Showing 27001 words to 28816 words out of 28816 words
Chapter 10 - SO DAYA Book Complete BY MARYAM ISMA'IL.txt
maki".
"Ku daina rokona,kunmun halaccin da ya kamata Ku bani umarni kawai Ku kuka rikemun d'ana ,babu abunda zance saidai godiya".
Murya na rawa kawu kabir yace" kaico na dana zama mai son kai,Ku yafe mani don Allah nikam tawa tazo karshe,Nina kashe d'an uwana da kaina dukdon na mallaki dukiyarsa kuma na samu hakan ,don Allah Ku yafemun kona samu rahama sharrin shaidanne,Shureim na cutar dakai matuka don Allah Ku yafe mun".
Tunda ya ambaci shiya kashe mata miji ta kasa fahimtar komai da yake fad'a ,zuciyarta na kuna da tafarfasa tana binsu da mugun kallo,ji takeyi kamar yanzu mutuwar mijin nata yake ,hawaye ne suka soma zarya a kuncinta ta furta"Kabir kun cucemu,kun maidani bazawara kun maidamun yara marayu dukdon kuji dadin duniya innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"sosai ita dasu Minal ke kuka.
Dukawa har kasa Aunty Aysha tayi tana fadin"sherin shedanne da son abun duniya,don Allah Ku yafe mana wallahi tun duniya munga sakamako"ta kare maganar hawaye na malala a fuskarta.
"Aunty kibar kuka ,mun yafe maku,kuje Ku nemi yafiyar ubangiji,ina Abduol da Murja?" Farooq ya tambaya.
Kara fashewa tayi da kuka tana fad'in"na gode Umar ,na gode,Umar Abduol an kamasu sunyi fashi ,akace kada su gudu shine shi yayi gudu suka harbesa ya mutu nan take,bayan mutuwarsa da sati d'aya daf ta taka Murja tabi kwalta,yanzu sora mu kad'ai ".
Wani mugun tausayinta yaji yana ratsashi hankali tashe ya isa gaban Mom ya duka har k'asa yace" Mom kiji halin da suka koma,komai zai faru ya riga ya faru,Mom don Allah Ku yafe masu"
Hawayen idanuwanta ta goge tace"Shureim na yafe masu duniya da lahira ".
Nan su Manal ma sukace sun yafe masu.
Da kyar kawu ya budi baki yana haki yace" mun gode sosai nikam mutuwa zanyi"file ya dakko na wasu takardu yaba Shureim a hannu yace "takardun gadonku Allah yayi maku albarka"
Nan take tari ya sarkeshi kafin suyi yunkurin cetoshi tuni ya rigamu gidan gaskiya(rai bakon duniya ,koya dade a ciki zai koma ,Allah ka bamu kyakyawan karshe)
Kuka rurusus Aunty Aysha tasa da su Manal kuka kawai sukeyi sosai suke tausaya mata,basu waniyi gayyaba aka rufeshi ,sai la'asar kowa ya kama gabanshi,anan akabar Aunty Aysha.
Yaukam duniyar ta idasa rudewa Farooq gasu zaune da yamma anata shirin tafiya kamu,Dr Nasir da yasan damuwarsa sai kara bashi shawarwari yakeyi,gashi dai zaune da rai amma zuciyarsa sai bugawa takeyi dakyar yake lalu bo numfashi hankali tashe,a haka suka shirya tsab dasu ango cikin gazna ash colour yayi masifar kyau,yayinda Nasir da Farooq sukasa ado cikin tasu gezna blue colour sunyi kyau sosai da sosai ,ango shi zai dauki amarya da kansa, don ha su da sauran abokansa suka wuce suka fara kai kawayenta wurin kamu.
*ALK'ALAMIN MARYAMA*
Maji dadi ceβπ»
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*SO D'AYA*
Story and written by
Maryam Ismail
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
Page 141βΎ145
Abunda kunnuwana suka jiyomin yasa na kara karkadesu domin ji nikeyi kamar ba daidai nake jiyowa ba haka mutanan wurin suma suka daskare domin bada wannan niyar suka zo ba, Iminat data jiyo daga cikin gida mikewa tayi tsaye tana bin Amma da kallo tuhuma, Farooq kam kallon Nasir kawai yakeyi yana fadin "bazai yiwuba waye yayi wannan da gaske kaji me naji kuwa Dr? "ya tamabaya a kidime.
"naji mana an daura auran *FAROOQ ISMAIL DA ZEENATU AHMAD DA KUMA AMEER JABIR DA AMRAH MUHAMMAD* akan sadaki nera dubu hamsin ko wannensu ina tayaka murna Angon Iminat maza muje yanzu mutane zasu fara nemanka "Nasir ya bashi amsa.
Shikam tsaye yayi ya kasa koda kwakwaran motsi hannu Nasir yasa ya jashi suka fito cikin mutane sai binsu akeyi da kallo da sauri Ameer ya iso wurin yace "Wallahi Nasiru bakayiba jifa koka gyarashi bakayi ba".
"au ladar kirana Nasirun zan gyara maka gawa taki ramin taka da yanzu mun kusa makabarta wallahi shege amma kuji yayi wuki wuki da idanu "Nasir ya kare maganar yana kyalkyalewa da dariya. Duka Ameer ya kawo masa ya goce shikam Farooq Ameer kawai ya tsare da idanuwa ko kiftawa bayayi, babbar rigar hannunsa Ameer ya karba ya saka masa ya gyara masa ya dora masa hularsa ya karbi takalmansa ya ajiye masa ya saka sannan yace "ko kaifa amma anga Ango a harmutse please kayi Murmushi ko kayi kyau, ina tayaka murna angon Iminat Allah ya bada zaman lafiya da hakuri da juna"ya kare maganar yana jan hannunsa suka kutsa cikin mutane, shikam Farooq ya kasa gane komai kawai dai yana godiyar taya murnar da ake masa mamaki kam ba adadi sai Bin Ameer yake da kallo da ko a kwalarshi sai mirnarshi yakeyi hardai mutane suka watse sannan yajashi tare da Nasir suka wuce parlon baki na gidansu Iminat anan suka samu meeting din da Papi ya hada kowa ya hallara su kadai ake jira, da sallama suka shiga dakin can nesa dasu Iminat suka samu suka zauna tare da gaishe da iyayen nasu.
Taro Daddy (Alhaji Ismail) ya bude da addu'a sannan yace "dalilin da yasa muka taraku anan nasan dukanku kuna cike da mamaki da tambayoyi to ba wani abun damuwa bane tunda Allah ya bamu yaro mai tunani da hangen nesa lallai Ameer ya cika Amini kuma dan uwa,jiya da dare ya samesu akan yanaso yau a daura auran farooq da zinatu, sam munki amince masa munki yarda, amma ya dage saida muka yarda zai maku bayanin wannan da kanshi Ameer bismillah "Daddy ya fada.
sunkuyar da kai yayi kasa yace "lokacin da najewa iyayenmu da wannan maganar Sun dauka na zautune amma Allah cikin ikinsa yasa na dage har suka fahimceni kuma nayi haka ne don cika burikan masoya guda biyu wanda idan dana auri Zeenat nasan na shiga hakkinsu domin Farooq ya fini bukatarta itace muradinshi duk abunda kukeyi na sani har ciwan daka kamu saboda soyayyarta tun daga ranar da kuka hadu gidan gona na gane itace Iminat dinka kai kuma kaine Shureim dinta na shareku ne na nuna ban sani ba saboda a lokacin konace nabar maka ita bazaka yardaba so ba karya bane tabbas naso Zeenat amma nayita addu'a har Allah ya yayemun, kuma a daran jiyane na nemi amincewar Amrah data aureni da farko taki yarda amma dana mata bayani ta yarda kuma ta sadaukar da soyayyar da takewa Farooq zuwa ga kawarta a cikin daran na samu auranta fatana dai abunda mukayi ya amfanemu wannan ba komai bane".
Parlon kaf kowa sakawa Ameer da Amrah albarka yakeyi domin Sun jinjina namijin kokarin da sukayi.
Zeenat kam kasa cewa Amrah komai tayi saidai ta fashe da kuka suka rungume juna, da kyar tace "Allah ya bani abunda zan saka maku dashi keda brother na".
Dariya Amrah tayi tace "karki wani damu Kin manta alkawarin da mukayi muna yara farkon ganina dake nace har abada zan tsaya maki har raina zai zama fansa gareki ".dariya suka saka.
Farooq kam rike hannun Ameer yayi yace "na gode lallai ka cika amini, Allah yayi maka yacce kayimun bazan taba mantawa dakai ba"
Da ameen kowa ke ansawa haka taro ya watse cikin farin ciki da annushuwa, akaci gaba da hidimar biki da yamma akakai Amare dakin su, gidan ya kasance babban Gate ne amma apartment biyu ne komai iri daya Daddy ne ya basu gidan amare sunsha kuka da nasihohi basu damu sosaiba kasancewar wuri daya zasu zauna kafin aka kaisu dakin mazajensu saidai fatan zaman Lafiya.
(yaufa farin ciki namuna kuzo mu taka rawar shoookiii)
#Maji dad'i βπ»
[2/14, 9:07 PM] Majidadin Kainuwa: ππΉππΉππΉππΉππΉππΉππΉπ
ππΉππΉππΉππΉ
*SO D'AYA*
Story and written by
Maryam Ismail
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* βπ»
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
Page 145βΎ150
Last page
πππππππ
6years later
Yarane kanana ke zagaye babban Gate din gidan sai faman kira Ummi takeyi tana fadin "Ummi kice yaya Haidar ya bani ball dina bazan yarda ba "kyakyawar yarinyar mai kama da IMinat sak ke fada.
Fitowar Daddyn dinta yasa ta ruga da gudu ta rungumi Farooq tana kiran "Daddy yaki bani ball"
Shafa kanta yayi yace "yi hakuri Mamana zai baki yanzu"
"meye na Mace dayin ball ta hana haidar sakewa, kinga Ikram bakyaji ko? "Iminat ta fada tana sabata ga kafada
Asalin sunan Ikram shine Halimatu takwarar Momy shine suke kiranta da ikram.
Khalid kuwa sai dariya yakeyi mata wai an anshe Ball.
Amir ne da Amrah suka fito ga Amrah da katon ciki tana rike da hannun yarta Mace mai suna Humaira, karbar Ikram yayi daga hannun Iminat yace "halan zalinta wannan yaran sukaci kukuma kun tusata gaba tana bata rai"
"eh Abba Yaya khalid da Yaya Haidar Sun hanani Ball dina fa"
Gardama suka shigayi da fadin bafa tata bace Abba, Kallon Iminat yayi yace "ina takwarana ban ganshi kin goya ba "
"yana bacci little kam"
Ba arziki ya saka yaran duka mota suka fice sake siyan kayan wasan sai yamma suka dawo Gidan.
Tsaye take gaban mirrow tanata faman daurin dan kwali shigowarsa kenan dakin ya rungumota ta baya yace "dama Kin daina daurin dan kwali so nake yau na kuma baki Baby fa ".
Zaro ido Iminat tayi tare da shafa cikinta tace "haba Yaya ka rufamun asiri duka yaushe na haifi Ameer "
"yara ishirin nike so ki haifaman fa yanzu duka Haidar da Ikram kika bani sai Ameer ".
hannu ta daura aka tana zura idanuwa harsun fara tara ruwa
Dariya Farooq ya kwashe dashi yace"wasa nike maki fa matsoraciya ".
Dariya itama tayi ta fada jikinshi ya rungume abunsa cikin farin ciki da tsantsar soyayya.
"kinsan dakin haifi namiji sunansa Farooq my lovely Buddy "Ameer ya fada yana shafa cikin Amrah
Murmushi tayi tace" nifa Mace nikeso nasa mata Zeenat "ta kare maganan tana kwabe fuska .
"naki wayan nidai kam,ga Khalid ga Humaira duka na baki su ni kuma Allah ya bani Farooq "
"To Allah ya bamu masu albarka "
Ya amsa da Ameen
Minal Da Manal ma sunyi aure har Minal ta haihu, Manal kuwa tanada tsohwan cikinta ,sai Shaheed da yanzu yake aiki ya gama karatunsa kamar yarda yayyansa suka gama.
Alhmdllh farin ciki ya wanzu Sosai a family dinsu mai albarka kullun ci gaba suke gani ,Amrah ta haihu burin Ameer ya cika ya samu Farooq kam.
Dukansu suna cikin farin ciki da soyayyar juna.
Alhmadllh godiya ga sarki Allah daya bani ikon rubuta littafin nan kuma yasa naga karshensa lafiya. Kurakuran dake ciki Allah ya yafe mana Allah kuwa ya bamu ikon amfana da abunda ke ciki.
Sakon gaisuwa ga dukkan masoyana a fadin duniyar nan aduk inda kuke ina alfahari daku ina kuma godiya da soyayyarku gareni, fatan alkhairi gareku ako yaushe bamayi Saidaku Kuma sai damu ina alfahari daku. Much love
Vote, comment and share
09030953294
#Maji dadin kainuwa