Showing 15001 words to 18000 words out of 28816 words
Chapter 6 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt
ya tsurawa paper din fake manne a bayanta tare da karanta abunda ke jiki ga d'alibai sunata fad'a da karfi.
Jin ta jikin mutum yasa ta saurin d'agowa.
Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe.
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Vote
Comment
Share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
76โพ80
Hawayen dake mak'ale a idanunta tayi saurin gogewa don bata buk'ar su gani,wani irin bugawa zuciyarta keyi da sauri sauri Wanda ke kusa da ita ze iya jiyo gaka daurewa tayi ta soma magana a hankali"babu komai Yaya Ameer na amince ,Allah ya shige mana gaba,babu Wanda yayi min dole".
Wani irin murmushi ne ya subucewa Ameer ,don jin soyayyar Zeena yake har cikin ransa a hankali ya furta"Alhmdllh,amma naji dadi sosai my princess ".
Haka sukaitayin fira jefi jefi mafi aka sarin firan Ameer keyinta gashi da tsokana,shikam Farooq har suka gama firansu be kuma saka masu baki ba,saida suka shiga gaishe da Amma,sun jima a gidan kafin suka tafi bayan ya cika Zeena da abubuwan arziki don sosai yayi mata siyayya .
Da k'yar take taka kafarta hardai ta samu ta iso gaban tankameman photon Shureim kamar ayi masa magana ya fito,sosai hawaye suka soma zuba daga idanuwanta,dukawa tayi gaban pic din tace"Yaya Shureim banyi zaton zaka iya daukar wannan tsawon lokacin ba tare daka zo gareni ba,na rayu da soyayyarka amma sai gashi yanzu na gagara rike maka alkwarin dana dauka maka,kuma hakan baya nufin ba bude zuciya wa wani ne,ka yafe mani yau na karbi soyayyar wani bayan taka,ka yafemin" daukar pic din tayi ta turashi bayan bed ta fad'i a wurin tare da fashewa da matsanancin kuka.
*********
"Ohni Aysha fito ,fito" Kawu kabir ke fad'i yayinda ya shigo a rud'e sai zufa yake ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Cikin sauri Mama Aysha ta fito a matuk'ar razane hawaye shabe shabe a fuska tana fad'in"na shiga Ukku ni Aysha ya zanyi da wannan abu".
"Ke dallah ni ki saurareni,ba kuka na tambayeki ba,customs sun kama mana kaya harna million 30,Wanda nayo order,wannan tashin hankali har ina".kawu kabir ya idasa maganar a rud'e.
Kuma fashewa da kuka Aysha tayi tana fad'in "wannan Allah turene,ya zamuyi,kaga yanzu Sule ya kirani a waya duk wata kaddararmu dake kauye da runbum da aka Tara amfanin gona ya kama da wuta kur'mus".
A razane kawu ke kallonta tare da dogon salati hankali tashe yace"yanzu ki daukomin jakar kudin nan dana baki ajiya muga kuma ya zamuyi dole mu tashi tsaye".
Cikin gaggawa Mama ta shiga d'akinta don daukar kud'in da ta ajiye,saidai me kud'i sukace daukeni inda kika ajiye,hannu kawai ta daura aka duka dakin saida tayi mishi bazabaza babu jakar kud'in nan babu alamarta ,da gudu ta fito tana fad'in" Alhaji banga jakarba,wallahi sun dauketa,kama ni ba shigarmin d'aki akeyi ba"
Wata Uwar tsawa Kawu ya daka mata ,tare da fad'in "harkin isa,kice haka ke ko yaranki zaku dauka INA Murja da Abduol?".
Kafin ya kuma magana Murja ta shigo gidan fuska daure,3quater ne jikinta sai T-shirt kannan yasha gashin doki ,shigowa tayi ko sallama babu,bata ko kalli itayenta ba ta nemi chair ta zauna tana maida numfashi.
" haba Murja daga ina kike, kwananki hudu baki gida,babu kuma labarinki"cewar Mama Aysha.
"Ke wannan ta dama,ke gidan ubanwa kikaimin kud'i ,shegu masu halin beta ko Ku fiddomin kudi kona sa a rufemun Ku" kawu ya fad'a a hassale.
Rai b'ace Murja ta mike tana jarewa iyayen NATA kallo sannan tace"kud'i daka bani ajiya ko,so nawa nake Ce maku banason ihu akai ,kuzo Ku wani dameni kud'i kuma ban dauka ba ,banason damu".
Daga hannu yayi zai sharara mata mari,cikin sauri Abduol dake shigowa yanzu yace"haba Dad ,dakata mana ,kawai daga magana sai duka,to bata dauka din bane ae".
Wata dariyar mugunta Murja ta sheke da ita tace"aeda ka barshi yayi kuskuren marina,wallahi daduk abunda kuka aekata saina fad'awa duniya ,an fad'a maku cin hakkin maraya wasane"tana zuwa nan taja tsaki tare dayin gaba abunta.
Dariya kawai Abduol yayi tare da fad'in "kud'i dai nina dauka,saka makon na tambayi kudi an hanani,kuma dai baga na ubanane".
Cikin zafin nama Kawu ya cafko wuyan Abduol yana fad'in" ka cuceni,ka gama da rayuwata".
"Mtwww ni ka sakeni malam,kadai cuci kanka, kaida ka kashe Dan uwanka kan dukiya" hannu yasa ya ture kawu gefe yayi ficewarsa.
Kawu kam tuni ya sarke da tari yana dafe zuciya ,faduwa yayi kasa a sume.
Ihu Mama Aysha tasa tana girguzashi amma shiru,don haka rasa aka daukeshi suka nufi asibiti.
Dama karshen alewa k'asa.
******
"Wallahi Momy da gaske nake,wannan lecturer din sak Shaheed har tafiyarsa,zanso ki ganshi Allah saidai shi sunanshi barrister Farooq". Cesar Minal.
Dariya kawai Momy tayi tare da fad'in " halittar Allah kenan".
"Ni wallahi inna ganshi sai na rikajin wani iri,kamar jinane shi" cewar Manal.
"To sai kuyitayin addu'a,Allah ya nuna mana Yaya Shureim, bawai tunani ba,kuma Allah ya tsaresa duk inda yake" Shaheed ya fada.
Duka parlon suka amsa da Ameen.
Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe๐คฒ๐ป
*AlKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Vote
Comment
Share
Maji dad'in kainuwa
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook
Maryam Ismail (maji dad'in Kainuwa)
91โพ95
Kallon Daddy kawai yakeyi ya kasa koda motsi daga inda yake,idanuwansa sun bushe k'am,zuciyarsa ta daskare ,ko kad'an baya fahimtar me Daddy ke cewa.
"Farooq,karka takura kanka ,ba dole shawara ce wannan ,kasan banason damuwarka" cewar Momy.
Wani murmushi ya saki tare da d'ago kansa,fara'ar karya ya dakko tare da dorawa akan fuskarsa "haba Momy narh ya zakice shawara,ae karki damuwa ,kinfi karfin komai wurina,na tabbatar kinason aurena da yarinyar ,kawai kuyi masu magana tare da fara shiri" Farooq ya fad'a yana sakin murmushi.
"Alhmdllh" Momy da Daddy suka fad'a a tare"Allah yayi maka albarka ya baka masu faranta maka yadda kayi mana".Momy ta fad'a.
Ameer da tunda aka fara magabar ya kura masa ido,Wanda yasan duk abunda take fad'i karyane ,"lallai kayi ganganci na karbar auran wacce baka so"Ameer ya fad'a a zuciya.
Mikewa yayi tare da nufan d'akinshi ,ruf da ciki ya fad'a a saman bed dinshi,wani tarine ya sarkeshi hankacif yasa tare da rufe bakinsa,jini ne ke fitowa daga bakin shi ,waro ido yayi tare da kara tabbatar da abunda ya gani,da gaske jininne maganar Dr Nasir Ce ta shiga dawo masa arai fal"ka rage damuwa Barrister, zuciyarka na dab da zuwa matakin karshe Wanda daga nan sai abunda Allah yayi,ka taimaki rayuwarka da kanka zuciyarka tayi sanyi da raunin da ba komai zata iya rik'ewa ba"wannan maganan itace taketa yi mashi a kwalwa,jin motsin Ameer yasa yayi saurin boye hankacif din tare da rufe idonsa kamar mai bacci.
"Meyasa zakayiwa kanka wannan gangancin ,ka karb'i abunda kasan baka iya rayuwa dashi kuma kasan Amrah wahala zatasha kawai wurinka" Ameer ya fad'a rai b'ace donji yake har cikin ransa.
Wani wawan kallo
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook
Maryam Ismail (maji dad'in Kainuwa)
91โพ95
Kallon Daddy kawai yakeyi ya kasa koda motsi daga inda yake,idanuwansa sun bushe k'am,zuciyarsa ta daskare ,ko kad'an baya fahimtar me Daddy ke cewa.
"Farooq,karka takura kanka ,ba dole shawara ce wannan ,kasan banason damuwarka" cewar Momy.
Wani murmushi ya saki tare da d'ago kansa,fara'ar karya ya dakko tare da dorawa akan fuskarsa "haba Momy narh ya zakice shawara,ae karki damuwa ,kinfi karfin komai wurina,na tabbatar kinason aurena da yarinyar ,kawai kuyi masu magana tare da fara shiri" Farooq ya fad'a yana sakin murmushi.
"Alhmdllh" Momy da Daddy suka fad'a a tare"Allah yayi maka albarka ya baka masu faranta maka yadda kayi mana".Momy ta fad'a.
Ameer da tunda aka fara magabar ya kura masa ido,Wanda yasan duk abunda take fad'i karyane ,"lallai kayi ganganci na karbar auran wacce baka so"Ameer ya fad'a a zuciya.
Mikewa yayi tare da nufan d'akinshi ,ruf da ciki ya fad'a a saman bed dinshi,wani tarine ya sarkeshi hankacif yasa tare da rufe bakinsa,jini ne ke fitowa daga bakin shi ,waro ido yayi tare da kara tabbatar da abunda ya gani,da gaske jininne maganar Dr Nasir Ce ta shiga dawo masa arai fal"ka rage damuwa Barrister, zuciyarka na dab da zuwa matakin karshe Wanda daga nan sai abunda Allah yayi,ka taimaki rayuwarka da kanka zuciyarka tayi sanyi da raunin da ba komai zata iya rik'ewa ba"wannan maganan itace taketa yi mashi a kwalwa,jin motsin Ameer yasa yayi saurin boye hankacif din tare da rufe idonsa kamar mai bacci.
"Meyasa zakayiwa kanka wannan gangancin ,ka karb'i abunda kasan baka iya rayuwa dashi kuma kasan Amrah wahala zatasha kawai wurinka" Ameer ya fad'a rai b'ace donji yake har cikin ransa.
Wani wawan kallo Farooq ya soma yiwa Ameer tare da fad'in"ninayi dakai bazan iyaba ?,ko nace maka bana sonta?".
"Oh I see ,nasan ka karb'i soyayyar Amrah ne don sadaukar da farin cikinka ga iyayenka ,eh shima abune mai kyau amma ba irin soyayyarku ake sadaukar ba ,kasan me kakeyi malam zaka kunnawa kanka wuta da kanka ni kaga tafiyata" yana zuwa nan a zancensa ya nufi hanyar fita,saurin barin wurin Momy tayi ,dama tasan haka dukda ba ita ta haifi Farooq ba amma tasan halinsa koda ido zaiyi magana zata gane,kuma tasan zuciyarsa har gobe babu kowa sai IMINAT.
Farooq kam kanshi ya dafe jin wani irin harbawa da takeyi tamkar zatayo tsalle ta fito waje, sosai yakejin jiki tare da jigatuwa da abunda ke damunsa,ganin ciwan k'ara gaba yake yasa ya sab'i key din motarsa yayi hanyar Asibiti tare da kiran Dr Nasir ya sanar masa zaizo yanzu.
Hospital
Kai tsaye ya shiga office din Dr Nasir tare da zama ya basa hannu suka gaisa .
"Barka da zuwa babban barrister, ya k'arfin jikin naka ina fatan ana samun ci gaba?" Dr Nasir ya tambaya.
Murmushi yayi nan ya ci gaba da fad'awa Dr abunda yakeji a yanzu.
"Kana wasa da lafiyarka Farooq,ina tsoran ranar da zamu kasa shawo kan matsalarka shekara nawa kana fama da ciwo,am sorry to say zuciyarka takai last step,drugs dinka zaka rik'a sha kawai sai kuma ka bata babban magani shine na daina damuwa,Allah ya baka lafiya " Dr Nasir ya fad'a cike da tausayin abokin nasa wanda ta dalilin ciwan nasa har suka saba.
Musabaha sukayi ,sannan ya mike tare d fad'in "ba damuwa ,insha Allah komi zaiyi daidai" sannan ya fita.
"Kunga wannan rigimar naku ya isheni ,asibitifa mukazo,amma kun tsaya maida yanda akayi ni kunga tafiyata" Mom ta fad'a tana wucewa.
"Twins ,nima kunga tafiyata wlh Mom yayi gaba" Shaheed ya fad'a.
Da gudugudun su twins suka shiga gabansu tare da fad'in "mu had'u a d'akin saimun rigaku ganin Babyn Aunty Nafisa ".
Saurin kara lek'a tagar dake kusa dashi yayi ,har abada koda zai manta komai a rayuwarsa to banda wannan fuskar,a guje ya fito wajen tagar saidai mi yaga wayam babu ko alamar giftawar wani a wurin,juye juye ya kamayi yana kiran" Mom,Mom,Mom",hankalinshi a matuk'ar tashe har wani b'ari jikinshi keyi"da gaske Mom na gani"duk inda hankalin Farooq yayi dubu a tashe yake.
*Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karshe*
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Pls
Vote
Comments and
Share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ
*SO D'AYA*
NA
*MARYAM ISMA'IL*
( *MAJIDADIN KAINUWA*)
*ุจุณู
ุงููู ุงูุฑุญู
ู ุงูุฑุญูู
* ___________________________________
*๐KAINUWA WRITERSโ๐ผ ASSOCIATION*๐ค๐ป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Follow me on Facebook at Maryam Ismail(maji dadin Kainuwa)
96โพ100
*wannan shafin naki ne munaya a fitattu sha biyar group 1,ina godiya sosai ina matukar jin dadin comments dinki,Allah yh saka maki da mafificin alkhairinsa*
Kuka takeyi kamar zata sike tare da daura hannu saman kai tana fad'in na shiga ukku na lalace in Aysha yanzu shikenan kabiru ya samu mutuwar barin jiki tun da jajayen sahu mukayi aure muke tare sai yau a wayi gari acemun bazai kuma tashi ba,ni ina zansa kaina Asha".
"Ba haka ya kamata kice ba,Hajiya Aysha hakuri zakiyi haka Allah yah kaddara kinji" cewar Dr.
Ko kulashi batayi ba tayi gaba tana ruzgar kuka.
Rayuwa kenan,Allah ka hanamu cin dukiyar maraya koda kuwa sisice.
"Wallahi har zuci nike fad'a maka wannan ,Daddy Farooq bayason Amrah naji da kunnena tana yana kokarin kyautata mana ne, yayinda shi kuma zai sadaukar da farin cikinsh" Momy ta karashe maganar tana duban Daddy.
Nisawa yayi cike da jimamin abunda yaji"inaga to vazamu tauye masa hakki ba,kibawa Hajiya hakuri ,bazan tab'a yiwa Farooq abunda baya soba ,kada ki kuma tada mashi wannan maganan a barta kawai"ya karashe maganar yana dubanta.
A take Momy ta dauki waya ta zayyanewa Hajiya duk abunda ke faruwa,a baki ta ansa da bokomai Hajiya Allah ne be nufa ba.sannan sukayi sallama tare da kashe way an.
Sakake haka takebin wayar dake hannunta da kallo cikin tashin hankali da zullumin wacce hanya ya kamata tabi.
"Meke damunki Umma ,kodai wani abun ya faru da Farooq ne,ki gayamin pls" Amrah ta jefo mata wannan tambayoyin duk a Jere.
"Amrah ,Farooq be amince da auranki ba" Umma ta fad'a.
A gigice Amrah ta mike tsaye tare da dafe kirji tace"mene ,me kike fad'a mani haka babu dad'in ji,nice matar Farooq bazan iya hakuri dashi ba,shine muradina babu wata katangar da zata shiga tsakaninmu dashi"tana zuwa nan ta kwashi key din motarta da gyalenta tayi waje tana sharb'ar hawaye zuciya cike da kunci tare da tarin bak'inciki,tunani tayi tabbas tana yawan ganinshi a wurin bata da tabbacin me yake zuwa,amma yanzu kam zata iskeshi wurin,ikon Allah kawai ya isa da ita wurin ko kad'an ta fita a hayyacinta bata gane komai dake wakana a wurin,keeee haka ta taka burki daidai jikin wurin shakatawar wani shu'umin murmushi ta saki ganin motarsa a wurin.
Takoyi sa'a inda ta saba ganinsa kullun yauma kamar kullun a wurin yake zaune shi kad'ai ,gabansa tarin kayan ciye ciyene amma ya kasa shan koda ruwa ne a wurin,sanye yake cikin ash colour din shadda dinkin zamani yayi masifar yi masa kyau ga hula kube daya black colour daya dora a kanshi sai fitarda wani irin sihirtaccen kamshi yake hannunsa d'aya ya daura akan goshinsa yayinda idanuwansa suke lumshe ya lula duniyar tunani kallo d'aya zaka masa kasan cewa yana cikin matsananciyar damuwa.
Har k'asa ta duk'a gabanshi yayinda idanuwanta ke zubar da zafafan hawaye "me yasa bazaka tausayawa zuciyar data fara so akanka ba,duk wani burinta ya kare wurin mallakarka ,kaki amincewa da auran wacce tafi kowa sonka dukduniya" ta karashe maganar murya a dishe.
Yakai kusan minti biyu ko motsawa beyiba balle tasa ran samun amsarshi,a hankali ya soma bude daradaran idanuwanshi masu kama damaijin bacci ya zuba mata su wani irin kallo yake binta dasu masu ma'anoni da yawa,"lallai ki lallashi zuciyarki tabarson abunda bazata tab'a tasamu ba har a bada,zefi kyau ki fita hanyata,wai yaushema na zama abokinki,ba laifi bane don mace taga namiji tanaso ta fad'a mashi ba,saidai vaki biyo hanyar dazan soki ba,First look dina dake a rayuwata naji banason sake ganin fuskarki"be jira cewarta ba ya mike tare dabin wata hanya a cikin wurin.
Waro ido yayi cikin tsantsar tashin hankali ya furta"Zeena".
Zeena kam ihu take daidai karfinta da neman kwatar kanta daga hannun garadan kartan dake kokowar sakata mota,sab'arta black yayi tare da jefata motar suka fure,itako ihu take tare da neman taimako tana dukan glass din motar.
Cikin gaggawa ya fad'a motarshi ,shima ya take masu baya tare da soma kiran layin wayar Ameer.
Kwance yake akan makeken gadonsa yana latsa laptop dagashi sai boxer ga mug din copee hannunsa yana sipping a hankali,kallon wayarsa yayi dare ruri tana Neman agaji,sunan Boddy ne ya bayyana a jikin screen din dukda yana fushi dashi hakan besa yayi k'asa a gwaiwa va wurin d'aga wayar ya furta"hellow "akan labbansa.
" kana ina,ka fito maza yanzu gani a titin sharad'a inabin bayan motar wasu mutane da suka dauke Zeena daga royal yanzu"Farooq ya fad'a.
"Kace mene,Zeena please ka timakeni ina zuwa yanzu kada su cutarmin da ita,idan na rasa Zeena tabbas Nima mutuwa zanyi,ina hanya ,kavar wayarka a kunne" be jira cewarsa ba ya zuri jallabiya ya saka da gudu yayo waje.
"Subuhanallahi Ameer yau kuma shakiyancin gudu ka tashi dashi,wannan yaro Allah ya shiryeka" Hajiya ta fad'a tana karewa ikon Allah kallo.
Beko kulataba yayi waje,figan mota tayi kai tsaye yahau hangar da Farooq ke kwatanta mashi yana sharara gudu a titi.
Amrah kam jin kalaman Farooq tayi kamar ana daka mata guduma akai,ga wani irin mumunan tashin hankali ,a guje tayi mota ta soma ja ba tare da tasan inda takeyi ba.
*Allah ka gafartawa iyayenmu,kayi mana kyakyawan karashe* ๐คฒ๐ป
*ALKALAMIN MARYAMA* โ๐ป
Vote
Comments
And share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โ๐โ๐โ๐โ๐โ