Showing 159001 words to 162000 words out of 196911 words

Chapter 54 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

son barin bacin rai yana masa tasiri ba.


Ba jimawa baba usaina ta fice,daga bisani hafsat din ta fito yaran suna biye da ita,hajiya a bayansu tana rabawa yaran alawa da manyan biscuits data saba basu,daga inda yake zaune yana kallonsu,yasan babu lallai su ganshi,har suka fice daga gidan ya kasa motsawa sai rakiya da yayi musu da idanu.


Sai da aka kira azahar ya fita masallaci yayi sallah,daya dawo sai ya bude setting room din gidan dake farfajiyar gidan ya kwanta,har yanzu abun yana masa yawo a zuciya,shi har yanzu baiyi girman da za'a daina kawowa hajiya da kawunnansa qararsa ba?,har yanzu baiyi girman da kunnuwan hajiya zasu daina jin matsalarsa da damuwarsa ba?,har yanzu hafsat batayi hankalin da zata zauna dashi su fahimci juna su warware matsalarsu ba shi da ita ba tare da duniya taji ba?,kansa ya kada a hankali yana kiran sunan Allah,ya rasa yadda zai rabata da wannan halin,bayan shi din har yau bayajin zai iya tuna wata rana da ya taba kai qararta gidansu ba.


Wayarsa dake saman kansa ya dauko,ya lalubo number dinta dake rubuce da sunan BABY DOLL ya kira, ringing daya aka daga,muneera ce,ta gaya masa sallah takeyi,yace idan ta idar ta gaya mata ta sameshi a setting room,ya ajjiye wayar yana gyara kwanciyarsa.


Minti biyar cikakku qamshinta ya fara marabtarsa,ya rufe idanunsa yana budesu,suka sauka a kanta,hannunta dauke da madaidaicin tray data dora wani glass jug akai da qaramin cup guda daya.


Ido ya zuba mata yana qare mata kallo son ranshi,kamar kowanne lokaci sai yaji damuwarsa tana raguwa,a nutse ta iso ta sunkuya a gabansa tana ajjiye masa jug din,sai ya fara yunqurin tashi,ta miqe zata ja baya ya samu nasarar riqota,yayi mata mazauni saman cinyarsa,kunya ta sanyata boye kanta a kafadarsa,taqi yarda su hada ido


"Ki kalleni please baby.......zuciyata ba dadi,nasan zan samu relief" har cikin zuciyarta taji wani abu ya tabata da fadin hakan,saita daga kanta da sauri,kodai qarar da mommy hafsat ta kawowa hajiya ce ta bata ransa?,ta tuna kalaman mommynta na qarshe


"Banda kai miji qara,abune mara kyau,koni bance ki kawomin qararsa ba,idan ya bata miki rai ki gaya masa ku fahimci juna" sannan ta tuna da kalaman ummunta


"Kome mijinki yayi miki ya isa ne,banason qorafe qorafe dakai qara" sannan tana tuna yadda take sanya yayyensu a gaba da fada duk sanda kika kawo mata qorafi akan mijinki,musamman idan bai gamsheta ba


"Kayi haquri" ta furta da tausasan labbanta da ko yaushe suke burgeshi,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ya rabb......ba ita tayi laifi ba,amma ita take bada haquri,ya tabbatar idan zai dige indai ba wuya ce tayi wuya ba zaiyi wahala wannan kalmar ta fita a bakin hafsa


"Zan haqura,amma saikin yarda na taba nan" ya fada yana mata nuni da qirjinta da yadan sake cika,da sauri ta kama hannunsa da yayi mata nunin dashi tana fidda ido waje,saidai kafin tace wani abu ya langabe mata kai kamar ba shine babansu mimi ba


"Don Allah,kiji tausayina mana" kafada ta noqe masa itama tana shagwabe masa


"To na kwanta agun ko na minti daya ne,idan kikace aah fa zanyi kuka" dariya yaso bata,amma tsoro tsoron da takeji ya danneta,kafin ta bashi amsa ya kama dukka hannayenta biyu ya riqe cikin nasa,ya kuma cusa fuskarsa da kyau tsakanin qirjin nata.


Sosai ya zuqi numfashi ya kuma fesar,ta lumshe idonta tana jin yadda dumin numfashin yake ratsa ta tun daga rigarta zuwa brassiere dinta,ya kuma tarar da fatar wajen.


Wani irin abu data kasa daurewa ya zarce dayi mata yana sake cusa kansa a wajen,ta zame hannuwanta daga cikin nasa ta riqe kansa da kyau,sai ya tsaya cak jin yadda jikinta ya dauki rawa,ya kuma zare fuskar tasa,ya sauke idanunsa da suka kada sukayi jaa saman fuskarta.


Sai daya dauki wasu sakanni yana kallonta sannan ya motsa bakinsa cikinn shaqaqqiyar muryasa yace


"Ina da buqatarki baby.....ina da buqatarki gaba dayanki,rayuwata na da buqatarki fiye da yadda ruhi yake da buqatar numfashi" kalaman sun mata nauyi sosai,saita kifa kanta kawai a qirjinsa bugun zuciyarta na qaruwa.


Sun jima a haka kafin ta zame jikinta ta sauka qasa ta bude jug din,smoothie ne na banana da yasha madara data jefawa qananun ice cube a ciki yayi madaidaicin sanyi,ta tsiyaya ta miqa masa a cup.


"Na gode" ya fada yana karba,kunyarsa tasa ta sakin murmushi kawai,ya kurba ya lumshe ido,dadinsa yana ratsa kunnuwansa


"Yaushe kika koyi wanann?"


"Jiya,yayi dadi" sai daya jijjiga kai sannan yace


"Over!" Yadda ya fada din ya bata dariya
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*


Page 83




"wait.....amma fa da matsala" saita tsaya tana kallonsa da idanuntan nan dake cike da quruciya da rashin wayau a wasu lokuttan,muryarsa ya sassauta sosai


"Eh mana,wannan abun da gani zai haifar da tashin hankali.......idan nasha ya zamemin matsala babu me saukemin hayaqin da zai tashi a kaina,gashi kedin raguwa ce,first night saida kika ziyarci asibiti" curewa tayi guri guda tana cewa


"Wayyo Allah ummu na"


"Wayyo Allah hajiyata,sonta zai kashe miki danki" ya fada cikin murya mai taushi qasa da tata jikinsa yana saki gaba daya.


Kasa jurewa tayi,saboda bugu da zuciyarta keyi,saita zane ta fice da sauri,ya bita da kallo hade da murmushi,haka auren me quruciya yake da dadi?.


Wayarsa dake ringing ce ta dawo dashi daga tunanin da ya lula,sai ya daukota yana duba me kiran.


Suraj ne,yadan shafi kansa kadan kafin ya daga,don yasan sai yasha qorafi.


Suna gama gaisawa qorafin kuwa ya biyo baya


"Ban san ko widad din ce ke boye ka ba kuma,tunda dai daa ba haka kake ba" murmushi ya saki yana kurbar smoothie din


"Yanayin aiki ne kawai"


"Anyway,next week zamu shigo kadunan da madam"


"Yayi,aikin ya biyo ta garinmu kenan" abbas ya fada,sai kuma suka fada wata hirar.


Ranar bai bar gidan ba sai bayan magariba,yana isa unguwarsu ana sallar isha'i,ya tsaya a masallacin layinsu yayi sallar sannan ya isa gidan.


Kamar ko yaushe,koda meye tayi masa baya fasa shiga sassanta idan ya dawo,ba don komai ba sai don yaransa,ya samesu kwance qasan carfet bacci yayi awon gaba dasu,ya tsallaketa tana zaune tana waya yasa hannu ya kwashesu ya kaisu dakinsu,duk da dakin ba'a kintse yake ba,amma kuma yafi falon data barsu,ya gyara zanin gadon ya kwantar dasu,ya duba laundry basket dinsu da yake cike taf da kaya da uban bedsheet dinsu masu kyau da tsada,amma sunyi datti kuma bata da lokacin da zata tsaya ta hadasu ta zagaya baya inda washing machine yake ta wanke ba,ko ta bayar wa sale yaron gidan ya wanke su ba


"Allah ya sawwaqe" ya fada a fili,yana raya a ransa gobe zai zauna da kansa ya gyara musu dakin nasu ya fidda kayan ya bayar a wanke musu kafin ya koma,don yaci alwashin ya daina mata gyaran sashe,tunda abun nata sake ci gaba yakeyi.


Kafin ya fito ta hattama wayar,saita sauke qafafunta dake saman center table tana fadin


"Sannu da zuwa"


"Yauwa" ya amsa sama sama yana zama hannun kujera,yayi imanin zaiyi wuya ya zauna cikin kujerar baici karo da danshin ruwa lemo ko fitsari ba


"A kawo maka abinci?" Ta tambayeshi tana danna waya,sai ya girgiza kai sannan yace


"Ajjiye wayar nan zamuyi magana" dan kallonsa tayi sannan ta aje wayar tana kallonsa


"Nace shekararmu nawa yanzu da aure?" Dan jim tayi sannan tace


"Kamar shida cikin ta bakwai"


"Good......me yasa har yanzu kika kasa fahimtar zahirin rayuwa hafsa?,me yasa har yau kika kasa gane kina tafka kusakurai da hankalinki ya kamata ace yakai kai kin kuma gyara" fuska ta bata sosai


"Wanne kuskure kuma nayi?,wai don Allah me yasa bakason zaman lafiya abban mimi?" Da ido ya tsareta,saita kauda nata idon daga kansa,ta sani nashi idanun yafi nata kaifi nesa ba kusa ba,ta hade rai sosai,ya janye idonsa yana miqewa hadi da saka hannunsa a aljihun wandonsa yana kallonta,baisan me yake damun kanta ba,gidadanci ne ko rainin wayo?,komai ka gaya mata ba zata gane ba, batasan maslaha ba batasan fada ba,duka dai dai take daukan kowanne,tunda taqi fuskantar alqibla,bari ya bita da zafi zafi tunda ya fahimci tafi ganewa hakan


"Tunda baki ganewa kuskure ko laifi......fine,gobe banason na tashi na samu wannan tulin qazantar dake sassan nan,idan ma ke tana miki dadin zama ne a cikinta,to karki sake na samu daki da jikin yarana a yadda na sameshi yau" ya qarashe maganar a zafafe,sannan ya juya da dan hanzarinsa ya fice daga sashen.


Kamar idanunta zai fado saboda kallon data bishi dashi,kallon da inda yana tsaye ne a gabanta bata isa tayi masa shi ba,taja dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta rasa wanne kalar miji Allah ya hadata dashi,taurin kai kafiya da kuma tsatstsauran ra'ayi,dole ta tattare komai.nata ta wuce daki,gwara ta kwanta da wuri ko ta samu ta tashi da wuri ta gyara iya abinda take ganin zata iya,a goben ma idan widad din bata dawo ba to tabbas zata dauki mota taje ta daukota da kanta ta dawo da ita cikin ruwan sanyi da kwantar da kai,ta yadda babu wanda zai fahimci manufarta.


**********Ranar lahadi,ranar daya zamana saura kwana guda suraj da matarsa suzo,yana gida ranar,don haka duk wasu ayyuka shi ya kama mata sukayi tare,suka gyara kowanne daki yadda zai dace da zaman kowa a cikinsu.


Dakinta ne na qarshe,sun gama komai tare,ta tsaya hannayenta riqe a qugunta tana kallon yadda ya sauya fasalin dakin tana murmushi.


Sanda take kallon dakin shi kuma ita yake kallo,wani short rubber wando ne a jikinta,wanda da kadan ya wuce gwiwarta,sai kuma rigar kayan mai gajeran kayan data fidda shape dinta sosai.


Da wani siririn rubber band kalar kayan jikinta ta daure gashin kanta,hakan ya baiwa doguwar jelarta mai santsi damar reto a bayanta.


Kusan yaune ranar farko data fara irin wannan shigar saboda aikin da zasuyi,amma iya yau din gaba daya ta hanashi sukuni,duk inda ta motsa idanuwanta suna biye dashi


"Finished uncle" ta fadi tana dubansa tana murmushi,sai ya mayar mata da murmushinta,yanason ya gaya mata ta debi wasu kayan nata da zatayi amfani dasu ta maida dakinsa amma kuma bayason plan dinsa ya rushe,gwara ya barta a hakan,sannu sannu bata hana zuwa.


*W A S H E G A R I*


K'arfe uku na rana su suraj suka iso kaduna,bilkisa matar suraj akwai fara'a kirki da kuma saurin sabo,tun ba yau ba suna hira sosai da widad din ta watsapp,wannan yasa ba wani baqunta can me yawa a tsakaninsu ba.


A nan falo suka zauna bayan abbas ya shiga musu da kayansu ciki,suka koma balcony din sashen suka zauna sukabar su widad din a falo.


Basu rufa mintuna ashirin ba aka kira sallar la'asar,saida dukkansu suka bada farali sannan suka zauna zaman cin abinci,su suna balcony din saman lallausan carfet,ita da bilkisa suna zaune a falon,suna ci suna taba hira.


K'arfe takwas na dare ta shigo dakin da bilkisa ta sauka,rigar bacci ce a jikinta wadda ta sauka har kusa da idon sawunta,saita dora hijabi a kai wanda bai wuce qugunta ba.


Da murmushi bilkisa dake gaban mudubi tana fa shafe shafen turaruka ta waiwayo tana amsa mata,widad ta qaraso tana hayewa saman gadon gami da jan pillow


"Na zaci har kin kwanta" kai ta girgiza


"Ina ni ina bacci mai gidana bai dawo ba" qaramin murmushi widad ta saki tana rayawa a ranta


"Kamar wani qaramin yaro" duk da cewa ita dinma tun dazu take leqawa ta window idan taji motsi taga ko uncle din nata ne,tunda suka fita bayan sun gama cin abinci basu dawo ba.


Duk da sun sha hira sosai da balkisa,ta kuma debe mata kewa amma sai takejin gidan gaba daya wani iri babu dadi


"Nima har na fara jin kamar bacci bacci" ta fada tana maida pillow din saman gadon zata kwanta,sai bilkisa ta juyo da sauri tana dubanta


"Aah.....shi kuma abbansu ahmad din na kaishi ina?"


"Zasu kwana tare da uncle fa" ta fada adan shagwabe


"Aah wlh ban gayyato ki ba,haka kawai kisa nayi baqinjini wajen yallabai yana ganin mutuncina?,daga zuwana na rabashi da amaryarshi"


"Mom Ahmad wallahi kema kin faye tsokana" widad ta fada tana gyara kwanciyarta,bilkisana qoqarin saka wandon sleeping dress dinta tace


"Banda quruciya dake dawainiya dake..... yaci ace kin karanci irin kallon da yake binki dashi duk sanda kika gifta ta gabanshi,ina tsoro nan gaba kada yallabai ya fara tafiya yana kiran sunanki,idan haka ta faru kam hafsat inajin hadiyar zuciya zatayi ta mutu"


"Kai mom Ahmad kai anty bilkisa" widad ta fada tana dariya sosai,don ita dariya ma maganar ta bata


"To ita kuma mommy hafsat me zai sakata mutuwa don kawai uncle na kiran sunana?" Tambayar data sanya bilkisa maida dubanta sosai ga widad,da alama dai har yau batasan wace kishiya ba,batasan kuma kishi ba,uwa uba batasan wace hafsat sani na badini ba,kallon zahiri take mata


"Kishiya irin hafsat ba zasu taba son suga miji irin uncle dinki.yana sonki ba,ba zasu taba so suga kina masa wani abu da zaiji dadi ba"


"Amma mom ahmad,ni bata taba nunamin komai ba" kallonta sosai ta sakeyi


"Ta gama yi miki komai din ai ba tare da kin ankara ba,saboda tasan ba lallai tunaninki ya kawo miki komai ba a kai" Shuru widad tayi tana juya maganar,zancan da suka taba yi da anty madeena ya dawo mata sanda take gaya mata ba gaskiya bane abinda hafsat din ta dinga gaya mata tana tsoratar da ita,to me hakan ke nufi?,wannan shine kishin?,idan kuwa shine yafi kama da HASSADA kawai


"Idan kina tantama daga yau ki sake mata dukkan aikin da kike mata.....ki kula da uncle dinki,don nasan har yanzu idan ta samu dama sakaki aiki takeyi" maganar bilkisa ta saka widad a tunani sosai,kafin tace komai muryoyinsu sun bayyana a falon alamun sun dawo.


Tare suka fita da bilkisa din,saidai suraj din kawai suka samu yana shirin shigowa ciki,dole widad ta yiwa bilkisa sallama ta wuce nasu dakin.


Ta tura dakin ta shiga,baya ciki amma ga kayanshi nan saman gadon,sai ta qarasa a hankali ta debesu,ta ninkesu sannan ta zubasu a laundry basket,takalman ma tayi musu waje,sai ta koma kan sofa bed ta zauna ta kunna data dinta ta shiga watsapp tana duba saqonni.


Qofar bandakin ya bude ya fito,daure da towel da ya daurashi daga qugunsa,duka duka tsahonsa kuma iya gwiwa,duk wata qirar jikinsa ta bayyana a waje sosai,qaqqarfan jiki daya ginu da excercise.


Bata zaci a haka ya fito ba....wannan yasa ta daga kai,saidai suna hada ido tayi saurin maida idanunta kan wayar tana raba idanu.


Karamin murmushi ya saki,har cikin zuciyarsa yana jin dadin yadda ta kasance,amma a fuska bai nuna ba,yadan basar duk da yadda taketa fusgar hankalinsa,don already ta cire hijabin ta ta ajjiye don tasha iska,yadda ta nannade gashinta yayi masifar jan hankalinsa.


Sannu da zuwa tayi masa tana ta babbasarwa,ya amsa mata yana janta da hira,yayi kaman bai gane ba,ya tsaya gaban madubi yana shiryawa yana satar kallonta ta ciki,cikin dace ya dinga kamata itama tana satar kallonsa,amma duk sanda ya gani din saita bagarar,abin ya dinga bashi dariya sosai,amma ya dinga cinyewa cikin miskilancinsa,har ya gama shirinsa tsaf cikin dakin ya kuma zauna ta zuba masa abinci ya soma ci.


Yana cin yana kallonta da lumsassun idanunsa har ya kammala,cin abincin da da wankan sun ja masa kusan awa biyu,zuwa sannan jikinsa ya gama saki,gaba daya muradinta yakeyi,sai ya miqe,ya zare kayan jikinsa,yabar iya boxer kawai,ya koma saman gadon ya kwanta rub da ciki yana lumshe idanunsa.


Shuru ya ratsa dakin,sai ya bude idonsa a hankali ya zube a kanta,daga yadda take zaune yasan itama kwanciya takesonyi amma tana shakkar rabarsa


"Baby...." Yayi kiranta a tausashe,muryarsa can qasan maqoshinsa,saita daga fararen idanuwanta ta kalleshi, idanunsu suka gauraya waje daya,wani abu taji ya taba zuciyarta sosai


"Am very tired........zo kiyimin tausa please baby" ya fada yana narkewa hadi da yin fuskarsa tausayi,idanunsa suna lumshewa saman fuskarta,yana jin kamar yakai gareta ya fusgota.
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*




Page 84




Yadda yayi din sai ya bata tausayi,don haka ta ajjiye wayar tana cewa


"Wai tausa da dadi ne?" Dariya ta taso masa amma a yanayin da yake ciki batayi wani tasiri ba,ya maye gurbin ta da murmushi don ta bashi dariyar sosai can qasan ransa


"Sosaima" ya furta a hankali yana lumshe idanunsa sanda tattausan tafin hannunta ya sauka a tsakiyar bayansa.


Tun tana dari dari har ta sake,ta dage ita bilhaqqi da gaske tausa take masa,yayin da idanunsa suka kasance a rufe,yana jin yadda hannuwanta ke kai komo a bayansa,shi kadai yasan abinda yake ji cikin ruhi da gangar jikinsa.


Kasa daurewa yayi,cikin wani irin zafin nama yayi mata wani irin juyi ya maidata gurbin daya tashi shi kuma ya maye nata gurbin ta hanyar mamayeta gaba daya,hadi da yi mata rumfa da mayalwacin qirjinsa.


Tsoro ya gani a rubuce cikin idanunta,ta soma rarrabasu tana kallon gajiyayyar fuskarsa dake cike da shauqi da mayen so da qaunarta,da kuma burin kasancewa da ita.


A tausashe ya rungumota cikin jikinsa,fatarsu ta hade guri guda,dumin jikin junansu ya gauraye waje daya,ya sanya kansa cikin wuyanta ta soma gaya mata wasu kalamai da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sakata narkewa a wajen ba tare data sake qwaqwqwaran motsi ba.


Cikin salo da kuma qwarewa ya fara aike mata da wasu saqonni da dukkan jikin da jini ke gudana a cikinsa zaiyi wuya ya tsallake musu,saqonnin da suka dinga bin dukka wata jijiya dake aike da tunani da kuma tantance abu suna tsinketa,suka dinga dilmiyar da ita zuwa wani bigire na daban,bigiren da dukka wani tsoro nata ya gushe yayi nasa waje.


Saida komai ya kankama sannan ta fara gani kuskuren data tafka,tuni aikin gama ya gama,ya sake tabbatar wa zuciyarsa da gangar jikinsa cewa ita din mallakinsa ce halak malak.


Kamar wancan karon,wannan karon ma yanayi ya shiga sosai,ya riqeta sosai cikin jikinsa yana sauraren siririn kukan da take fitarwa,wanda kusan fiye da rabinsa shagwaba tafi yawa a ciki,yasan yau dinma dole zata jigata ta kuma ji jiki,don shi kansa yasan halinsa ta wannan fannin,amma kuma bazai kai karonsu na farko ba,baiji komai ba ya biye mata ya dinga lallashin abarsa,yana kuma dauke kowanne hawaye nata da harshensa.


Jinta yake takai masa ko ina,koma meye zai iya yi mata,haka ya lalace wajen rarrashinta.


Har sukayi sallar asuba suka idar taqi duban fuskarsa,ta gaidashi kanta a qasa,ya saki murmushi,ya matso kusa da ita ya zauna sosai har gwiwoyinsu suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login