Showing 75001 words to 78000 words out of 196911 words

Chapter 26 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

ruwana" haka ta dinga fada tana sharar qwalla,su kuwa ganin abun suke kamar almara,wai yau widad din ummu ce aka aurar?,a wata uwa duniya?,ta tafi tabar ummu duk qaunar dake tsakaninsu?,Allah ne ya kawo anty madina ta korasu,sannan ta kada kan widad zuwa wanka,bayan ta fito kuma ta shiryata da kyau cikin wani lace da yayi masifar karbarta,ya fidda kyau da hasken fatarta,ita kanta ta dade tsaye gaban mdubi yana kallon kanta,tana ta zuba shirmenta na kyan da tayi,anty madina na binta da murmushi gami da goge qwalla a fakaice.


Daga bakin gadonta take zaune riqe da waya a hannunta,lokaci lokaci tana saka hannu ta share hawayen fuskarta,duk furuci daya da zatayi da anty ummee tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda baqinciki bacin rai da zallar kishi kai daci


"Har kusan qonewa nayi garin saurin na hada masa tea nakai masa,amma wallahi acan na sameta,namiji dan babansa......alamun dana gani ma sunsha dambene,saboda ko dankwalin kanta gashi nan watse a qasa,don Allah anty ummee mai zaiyi da wannan mitsitsiyar yarinyar,banda tsabar cin fuska?" Tayi maganar tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta.


"Kinga ki ajjiye wannan a gefe,matuqar zakici gaba daga inda kika tsaya,zaki nuna komai ba komai bane.....hatta kusantar tata ma saikin hanashi gaba daya,meye a cikin ido ne banda ruwa?,ai nasara tana tare da jajircewa"


"Wannan nasarar anya kuwa tana tare dani?"


"Kin saare a dare daya kenan?" Anty ummeen ta tambayeta tana jinjina zallar gajen haquri irin na hafsa din


"Shin ba'a gabanki komai ya dinga gudana tsakanina da amaryar abban sayyid ba?,yanzu tana ina?"


"Banqi ta taki ba.....amma akwai nisan tazarar banbanci mai yawa tsakanin abbas dashi.....abbas anty.....yana da ra'ayin riqau kafiya da kuma magana daya,yana da wuyar sha'ani,yana da wuyar canza ra'ayi,idan yace eh.....tofa a haka zata yita tabbata"


"Uhmmm,mace fa tafi gaban tunanin dukkan wani mai tunani,saidai idan ba zaki iya ba"


"Zan iya" ta fada tana son sake bawa kanta qarfin gwiwa,ji take kamar ta rufe idanu ta kuma bude taga komai ya tarwatse,komai yazo qarshe,ta rufe idanunta kana ta budesu duk kusan lokaci daya sannan tace


"Na rasa ta yadda abbas yaga yarinyar nan anty ummee......abbas fa?,mara damuwa da abubuwa masu yawa,wanda wani abun ma sai kinta cewa kalli....ko ka gani" ta jefawa anty ummeen tambayar da taketa damunta tare da yi mata yawo a kai,har yanxu kums bata samu amsarta ba


"Namiji yafi gaban haka,kedai ki maida kai ga mission dinki....."


"Ina zuwa" ta fada da sauri tana sauke wayar daga kunnenta sanda fa jiyo alamun taku ana nufowa dakin,ta kuma san babu wanda zai shigo din sai shi.


Da hanzari ta ajiye wayar,sannan ta fada bandaki ta maida qofar,da tattausar muryarsa yayi sallama ya tura qofar ya shigo,sai ya tsaya daga bakin qofa yana qarewa hargitsatsen dakin kallo,komai baya kan tsarinsa,baisan kuma sai yaushe zata gyara ba.


Ajiyar zuciya ta sauke,ta matsa gaban babban madubin dake bandakin wanda ya cika da jirwayen ruwan wankan da ba'a wankewa,ta debi ruwa ta wanke fuskarta,saboda batason ya gane ruwan hawaye ya fita a idanunta,taja zaninta da tayi daurin qirji dashi saman t.shirt dinta ta gyara daurin,sannan ta goge fuskarta da towel ta fito.


Suna hada idanu ta cika fuskarta da fara'a,sai ya dan lumshe idanunsa ya kuma budesu lokaci daya yana kallonta,qasan zuciyarsa kuma yana masa sanyi na yanayin da ya ganta a ciki,ba wata damuwa


"Yanzu nake shirin fita mu gaisa da baqi,gashi ka tarar dani" ta sake fada tana murmushin da ita kadai tasan ciwon da yake mata.


Agogo ya kalla kafin ya amsa mata


"Kaman yayi wuri,gwara ki kwanta ki sake hutawaYou are very tired, you need a rest maman nawwara" ya fada yana sauke mata murmushi.


Duk da cewa bata kalleshi ba amma tana jin saukar murmushin nasa har tsakiyar zuciyarta,murmushi ne da ita kadai tasan tsadarsa


"To ya za'a yi,kamawa takeyi ai,gashi na kasa hada musu breakfast" ta sakeyin maganar tana zaqulo hijabinta cikin hargitsatsun kayan wardrobe dinta wadanda yana daga tsaye yake tayata kallon yadda suke a hautsine,haka suke koda yaushe,idan kayi magana tace su nawwara ne tana bacci suka aikata,ko kuma suna neman teddy dinsu ne


"Ba matsala,kinyi qoqari sosai,zan saka a kawo musu breakfast"


"Da dai yafi,na gaji da jegon jaka" ta fada qasan ranta tana zura hijabin a jikinta,sannan ta matso tana cewa


"Bari naje mu gaisa kada suga rashin kyautawa ta,mun tashi gida daya ban leqasu ba" da kallo ya bita,duk da qoqarin sakewarta amma yana hangen wani.abu can qasan qwayar idanunta,zuciyarsa na alaqanta hakan da kishin da takeji a kansa.


Hannayensa ya bude mata,cikin taushin nan nasa


"Zaki wuce bamu gaisa ba madam" kallonsa tayi saita kauda kai tana qoqarin kawo murmushi kan fuskarta,tabbas idan tace zata shiga jikinsa a wannan yanayin kuka zata barke dashi,kukan kuma zai zame mata tonon silili ne.


"Ina kwana oga?" Ta fada tana ci gaba da tafiya,sai ya maida hannayensa yayi folding nasu a qirjinsa yana kallonta,qaramin murmushi na sauka saman labbansa,irin gaisuwar da yafi qauna daga wajenta kenan,amma dama yasan zaiyi wahala ya samu yadda yakeso din


"Alhmdlh madam,a dawo min da yarana mana?"


"Zasu dawo dole yau" ta bashi amsa ba tare data juyo ba


"Alright" ya amsa mata yana kallota ta cikin madubinta


"Bari naje na dawo" ta fada tana jan masa qofar,tana so taje ta saje tantance widad din,yadda ta ganta a jiyan haka take ko idanuwanta ne da kuma sharrin dare?.


Idanuwanta nakan dukka wani kayan qawa na falon,da qyar ta iya riqe kanta saboda yadda zuciyarta ke wani irin tsalle,ko ba'a gaya mata ba auren 'yar gata ne daga dukkan alamu,saboda yadda aka shirya gami da qawata sassan nata gaba daya,babu ce kadai babu,jere mai aji da nutsuwa.


Ta basu fuska sosai ta gaidasu inna laila dasu momma,har tadan zauna suna dan taba hira,tana ta baza ido taga ta inda widad din zata fito,saiga nujood,kamar inna laila tasan buqatar ta tace da ita


"Kira widad,kice tazo ta gaida yayarta"


"To" ta amsa tana okomawa ciki da mopper din hannunta data goge inda ruwa ya zuba.


"Yaaa latifa" widad din ta fito tana fada,hannunta riqe da dankwalin lace din nata da yaqi dauruwa,anty deena dake wanka kuma tace lallai saita daura.


Hankalin hafsa ya fara kaiwa wajen,tana tafe da dankwalin fuskarta a kwabe tamkar shagwababbun 'ya'yan fari,gashinta dake wani irin sheqi da walqiya a daure cikin ribbon jelarsa na reto a bayanta, yanayin qirar jikinta kadai abar kallo ce,sai kace wata babbar budurwa,tun a yanzun coca-cola shape dinta ya fita sosai,kallo dayan data mata ya kusa tafiya da numfashin ta,ta dinga qoqarin riqe kanta da kyau,kada ballinta ya watse a wajen.


*Arewabooks:Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171
Maryam sani
Access bank


Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070


*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261


*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63




*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
[3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)


Page 39


Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata 'yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa.


Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa


"Lafiya dai ko?,ba wani matsala?" Gyara tsaiwarta kadan tayi


"Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba"


"Ya salam" ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda


"Matsala kan matsala" ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki.


Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate.


Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa


"Tashi muje" ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa


"Gida zaka kaini wajen ummu?" Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu


"Wait....zo mana kiji" ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau


"Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu"


"To" kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa.


Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah.....a sanda kake buqatar ka huta......wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?.


Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa


"Allah ya kiyaye hanya,saina taho" ta zura hijab din tayi gaba abinta.


"Na shirya" ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa.


Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta.


A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun.


Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau.


Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida.


Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri.


Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad'i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa.


Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi.


Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar


"Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru" ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar.


Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska


"Barka da dare" ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi


"Tana ciki ne?" Kai ta girgiza


"Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye" saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu.


Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?.


Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace


"Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha'afa" hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la'asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye


"Qanwarki keta rigima nadan fita da ita" sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa


"Ayyah.....haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba" ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din


"Ka wuce ka huta,bari na rakata" ta fada tana kallonsa.


Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi buqata a yanzu irin ya watsa ruwa a jikinsa ya kwanta.


Sai data tabbatar tayi nesa da widad daga inda abbas yake sannan ta fito tabar sashen,bayan ta gama mata lallashin qarya da nuna kulawa,wanda qasan zuciyarta cike yake fal da tsana da kuma qiyayyar yarinyar,tana jin kamar ta budi idanu taga babu ita kwata kwata cikin gidan.


Latifa ce ta sakata a gaba kan sai taci abinci,da yake a gajiye take,kuma yunwar take ji da gaske saita zauna taci din,tana tsaka da cin ma baccin ya kwasheta ko.hannu bata wanke ba,sai tatifa ce ta gyara wajen ta kuma tasheta ta koma dakinta.


Washegari tunda wuri latifa taga kiran ummu,bata yi jinkiri ba ta daga,don dama tana da niyyar kiran nata,bayan sun gaisa widad ta fara tambaya,bata boye mata ba ta gaya mata yadda suka wuni jiya,muryar ummun ta canza,da alama ita kewar widad din tata takeyi,sai tace takai mata wayar.


Bacci takeyi amma sanda tace mata ummu ce sai gata ta wartsake sarai,ta karba wayar tana kiran sunanta hawaye na shirin balle mata,tausayinsu duka ya kama latifan,sai ta fice tabar mata dakin bayan taja mata qofar.


*Arewabooks: Huguma*


KI KULANI miss xoxo


DAUDAR GORA Billynabdul


RUMBUN K'AYA hafsat rano


IDON NERA Mamuhghee


A RUBUCE TAKE huguma


_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_


_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_


0022419171
Maryam sani
Access bank


Saiku tura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login