Showing 1 words to 3000 words out of 28816 words

Chapter 1 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt

ο»Ώ[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: βšœπŸ’•βšœπŸ’•βšœπŸ’•


*SO 'DAYA*


*NA*
*MARYAM ISMAIL*


*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*




2β™Ύ5




Amma kallon IMINAT tayi tace"kinsan ki rufemin bakinki a wurin, kizo maza kiyi home work baki"


Bata fuska tayi tuni hawaye suka fara zuba a idanunta, jan towel din dake daure jikinta tayi tana share hawaye dama wanka aka gama mata baki na rawa tace"ni Amma yaya bezoba, bazan iyayin home work ba".


Amma sake da baki take binta da kallo, magana takesonyi amma IMINAT bata ko sauraranta jin karar motar da ake kawo SHUREIM, kofa ta zubawa ido, shiko dinne, tsayawa yayi bakin kofar dakin yana mata murmushi wani ihu ta saki ta ruga ta rungumeshi tana masa oyoyo.


Shafa fuskarta yayi yajawo suka karaso ciki har kasa ya duka ya gaishe da Amma, cikin sakin fuska ta amsa,tare da tambayarsa yasu Momy ya amsa da suna lafiya.




"Maza kizo nasa miki kaya saiku fara"cewar Amma.


"No ki bani kayana yaya zai shiryani, banason naki"IMINAT ke fada.


Mika mata kayan tayi tare da lotion dinta, saman jikin SHUREIM ta dora kayan, lotion din ya shafa mata tare da powder, dogon rigane ya saka mata ya shafa mata turare sannan suka soma home work din, har Papi ya dawo wato baban IMINAT, sosai yaji dadin ganinsu ya zauna suna home work din tare.


*********


"Haba Abban Murja ae nasan badaga baya kake ba, indai ka tabbatar yasha din, yo me ake da dan banza"cewar Mama.


"Hmm wallahi shiyasaha ki jira nanda mintoci zakiji waya ya mutu uban kowa ya huta, shege me jajayen kunnuwa"kabir ya fada yana jan tsoka.


Matso kaji Aisha ta fada, rada tayi masa, suka kwashe da dariya tare da tafa hannu. Hmm mata da miji kenan.


"To amma in Hajiya kaka taji fa, ya kakeso ayi mana".


"Ahhab kokin manta tafison zaman katsina, itako wannan shegiyar matar tasa dole ta koma gidan ubanta kuma ta barman y'ay'an dan uwana tunda badasu tazo ba".


Haka sukaita tattauna tsakaninsu.


Har bakin Mota IMINAT ta rako SHUREIM, saida driver dinsa ya tada mota taga fitarsu sannan ta koma ciki cike da farin ciki.




"Oh God Manal baxaku barni na huta ba, gashi duk banajin dadi"cewar Momy.


Kallonta Minal tayi tace"to ki huta Momy munje wurin Daddy"kafin ta basu amsa tuni sunyi part din Daddy suna kwallah masa Kira, abunda suka gani shiyasu kwalawa Momy Kira, dukda suna yara sunsandai ba lafiya ba, jin ihun yaran nata yasata mikewa da sauri ga bugun zuciyarta daya tsananta har idonta ya kawo ruwa, amma tsaye take Cak ta kasa daga kafarta, a guje Minal ta safko daga bene tana haki tana kiran"Momy, Daddynmu jikinsa duk jini yana kwance a kasa".


Hakan kuma yayi daidai da shigowar SHUREIM a gidan kunnuwansa suka ji masa abunda Minal ke fada, a guje ya gittasu ya nufi dakin Daddy, sai lokacin Momy ta samu kwarin gwaiwa na shiga dakin turus tayi ganin mijinta kwance alamar babu rai a jikinsa, sunayen Allah kawai take Kira hannunta na kyarma ta Kira family Doctor dinsu, cikin kankanin lokaci ya iso, da kyar ya iya kwace Daddy daga jikin SHUREIM, ba yadda beyiba akan ya fita ya dubasa amma yaki dole ya barsa ya dubasa yana kallo kuma anan ya tabbatar da mutuwar Alhaji Ahmad,cikin lallashi da tausasa murya ya fada Momy kyarma ta dauka take cikinta ya juya ta fadi tana nakudar dole, SHUREIM ko faduwa yayi kasa a sume, dandanan aka kwashesu akayi Asibiti dasu, Lebo room aka kai Momy yayinda aka shiga da SHUREIM emergency.




Kafin kice me tuni gari ya karade da rasuwar Dr Ahmad farooq gida ya cika makil ciki harda kabir da iyalansa suna sharbar kukan karya, ga haji ya Kaka harta iso.




*comment and share pls*






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: βšœπŸ’•βšœπŸ’•βšœπŸ’•


*SO D'AYA*


*NA*
*MARYAM ISMAIL*


*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


*MARUBUCIYAR*
*SANADIN GATA*
*DALILIN SO*
*YAUDARA KO BUTULCI*
*HANAN*
*ASALI NA*
*TABON D'A NAMIJI*
*ADDINI NA*


*bismillahirrahmanur rahim*


*ban yadda wani ko wata su juyamin novel ba, batare da izinina ba*


1
Rugawa yakesonyi tanata kiciniyar saka masa rigar uniform dinsa yarone dan kimanin shekara aha biyu(12), amma dukda haka Momy ita ke shiryashi, shagwabe fuska yayi ganin Daddy ya shigo, cikin sauri Daddy ya iso ya karbi rigar yana fadin"haba my Boy kada kayi kuka mana, yanzufa mun girma ko", hannu ya mika masa suka hada.




"Ae dama sai kananan yake wannan shiriritar, yanzu na tabbatar an gama shirya su Manal amma shi ji ko break beyi bafa"Cewar Momy.




Jawota Daddy yace have"we are sorry, ki kawo na basa a mota kawai".




Mikewa sukayi bayan ya gama shiryashi suka fito parlor, anan suka samu Manal da Minal a shirye tsab cikin uniform, yara ne yan kimanin sheka 5, da gudu suka rungumi iyayen nasu suna gaishesu, Momy kam kitchen ta shiga ta hadawa SHUREIM abinci a lunch box, ta fito, har mota ta rakasu, Saida Daddy ya shafa katon cikin dake gabanta sannan ya mata kiss a goshi ya saka yaransa mota suka cillah kan titi cikin tsadaddiyar motarsu, ba wani jimawa ya saukesu school ya wuce office.




SHUREIM Dane ga Alhaji Ahmad, asalin sunansa Umar farooq sunan baban Momy ne shiyasa suke kiransa da Shureim, yarone dan gata dukda yana da kanne Manal da Minal amma basa samun gatan da yake samu ko kadan iyayensa basa iya boye soyayyar dan nasu kowa yasan wannan, Daddy babban likita ne da akeji dashi a garin kano, tunda ya auri hajiya Maryam wato Momy sun dade basu haihu ba harsun fidda rai, daga baya sai Allah ya basu shureim, yanzu yana JS 1, fannin islamiyyah yayi sauka,.






Tsaye yake anyi break kallon hanya yake da gudu ta, ta taho har haki take yarinyace yar kimanin shekara 5,kusan faduwa tayi a gabansa yayi saurin riketa, bata fuska yayi yace"bana hanaki gudu ba".




Kama kunne tayi tana fadin"am sorry Yaya bazan sakeba, abincin na kawo maka".




Murmushi yadanyi suka zauna tana bashi abinci a baki tana surutu, tana sakashi dariya harya koshi, sannan ta somaci, spoon din ya karba shima yana bata, kaidace wannan IMINAT batacin abincin saita tabbatar SHUREIM ya koshi ko zata iya saka wani abun bakinta.




IMINAT y'a daya tak ga ENGINEER Muhammad da Hajiya Fatima, asalin sunanta Zinatu, yan asalin garin Gombe ne aeki ya kawo mahaifinta garin kano.






Koda aka tashi school saida IMINAT ta jira Daddy yazo daukarsu SHUREIM sannan ta yarda driver dinta ya dauketa zuwa gida.


Wannan zumuncin nasu SHUREIM yasa har iyayensu suna gaisawa.




Suna isa gida suka samu kabir kanin Daddy da matarsa da yaransa Abduol da y'arsa Murja, sosai sukayi murnar ganin juna, don daga tafiya suka dawo, tsakani da Allah su Momy suke tare dasu babu banbancin koda a tsakanin yaransu ne, amma sukuwa sun zama masu fuska biyu.


Zama Daddy yayi inda ya dora SHUREIM a cinyarsa yana cire masa shoe.




"Haba yaya har yanzu faruqu bai girmaba, kaki daina daukarsa shiyasa dukya sakalce kannansa duksun fisa wayo"cewar kabir.




Dariyace ta kubucewa Daddy yace"duka SHUREIM din nawa yake, miya iya ".


Haka dai suka yini a gidan kafin da dare suka wuce gida, cike da tsanar SHUREIM.






*yaya kukaji naci gaba kona tsaya, sai naga karbuwarsa da ruwan comments sannan zanci gaba*




*bana bukatar sticker a novel dina, ko godiya kumin sharhi ta hakan zansan gyara na, da kuma in sakon na isa gareku*






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: βšœπŸ’•βšœπŸ’•βšœπŸ’•


*SO 'DAYA*


*NA*
*MARYAM ISMAIL*


*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


6β™Ύ10


Cikin ikon Allah Dr ya samu Momy ta haihu lafiya, ta haifi yaronta namiji lafiyayye, saidai jininta yahau sosai, dalilin hakan yasa sukayi mata allurar bacci.


Bangaren SHUREIM kuwa sunyi iya yinsu amma abun yaci tura, har yanzu be farfadoba saidai jijiyar juyansa na harbawa shine kadai zaisa ka gane yanada rai, don haka suke basa kulawa na musamman.




Y'an awanni Momy ta dauka tana bacci, furgigit ta mike tana juye juye, cikin sauri Dr ya shigo dakin, mikewa tayi tace"na hadaka da girman Allah ka fadamun meya samu mijina, kuma ka barni naje kafin a rifesa ka taimakamun".




Sosai ya tausaya mata cikin dakewa yace"ke musulmace kuma kina daukar kaddara mijinki guba aka basa Wanda yayi sanadiyar mutuwarsa, kiyi hakuri ki dauki dangana".




Wani irin zafi takeji a zuciyarta da kunar rai, hawaye masu dumin gaske suka sauka a fuskarta, daukar abunda ta haifa tayi tace"muje ka kaini gida, ya jikin SHUREIM? "


"Alhmdllh yana bacci, saidai yana bukatar hutu, muje gidan".




Lokacin daya kaita gida kofar gidan damkam da al-umma, an dawo daga kai Dr Ahmad(saidai muce Allah ya jikansa), kowa binta yake da kallo cike da tsabar tausayi, tsayawa tayi a parlor tana karewa dakin kallo, jiki ba kwari ta samu wuri ta zauna kusa da Hajiya Kaka tana matsar hawaye.




"Kiyi hakuri kinji, Maryama haka Allah ya rubuta, su Kabiru ne sukace a gaugauta kaisa makwancinsa ana son haka, kiyi hakuri kinji".




Momy bata iya furta komaiba sai hawayen da takeyi, sai a lokacin aka dafa mata ruwa tayi wanka, tasha tea badon dadi ba.


*****




"Wai meke damun yarinyar nanne, yau kwana biyu bata da sukuni dukta fita hayyacinta". Papi ya fada yana shafa kan IMINAT dake lafe a jikinsa.




Kallonsa Amma tayi tace"aekaima kasan kwanan zancan, SHUREIM take nema, kuma wai baya zuwa school shinefa damuwan".




"Ni hankalina bekaiba, ya kamata mu duba muji ko lafiya, tashi maza ku shirya"cewar Papi.




Sai a sannan IMINAT ta dago fuskarta dauke da kayataccen murmushi ta rungumi Papi jin yace zasuje wurin SHUREIM.


Cikin kankanin lokaci suka shirya, ba wani jimawa motarsu tayi parking kofar gate din gidan Dr Ahmad inda yake cike da manyan mutane ana addu'ar sadakar ukku, nan Papi ya zauna tare dama su kabir gaesuwa yayinda Momy suka shiga ciki.




Sosai Momy ta girgiza dajin mutuwar Daddy ga SHUREIM dake kwance kwana ukku ko motsi beyi bahankalinta ya kara tashi data tuna halin da y'ar tata tilo guda d'aya zata shiga sanadin sakuwarsu da SHUREIM, sosai ta jajanta masu sannan ta karbi yaron dake hannun Momy sannan tace"kin rada masa suna? ".




Hawaye nabin kuncin Momy tace"nasa masa Ahmad zan kirasa da SHAHED".


Kurawa yaron ido IMINAT tayi sannan tayi murmushi tace"kamar yaya na, ina son wannan shima, Momy ina yaya? ".




"Kiyi shiru, yanzun zamuje na kaiki wurinsa"cewar Amma.




Sun dauki lokaci a gidan kafin suka tafi kai tsaye Asibiti suka nufa, inda aka kaisu har dakin da SHUREIM yake har yanzu yananan yadda yake sai na'u'rori dake aeki a jikinsa.




Wani irin ihu IMINAT ta kwallah ta makalkale SHUREIM tana kuka, daidai saitin fuskarsa ta tsaya tace"ka tashi kaji, banason suyi maka allura, zan kirga ukku saika tashi ko"yatsun hannunta ta daga face"1,2"ana ukku ta hada hannuwanta suka bada kara kas kas kas sannan face"3", ta saba haka yakeyi mata ba kaman idan tana fushi.




Jin karar da takeyi da hannu yasa ya soma motsa yatsun hannunshi da kafarsa ta gefan dama, sosai Dr yayi murna da samun wannan canji, IMINAT kam saida akayi da gaske tabar asibitin baya ga kuka babu abunda takeyi dukta damu.




4days latter




Yanzu kam kowa ya watse a gidan DR Ahmad babu kowa sai matarsa da yaranta, shigowarta kenan cikin gidan ta dawo daga dubo SHUREIM, tsaye tayi turus ganin Kabir da Aisha sai yaransu subata holewa a parlon cikin farin ciki da annishuwa.




"Dakata daga nan, mugun iri, wallahi bazaki shigowa tunda ba gidan Baba bane, ae ah hakura a koma gida tunda kin kasheshi kin huta"cewar kabir.




Murya na rawa tace"ban ganeba"


"Ae bazaki taba ganewa ba, zaman ya kare a gidannan, ki wuce garinku maza kuma ki bamu yaranmu"cewar Aisha.




Murmushin takaici Momy tayi tace"lallai zuciya mai mance alkairi, kamar yadda kuka fada zan tafi amma kunsan bazan taba bar maku yarana ba"ta fada tana kara rike hannun Manal da Minal ga Shahed goye a baya.




"Halan dasu kikazo?, shikenan ma kin hutar damu kije dasu amma bazamu baki komai nasuba bare ki handame, kije dasu amma SHUREIM yana nan".




Zaro ido tayi tana kallon Kabir hawaye suka gangaro mata a fuska tace"kasan bazan iya barmaka Babana ba".




Be jira cewarta ba ya ingijeta ya rufe kofar, ya Kira asibiti ya gargadesu akan kada Wanda sukaba SHUREIM, inko haka ta faru zaiyi shara'a da mutum.




Allah yaso Momy nada kudi kuma a jakarta akwai ATM kuma tanada isashshin kudi, Asibitin ta nufa duk yadda taso a bata SHUREIM haka suka hanata koda ganinsa, dole ta hakura ta dauki sauran ta wuce Gombe tana mai tsananin kuka.






IMINAT kuwa dukta rame ta fita hayyacinta, ko kadan bata da sukuni duktayi wani sukuku.




Comment and share pls.




*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


___________________________________βšœπŸ’•βšœπŸ’•βšœπŸ’•


*SO 'DAYA*


*NA*
*MARYAM ISMAIL*


*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


11β™Ύ15


Wani irin Kara SHUREIM yayi tare da mikewa ya fige drip din dake hannunsa, dafe kansa yayi take komai ya shiga dawo masa juya kai kawai yake alamun tashin hankalin yafi karfin shekarunsa wasu zafafan hawayene suka soma zarya akan fuskarsa, hakan yayi daidai da shigowar Dr tare dasu IMENAT, kafin kowa ya isa garesa ta ruga ta tsugunna tare da kama hannayensa duka biyu, rinannun idanuwansa ya bude ya saukesu gareta wata irin karayar zuciya ta kuma zo masa kuka ya saki tare da Dora kansa a cinyarta.




Bubbuga bayansa taci gaba dayi alamar lallashi gata itama idanuwan nata sun ciko da hawaye ga matukar tausayin da yake bata sannu a hankali nata ma suka fara gangarowa, cikin dakiya tace"Ayyah Yaya narh kayi hakuri kaji, kaifa ke koyamin hakuri da rayuwa da kuma in na rasa wani Abu da nakeso na jure".






D'agowa yayi yana share hawayen idonsa idanu ya zuba mata kafin ya budi baki da kyar yace"ina Momy, Manal da minal suke? ".




Kafin ta bada amsa kawo kabir dake shigowa yanzu yace"kama daina tunaninsu, sun tafi garinsu sun barmin kai nan, sbd kai namijine Kuma ta sake haihuwan wani namijin, yanzu tunda Ka warke saika tashi mu tafi gida".




Wani irin kallo SHUREIM ya soma yiwa Kawu Kabir ga maganarsa dake kuma yaduwa a cikin kunnensa.




"Kaji yaro marar tarbiyya uban naka kake kallo haka, da idanuwa kaman na mujiya"Mama Aysha ta fada.




Magana Papi yakeson yi masu amma fir sukaki kulashi, janye SHUREIM sukayi daga jikin IMINAT, jan hannunsa kawai suke ko jira basuyi Dr ya basa sallama ba, kallon juna kawai suke har IMINAT ta daina hango SHUREIM kafin wasu hawayen suka zubo mata, da kyar Ammi ta lallasheta suka shiga Mota sukayi gida.




Bangaren SHUREIM kuwa koda suka isa gida ganin sauyesauyen abubuwa yasa ya ida yarda tabbas Momy bata gidan, dakinsa yazo shiga.


"Kaiiii me nake gani haka, zo nan maza"Mama Aysha ta fada a hassale.


Kansa kasa ya tako har inda take, murde masa kunne tayi tace"Dan uwarka, in babba ya kiraka baka iya dukawa ba munafiki mai kama da yan China".


Har yanzu be kalketaba saidai yaji zagin data masa har cikin ransa dukawa yayi hawaye nason zubo masa.




Tsuka taja sannan ta hakince a d'aya daga cikin royal chairs na dakin tayi crossing leg dinta tace"daga yau bananne dakinka ba, nan dakin Abduol ne, kayan dazan iya baka kayi amfani dasu an kai maka kusa da dakin mai gani wannan karamin dakin na kusa da nashi ya isheka rayuwa, banaso kana shigowa parlor harsai inni na kiraka banason dattin jikinka, maza bacemin da gani".






Daradaran idanuwansa ya d'ago yana kare mata kallo, wata uwar tsawa Kawu kabir ya daka masa dake saukowa daga stair's yanzu, beko jira maganar kawunba ya mike ya fice zuciyarsa na tafarfasa, dakin da akace nashi nan ya shiga tsaye yayi cak yana karewa dakin kallo, wata yaloluwar katifa da wani yakutsa zanin gado ya gani, ga kayan sawa jefi jefi tsaffi na Abduol su aka zuba masa, a kyamace yake kallon dakin, dama gashi SHUREIM yanada kyama sosai bayason kazanta.




Numfasawa yayi yace a fili"tabbas yau na tabbatar na rasa gata, na rasa mahaifina ga mahaifiya ansa ta tafi ta barni"kuka yake rurus ba yanda ya iya dole yayi biyayya yayi hakuri ya zauna gefan katifar ya zauna yana aekin kuka.




Some days later.


Abubuwa da dama sun faru, SHUREIM ya tabbata maraya kuma main da gidansu duk wani aekin wahala yanzu ya saba dashi, shikema Abduol da Murja wanki da gyaran rooms nasu babu abunda yake tada masa hankali irin makarantar da aka ciresa kullun yana zaman bauta ga abinci ba'a bashi sabo Sai Wanda ya kwana tun baya zurewa har ya soma jurewa, kuma Kawu yace shi namiji ne yaje ya nema kama daga sabulun wanka, na wanki, abubuwan yaudai da kullun shi ya nema ma kansa.




Wanki ya gamayi da sauri ya zuri sidadiyar slifas dinsa ya ruga da gudu zuwa inda suke bara shida wani abokinsa Dani, yakoci sa'a motar da yake dako bata wuceba lokacin zuwanta kenan, wurin motar ya karasa da sauri.


Motar kirar Benz ga ko ina bakin kirin baka iya hango Wanda ke ciki, saidai shiya ganka, gilas din motar aka zuge kadan kamar kullun takeaway ne da dari biyar kullun haka take basa, mika hannu yayi ya karba yana godiya yayinda ta kuma mikowa Sani nashi, cike da murna suka karba tare da juyawa.




Komawa jikin chair din motar IMINAT tayi tana share hawayen idonta, kuka ya kwace mata sosai dukda tanada kananun shekaru besa ta kasa gane halin da SHUREIM dinta yake ciki ba, ga Kawunsa ya hana Papi sakashi makaranta, har suka isa school kuka take kullun haka takeyi, fita tayi Driver yaja ya koma gida, daidai inda suke zama da SHUREIM nan ta kallah tana wani kukan zuciyarta cike da kunci yanzu dukta canza ta fita hayyacinta kullun haka take zama sukuku har lokacin tashi yayi.






*ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: βšœπŸ’•βšœπŸ’•βšœπŸ’•


*SO 'DAYA*


*NA*
*MARYAM ISMAIL*


*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*


(United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)




16β™Ύ20


Bangaren SHUREIM kuwa bakin wata bishiya suka zauna shida Sani, abincin sukeci suna dan fira jefi jefi kasancewar SHUREIM baya da hayani, kallonsa sani yayi yace"yanzu kaga kudinnan sai naje na siyi sabulun wanki na wanke kayana ko nadan fito tatas".




Murmushi SHUREIM yayi yace"sai ka godewa Allah da kuma wannan baiwar Allah da take kokarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login