ya kasa ganesa.








Kallonsa ya maida ga Zeena dake kwance a k'asa idanuwansa basu sauka ko ina ba,sai akan kyakyawan farin bayanta da yake tas sai wani Jan tabo kamar kwanciyar jini a jiki,dafe kansa yayi yana fadin"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,meyasa haka ?meyasa?"tabbas wannan iminat dinshi ce saidai tazo mashi a lokacin daya kamata ya sadaukar da ita,bazai tab'a mance wannan tabon nata ba,dafe kai yayi tare da zama akan wani Dan dakali dake bayansa,kirga ya farayi "1,2,3" tare da had'a hannayensa suna bada k'as k'as, cikin firgitarwa ta mike tsaye tana binshi da kallo a galabaice tana son karasawa wurinsa,ga bakinta dake k'yarma tana son furta wani Abu,dajan kafa ta iso gabanshi yayinda fuskarta ta koma kamar anyi ambaliyar hawaye zuciyarta na dad'a bugawa da sauri da sauri.hakan yayi daidai da isowar Ameer wurin saidai ya tsaya cak donjin me take fad'a.




Cikin kuka take fad'in"wallahi kaine Yaya Shureim dina,kuma kacemin bakai bane,tun daga sauyawar bugun zuciyata na gane,nicefa Iminat dinka farin cikinka".








Wata Uwar tsawa ya daka mata tare da fad'in"ki dawo hayyacinki Zeena ,ni sunana Farooq ban kuma San wata Iminat ba,nazo nanne domin darajar abokina".








Wata razananniyar k'ara ta saki tare da sulalewa k'asa a sume,kafin takai k'asa tuni Farooq da Ameer sun kawo hannuwansu a tare domin riketa karta bugu da k'asa,hannuwansu ne ya had'u ta fado tsakaninsu,suka shiga kallan kallo.






Fatan Farooq d'aya Allah yasa Ameer beji me Zeena take fad'a ba.








Ganin mutane na kara yawa a wurin yasa Abduol da yaransa guduwa,sukabar gidan.








*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*








*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻








Pls


Vote
Comments
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)





*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook at
Maryam Ismail (maji dadin Kainuwa).


111♾115




Shikam Ahmad yana zuwa gida a parlo ya samu hajiya,wani shek'akken kallo ta masa tace"halan har yanzu baka girma ba,ina ganin ka kara hankali ansa bikinka amma abun sai kara tuburewa yake ke Ameeru".








Turo baki yayi"nifa Hajiya basan Amirun nan nake ba ,kin sani, gidansu Zeena naje ni bata da lafiya na dubota"ya karashe maganar yana zuba wa Hajiya ido.








Sake da baki take binsa da kallo ta rasa yaushe Ameer zaiyi hankali kodon yana auta oho"lallai wannan had'i beyi ba,Allah sarki Zeena y'ata zatayi fama".




Murmushi kawai yayi ya mike ya wuce d'akinshi,saman makeken Bed dinsa ya yarda zango ,idanuwansa na kallon sama yayinda yasa hannuwansa yayi pillow dasu wata iriyar soyayyar Zeena ke ratsa shi ya rasa ya zaiyi ,ganin ba mafita yasa ya tashi tare da dauro alwala ya soma Sallah duk yinin ranar a d'aki yayi shi har abunci anan yaci.






*******




Kamar a mafarki haka take jiyo kamalan Shureim suna mata yawo a kwakwalwa a razane ta farka tana zazzare idanuwa ,cikin sauri Ammi ta riketa tana tofa mata addu'o'i dukdon ta natsu saboda ta lura kwata kwata bata cikin hayyacinta,wani irin kuka ta fashe dashi tare da rungume Ammi tana fad'in" Ammi na wallahi na ganshi shine Ammi na,amma yace bai ba shi bane wai be ganeni na"wani kukanne yaci karfinta ta danne baki tana zubda kwallah"Ammi don Allah kice yazo gareni ,wallahi ban iya rayuwa babu shi,inya barni mutuwa zanyi Ammi na".








"Sai dai ko ki mutu ina gaya maki wannan ,soyayyar da nake maki bazatasa na zama k'aramin mutum ba,ki rok'i Allah ya cire maki soyayyar wannan yaron ,kima fara son mijinki Ameer don aure anyi an gama,kuma ina mai Jan kunnenki da kada ki bari Ameer ya gane komai ko yaji labari na fad'a maki wannan ko sunan Shureim naji kin kuma kira zakiga yacce zamu kare"Papi ya fad'a murya murtuke babu alamun wasa.








Sake da baki haka takebin Papi da kallo ,yayinda zuciyarta ke wani irin bugawa kamar tayi tsalle ta fito daga kirjinta" pa.....pi"kamar mai koyon magana haka ta kira sunansa.




Ko kallonta beyi ba ya wuce warsa,aekam kamar an tunzurata ta kuma fashewa da kuka tana fad'in"na dauka kune na farko da zaku iya dawo da Yayana gareni aduk Inda nake,Ammi bani da wata kawa data fiyemin ke,wallahi na rayune sabodashi ban tab'a zaman awa ba tare da tunaninsa ba kullun shine a rai,Ammi Ku tausaya min don Allah ".








" Zeenat bani da ikon yanke hukunci akan abunda mahaifinki yace kinsan me zakiyi ?,komai kikaga ya faru da mutum to an rubutashi dama can a allon kaddararshi kiyi hakuri ,mai makon ki zauna kina kuka da damuwa,gara ki zubar da hawayenki akan tabarmar sallarki ki mika lamuranki ga Allah,tashi ki wuce ciki.








2weeks later.






Tafiya yakeyi yasha ado cikin blue din Shadda dinkin yayi matukar k'arb'ar jikinshi dukda kallo d'aya zaka masa ka gane tsantsar ramar da yayi ya kuma d'anyi duhu ga y'ar suma daya tara, shi yabarta ne saboda tsabar damuwa bayaso yayi aski amma sai ta haska fuskarshi yayi Kyan kallo,tuk'i yake yi a hankali daga asibiti yake yaje ganin Dr.


Itakam hankalinta kwance take tafiya ko kad'an bata ga Mota na tahowa akan titin ba,hurn yake mata amma ina abun yaci tura tuni karar motar ta rud'ata ta rasa ina zatayi,ji kake keeeee ya tashi da ita sama ta gangaro saman glass din motarshi ta fado kasa a sume.








"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un" shine abunda Farooq yake fad'a lokacin da kansa ya bugu da aitiyari duka ya rasa kwarin jikinshi ,dakyar ya iya bude motar tare da fito da kafarshi waje yana niyyar fitowa.








"Wayyo Allah na shiga ukku na,ji yadda ta koma wayyo Minal d'ita kada ki tafi ki barni don Allah " a guje Manal tazo ta rungumeta tana ihu tare da jijjigata tana kiran sunanta.








Dafe kai yayi ganin yadda take zubar da jini hankali tashe ya sureta,yayinda Manal ta biyoshi suka shiga Motar tana ta wani irin kuka ta rungume Minal,da wani irin gudu ya juya zuwa asibitin tun Kafin ya iso ya kira Dr Nasir,suna isowa Nurse's suka dauketa kan gadon mararsa lafiya sukayi Emergency da ita.






Zama yayi tare da dafe kai yana tunanin Mae yake tunani haka harya buge y'ar mutane,sai lokacin Manal ta gane Barrister Farooq ne lecturer dinsu Minal ,amma d'azu bata gane komai.






"Kiyi hakuri dan Allah wallahi bada Sani ba na bigeta,ita ta shiga hanyata,kuma nayi kokarin kyauce mata amma abun yaci tura,ina ne gidanku".Farooq ya tambaya cike da kulawa.






Sai lokacin tunaninta ya bata data kira Momy amma kwatakwata da hankalinta be kaiba.








*Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe*






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻






Pls
Vote
Comments
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ⚜💕⚜💕⚜💕⚜💕⚜
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)





*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook
Maryam Ismail(maji dadin Kainuwa)


106♾110


Saurin Janye hannunsa Farooq yayi yana kallon Ameer.




"Zaman me mukeyi anan Boddy ?,ka tashi kaja mota mu kaita Asibiti don Allah kada na rasata itad'in rayuwa tace"Ameer ya fad'a murya cunkushe.




Shikam Farooq ji yayi ya rasa dukkan wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login