Showing 156001 words to 159000 words out of 196911 words

Chapter 53 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

taba zuciyarsa,irin abinda bai tana jin kamarsa ba,duk da dama shi din kusan weak point dinsa kenan


"Is okay" ya fada yana sanya hannunsa cikin nata,sannan ya bawa samuel umarnin canza titi zuwa titin da zai kaisu unguwar gida dubu.


Ajiyar zuciya ta sauke,ta sake lafewa tana dan sakin murmushi


"Na gode" waiwaya yayi a hankali ya kalleta,sai ya sanya hannu yaja hancinta


"Karkiyi saurin godemin,don idan munje ba lallai bane na barki ki kwana ba" baki ta tura gaba,sai ta kwantar da kanta ba tare da tace masa komai ba,ya sake sakin qaramin murmushi yana kallon hanya hadi da matse hannunta sosai kuma a tausashe cikin tafin hannunsa,can qasan zuciyarsa yana jin wani abu mai qarfi a kanta yana sake ginuwa.


Ita ta fara shigewa gidan hajiyan cike da karsashi, zuciyarta fal farinciki,don kusan wata guda kenan bata zo ba,zuwanta na qarshe har suka koma batazo gidan ba.


Su biyu ne falon,ita da gwaggwo fanteka suna taba hira,sun gama cin abinci kenan tayi sallama,sosai farincikin dake fuskar hajiyan ya bayyana,ta amsa sallamar tana cewa


"A'ah,mutan kaduna.....irin wannan ba zata haka?"


"Aiko dai,haka amaryar abas din ta fara canzawa,ah lallai yarinya taji kiwo" gwaggwo fanteka data kama haba cike da jin wani abu a ranta me kama da qyashi qyashi ta fada,maganar da ta yiwa widad din nauyi,karon farko da kunyar hajiya ta kamata,musamman da ta tuna abinda ya wanzu tsakaninta da abbas din,sai take ganin kamar ma kowa yana iya karantar hakan,don haka tun daga dan nesa dasu ta zube tana gaidasu.


Cikin kulawa hajiyan ta amsa, gwaggwo fanteka kuwa ta zuba mata ido tana kallonta,sosai widad din ta canza,ta fara cika ta kuma yi kyau abinta,ta amsa tata gaisuwar tana sauke numfashi hadi da gyara zamanta


"Kundai tafi kunbar uwar gida da jiran gida ko?" Ta jeho widad da batasan ma kan asalin abinda kae faruwa ba tambaya


"Uhmmm,ina ruwan widad,ita da batasan komai ba akai" hajiya tayi saurin karbar zancan


"To ai shikenan,Allah ya kyauta" ta sake fada tana gyara zamanta,dai dai sanda abbas yayi sallama ya shigo parlor din,qaninsa muneer yana biye dashi da babban ledar da muddin da ransa da lafiyarsa baya gaza shigowa da hajiyan tashi ita.


Washe baki gwaggwo fanteka tahau yi tana sake gyara zama,lallai yau din ta shigo a sa'a,tasan cewa shar da ita zata fita,harda ita wajen marabtar abbas din,ya duqa ya gaidasu cikin girmamawa sannan ya koma ya zauna sosai daura da hajiyan tasa.


Miqewa gwaggwo fanteka tayi tana cewa


"Ni bari na wuce gida,naga la'asariya ta kusa"


"Ki tsaya mana ki karbi tsarabar taki?"


"A'ah haba,kya dai aiko muneera ko muniru ya kawomin,yallabai Allah ya huta gajiya" hannu abbas ya sanya a aljihunsa ya fidda sabbin 'yan dubu dubu ya miqa mata,tasa hannu kuwa ta amshe babu tayi tana zuba godiya.


Nan falon hajiyan yayi zamansa suna hirar yaushe gamo,duk danda widad dake kitchen tare da muneera ta gifta sai taji ranta ya mata sanyi,ta kuma sake godewa Allah,kallo daya ta yiwa abbas din harma da widad din ta karanci akwai wani gagarumin sabon canji cikin rayuwarsu,walwalar abbas din ta qaru,idan ma ba idonta bane ke mata gizo har 'yar qiba taga yadan qara,abinda bata taba gani a tare dashi ba,sannan duk sanda widad din zata gifta idanuwansa suna biye da ita,kamar yadda itama duk sanda ta ratso ta falon saita saci kallonsa.


Ana idar da sallar la'asar yayi shirin wucewa gida,yace ta fito su wuce,amma saita sakar masa darunta tana maqale wuya,idan zata shekara tana masa wannan shagwabar yanason gani,ba kuma zai gaji ba,tilas ya haqura ya barta bayan hajiya ta sanya baki,ya wuce gidan shi kadai,amma cikin jikinta da zuciyarsa duka sai yakejin wani iri babu dadi,kamar ya baro wani b'ari ne na zuciyarsa a wani waje.
[3/18, 3:06 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 81




Kamar ko yaushe a harabar gidan ya cimma yaran,sunata wasan qasa sunyi futu futu dasu,qasa har saman kansu,amma hakan bai hanasu murnar ganin juna ba,ya tsugunna ya kwashe abinsa sunata masa surutu yana kerbewa.


Dab da zai shiga sashen nata ta fito,sanye da atamfa dinkin doguwar riga,tayi daurin ture kaga tsiya,duka gashinta da ba kasafai ta fiya son kitso ba ya fito abinsa ta qasan daurin,hannun brassiere dinta daya fito ta kafadarta ya sake muzanta shigar tata,atamfar anko ce da sukayi biki tun shekaran jiya,kuma tun shekaran jiyan take jikinta bata cire ba,sam batayi tsammanin zuwansa a yau din ba,shi yasa ta saki jiki ya sheqi baccinta,bata jima da tashi ba ta biyo sahun su mimi jin shuru ba motsinsu tun dazun.


Tare hanya tayi tana masa sannu da zuwa hadi da karbar jakar hannunsa,bata son ya shiga sashen nata,saboda ita kadai tasan irin badaqalar daya kwasa ba,don hatta da uniform din mimi yana zube a falon da school bag harma da tsadajjen lunch box dinta daya siya mata


"Mu qarasa sashen naka,dama fitowar da nayi gyarawa zanje nayi" ta fada tana sake kankane hanyar.


Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa.


Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa


"Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din" manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta


"No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana".


Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace


"Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye....."


"Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s......" Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe


"Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?" cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai


"A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba".


Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad.


Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace.


Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru.


Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera.


Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za'a mayar 'yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma.


Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa.


*_W A S H E G A R I_*


Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki.


Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa.


Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra'ayin sunyi hannun riga da ta'ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa'a ranar tana da ra'ayinsa.


"Fita zakayi kenan" ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta


"Eh,akwai wani abu?" Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa.


"Aah,inason zuwa gidan hajiya ne" dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta.


A ka'idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita


"Saikin dawo" ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu.


Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare.
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 82




Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta.


Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba.


Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa


"Koma kiyi sallama" da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo


"Ikon Allah,ashe tare kuke" hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa.


Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata.


Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din


"Hajiya ina kwana?" Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai


"A'ah yau kece a gidan?" Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad


"Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen" ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta.


Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe


"Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai" aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan?


"Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi"


"Tooo.... ikon Allah,koma to ka zauna" hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba.


Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din.


Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa.


Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana.


Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice


"Tirqashi" ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za'a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?.


Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi.


Motsawa baba usaina tayi


"Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi"


"Haba,kiyi zamanki,duka ba 'ya'yanki bane" hajiya ta fada da kyakkyawan nufi,dama haka takeso,don haka ta koma ta zauna din tana cewa


"Hakane,ia bakaqi ba,kada aga kamar bakasan matsalar kowa ba sai taka,d'a ai na kowa ne, bare abbas da kowa yakecin moriyarsa?".


"Ina jinki hafsatu,mene ya faru?,ina fata ba matsala bace" fara matsar hawaye tayi sannan ta magantu


"Matsala ce hajiya, matsalar kuma abban mimi ne da kansa yakeson haifar da ita cikin gidansa"


"Tofa!,tirqashi!" Baba usaina ta fada da madaukakin sauti bayan ta kama haba,yayin da abbas ya bude dukka idanunsa a kanta yana kallonta,tare da sauraren wanne kalar sharrin kuma zatayi masa


"Mene ne ya faru?,gayamin" gyara zaman


"Hajiya,kwata kwata abban mimi bambanci yake nunawa tsakanin da widad muraran,bayason huldarmu ni da ita,qiri qiri sai suzo weekend har su gama bazanga fuskarta ba bare ta zauna a gidanta ba,wasu ma basai suyimin sharrin na hanata zama ba?"


"Laahhhh,da gudu kuwa,mutumin yau da baka iya masa?,tabdi" baba usaina ta karbe zancan


"To bama haka ba,ta yaya zamu shaqu mu fahimci juna da ita hajiya tsakani da Allah,sannan su kansu yaran nan bakiga yadda sukeson zama da ita ba,amma gaba daya basu samun ganinta,a haka kan iyalinsa zai hadu?" Shuru hajiya tayi tana jinjina kai,maganarta ta qarshe ce kawai taja hankalinta,har takega tayi magana me ma'ana,baba usaina nason tsoma bakinta tace wani abu,amma kuma kwarjinin abbas din ya hanata,banda


"Gaskiya ya kamata a aduba,saboda gobesu dana yaran" shi taketa maimaitawa


"Kinzo da magana me kyau da ya kamata a duba,ki kwantar da hankalin ki, za'a gyara lamarin in sha Allah, Allah yayi muku albarka,ya qara hada kanku,ya wanzar da zaman lafiya a tsakaninku"


"Ameen ameen.... yauwa,hakan dai yafi gaskiya,ta nan ne zasusan darajar juna,ita tasan darajar uwargidanta".


Taso ta sake qirar wani abun,amma hada idon da sukayi dashi yasa ta kasa cewa komai,sai kawai ya miqe ya fice afalon ransa yana masa suya,fita yasoyi amma sai ya kasa,yana daya daga cikin kujerun dake harabar gidan ya zauna kawai,qafarsa daya kan daya yana dan jefata a hankali,bacin ransa yakeson dannewa,ba kasafai ya fiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login