Showing 135001 words to 138000 words out of 196911 words
Chapter 46 - A RUBUCE TA KE book 1 Completed Huguma .txt
faru,bashi da nauyin bacci sam,kamar yadda bai saba dogon bacci ba,amma yayi mamakin yadda jiya har akayi aka gama abun baiji ba,lallai da gasken gaske 'yar qaramar yarinyar ta gigita masa rayuwa da kyau a jiyan,ta kuma shirya janshi zuwa wata rayuwa ta daban,baisan sanda wani siririn murmushi ya kubce masa ba.
Wannan case daya faru a unguwarsu ya hanashi komawa gida da wuri,sunata bincike kan abun har sai da suka samu nasarar tracking barayin cikin taimakon Allah da kuma qwarewar da yake da ita,sai wajen qarfe daya na rana sanann ya gama nasa aikin,ya danqawa wadanda alhakin kula da area din yake a hannunsu,ya zare safar hannunsa ya miqawa daya daga cikin police din,gaba daya hankalinsa yana kanta tun dazun,dauriya kawai yakeyi.
Sama sama ya amsa gaisuwar yaron gidan nashi ya wuce zuwa cikin gidan,kai tsaye sashensa ya wuce,ya tura qofar falon ya shiga,bata falon bata bedroom din,sannan bata toilet,sai zuciyarsa ta raya masa ko tana sashenta,don haka ya juya akalarsa zuwa can.
Kaf ya gama dubawa bai ganta ba,sai abun ya shiga bashi mamaki,baya da niyyar shiga sashen hafsat din yau gaba daya,amma dole ya shiga ya gani ko tana can.
Dukkansu suna falo ita da yaran,tuni falon ya koma 'yar gidan jiya,tana saman kujera zaune abinta,ta cika tayi fam da fushi,daga abbas din har widad din kowanne da nasa laifin a wajenta,donme yarinyar zata tafi gidan hajiya tayi zamanta?,uban waye zaiyi mata aikin da tafi kowa sanin itace zata yishi?,sannan abbas din me yake nufi da ita?,har azahar tayi amma ya kasa leqowa yaga lafiyarsu?,jikinta ya soma sanyi amma wani sashen na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwa,tare da sake kambama mata laifukansa,duk da haka ta soma rasa qwarin gwiwarta,tasanshi....yana da danne zuciyarsa da hanata saurin fushi,amma kuma idan yayi fushin bashi da dadi sam.
Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taga shigowarsa,ya tsugunnawa yaran suka haye bayansa,fuskarsa na fidda murmushi,zuciyarsa dauke da tausayinsu,da babu alamun an musu wanka
"Ina antynku?"
"Daddy ta dawo?,ka kaini wajenta" mimi ta fada,abinda ya tabbatar masa kenan bata shigo ba kwata kwata
"Ina kwana?" Ta fada ganin yana niyyar miqewa ba tare daya kalleta ba
"Lafiya"
"Ga breakfast dinka har ya huce baka ci ba"
"Na qoshi" ya amsa mata yana ficewa riqe da yaran.
Hankalinsa yadan tashi,ina ta tafi to?,ya tambayi kansa,sai ya jawo wayarsa ya kira layinta,a kashe layin yake,ya sauke wayar yana fidda iska daga bakinsa,gidan hajiya ta koma?,wata zuciyar ta gaya masa,har ya danna kiran layin hajiya sai ya kashe,idan ta tuhumeshi dalilin komawarta baisan me zaice mata ba,don haka ya kira layin umar.
"Kana gida ne?"
"Eh hajiya za'a baka?"
"Weedad tazo?"
"A'ah yaaya,tun jiya dai dana kawota gida"
"Okay,karka cewa hajiya ga abinda na tambayeka"
"To yaaya" umar din ya fada ,kafin ma ya qarasa abbas din ya katse kiran,sai yaji hankalinsa ya sake tashi.
Muhsin ne ya fado masa,baiyi qasa a gwiwa ba yayi kiransa bayan sun gaisa kafin abbas dinma yace komai ya rigashi magana
"Jiya jiya muke zancanku,inajin madam fa gobe ko jibi zata shigo ganin diyarta,nace ban da tabbacin kunxo weekend wannan satin"
"Jiya mukazo,amma kuma banajin zamu jima zamu koma,yanzun ban fiya sakewa a bauchi ba,ayyuka sunyi yawa a kaduna" hira kadan suka taba sukayi sallama,don shima muhsin din fitowarsa kenan daga gida yana kan hanya yana driving.
Wayar ya ajjiye,ya koma gefen gadon ya zauna hannuwansa cikin sumarsa yana murzata a hankali,yanason qwaqwalwarsa ta hasaso masa mutum na gaba da zai kira ya bincika ko can taje,ya akayi ta iya fita daga gidan har ta fita ba tare da wani ya ganta ba?.
Kasa zama yayi,sai kawai ya miqe ya dauki key din motarsa,tsoronsa daya kada yarinyar mutane ta bata cikin garin daba nasu ba,don yana da tabbacin zaiyi wuya ace shigowa akayi aka dauketa,don ya duba duk wani abu da zai iya bada alamun hakan bai gani ba,sai ya fita da yaran ya zubasu a motar suka fice daga gidan.
Layi layi titi titi ya dinga bi yana dubata amma sam babu ita ba alamarta,har wajen azahar,ya tsaya a wani restaurant ya siyama yaran takeaway,ya dawo cikin mota ya zauna kenan wayarsa ta dauki tsuwwa,ya duba me kiran sai yaga muhsin ne
"Kasan matarka ta tafi kano?"
"Kano?" Ya tambayi muhsin din cikin mamaki qwarai,duk da dama yana cikin dimuwar son sanin ina tayi
"Eh,yanzu muka gama waya da ummu,ta kirani tace na shaida maka,don tafiyar batayi mata kama data nutsuwa ba" qatotuwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata nutsuwa na saukar masa
"Alhamdulillah" ya fada a fili
"Ka ganni a gefan hanya,tun dazun nake checking ko batayi nisa ba,ina shirin kira headquarter ma su bani mutane muyi aikin tare"
"Subhanallah.......wanne irin sakarci ne wannan?,halan bata gaya maka ba bakasan da tafiyar tata ba" qaramin murmushi ya subuce masa,yasan sarai muhsin ba wasa,yanzun nan idan yace zai gaya masa gaskiya sai yace zai taba masa mata,shi kam a yanzun a yadda widad takai har cikin ruhinsa,baya jin ko ruwan sama zai lamunce masa ya taba masa ita
"Me na tone tone?, tunda ka isar da saqon ummu shikenan,zan kirata"
"Please abbas......kada kace zakayi kawaici,ka gayamin gaskiya"
"Amma dai kasan indai kace zaka shiga tsakanin miji da mata zakaji kunya ne ko?"
"I know.....but....."
"But what?,shikenan kawai,ka qyalemu tsakaninmu ne"
"Alright,Allah ya sawwaqe" daga wannan sukayi sallama ya aje wayar.
Mamaki ya sake kamashi,yayin da qaramin murmushi ya subuce masa,rigimammiya ce yarinyar ta ajin qarshe,ya akayi har ta iya kai kanta kano?,da gaske batasan wannan rayuwar ba,batasan meye ma'anar aure ba at all
"I will teach her......bazan bari ki subuce min ba,zan koya miki abubuwa masu zafin da zuciyarki zatayimin riqon tsauri da kyau" ya fada shi daya kamar me sambatu,abinda yake ji a ransa game da ita yafi qarfin a kirashi so,saidai wata irin zazzafar qauna da bai taba jin kamarta ba.
Aje wayarta ummu tayi tana sauke dubanta ga widad data cusa kanta cikin pillow tana ta sheqa kukanta,kukan da tunda ta iso kano take kwararashi,tayi tambayar duniya amma taqi daga kai ta kalleta ma bare akai ga amsawa.
Abu daya ne yasa hankalin ummu bai wani daga ba,widad din tata tayi fes tayi fresh,ta sake murjewa,ga kuma girma data qara,ta fara zama budurwa sosai,aure ya kwarzantata
"Widad" ta sake kiran sunanta,shuru bata amsa ba sai kuka,tana tsoron su hada ido da ummun,tana ganin kamar zata gane abinda yayi mata a daren jiyan
"Kinga idan ba zaki amsa min ba,ki daina kukan kada kanki yazo yayi ciwo" ummu ta fada tana miqewa
"Ki samu waje ki kwanta" ta sake fadi bayan ta isa gaban wardrobe dinta ta fidda hijab,tayi sallar azahar sannan ta dauki wayarta ta fita tabar mata dakin,cikin ranta tana juyayin abinda ya faru,kodai ita da kishiyarta ne?,tunda muhsin ya sake kiranta yace abbas din yace babu komai,amma kishiya kuma......nawa widad din take da har kishi zai hadasu tayi wannan tafiyar afujajan.
Da wannan tunanin ta isa falonta,ta iske latifa tana aje abincin rana
"Batace komai ba ummu?" Latifan ta tambaya cikin damuwa
"Uhmmm.....bata ce ba,nifa banga wani alamun damuwa tattare da ita ba,nafi zaton shirmenta ne kawai ya motsa,idan kuwa haka ne zataci qaniyarta,ta yaya zata dauko qafa daga bauchi ta taho kano ba tare da izinin mijinta ba?,baya ga haka kuma ita kadai a wannan rayuwar da muke ciki?" Ajiyar zuciya latifa ta sauke
"Ayi mata dai a hankali ummu,ai ruwa baya tsami banza"
"Kin manta widad din ne ashe" ummu ta amsa mata,wanda tana rufe bakinta momma tayi sallama
"Barka da rana ummu" ta fada tana 'yar fara'ar da batakai zuci ba,da kallo ummu ta bita
"Ke kuma daga ina da rana haka fatsar fatsar?" Murmushi ta danyi tana wuwwulga idanunta wai ko zataga himilin kayan widad din da akace an ganto ta shigo ita kadai
"Zan fita ne nace bari na leqo,idan kina da canji ki aramin"
"Canji?" Ummu ta maimaita cikin mamaki,saboda irin wannan ita baya hadata da surukanta
"Eh....eh" dan shuru tayi tana karantar momma din,sai kuma tace
"Allah ya kyauta,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta baki" amsa mata tayi sannan ta nufi kitchen din tana kalle kalle a falon ta gefan idanunta.[3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 72
"Umman walidi.....amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba"
"Me take ce miki?" Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi'ar banza
"Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata"
"Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?" Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon
"Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din"
"Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin" wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane.....hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba.
Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa
"Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku".
Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din.
Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa
"Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri" kai ya jinjina yana murmushi
"Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?"
"Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin 'yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun"
"Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo" anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin.
Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka?
"Me ya faru anty naga kina kallona" murmushi tayi tana sakin habarta
"Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi" dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta.
Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai.
Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai
"Ashsha.....ashsha" sai yaja tsaki
"Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?"
"Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali" abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin.
Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada
"Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?" Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba.
Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi
"Tunda na tafi fa anty banzo ba ba'a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba"
"Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso" dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa.
Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za'a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya.
*_BAYAN WATANNI HUDU_*
*********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin
"Alhamdulillah".
Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar.
Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane.
Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala'in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai
"Yadai...." Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a 'yan kwanakin nan haka take ji a kansa
"Ba komai......"sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan.
Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi.
Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth
"Shikenan?,i have done?" Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa
"Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana" yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu'amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa.
Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira.
Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura
"Can you help me?"
"Dame uncle?"
"Idan kin gama gyara sassanki please" murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya
"Za'a yi in sha Allah uncle"
"Thank you" murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin.
Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi.
Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun