Showing 6001 words to 9000 words out of 28816 words

Chapter 3 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt

sannan tace"ban jiki ba ne".




"Ni dai sunana Amra daga Nigeria nake aeki ne ya kawo Daddy na anan kasar ,kuma daya gama zamu koma" cewar Amra.




"Nice to meet u,ni kuma sunana Zeenatu".




Tun daga ranar Amra da Zeenatu suka zama abokai gashi class dinsu daya tun IMINAT na nokewa harta saki jiki da Amra,sun shaku sosai,komai nasu yanzu tare sukeyi harta kayan sakawa tare sukeyin komai,har iyayansu sunsan juna.






" IMINAT wai ba kiranki nikeyi ba,maza ki fito nan"cewar Amma ,tana kokarin zama a chair.






Fitowa tayi fuskarta daure ba annuri gaban Amma ta zauna tace"Amma na rokeki ki kirani da Zeenatu, kina fadan mun da gaba duk lokacin da kika kirani da IMINAT"sai kuma hawashe cur cur a fuskarta.






Rike da haba Ammi ke kallon IMINAT tace a ranta oh munyi sake yarinya tun tana y'ar Karama soyayya ta shigeta,ban taba tunanin abun zaikai haka ba,dole musan abunyi a fili kuma tace"Mama na tashi ki koma d'aki".






London.




Aunty sai kallon FAROOQ takeyi yanata zuba karatu cike da mamaki take kallonsa don ita a tunaninta beyi school ba,amma sai gashi da sukaje School sakashi sun daukesa a js 3,kwalwarsa ma ta wuce nan,result na primary suka biya aka masa kawai ya dona ga islamiyyah saidai hardar littafai yajeyi ya riga yayi hardan al-qur'ani mai girma.






Sosai ta damu da tasan labarin rayuwarsa,saida yaga ta damu sosai,lokacin Uncle yazo London sannan ya basu labarin shi,lallai sun tausaya masa ga kuma soyayya tun yarinta.






Gaba d'aya FAROOQ ya canza,ya ida zama mishkilin kansa, magana ma wahala take masa ga yawan tunani,cikin jin dadi da gata yake rayuwa.tunda ya mika da karatu yakai SS Aunty ta koma Abuja saidai suzo ziyara wurinshi,amma shi tunda ya baro Nigeria bai kuma komawa ba har yanzu da yake shekarar karshe a jami'a yana karantar LOW.,kuma yayi Doctoring akan English.






Some years later.




Cikin fara'a Papi yake tsaye yana jiran fitowar iyalansa Wanda hada iyayen Amra ,cikin nutsuwa suke taka matakalayen jirgin ,wasu Dattijan mata na gani ,sai bayansu y'an mata guda biyu komai basu iri daya sunyi matukar kyau cikin shigar black gown din sunyi rolling da veil white colour,daya tafi daya haske da kyau,yayin da dayar bata da haske sosai.




Farar naga ta dafa tace" Baby zeenat yau kina murna ko,bayan shekaru kin dawo garin masoyinki".






Murmushi Zeenatu tayi sannan tace"farin ciki kai,can't wait to see him sis".




Dariya sukayi ,cike da murna suka gaishe da Papi sannan suka shiga mota zuwa gidansu na Abuja don yanzu kam sun dawo Abuja da zama,papi ya aje aeki sun koma business shida Daddyn Amra.






Lallai nayi mamaki dana gane wadannan Yan matan IMINAT Ce da Amra,sun zama Yan mata sosai komai na cikar mace ya gama bayyana a jikinsu.






Tunda suka dawo Papi yayi masu registration na makaranta a Department of low ,su duka biyun.








*ALKALAMIN NARYAMA* โœ๐Ÿป




Vote
Share and
Comment
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*







*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ___________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
41โ™พ45






Koda suka koma gida daki ta shiga,tayi wanka tare da sauya tufan dake jikinta,kwanciya tayi da nufin yin bacci amma Sam yaki zuwa da zarar ta rufe idonta suffar Farooq ke mata yawa ga daddadan kamshinshi daya kasa barinta,murmushi kawai take saki lokaci zuwa lokaci.


(Tab akwai aeki reader's kuna ganin meke shirin faruwa).






******


Zaune take cikin tankameman parlo dinsu,sanye take da dogon riga na material colour dinsh purple babu makeup a fuskarta amma tayi kyau sosai,idanuwanta duka suna kallon katon plasma din dake manne a bangon dakin,zakayi tunanin kallo take,amma Sam hankalinta baya wurin donko ta dade da lulawa duniyar tunanin,bata ma San meke wakana a cikin parlon ba.






Tsaye Amma tayi cak a kanta,tayi kimanin minti 5,amma sam batasan da zuwanta ba,ajiyar zuciya Amma ta sauke cike da tausayin yarinyar tata,zagayowa tayi ta zauna tare da dafata ,ta kuma kama hannayenta duka biyu sannan tace"Mamana sai yaushe zaki saukakawa zuciyarki wannan tunanin,sai yaushe zaki manta baya ki fuskanci gaba,ki kuma yadda da cewa kaddara ta rabuku da SHUREIM?".






Hawaye ya soma ambaliya a kyakyawar fuskarta baki na rawa tace"Amma har yanzu ina sansa,wallahi ya zama rayuwata,nasan duk inda yake yana tare dani ,shin meyasa ni bazan tunasa ba ,na kuma rike masa alkawari Amma na"Zeenatu ta fada murya a matukar raurane.




Girgiza kai Amma tayi sannan tace"hakan baya nufin kisa tunani a ranki, ki koma zubar da hawayenki addu'a zakiyi,Allah ya hadaku da alkairi,yanzu ki daina wannan kukan ki tashi ki shirya kije shopping dinnan kinji Mamana".






Share hawayen idonta tayi ,ta mike jiki a sanyaye ta shiga dakinta,bata wani b'ata lokaci ba ta shirya cikin Riga da sket na atamfa ,tayi matukar kyau sosai,mayafinta da bag d shue duka iri d'aya,drawer ta bude ta iba kudi ta zuba a bag dinta ta fito rike da key din motarta a hannu,kai tsaye dakin Amma ta nufa,dauke da sallama a bakinta.




Papi ne ya amsa sallamar,tsaye tayi cak tare da sakin dariya tace"Papina yaushe ka dawo"karasawa tayi ta zauna gabansa tare da dora kanta bisa cinyarsa,shafa kanta yayi yace"Allah yayi maki albarka Mamana yanzu na shigo,sai ina haka".






"Aekin kenan ,ke kullun baki girma,shopping zataje kasan sun kusa fara zuwa school" Amma ta fada.




Turo dan karamin bakinta tayi tare da mikewa tace"zan wuce,tunda ba'aso na zauna wurin Papi na".




Dariya sukayi duka,kudi Papi ya kara mata,sannan sukayi mata saita dawo ,kai tsaye motarta ta shiga tayi mata key ta fice daga gidan.






**********






Tsaye yake yasha kananun kaya duka komai black colour babu laifi shima ya hadu ,saurayi ne na yayin y'an mata a wannan lokacin,sai zuba kamshi yake,abokansa ne har biyu zagaye dashi dunata kirarashi ,Abduol kenan yaro maiji da tashe.kai tsaye cikin plaza din suka tura Kansu ,tsayawa yayi yana hangota Wanda dalilinta ne yasa ya shigo wurin yanzu,sosai take burgesa ga wata irin sha'awarta data damesa a haduwarsu lokaci daya,lashe baki yayi yace"sugar baby".takawa ya somayi ya doshi inda take.








Itako bata San da wani Wanda ke binta ba,basket dinta ta dauka,ji kake gam,jikinsu ya had'u ,tafiya tayi luu zata fadi,harta rumtse idanuwanta Wanda suka ciko da hawaye ta sadakas da irin mumunar faduwar da zatayi.






Saurin tarota yayi,ta fado bisa faffadan kirjinshi,wani irin Yar sukaji gaba dayansu lokacin da jikinsu ya had'u.






Hakan kuma ya tilastawa Abduol da tawagarsa tsayawa cak,yayinda wani kululun bakin cikin ya masa tsaye a zuciya.






Kallon kyakyawan fuskanta ya tsayayi,wani mumunan faduwar gaba ta ziyarceshi lokaci daya yaji rayuwarsa ta baya ta dawo masa,saurin sakinta yayi,ya duka ya soma tattare mata kayanta daya zubar.






Itako kafeshi tayi da idanuwa,hankalinta a matukar tashe,tunda take duniya babu Wanda ya tab'a mata haka sai Shureim,gani take inama ace yana wurin inama ace shine,wasu zafaffan hawayene suka ci gaba da kwaranya a fuskarta.






Kallon mamaki ya bita dashi ,da kuma tambayar kansa meya sata kuka,tsintar kansa yayi da fadin"kiyi hakuri bada sanina bane".yana zuwa nan ya aje mata basket dinta ya fita daga wurin,da wani irin gudu ya figi motarsa yayi gida hankalinsa a matukar tashe,sosai Iminat ta dawo masa a rai.






Itama jiki ba kwari ta ida abunda zata ida ta wuce gida,saida tazo shiga gate sannan ta tabbatar akwai mai binta a baya,sharewa tayi ta shigewarta.






Shiko Abduol shu'umin murmushi ya saki ,da murnar yaga gidan su Baby dinshi.Jan motarsa yayi kai tsaye club ya wuce,acan ya samu Yan matanshi sukaci gaba da sheke aya.






Abduol ya taso cikin gata da sangarta,bashi da tarbiya ko kadan,duk laifin da Allah ya haramta shi yanayi,mazinaci ne mashayi ne,burinshi kawai dayaga yarinya ya lalatata yayi gaba,mayaudarine na bugawa a jarida,iyayensa ko kadan basa ganin laifinsa,komai zaiyi daidai ne,(Allah ka shirya mana zuri'a).








Yanzu kam duk yadda yaso yayi controlling kansa ya kasa,wata iriyan bugawa zuciyarsa keyi ,wurin Aunty kawai yake bukatar isa,jiki na rawa ya shiga bedroom dinta ko sallama ya kasa, zaune take a chair tunda ta gansa haka ita kanta tasan damuwar tasa,zama yayi a kasa ya dora kansa bisa cinyarta ya fashe da kuka mai cin rai ga tsananin rauni da karya zuciya,batayi kokarin hanasa ba tasan shine kadai ke sanyaya zuciyarsa duk idan ya shiga wannan yanayin,bubbuga bayansa takeyi kawai,shiko be sauraraba saida yayi mai isarsa yaji zuciyarsa tad'anyi sanyi.










*ALKALAMIN MARYAMA* โœ๐Ÿป




Vote
Comment
Share




09030953294
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*







*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ___________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________


36โ™พ40




*ina gaesuwa a gareku masoyan So d'aya,kullun kara yawa kuke godiya marar adadi,wannan shafin nakune kuyi yadda kukeso dashi ,one love*.






โž–"zaman me kikeyi har yanzu anan,kinsan na fada maki zamuje gidan Hajiya Halimatu tarba ,ke komai saikin bata lokaci".Umma ke Fada.






"Waini Umma nafa shirya,zaman jiranki nikeyi,shinefa na tsaya waya da habeebty" cewar Amrah.




"To ae saiki tashi muje din" Umma ta fada tana gaba abunta.






Mikewa Amrah tayi ta rufa mata baya, driver ya kaisu har gidan Hajiya Halimatu, Masha Allah ko bangon gidan abun kallo ne tsayawa fadar tsaruwarsa bata lokaci ne.




Da sallama suka shiga tankameman parlon gidan Wanda ya gaji da had'uwa,cike da murna hjy Halimatu ta tarbi aminiyar tata tare da rike hannun Amrah tace"Allah mai iko da a hanya naga Amrah wallahi bazan ganeta ba,rabon dana ganta tun tana primary school da naje America".




"Wallahi kuwa,gadai ta nan kinga an zama budurwa,yanzu ae ta rika zuwa gaeshe da Ummarta" cewar Umma.






Dariya duka sukayi,har kasa Amrah ta duka ta gaeshe da hjy Halimatu cikin ladabi.






Sosai yarinyar ta burgeta sai nan da ita.




Alhaji Isma'il ne ya fito yana kafa hula akai,yana fadin"jirginsu ya kusa sauka na wuce daukarsa".






"Ohni Daddyn FAROOQ kama fini zumudi wannan ae,to ae ga Hajiya salamatu nan kwa gaesa ko" cewar Aunty.






"Hm bazaki ganeba,I miss him ,ina bukatar naji dimin d'ana a tare dani,anzo lafiya Hajiya".cewar Uncle.




" lafiya Alhmdllh"Umma ta fada.




Cikin natsuwa Amrah ta gaeshe da Uncle kafin ya fita cikin sauri,mota biyar aka shirya domin dauko Farooq ,gudu kawai suke shararawa har suka iso Airport,hakan kuma yayi daidai da saukar jirgin.




A hankali kamar bayason taka kasa haka yake tako matattakalar jirgin,sanye yake da White wando da whit t-shirt,daga suite dinsa zuwa belt,shoe,da agogo duka blue colour yayi masifar kyau ga wani irin sihirtaccen kamshi yana fitarwa,yana da cikar zati duk inda namiji yakai to wannan guy din yakai ga saje shimfide a kyakyawar fuskarsa,fuskars tamke take kamar an aeko masa da mutuwa,janyo trolley dinsa yayi ,ganin Uncle na masa murmushi yasashi sakin wani k'ayataccen murmushi Wanda ya kara fito da kyansa,FAROOQ ISMAIL kenan.






Rungumar juna sukayi cikin farin ciki da soyayyar juna,a hankali yayi magana Wanda inba na kusa dashi ba,bazaka iya jin me yake fada ba a hankali ya furta"miss u Uncle"




"Miss u too my Son,nayi murna da zuwanka".




Murmushi kawai yayi ,suka rankada suka shiga Mota,inda ma'aekatansu sai gaesheshi sukeyi,hannu kawai yake d'aga masu,sukaja motar zuwa gida.






Cike da takun izza da isa ya shigo cikin parlon Wanda hannunsa na sarke cikin na Uncle dinsa,murmushi Aunty ta sakar masa,shima hakan ya faru garesa ,da sauri ya karasa ya rike duka hannayenta biyu ya rada mata" I miss u Aunty".




"Miss u too my Son,ya karatun?". Aunty ta tambaya.


" Alhmdllh"kawai ya fada.sai lokacin ya kalli Umma yace"barka da wuni".






"Barka dai yaron albarka,ya karatun?,sannu da hanya".Umma ta fada washe da baki.








Tunda ya shigo dakin,gaba daya duka hankalinta ya koma garesa ,ta rasa natsuwarta gaba daya wata iriyar madiffafiyar soyayyarsa ta darsu cikin zuciyar Amrah,kallonsa kawai take ta kasa dauke idonta daga garesa,saurin zungurarta Umma tayi data lura da halin da Y'ar tata ta shiga lokaci d'aya.






Firgigit ta dawo ,alama Umma ta masa data gaesheshi.








Cikin in'i'na tace"Yaya Farooq,sanu da dawowa ,ya hanya?".


Dago daradaran idanuwansa yayi ya zuba mata su,shi harga Allah be gantaba,be kuma San da ita a cikin parlon ba,wata iriyar zubawa tsikar jikinta tayi dukta tashi,lokacin da sukayi 4eyes saurin kawar da nata tayi,tabe baki yayi tare da mikewa ,saida ya kusa hawa stairs sannan yace" lafiya ,Alhmdllh, Aunty I need to rest "be jira amsarta ba ya haye sama abunsa.






Duk yinin ranar Amrah sukuku ta yini hardai suka tafi Gida.






*ALKALAMIN MARYAMA* โœ๐Ÿป




Vote
Comment and
Share
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ๐Ÿ’•โšœ
*SO D'AYA*






NA


*MARYAM ISMA'IL*







*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…* ___________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
46โ™พ50






Ajiyan zuciya yake saukewa kamar Wanda yayi wani aeki,ba laifi zuciyarsa tayi sanyi.




Aunty kam hannayensa ta kama duka biyu tace"haba jarumin namiji,ya zaka kasa daukar kaddararka,ya kamata ka rage wannan damuwar kasan gobe zaka fara zuwa court ga visiting lectures din da zaka rikayi a department of low,u know yanzu aeki zai maka yawa kuma kwalwa na bukatar hutu Farooq,nasan duk inda IMINAT take tana tare dakai kuma nasan zata jiraka duk daran dadewa ,ka daina sanya damuwa a ranka indai har ka yadda da alkawarin da kukayiwa juna".






Ko yaushe wannan sune kalaman da Aunty keyiwa Farooq ya samu saukin zuciya shiyasa duk inda yake yaji damuwa irin haka to saiya dangano da ita koda ta waya ne.




Murmushi ya saki tare da fadin"I love u Aunty,kullun kece bango abin jingina a tare dani,Allah yabarmin ke"






Shigowar Ameer yasa suka maida dubansu garesa tare da ansa sallamarsa.


Ameer abokin Farooq ne,a London suka hadu tare sukayi karatu.




Cike da ladabi ya gaeshe da Aunty,tare da zama bisa chair yace"aekin kayi ko,kamar wata mace daka zauna sai kuka,ni dama zan rigaka ganin IMI din in fada mata mijinta raggo ne wallahi".






Dukan wasa yakai masa,shiko ya koma bayan Aunty yana masa kwalo.






"Kaga dakata kada ka illatamin Dan saurayin da nake burin aurarwa ,ba Wanda bansan ranar girmansa ba" cewar Aunty.








Kwafa Farooq yayi yace"zaka sani, dama dakaga Aunty saiku hademin kai ko ,zaka iskeni daki ae".mikewa yayi kai tsaye part dinsa ya nufa.








"Aeko binka ba fashi,daga fadar gaskiya malam nata'ala" Ameer ya fada yana kunshe dariyar data taso masa.






Wata Uwar harara Farooq ya banka masa yayi gaba don bayason yana ce masa malam nata'ala.yana shiga daki ya fada kan bed yayinda idanuwansa ke kallon sama.




Turo kofar Ameer yayi,ko kadan be motsaba don yasan iyayensa sai Ameer su kadai ke shigowa dakinsa kai tsaye.yanzu kam very serious Ameer ya shigo dukya ajiye shakiyanci a waje,kallonsa yayi cike da damuwa,sosai yakejin Farooq cikin ransa kamar uwa daya uba daya,wata iriyar shakuwa da soyayyar juna ke a tsakaninsu,abotarsu ta zama Yan uwantaka,dukawa yayi ya soma cirewa Farooq shoe yana fadin"tunda kafison kullun ka ganni cikin tashin hankali zan daure haka".






Tasowa Farooq yayi yace"Boddy(Amini) ,kayi hakuri badason raina bane,wani lokacinma bana sanin nayi ,kumin afuwa don niko rayuwa tazo karshe tunda har yanzu mahadinta bezo gareta ba".






Saurin rufe masa baki Farooq yayi yace"nace ka daina fadan irin haka,inaji a jikina ta kusa zuwa gareka,na taho maka da labari mai dadi,amma na sameka kana halin naka".






Waskewa Farooq yayi ya saki dariyarsa mai birgewa wacce baka ganinta sai yana gaban Ameer ko Aunty da Uncle,sosai kyawunsa ya ida fitowa saida yayi mai isarsa sannan ya tsurawa Ameer ido yace"u know zan gane ae ko baka fada ba,ur in love Boddy".






Mikewa Ameer yayi yana sakin murmushi ya kwanta yana fuskantar abokin nasa yace"she is beautiful, gani daya ta tafi dani ,zuciyata na matukar sonta, inka ganta kamar hurul aen na aljannah".






Dariyace ta kuma subucewa Farooq yace"mai yasa bata jiramu a lahirar sai munzo ba".






Kwabe fuska Ameer.




"OK Sorry,let us be serious wacce mai sa'a Ce wannan lokaci daya ta zubarmin da Boddy kasa haka,lallai itadin ta dabance" cewar Farooq.




"We'll nasa amin binciken inda take da kuma sunanta,da gaske ni auranta zanyi,mahaifinta zan fara gani ya bani izinin fara nemanta".




" Allahu saya,wannan dole in muka samota Aunty da Mami su bani goron albishir".Farooq ya fada.




Dariya suka saka duka,haka sukaitayin firarsu cike da soyayyar juna.








Ganin Motar Amrah hakan ya tabbatar mata da tazo gidan,kokarin daidaita natsuwarta tayi ta shiga parlon da sallama,Amrah Ce ta amsa da sauri ta taso ta rungumeta tace"beby I miss u,kin Dade inata faman jiranki".




"Baby siyayyan kinsan da yawa ,so nake mu hada komai kafin mu fara zama busy" cewar Zeenat .




Ciki suka karaso babu kowa parlon don haka suka wuce dakin Zeenat,a bed suka zube suka fara kallon kayan da ta siyo komai bibiyu ne kuma irinsu daya,sauke ajiyar zuciya Amrah tayi tace "baby u know what?".




Girgiza kai kai zeenat tayi tace"saikin fada,dama naga akwai magana a bakinki".




Dariya ta saki tace"baby kyakyawa ne ajin farko son kowa kin Wanda ya rasa,yana da class kai in takaice miki duk inda namiji yakai Farooq yakai,baby am in love,saidai damuwana d'aya yanadajin kai sosai bana tsammanin zai soni koya kulani,magana ma wahala take masa"ta karashe maganar a raunane.






Kama hannuwanta Zeenat tayi suka zauna tare da fuskantar juna tace"waye shi ,meya mallaka dahar wannan kyakyawar budurwar tawa zatace tana sonsa yaki amincewa,lallai yana da sa'a a rayuwa,baby babu namijin dazai ganki ya k'iki,just ki kwantar hankalinki zamita addu'a zai kawo kanshi"
(Hhh๐Ÿคฃ๐Ÿคฃreaders kunji wani mafarki fa da Zeenat keyi,da Neman rigima).




Sosai maganganun kawar tata suka ratsata,ta kumaji dadi hankalinta ya kwanta,fira suka shigayi,tanata bawa zeenat labarin Farooq.






***********
"When zamu ganshi Momy,kinsan ni ban sanshi bafa" cewar Shaheed,Wanda ya zama saurayi yanzu har yaje ss2.




"Bakai kadaiba Broz wallahi muna missing ya Shureim " Manal ta fada.








Murmushi kawai Momy tayi tace "Ku daina damuwa,inda rai da rabo kuma yana raye zamu ganshi,Ku cire damuwa a ranku kunga gobe zaku fara zuwa school,inaso na samu likita da lawyer a gidana,ga kuma nevy a gefena"




Dariya sukayi duka,sannan suka tashi sukayi ciki abunsu.




Guntun hawayenta ta goge ta daga hannu sama tace"ya Allah ni uwace,ya Allah ina rokonka ka karemin rayuwar Shureim aduk inda yake,ka kuma sakashi a hanyar daidai,ka kuma jikan mijina".


(Nima dake gefe nace Ameen Momy๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ).






Tunda Momy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login