Showing 132001 words to 135000 words out of 196911 words

Chapter 45 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt

dayi,ba zaki taba samun wannan daga gareni ba har abada.....abu na uku kuma.......bake kadai bace Allah ya halattamin ba,sannan kuma bake bace autar mata,ki jiqa abinki ki shanye,indai abbas ne na haifu,kuma dan halak ne ni gaba da baya" daga wannan ya fara takawa a hankali yana ficewa daga dakin,yana tafiya yana cije labbansa saboda yadda yakejin mararsa kamar zata tsage.


Gaba daya maganganunsa sun gigita ta,babu zance mafi gigita kuma a ciki daya ce mata ba ita kadai Allah ya halatta masa ba......yana nufin widad?,shi yanzu sai ya kusanceta?,bazaiji kunya ba?,yarinyar da ya kusa haifarta?,zumbur ta miqe,tana jin kamar taje ta dawo dashi yayi abinda yayi nufin yin.....don da ya aikata abinda yake nufi a zancansa gwara ta bada kanta ta dawo dashi,amma kuma tana taku uku wata zuciyar ta dawo da ita


"Zaki zubda mutuncinki da ajinki a wajensa" sai taci gaba da gamsar da kanta cewa abbas din bazai iya ba,yarinyar tayi quruciya da yawa,bazata taba iya gamsar dashi,kai ba zata daukeshi bama,ko ita da yaya suke qarewa bare widad din dako qasusuwanta basu gama yin qwari ba,ta tabbatar bashi yiwuwa


"Namiji nefa,idan komai bai kawoshi ba buqatarsa zata dawo dashi,basu da haquri ta wannan fannin" ta sake tabbatar wa da kanta,sai taja tsaki ta koma tayi zamanta,har fana tuhumar kanta


"Kin faye rawar kai akan abbas din nan,shi yasa ya rainaki,ya kasa ganin kimarki" wata zuciyar ta sake gaya mata,da wannan taja mugun tsaki ta miqe ta dauko wayarta dake ringing tana duba me kiran,baquwarta ce da zata kawo mata biyan bashi,saita aje wayar ta shiga bandaki tayi tsarki da alwala ta fito,saidai har a sannan itama tana ji a jikinta,don ba qarya tayi missing abbas din,sannan tarkon daya dana mata banda akwai wani quduri a ranta.....ta kuma yi da gaske ta dace da zuciya mai tauri bata isa ta tsallake ba,a ranta taji tana fatan tattaurar zuciyarsa ta sauko da wuri ya karyo ya nemeta,don itama a buqace take.


Tunda ya zube a dakinsa bai iya tashi ba,a nan yayi sallar magariba ya kuma yi isha'i ya koma ya kwanta saman abun sallar,rub da ciki yayi tun tsahon awannin yana fatan ya samu sassauci na zuciya da kuma gangar jiki,gaba daya ya manta zaije dauko widad,sai da yaga kiran hajiyarsa.


Bayaso yace mata baya da lafiya,yanzu zata daga hankalinta,kuma yasan babu driving din da zai iya,sai yace mata yana zuwa.


Number k'aninsa umar wanda daga shi sai auta ya kira yace yazo ya karba key din motarsa ya kawo widad din,idan hajiya ta tambaya ya gaya mata baqi yayi,a ladabce ya amsa masa,ya katse kiran,ya aje wayar yana cusa hannunsa cikin fuskarsa.


Ita kuwa hakimar tana falonta a zaune,duk sanda taji wani motsi saita leqa taga waye,so take taga shigowar widad din ta tsareta da ayyuka,idan da hali ma yau kwanan dakin su mimi zata sakata yi,taso acema key din part dinta yana wajenta tace mata ya bata,batasan me yasa bata saka mata dokar ajeshi a wajenta ba,amma daga wannan zuwan abinda zatayi kenan,ta dinga barinsa a hannunta,idan suka dawo ta dinga karba.
[3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*


Page 69




A idanunta akayi sallar magariba bataga gilamawarsa ba,akayi isha'i ma haka,sai jikinta ya bata lallai ciwon cikinsa ya tashi ne,indai kuwa hakanne babu inda zai iya tafiya dauko yarinyar,hankalinta taji ya kwanta,ta kuma sake abinta,gwara yarinyar ta kwana a gidan hajiyan akan ta dawo cikin gidan yana cikin wannan yanayin,ta sanshi sarai,tamkar mayunwacin zaki yake,haram ce kadai baya iya dosa a irin wannan yanayin,saita koma ciki taci gaba da lissafin kudinta da kuma sabgoginta.


Ta riga ta gama saddakarwa,wannan ya sanya shigowar umar da fita da motar duka bata jisu ba,ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta kunna kallo abinta,saurana abincinsa da bai cinye ba shi ta zubawa yaran sukaci abincin dare dashi,hakanan suka tsakura,saboda sun gaji daci,shi sukaci tun rana sukaci da babansu yanzu ma kuma gashi shi dinne,sunata wasansu tana chart, hankalinta ma baikan tv din,tana bawa anty ummee labari ita kuma tana cin dariya


_shegiya,wannan mafa hanyar samun kudi ce a wajen mace bana wasa ba_ anty ummee ta gaya mata


_wallahi a wani group wata hamshaqiyar hajiya ta bamu sirrin,ina nan ina zuba ido,idan ya gaji ya kawo kansa ya kuma biya price sannan a bude masa gate_


Daga can anty ummee tana ta dariya,cikin ranta kuma tana gulmar hafsat din,sai kace wata hamshaqiyar mace,banda ma abin namiji,ai ita qoqarin abbas take gani,duk da tsananin tsaftarsa amma yake iya tarayya da hafsat din,harda qulafucinta haka?,lallai abar rai da abinda yakeso kawai.


Sun jima suna hirar anty ummee na sake dorata akan keken bera,don itama tanaso idan ta yagi kudin ta yagi nata kason itama,tanason canza kayan kwalliyar falonta, hankalinta ya dauku ga hirar ta wuce kitchen dauko lemo,tafison tana yi tana korawa dame sanyi,dai dai sannan motarsu widad din ta shigo,ya tsaidata a parking lot.


"Matar yaaya,yace ki sameshi a bangarensa,ga key din motar,saiki tafi masa dashi"


"To,sannu na gode" dariya ya danyi kadan,itakam halinta dabanne,duk da sun girmeta,bai taba jin hafsat ta aikesu tayi musu ko sannu ba bare godiya.


Tare suka fita a motar,shi ya doshi gate ba tare da yayi tunanin zuwa su gaida da hafsat ba,don sai suyi zuwa dari ba wanda ya kalli sashenta,sai dai idan sunga idanun abbas din,ko shi yace su shiga su gaisheta.


Kallon sashen hafsat din tayi,gabanta yadan fadi,ta tuna kiran data dinga mata bata dauka ba,wanda shine tun daga ranar bata sake kiranta ba,saita dauke kanta,ta doshi sashen abbas din da dan hanzari,tana Allah Allah ne ta shiga ta bashi ta fito ta wuce sassanta.


Tayi mamakin ganin wutar falon gaba daya a kashe,babu hasken komai sai na wutar bedroom dinsa,sarkin tsoro tsoron nata ya motsa,duk da bawai duhu can can yayi ba,don hasken fitilun waje suna ratsowa ta labulayen falon,ta fidda wayarta ta kunna torche sannan ta doshi dakin.


Da siririyar muryarta tayi sallama tana shiga dakin,bata lura dashi ba har sai daya dan motsa daga kwancen yana amsa mata sallamar,ta danja baya adan tsorace,sai ya koma rigingine yana kallonta da rinannu idanunsa


"Uncle.... Lafiya?" Ido ya lumshe sannan yayi qoqarin miqewa yazauna yana cije bakinsa kadan


"Lafiya lau,ina umar din?"


"Ya wuce,ga key din yace na kawo maka" ta qaraso gefansa ta duqa ta ajjiye,qamshinta ya huro masa har inda yake,sai ya maida idanunsa ya rufe


"Yunwa nakeji,zan samu abinci?" Da mamaki ta kalleshi


"Mommy hafsa fa?"


"Zan samu abinci?" Ya sake maimaita tambayar tasa ba tare da yabi takan maganarta ba,sai ta gyada kanta da sauri


"Okay,dafamin wani abun mai sauqi mai ruwa ruwa" sai a yanzun ta lura da yanayin fuskarsa,gaba daya ta nuna bashi da lafiya,jikinta yayi sanyi,ta matso sosai kusa dashi,tasa hannu tana dan taba fuskar tasa


"Uncle kamar baka da lafiya fa" ji yayi kamar ta zuba masa wani abu me sanyi a gangar jikinsa,ya rufe idanunsa ya budesu a kanta


"Bani da lafiya weedad" sosai fuskarta ta nuna damuwa qwarai,ta tsugunna gabansa tana ajjiye jakarta


"Amma uncle ne yasa ba zakasha magani ba?" Ido ya zuba mata sosai,yana ji a ransa inama zata iya dauke lalurarsa,inama tace zata zame masa maganin?,ya sani matarsa ce.....amma yasan halittar da Allah yayi masa a shekarunta yana ganin indai ya fuskanceta da wannan zai iya cutar da lafiyarta


"Zansha weedad......bani wani abun tukunna" da saurinta ta miqe ta zame mayafinta da jakarta duka ta aje a wajen,suman zaune ya kusayi,dogon sassalkan gashinta na kwance a bayanta,tunda ta shigo daman dankwalinta yana jakarta,ba kasafai take daura dankwali ba don basa shiri, skert din ya fidda shape dinta sosai,ta baya zata dauka takai shekaru ashirin da wani abu,sai a lokacin yaga girman da yaji 'yan uwansa na fadin tayi,ya koma da idanunsa luuuuu ya rufe yana kiran sunan Allah.


Faten dankali ta shirya masa,duk da yadda yayi dadi amma gaba daya baya gane taste dinsa akan harshensa,zamanta kusa dashi yafi komai dagula masa lissafi,ita kuwa ta zauna ne bilhaqqi tana matsa masa yaci


"ko baiyu dadi bane na sake maka wani uncle?" Ta fada a shagwabe saboda sam bata jin dadin yadda taga baya ci din sosai,kansa ya girgiza dankalin yana wuce masa wuya da qyar,sai ya aje plate din ya zuba mata idanunsa gaba daya yana mata wani mayunwacin kallo


"Maganin zaki bani" ya furta da wata birkitacciyar murya,itama shi take kallo,karon farko da taji kallonsa ya saukar mata da wani abu mai nauyi a jikinta da zuciyarta


"Ina maganin yake saina dauko maka" tayi masa tambayar tana janye qwayar idanunta daga kansa,saboda wani nauyi da taji ya saukar mata lokaci guda.


Kanta ta daga sanda taga ya miqo mata hannunsa,ta kalli hannun ta kuma kalleshi,bata fahimci komai ba


"Zo na gaya miki inda yake" a mamakance ta miqa masa hannunta,bata kai ga tuna komai ba ta samu kyakkyawan masauki a jikinsa daya dauki dumi,cikin qirjinsa ya lullubeta gaba daya yana sauke wani irin numfashi a jejjere,komai ya fara koma masa sabo,tunaninsa ya fara nisa ya fara daina gane komai.


Yamutsa ta ya fara yi,abinda ya tsorata ta ta fara kiran sunanshi tare da qoqarin kama hannuwansa dake yawo a sassan jikinta,ko harafi daya bai gane ba cikin maganganunta,illa dai yana jin sautinta kamar mutumin daya sanya bakinsa cikin kofi yana magana(sama_sama),a yau ya ware dukka hannayensa a kanta,duk inda suka kai bai musu shamaki,haka nan bakinsa.


Sanda ya hade fatar jikinsu waje daya daukewa numfashinsa yayi cak na wucin gadi sannan ya samu ya qwatoshi da qyar,qasan da suke yaji tayi masa kadan,ya dagata zuwa tafkeken gadonsa ya shimfidar da ita,zuwa sannan tsoro ya kusa halakata,abinda bata taba gani ba,bata kuma taba zata ko tsammani ba.....yayin da abbas yayi nisa a wata duniya, duniyar da tunda yake bai taba tunanin ana kaiwa har can ba,tun daga tsarin lallausar fatarta zuwa daddadan qamshin jiki dana sumar kanta komai ya sake kwance masa,ya rasa ta inda zai juyata,ko ina ya juyatan sai yaji yayi masa kadan.


Kuka mai qarfi ta saki sanda taji ya soma rabata da sutturar jikinta,ta shiga roqonsa da kyau akan kada yayi mata komai......ummu ta hanata......idan yayi ummu zata kasheta,amma ina samm samm baiji ba,abu daya ne ya maidoshi duniyar sa,daukewar numfashi daga gangar jikinta bayan taja wani dogon numfashi sanda ya soma buda hanyarsa zuwa sabuwar rayuwa da sabuwar duniya.... dole ya zare jikinsa daga gareta ba tare da yakai ga cimma gaci ba,ya koma qoqarin ganin daidaituwar numfashinta.


Tun da safe ta tashi da sha'awar cin awara,sai da yaran sukayi bacci sannan ta fita da 200 zuwa bakin gate dinsu,ta bawa yaron gidansu ya siyo mata


"Ka riqemin kudi na da kyau,don idan ka yarmin sai ka biyani" kudin ya kalla sannan ya dubeta


"Hajiya dari biyu ce fa" ya fada qasan ransa fal mamaki,kaf unguwar kowa yasan waye ASP abbas din,amma ita sam bata jin kunyar yin aike da qaramin kudi


"Na sani,ko bani na baka ba?" Sai ya gyada kai


"Hakane" daga haka ya juya yana fita daga gidan,cikin ransa yana tur da irin halinta.


A hanyar dawowa ta kalli motarsa,har yanzu bataji motsinsa ba,wani sashen na zuciyarta yana mintsinarta kan ta shiga ta duboshi,wani sashen yana fadin ki shareshi,zai kawo kansa da kansa,kulawa ma yabawa ce ai.


Kamar giftawar iska taji fitar sautin qaramin ihu,wanda banda hankalinta dama akan sashen yake babu lallai taji,birki taja ta tsaya,gabanta yayi wani mugun faduwa,ta tsaya cak tana duban sashen nasa,muryar tayi mata kama da muryar widad,to amma yaushe ta shigo gidan?,tunda dai ita bata ji shigowar kowa ba,hakanan bataji fitar kowa ba,ta zubawa sashen idanun sosai ko zata sake jin wani motsi amma bata ji komai ba,sai hankalinta ya rabu biyu,wani sashen na zuciyarta na bata shawarar ta shiga ta duba,wani sashen kuma yana cewa tsarguwa ce kawai tayi,duk da haka saita kasa gamsuwa,ta dawo farfajiyar gidan ta zauna saman fararen kujerun da abbas din ya zuba a wajen saboda baqi,idanunta nakan sashen tana nazartarsa.


Babu ma alamun haske gaba daya,wanda wannan sign din da take gane abbas din yayi bacci,don baya kwanciya da haske a kanshi,sai taji zuciyar dake gaya mata tsarguwa ce tafi rinjaye,amma duk da haka zata jira dawowar yaron,tasan zaiyi wuya wani ya shigo ko ya fita baya wajen.


Bai jima ba ya dawo da awarar a farar leda karrr kana hangota quru quru,tasa hannu ta karba tana dubansa


"Babansu mimi ya fita ne dazu?" Kai ya girgiza


"Anya?,tunda ya dawo dai banga ya fita ba"


"Bayan shi fa ba wadda ta shigo gidan nan?" Kai ya jinjina


"Babu gaskiya" saita gyada kai tana sauke ajiyar zuciya


"Shikenan jeka" sai data qara wasu sakanni sannan ta miqe ta koma ciki,tana tafe tana waigen sashen, zuciyarta taqi gamsuwa,amma ranta ya aminta da abinda yaron ya fada,tsaki taja daga qarshe,ta maida qofa ta rufe sashenta.
[3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*


*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*


Page 70




Duk da cewa baikai ga cimma gaci ba,duk da cewa buri da muradinsa bai cika ba......amma ta kaishi wata duniya data sake haukata tunaninshi,ta sake ninka burinsa......ta sake kwadaita masa ita,ta kuma haifar da wani yanayi da kai tsaye zaka kirashi da ZAZZAFAR K'AUNA a karon farko,cikin jininsa ya dinga ji cewa eh weedad din ta dabance,zata iya zamowa ta musamman cikin mata..... za'a iya kiranta da 'yar baiwa,ya samu wani irin nutsuwa da tarin ni'imomin dake hutar da zuciya su kuma sanya ma ruhi nutsuwa tattare duka a iya jikinta kadai,tun baikai ga afkawa waccar duniyar ba.


Wani irin ciwo yakeji har cikin zuciyarsa sanda take rera wani irin kuka,ciwo ciwo takeji daga can qasanta duk da baiyi yawa ba,saidai hankalinta a mugun tashe yake,me ya aikata mata kenan?,da wanne fuska zata kalli mutane?.


Yayi lallashi yayi ban bakin amma a banza,har sai da bacci ya taimakeshi ya dauketa,sai ya zareta daga jikinsa a hankali ya shimfidar da ita,ya kunna bedside lamp ya matso da ita kusa da fuskarta sosai.


Kallo na haqiqa ya zauna yana qare mata,baisan da wanne suna zai kirata ba,baisan kuma a wanne matsayi zata iya tsayawa cikin zuciyarsa ba daga ranar da ya maidata tashi,a yanzun Allah ne kadai yasan me yakeji a kanta,qauna soyayya tausayi da kuma shauqi gaba daya, mintuna qalilan amma sun canza matsayinta daga wani bigire zuwa wani bigiren na daban.


Ya jima zaune kamar mai karanta littafi yana kallon baby face dinta da tayi jazur da ita,sannan ya sauke ajiyar zuciya,ya zura qafafunsa ya sauka daga saman gadon ya shige bandaki.


Tsarkake kansa yayi sannan yayi wanka,ya fito ya tsane jikinsa da kyau ya sauya kaya sannan ya koma saman gadon,bai jishi dai dai ba har sai daya jawota jikinsa,tunane tunane ne masu tarin yawa ke masa yawo a kai,shi kansa idan yace ga dai dai lokacin data ma zuciyarsa wannan muguwar illar yayi qarya,wani abu mai qarfi akanta ya dinga shigarsa,sai ya dinga jin gaba daya duniyarsa ta ta'allaqa da ita.


Kiran sallar asuba ne ya tasheshi,har ya gama shirinsa na fita masallaci bata ko motsa ba,bacci take sosai tana kuma sauke ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci,har sunkuya saman kanta zai tasheta yaji ya kasa tashin nata,yaja mata bargon ya rufeta bayan yayi kissing goshinta,ya fita yana waiwayawa kamar wanda akace za'a dauketa kafin ya dawo.


Sanda ya fita sallar yayi mamakin ganin cunkoson jama'a a layin nasu,ya qarasa a hankali ya fara musabaha da mutanen dake wajen


"Munyi tunanin baka gari ai yallabai" daya daga cikin dattawan layin ya fada yana duban abbas


"Me yake faruwa alhaji audu?" Abbas din ya tambaya yana dubansa


"Wallahi daren jiya 'yan fashi suka shigo gidan maqocina alhaji isah"


"Subhanallah" ya fada cikin alhini


"Kusan kowa yaji abun,don tun wajen karfe daya na dare suka shigo unguwar,basu fita sai qarfe uku"


"Ya salam,Allah bai sa naji ba,amma aka rasa wanda zaiyi kiran koda wayata?"


"Wallahi Allah ya daukewa kowa wannan tunanin" matsawa gaba ya fara yi zuwa gidan alhj isah din,inda mutane suka fara dandazo


"Badai wanda suka raunata ko?"


"Eh to,sun harbi yarinyar sa,suna hanyar kaita asibiti"


"Kun kira jami'an tsaron?" Cikin alhini alhj audu ya girgiza kai


"Kusan awa guda kenan amma babu su ba dalilinsu" sosai ran abbas din ya baci,ya tambayi police din wanne area dinne alhaj audu ya gaya masa,sai ya fidda wayarsa yayi kiran dabai wuce na minti uku ba cikin bacin rai


"you must be there before thirty minutes" abinda ya fada kenan ya kashe wayar ya mayar aljihu


"Kada kowa ya shiga cikin gidan,sannan suma mutanen gidan a gaya musu su nisanci inda abun ya faru.... alhaji muje muyi sallah tukunna" tare suka rankaya da alhaji audu zuwa masallacin suna sake tattauna yadda abun ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login