Showing 18001 words to 21000 words out of 41935 words
ta je ta sayo musu maganin ciwon kai, bayan ya karya ta basa maganin ya sha, Ko da ya sha shine ya ɗan samu sauƙi, ganin barci ya ɗauke sa ne yasa ta fita ta bar masa dakin. Ita kuma Nana ta fara aikin gida. Hajja tana zaune Nana na kama mata kai shi kuma Ibrahim ya shiga wanka sai ga wata ƴar makwabtansu ta shigo da gudunta tana kiran sunan Nana. Har sai da suka tsorata bata ko tsaya wata-wata ba ta fara faɗin "Nana zo kika sirikarku ta zama tauraruwa. Tana faɗa tana turawa Nana wayar da har ta miƙe tsaye zata gudu, Hajja da kuwa tuni itama ta miƙe kasancewar har yanzu tana da ɗan kuzarin ta bata sakwarkwace sosai ba. Har Hajja zata fara masifa amma idanunta ya sauƙa a kan wata mai kamar Siyamar Ibrahim dinta sanye da wasu kaya komai nata a waje. Da dan mamaki Hajja ta ce "Me zan gani haka, wacce wannan ɗin jiki duk a waje? Yarinyar mai suna Fatima ta ce "Hajja ai Siyamar Ibrahim ce, ina wannan taron da a keyi na sarauniyar kyau, to shine fa ta shiga kuma gashi Alhamdu Lillah ta zo ta biyu. Fatima ta ƙarasa tana sakin murmushi. Hajja ta saki dogon salati har zuwa ƙarshe kafin ta amshi wayar daga hannun Nana da tayi shiru tana mamaki. Hajja ta ƙara kafawa wayar ido kamar zata shige ciki. Ta kai minti biyu kafin ta ce "Lala-lala wannan ba Siyama ba ce, Nana gane min wannan yarinyar da idanunta babu ko a lamar kunya, kalli yanda take abun fa da gani kasan ta saba, wannan ba Siyama bace. Ganin dai Hajja taki yarda yasa Nana faɗin. "Hajja ita ce mana ai shine dalilin da yasa Yaya wannan ciwon. Daidai lokacin kuwa sai ga Ibrahim ya fito daga wanka ai kuwa Hajja ta miƙe ta samesa ta na nuna masa wai da gaske Siyama ce wannan? Ibrahim ya kalli Fatima da ta sunkuyar da kai ganin sa ya fito, ya ce "Karɓi wayarki ki bar gidan nan" Hajja ta ce "Taje ina baka sanar da ni gaskiya ba? Ganin Ibrahim yana ƙoƙarin ajiye bokitin hannunsa ne yasa ta amshi wayar ta ta bar gidan da sauri. Hajja kuwa gaba ɗaya ta shiga ruɗani ita dai har yanzu bata yarda Siyama ce wannan ƴar duniyar da ta gani ba. Nana ma dai abun yazo mata a bazata, domin dai Siyama barta da iyayi da girman kai, amma sam halinta bana kwaɗayi bane, sannan a ɗan sanin da tai mata tun da suka dawo wannan unguwar zata iya tabbatar da cewar yarinya ce ba mai hangen nesa ba, to ko dai ɗan wannan kyawun da take da shi ne ya ruɗeta har ta shiga wannan harkar. Haka kawai taji ta fara tausayin Yayanta domin kuwa tabbas tasan ya rasa Siyama kenan kuma tasan irin son da yake mata.
Ibrahim kuwa haka ya shiga ya shirya sannan ya fito da kayan aikin sa na zuwa gareji, kallo ɗaya Hajja tai masa ta tsorata domin kuwa tabbas ya rame sosai. Hajja ta ce "Ina kuma zaka je bayan baka da lafiya? "Hajja kirana a kayi wani aiki zamu karasa yanzu zan dawo " Ya faɗa yana ƙoƙarin fita. Hajja ta ce "To dan Allah dai karka dade idan kasan ba zaka iya ba ka dawo gida kaji?" Ibrahim ya amsa da tom kafin ya sa kai ya fita. Koda ya fita ya fara takawa a ƙafa har gurin aikin nasu. Yana zuwa ogan nasu ya fara tambayarsa lafiya yau ya makara Ibrahim ya sanar masa cewar baya jin dad'i ne shi yasa. Haka suka fara aiki amma ina wani irin sabon zazzaɓi ne ya rufe sa, ogan nasa da kansa ya tare masa mai mashin ya dawo da shi gida. Ko lokacin da ya dawo gida labarin Siyama ya gama yaɗuwa, izuwa yanzu Hajja ta yarda da cewa Siyama ce domin kuwa yadda mutane suka dinga kawo mata tsegumi kamar ba gobe. Nan dai Hajja ta shiga basa baki akan yayi hakuri ai tana sonsa wannan ma kuskure ne idan yayi mata faɗa zata bari. Shi dai Ibrahim babu abun da yake masa zafi sai idan ya tuno da cewar Siyama fa bata taɓa son sa ba, tayi amfani da shi ne kawai, a takaice dai yaudarar sa tayi. Idan ya tuna wannan shine ciwon ke ƙaruwa ga kuma wani irin sonta da yake ɗawainiya da shi, ji yake kawai ita yake son gani ko da kuwa zaginsa ne zata yi, gashi har yanzu bata kunna wayar tata ba. Wani abokinsa ne ya shigo gidan mai suna Haladu wanda ya bashi aron wayar da yaga video ɗin a ciki. Ya ce "Daga garejin ku nake aka ce ka dawo gida yanzu? Ibrahim ya meƙe zauna ya ce "Eh yanzu na shigo zazzaɓi ke damu na" Haladu ya ce "Ka dai saka damuwar wannan yarinyar kawai, ai dama kaga abun da nake faɗa maka, wallahi yarinyar nan ba dan Allah take sonka ba, amma kai kace ƙarya ne, to yanzu ka gani abun da nake so da kai shine wallahi tun wuri kayiwa kanka karatun ka natsu ka manta da wanzuwarta ka kama gaban ka, ka dai ga inda ta dosa harkar zubar da mutunci da wulaƙanta.
Ibrahim da ya kafe Haladu da kallo har sai da ya gama kafin cikin ƙarfin hali ya ce "Haladu wallahi daga ranar da abun ya faru zuwa yau wani irin sonta ne ya ƙara ƙaruwa a zuciyta, wallahi ina son Siyama sosai, domin ina ji kamar zan yi hauka idan na rasa ta, please dan Allah ka bani shawarar da zata kaini ga samun Siyama please? Haladu ya ɗanyi dariya kaɗan kafin ya ce "Kaga IB karka ɗorawa kanka abun da Allah bai ɗora maka ba, tun wuri ka fita batun wannan yarinyar, ni dai ita ce shawarar da zan iya baka. Ibrahim ya ce "Wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba, domin ni sabo da Allah nake sonta, kuma itama tana sona inaga wani ne yayi wasa da tunaninta kasan mace kuma yarinya ce. Haladu ya ce "Ina waya ta? Ibrahim ya ce "Kasan me ya faru jiya tsakanin mu da ita? Haladu dai ya ce "Dan Allah ka bani wayata ana jirana. Ba tare da ya ɗauko masa wayar ba ya ce "Dan Allah ka kira min ita da wayar ka ni inaga tayi blocking dina ne. Cike da mamaki Haladu ya ce "Sabo da me? Domin kuwa shi kansa Haladu ya san da cewar Siyama tana nunawa IB so amma shi dai yasan ƙarya ne, babu yadda za'ayi mace irin wannan ta kamu da son mutum kamar IB wanda ko a cikin abokansu yafi kowa ƙazanta ga shi dai wani lokaci yana abu kamar mara wayo ko dolo. Amma kam tabbas idan baka san wacece mace ba tsaf zaka yarda cewar Siyama son sa take. "Ta ce wai daga yau babu ni babu ita wai tayi amfani dani ne domin cika burin ta kuma ta cika saboda haka karna ƙara nuna nasanta, Kuma tun juya ina kiran number ta bata shiga. Ibrahim ya faɗa hawaye na zubo masa. Haladu ya saki baki yana kallon ikon Allah. Ya ce "Ita ce ta kalleka ta ce karka ƙara nuna kasanta? IB ya gyaɗa kai. Haladu ya ce "Babbar magana wai kare da kiwon kura. Ya ce "Amma yarinyar nan ba ƙaramar jar wuya bace, wato anci moriyar ganga ko? To wallahi bata isa ba, ai yanzu ta zama sele kuma tayi kuɗi sabo da haka dole ta biyaka duk abun da ka kashe mata harda ƙari, kai nifa wallahi idan nine kai sai ta siya min gida da mota da kuma jari mai gwaɓi harda raran kudade a account, yo kai ai dama ce tazo maka mai kyau, kawai ka manta da ita. Ibrahim da ya gama zuwa ƙarshe ya ce "Haladu bana son zancen banza, wallahi ko kaɗan kudinta bai dame ni ba, ni ita nake so kuma wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba. Haladu ya katse shi da faɗin Ita dai sarauniyar kyau ɗin ko?. Sosai ran sa ya ɓaci har ya fito ya nunawa Haladu ɗin a fili kar she dai haka suka rabu. Da yamma ya tashi ya nufi gidan su Siyama ɗin amma haka ya ƙaraci zama bata ko fito ba, haka ya hakura zuwa gobe domin gobe ne za'ayi sadaƙar uku na Zainab, haka nan ma yanzu amma bai samu ya ganta ba. Sosai Ibrahim ya shiga damuwa babu yadda Hajja bata yi da shi ba akan ya hakura da ita amma ya kasa.
Yau kwana takwas da faruwar komai kuma izuwa yanzu bai daina ziryar zuwa gidan su Siyama ɗin ba, hardai yaci karo jiya a gurin sadaƙar bakwai suka haɗu da Nasiru yake sanar da shi baya samun wayar Siyama. A nan dai Nasiru yake sanar masa cewar ai bata da lafiya ne, haka Ibrahim ya ƙarbi number sa akan idan yazo gobe zai kirasa sai ya turo masa ita. Haka washegari da kyar ya samu Haladu ya rakoshi akan zasu duba jikin Yaya Bala ne da Nasiru. Koda yazo ya kira Nasiru yazo ya shigar dasu har cikin gidan suka duba Yaya Bala sannan suka gai da Umma sannan suka sake yi musu ta'aziyar rashin Anty Zainab. Bayan sun fito ne Nasiru yaje ya kira musu Siyama akan Ibrahim na waje yana jiran ta. A lokacin zuciyar Ibrahim kamar ta fita tazo gareta jin ance bata da lafiya sai yake tunanin kamar abun da tai masa ne yasa, yasan itama tana sonsa ba zata iya rayuwa ba tare da shi ba. Haka suka dinga tsayuwa zaman jira har dai Haladu ya fara magana, wasa-wasa sun kwashe kusan awa da rabi amma shiru. Hakan yasa Ibrahim sake kiran Nasiru yana ɗagawa ya ce "Har yanzu fa bata zo ba. Cike da mamaki ya ce "Wace ɗin?" Yayi tambayar da mamaki ganin kusan awa biyu da kiranta.
*SIYAMA*
Wayarta ta ɗauko ta jona a chaji tana jin yau dai ya kamata ta ɗan matsa ko Aida ta samu ta kira taji yaya a ke ciki a Team. Ita har ta manta da batun wani Ibrahim a waje, suma su Fati sun ma manta har sun bar maganar. Tana ƙoƙarin saka wayar a chaji sai ga Nasiru ya shigo hannu a saƙale ya na faɗin "Siyama wannan wani irin rashin hankali ne zaki bar mutum sama da awa a waje yana jiran ki, baki da hankali ne? Siyama ta ja tsaki a fili ta ce "Amma ai nace maka kace masa bana da lafiya ne ko? Kuma ai na sanar da shi babu ni babu shi to mai kuma yazo yi mini" Fati da Binta suka cika da mamakin jin cewar har yanzu Ibrahim na tsaye. Nasiru da ransa ya gama ɓaci, gashi dama cike yake da ita, jira yake kawai ya warke sai ya saita mata zama. Ya ce "Na tsare da Allah idan baki tashi kin fita ba sai na ɓata miki fuska da mari, dan ubanki waye ya kawo shi a matsayin wanda take so, na rantse kika ƙara magana a gurin nan sai na tar watsa miki baki wawiya kawai mara hankali. Jin haka yasa ta tashi ko hijjab bata tsaya ɗauka ba, kanta babu ko hula ta nufi hanyar fita. Sai dai ganin Umma zaune a palon ita da Kawu Inuwa suna tattaunawa ne yasa ta juya da sauri ta saka hijjab ta fito fuska a haɗe, babu wanda taiwa magana Palon ta sakai ta fita. A nesa ta hango su, hakan yasa ta nufe su da sauri tana aiyana irin cin mutuncin da zatai musu. Kallo ɗaya tai masa taga ramar da yayi harda wani dogon wuya kamar yaron raƙumi. Tana zuwa babu ko sallama ta ce...📝
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza writer
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza_
*FCWA*
*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*Page 7️⃣*
"Uban me ya kawoka ƙofar gidan mu bayan na maka iyaka da ni, na faɗa maka babu ni babu kai, abun da ya rage tsakanina da kai shine ka lissafo duk abun da kasan ka taɓa kashe mini zan ninka maka kayan ka, bayan haka karka ƙara nuna ka sanni idan kuma ba haka ba, wallahi Ibrahim sai kayi da ka sanin sanin Siyama da kayi a rayuwar ka, zan sa a ƙulleka har karshen rayuwarka. Siyama ta faɗa ranta a mugun-mugun ɓace, domin har ga Allah ya kaita bango, gara tai masa barazana ko zaiji tsoro ya rabu da ita ta sakata ta wala arayuwarta. Cikin karyewar murya Ibrahim ya fara faɗin "Siyamata karki min haka wallahi na yarda zan barki ki ci gaba da yin wannan aikin naki amma ba zan iya rabuwa da ke ba, wallahi da gaske ne ina sonki kuma na hakura da komai dan Allah karki min haka zan iya mutuwa wallahi" Ya karasa yana sunkuyawa har ƙasa. Wani irin banzan kallo tai masa kafin ta ce "Innalillahi wai nima mai ya kaini ai ga shi zan jawa kaina annoba. To bari kaji, na rantse da girman Allah ko mutawa zaka yi ka dawo duniya ka ƙara mutuwa ba zan ƙara bari ka ganni ba, na baka nan da kwana uku ka kawo min lissafin ka zan biya komai idan kuma muka wuce kwana uku to duk abun da ya same ka kai ka jawa kanka. Ta kalli Haladu da ya rakuɓe gefe ta ce "Idan shi wawa ne kuma dolo bai san abun da yake yiba, to kai ka sanar da shi, babu ni babu shi, idan kuma yaƙi ji ba zai ƙi gani ba, soyayya ce munyi a baya yanzu kuma nace na gama ba zanyi ba, kana dai ji ko?" Haladu ya ɗaga kai da sauri ita kuma ta juya zata shige gida. Da sauri Ibrahim ya kamo gefen hijjabin ta yana faɗin dan soyayarki da Annabi Muhammad s a w Siyama karki azabtar da zuciya da sanki, wallahi Siyama babu wasa a magana ta, zan barki kiyi komai ni Ina son ki a haka please. Siyama ta juyo a zuciye ta ce "Sakar min hijabi kafin na wanke maka fuska da mari, wai kai wani irin maye ne mara zuciya, ana soyayya dole ne. Ibrahim ya miƙe tsaye yana kallonta ganin yanda ta ɗanyi fari alamar rama sai hakan ya kara fito da hasken ta, ga wani kyau da tai masa fiye da kullum, jin sonta yake har wani fusgarsa yake kamar magineto ya ce "Siyama ke da kanki kika min alkawarin bazaki barni ba, kuma kince..."Kafin ya ƙara cewa komai ta fusge hijjabin ta ta juya zata shiga gida amma bata an kara ba sai jin ta tayi a cikin jikin Ibrahim kwance kamar ta samu gadon baccin ta. Sosai ya haɗe jikinsu a karo na farko yana sauke ajiyar zuciya har wani lumshe ido yake, yana jin ina ma zasu dauwama ahaka shi da Siyamar sa. Shi kansa Haladu ba karamin shok ya shiga ba ganin abun da Ibrahim ɗin yayi, sosai ya tabbatar da cewar Ibrahim baya cikin hankalin sa, idan kuwa ba haka ba tayaya zai rungumeta bayan nuna masa tsana da take yi har tana faɗin ko mutuwa ma zai yi sai dai yayi. Ita kuwa Siyama tsabar mamaki yasa bata fahimci komai ba, sai da taji yana ƙara kwantar da kansa a wuyan ta, har wani sauke ajiyar zuciya yake, idan bata yi ƙarya ba har wani wari yake yi na ƙazanta. Sosai ta dawo cikin hankalinta, ai kuwa da wani irin ƙarfi ta shiga raba jikinsu amma Ibrahim yaki bata damar hakan, tayi iya yinta amma ya manne ta sosai har neman ƙaryata yake yi. Ita kuwa ganin ta kasa kwacewa ga azabar ruƙo yasa ta fashe da kuka, amma ina Ibrahim bai san tana yi ba, sosai take kuka tana dukan sa ta ko inna amma shi sai lumshe ido yake ya faɗa duniyar tunani. Ganin dai kamar baya cikin hankalinsa ne yasa Haladu zuwa ya shiga ƙwatarta da ƙarfi, da kyar ya yageta daga jikin sa yana jan sa baya. Ita kuwa Siyama ganin haka yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida. Daidai zata shiga Palo shi kuma Kawu Inuwa zai fito suka haɗu. Ya ce "Lafiya ke kuma keda waye haka?" Siyama ta fashe da kuka mai ƙarfi tana nuna waje. Kawu Inuwa ya leƙa sai dai bai hango kowa ba, ganin ta shige ciki ne yasa ya girgiza kai ya bar gidan yana mamakin Siyama. Ko da ta shiga ɗakin su ta tarar da Fati da Binta kowacce na danna waya, bata ko bi ta kansu ba ta shiga rusar kuka kamar wacce aka yankewa ƙafa. Miƙewa tayi ta shiga toilel ta sakarwa kanta ruwa ba tare da ta cire kayan jikin ta ba, sosai Fati suka bita da kallo jin irin kukan da take, har Fati zata tambaye ta amma taga ta shige toilel hakan yasa ta fita izuwa dakin Nasiru. Sosai ta shiga wanke jikinta har lokacin tana jinsa a manne a jikinta, tana kuka tana tsine masa. Koda da fito Binta kawai ta gani a dakin bata ce mata komai ba ta kwashi kayan da zata sake ta komai toilel ɗin.
Tana gama shirya wa ta fito Palo domin ɗaukar a binci, amma tana zuwa taga Umma da Nasiru da yaya Bala da Kawu Inuwa Harda Fati duk sun saka waya gaba suna kallo. Gabanta ne ya bada wani rass domin jin ana kiran sunanta a cikin maganar da a keyi ta cikin wayar duk da cewar kuwa da turanci ake maganar. Kallon Umma tayi taga wani irin kallo da take mata, haka yaya Bala shima. Ƙamewa tayi a gurin ta