Showing 123001 words to 126000 words out of 196911 words

Chapter 42 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

ya zura hannunsa ya kashe wayar gaba dayanta.


A hankali a hankali ya fara fitar da numfashi da gudu gudu,tun tana tunanin ba komai bane har hankalinta ya kawo kan canzawar da taji yayi,hakanan bugun zuciyarsa sosai yake shiga zuwa ga kunnuwanta dake kwance saman qirjinsa dake shimfide da lallausar gargasa,a hankali ya daga kanta tana duban fuskarsa


"Uncle.....baka da lafiya?" Murmushi ya qwace masa,gumi na saukowa ta saman goshinsa kadan kadan


"Am fine,kwanta kiyi baccinki" ya qarashe maganar yana cije labbansa,saboda yadda mararsa ta murda masa


"Gumi fa kake uncle"


"I know,na sani"


"Ka bari na taso hajiya"


"Aah"


"To akwai magani na dauko maka?"


"Kece maganin" ya fada muryarsa tana rawa,sam bata fahimci me yake nufi ba,don batasan ainihin abinda yake damunsa ba


"Ni kuma uncle?"
"Yes,but.....ki kwanta kawai nace" ya fada da dan kaushi,saboda ciwon da cikinsa ya fara,jiki a sanyaye ta zame kanta daga jikinsa zata kwanta gefe,sai yasa hannunsa ya tarota


"No,don't leave me,stay here,i will be okay" gaba daya sai taji bata da kuzarin musawa,ba wani sauran tsoro tattare da ita,tana jin sanda ya matso da ita zuwa jikinsa sosai,sai taji tausayinsa ya kamata,tana da saurin kuka da karyewar zuciya akan mara lafiya,don haka tasa dukka tafukan hannuwanta biyu a kuncinsa hagu da dama tana masa sannu da muryarta can qasa,abun sai ya zame masa kamar fami,don haka yasa hannayensa ya cire hannun nata,ya kuma jawota jikin nasa still yana cewa


"Kiyi bacci,good night".[3/14, 7:17 PM] +234 816 133 8078: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 64




Shi kadai yasan yadda yayi surviving wannan daren,ya azabtu da yawa,daga baya da yaga ba sarki sai Allah dole ya zareta daga jikinsa bayan yaji saukar numfashinta tayi bacci.


Ya dade yana kai komo,zuciyarsa na gaya masa ya aika abinda zai samu sassauci,to amma yana tuna abinda zaije ya dawo,har yanzu ya tabbatar bata gama sanin meye aure ba,bugu da qari rainon zuciyarta yakeyi,baida tabbacin soyayyarsa a ranta,beside ma hajiya na gidan,bai kamata haka ta kasance ba a karon farko.


Sai wajen biyu na dare ya samu kansa da qyar,da kansa ya zabi kwanciya a qasa,zuciya da ruhinsa cike fal da tunani,wannan din ba komai bane sai kasawa da gazawar hafsa,bai taba zuwa mata weekend ko tafiya irin wannan ya samu irin tarbar da yakeso ba,bai taba dawowa sun rabu lafiya lau da ita ba,duk yadda kuwa zaikai gakai zuciyarsa nesa da dauke kansa,ya tabbatar inda ya samu ko yana samun yadda yakeso daga gareta,duka hakan ba zata faru dashi ba,saidai kuma ajizanci irin na dan adam.


Kusan tare suka tashi sallar asuba shi da ita,abu na farko data fara tambaya tun batayi alwala ba shine lafiyarsa,ya jikin nasa,ya saki murmushi yana jin dadi hat xikin ransa,saboda baisan da kalar wannan kulawar ba,yana iya yin ciwo har ya warke hafsat din bata sani ba saboda tsabar rashin kulawa irin nata


"Na warware alhmdlh"


"Sannu uncle,Allah ya sawwaqe"


"Ameen" ya amsata yana murmushi,da gaske yarinyar ce,wadda aka raineta bisa tsaftataccen tarbiyyar da har batasan meye ainihin ma'anar aure ba,batasan sha'awa ko wani abu daya danganceta ba,abu kadan ta sani wanda baikai girman da zai shiga tunani ya lalata mata rayuwa ba, tashin farko da yaji rashin sanin meye aure da batayi ba bai wani dameshi sosai ba,saboda wannan shine yake basji guarantee na cewa ita din mai tsaftataccen tunani ce da batasan komai ba,zaiyi dashensa yayi shukarsa ya kuma yi girbinsa yadda yakeso kenan.


Tana kan abun salla tana tunanin me zata dafa da safen,wayarta da tayi qara ta katse mata tunaninta,ta tashi ta dauko wayar tana duba me kiran


"Mommy hafsa da safen nan?" Ta tambayi kanta gabanta yana faduwa,sai a sannan ta tuna a dakinshi fa ashe ta kwana,ko wani ya gaya mata ne?,wannan tunanin ya hanata daga wayar har ta katse.

Iska mai zafi hafsa dake tsaye cikin dakinta ta furzar,ta daura alwalar amma ta gagara tayar da sallar,ta manta gaba daya gidan daki biyu gareshi,hakan yana nufin hajiya na daki daya,ita da abbas dinta zasu kwanta daki guda shimfida guda?.


Ko yanzun data kiratata bata daga ba, zuciyarta na kissima mata qila a daren jiyan ya samu yadda yakeso ne,babu yadda take shi yasa ta gaza daukar wayarta,wannan tunanin ya tashi hankalinta,ta koma gefan gadon ta zauna ta shiga jera mata kira ba qaqqautawa.


Abin da ya sake tsorata widad kenan ta kasa daga kiran,lallai tasan a dakinsa ta kwana,kuma tambayar da zata mata kenan tunda taketa kira,sai ta ajjiye wayar tana kallonta gabanta yana ci gaba da faduwa,har zuwa sa'ar da abbas ya dawo daga sallah,ya buda qofar dakin ya shigo.


Idonsa akan wayar,don itama ita take kalla,hannunsa zube a aljihunsa ya qaraso,ya dauke idonsa daga kan wayar ya maida kan fuskarta,saita dan dauke kai tsoron kiran da ake mata,da kuma kunyarsa suka hadar mata


"Ina kwana?"
"Kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau ya jikin naka?" Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu yana sakin murmushi, lallai quruciya na damunta da gaske


"Da sauqi,na warke" kai ta jinjina masa,sai ya sake duban wayar


"Ba kiranki akeyi ba ki daga" fuska ta kwabe sannan ta girgiza kanta,bai sake cewa komai ba ya matsa wajen kujerar da yakan zauna yayi karatu da asuba ya jawota ya zauna,sai widad din ta miqe a hankali ta nade abun sallar nata,ta nufi qofar fita a dakin


"Ina zuwa?" Waiwayowa tayi


"Xanje gaida hajiya" sai ya gyada mata kai kawai.


Daga inda yake zaunen yana hangen hasken da wayar taketa yi,yadda aketa kira ba qaqqautawa ya bashi mamaki,ba tare daya shirya ba ya miqe,ya isa ga wayar ya dauko,sai yaga sunan mommy hafsat,abun ya daure masa kai,ya juya yana duba wayarsa waiko zaiga miscall dinta,may be ta kirashi ne baya kusa bai daga ba,wani abun kuma ya faru,amma sai yaga babu kiranta ko daya,ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da yin sallama.


Jin muryarsa ya qarasa fadar mata da gaba,jikinta gaba daya yayi laushi,ta saki abun sallar a qasa,da gaske suna tare,tare suka kwana,kasa motsawa bakinta yayi,ta riga data samu amsar abinda take nema,don haka ta kashe wayar tare da sulalewa a wajen ta saki wani irin kuka mai tsananin zafi da cin rai,shikenan,ta faru ts qare.


Jin alamun an katse ya sashi daga wayar ya kalli screen din wayar,sai yadan tabe baki ya maida wayar ya ajjiye,har ya taka zai bar wajen sai hoton fuskar wayar ya dauki hankalinsa,ya koma ya sake dauka,ya koma saman kujerar ya zauna,ya buda gallery ya soma kallon pictures din a hankali har baisan sanda murmushi ya dinga kubcewa daga fuskarsa ba,kowanne hoto da kalar quruciyar da za'a nuna a jiki.


Hannunsa ya miqa,ya dauki wayarsa ya buda,yayi marking wasu daga ciki ya tura.


Ranar kaf qin yarda tayi ta sake komawa dakinsa,ko hanya qin yarda tayi su hada dashi,tana tsakanin dakin hajiya da kitchen,bayan sun hada breakfast ita da muneera suka shirya komai a falo,tare sukayi break din har hajiyan,sunayi ana taba hira,da suka gama suka sake gyare gidan tare,shi da hajiyan suna dai falo suna hira,a nan sukaci abincin ranar tare da hajiyan,sannan ya koma daki ya shirya ya fice.


A daren ranar yana zaune daga bakin gadon sa,qaramin littafin addu'o'i ne a hannunsa yana karantawa,ya gama komai,kammala addu'arka ne kawai ya rage masa,amma sam baiji motsinta ba,lokaci lokaci yana daga kai ya kalli bakin qofar dakin nasa a haka har ya kammala addu'ar,ya aje littafin gefen bedside ya zuro qafafunsa ya zura bedroom slippers dinsa ya miqe a hankali ya fito daga dakin.


Babu kowa a falon,amma yaga dakinta a bude,yasan suna ciki,yayi gaba zuwa dakin,ya tura qofar bakinsa dauke da sallama.


Dukkansu suka amsa,hajiya na zaune gefan gado,muneera da widad na saman qaramin carpet din dake shimfide qasan dakin,muneeran na maidawa weedad kalbar kanta da santsin kan ya sanya ta ware kamar ba'a taba yinta ba,bataso a taba mata kai tana ta qorafi muneeran na fadin saita yi mata,hajiya na goyuwa da bayan weedad din.


Kadan ya kalli sashen da suke,ya qaraso ciki,ya samu gefan hajiya ya zauna


"Bakiyi bacci ba hajiya?" Sai tayi murmushi


"Banyi ba,ina dai shiri"


"to yayi kyau,kin hada komai naki waje daya ko?, saboda gobe sha biyu zamu fita"


"Komai a kammale yake"


"Ma sha Allah.....shikenan,dama zuwa nayi nai miki sallama,sai da safe"


"To Allah ya bamu alkhairi ya tashemu lafiya" sai ya juya yana ficewa a dakin,minti biyu hajiyan ta kalli widad


"Maza tashi ki tafi ki kwanta kin baro mijinki,nikam sai da safenku" dif widad tayi,don ita gaba daya ta gama tsarin kwana a nan din,ta dan dubi muneera taga itama ta fara shirin kwanciyar,dole ta miqe,ta dauki siririn gyalen abayarta ta dora saman kanta,ta bude closet dinta ta dauki rigar bacci tayi musu sai da safe ta fita.


A sanyaye ta tura qofar dakin tashiga da sallama,yana zaune daga bakin gado yana amsa waya,haka kawai yaji sanyi har cikin ransa sanda yaga ta shigo din,bandaki ta wuce,ta fidda kayan jikinta tayi wanka,don zuwa yanzu tayi mugun sabo da wankan dare,ta shirya cikin kayan baccin ta fito.


Dim light ne a dakin,yana iya hangen sanda ta fito da kuma hawanta saman gadon,taja duvet ta kwanta ba tare data ce komai ba,qaramin murmushi ya saki,abinda ya faru jiya yana dawo masa,sai ya samu kansa da janyo wayarsa,ya duba wajen music ya lalubo kukan magen jiya ya saka.


Curewa tayi waje daya,tun tana iya ganin zata jure harta kasa,sannu sannu sai gata cikin jikinsa ta cukuikuye shi,ya saki murmushin nasara ya sanya hannunsa ya lullubeta cikin qirjinsa yana sakin murmushi,ita kuna tayi lamo tana sauraren bugun zuciyarsa da nata da kowannensu ke fita da sauri da sauri.
[3/14, 7:17 PM] +234 816 133 8078: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 65






"Tom.....zamu tafi" abbas ya fada yana duban qwayar idanun widad din,hannunsa zube a aljihun wandon lallausan yadinsa da aka yiwa wani irin dinkin girma.


Daga kai tayi da nufin kallonsa,duk yadda taso ya hadiye abinda takeji a qasan ranta amma ta kasa,dole haka ta saka qwayar idanunta a tasa,dai dai sanda hawayen da take riqewa ya sulmiyo daga idanunta,maganar da zatayi ta riqe mata a maqoshi,sai ta saki kuka sosai,abind aya tilasta mata saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.


Duka idanunsa ya fiddo,ya ciro hannayensa yana matsowa inda take tsaye


"What's happening weedad?" Kai ta girgiza masa,saidai kukan take har yanxu


"Noo....noo,kada muyi haka dake mana uhnnn?" Ya fadi a tausashe,sai ya sake matsawa gabanta,ya saka duka hannuwansa ya zare nata tafukan hannayen daga fuskar tata yana kallonta


"I will be back in sha Allah.....ki daina kukan nan,yana qona ni,zuciyata tana zafi.....ko kinaso nima nayi kukan?" Ya fadi yana jin wani irin rauni da bai taba jin kamarsa ba,kanta ta girgiza amma ta gaza tsaida hawayen


"It's okay,i promise you bazamu dade ba,shikenan?"saita sake jinjina masa kai,haka kawai takeji wani tashin hankali da rashin sukuni a tattare da ita,sai takejin kamar zai tafi ya barta,kamar bazai dawo ba,tana jin kamar an dauke wani muhimmin sashe ne a jikinta,batasan wanne irin feeling bane wannan,tsahon rayuwarta bata taba fuskantar irinsa ba.


Tas yasa soft handkerchief dinsa ya goge mata hawayen,sannan ya bude tafin hannunta ya saka mata shi,ya maida ya dunqule hannun nata cikin nasa,sai yaja da baya kadan yana gyara zaman rigarsa data cukuikuye yana kallonta,cikin ransa yakejin wani shauqi yana saukar masa,ganin wani yana kewarka.....ya shiga damuwa saboda zaiyi rashinka a kusa dashi......wani irin dadi kima da daraja gareshi a zuciya,wani irin yanayi da bazaice ga lokaci na qarshe daya ganshi tattare da matarsa ba,sai ya buda dukkanin hannayensa yana kallonta da idanunsa masu girma da zuwa yanzu suka rusuna,girmansu ya ragu


"Oya.... give me a hug" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,qaramin miskilin murmushinta ya subuce zuwa saman labbanta,a yau din sai taji bata shakkar yin hakan,ta fara takawa a hankali kamar wadda aka sakawa wani kida na musamman,yayin da idanunsa yaji sun fara narkewa a kallonta,cat walking takeyi,irin tafiyar da sai wance da wance cikin isassun mata,bai taba lura da hakan ba sai yau,ya qaraso gareshi a hankali,ta shige jikinsa kuwa gaba daya,harda qoqarin saka hannuwanta ta zagayo dasu ta bayansa,sai ya tallafa mata,ya durquso ya sakata sosai a jikin nasa,yana jin kamar ya maidata cikinsa.


Sun jima sosai a haka kafin ta fara janye jikinta,ya danyi baya jikinsa a mugun mace yana maida numfashi,kusan minti hudu kafin ya dai daita kansa


"Ayimin rakiya mana" kai ta girgiza tana murmushi,duka idanunsa ya bude a kanta


"Why?"


"Hajiya fa.....so kake ta gane ka rungume ni,sannan tun dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji" ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye


"Ok, come closer" ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa


"Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki" ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta


"A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya" lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba'a taba masa addu'a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta.


Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa'a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe


"Ku bawa mommynku" ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace


"Tace bacci takeyi" idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya


"Alright....idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku"


"A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi" murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma


"In sha Allah mimi na,i love you"


"I love you too daddy" ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara


"Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy" tayi maganar tana kwata muryar yarinyar


"Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba" taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa.


A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita


"Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan" .


Yasan dai ba yadda za'a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad.


Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso


"Iyeee .... dole wai so take ta fini iya girki...... alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana" da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida.


Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login