Showing 27001 words to 30000 words out of 41935 words
fa Umma yanzu maganar barin karatu har sai wata shekarar ba dabara bace, domin idan shekarar ta dawo sai mun biya komai da muka biya a baya, kuma shi kansa ba zai ji daɗin karatun ba. Umma tayi shiru cen ta ce "To ko zaka je gurin masu gidan naku su bada kuɗin hayar wannan shekarar ne idan yaso kaga ko shekarar ta ƙare sun biya kenan ko? Yaya Bala yayi murmushi ya ce "Umma ko wata biyar bai yi bafa da suka bamu na waccer shekarar, kuma shima da yaya suka haɗa mana, yanzu kuwa muna zuwa zasu ce ai shekarar bata yi ba, kawai dai Umma bari na kira shi Nasiru ɗin muji ta bakin sa. Daga nan yaya Bala ya shiga kiran Nasiru sai gashi ya fito rike da waya a hannu, hannun ciwon nasa ya kumbura sosai babu ko kyawun gani. Bayan ya zauna Umma tace ya tashi ya kira mata Fati. Bayan sun zauna ta mayar musu da duk yanda sukayi, Nasiru ya ɗago da sauri jin abun da ake ciki. Ya ce "Yaya shekara mai zuwa fa cikin jiniyoyina fa zan shiga duk abokaina lokacin sun tafi sun barni, gaskiya Yaya a'a ba zan iya jira har wata shekara ba. Umma ta ce "To da wani hannun zaka yi karatun da rubutun ana magana kana faɗin ba zaka iya ba kamar wani karamin yaro, ko baka fahimci matsalar da ake ciki bane, duk akan maganar kuɗi ne, yanzu ma asibiti za'a koma a kan wannan hannun naka amma kazo kana abu kamar karamin yaro. Nasiru dai ya cuno baki ya shiga haɗa rai. Fati dai tayi shiru tana sauraronsu. Bayan kamar minti biyu Umma ta ce "To ko za'a saka wancen gidan a kasuwa ne, idan yaso sauran kudin sai ka fara wani kasuwancin da shi, tunda kaga aikinku ba kullum ake samu ba ko? Da sauri Yaya Bala ya ce "No a'a Umma ba zamu sayar da abun da muka mallaka na gado ba. Ya ce "Umma idan muka sayar da gidan zamu zo muyi da na sani, domin gidan Nasiru nake so idan Allah ya kai mu lokacin auransa sai kawai a gyara ya shiga. Cikin faɗa Umma ta ce "To Allah zai hore muku in sha Allah kafin lokacin ku siya wani, yanzu yaya kake so ayi, wannan dai gida naku ne, bayan shi baku da wani abu da za'a sayar asamu lafiya da kuma ci gaban karatun ku, to yanzu ni dai na gama magana aje a sayar Allah zai hore, lokacin da ka sayi wannan gidan kasan zaka samu kuɗin ne, Allah ne yaso kuma ya nufa har ka siya, sabo da haka ku dinga kyautata zato mai kyau ga ubangijinku shine ke yi a lokacin da babu mai baka. Sosai Umma ta shiga faɗa cikin na nasiha hardai suka yarda akan za'a sayar. Bayan an amince ne yaya Bala ya ce "To Umma yanzu mu sanarwa da Kawu Inuwa da Baba (wato Husaini ƙanin mahaifinsu shi suke cewa Baba) Umma ta ce "Eh ai dole zasu sani. Fati dai tuni ta tashi ta shiga cikin gurin Binta da ta bari tana ƙarasa abincin nasu, ganin bata gama bane yasa ta ɗauki kwano ta ɗebo kaɗan domin yunwa take ji. Haka ta fito palon ta zauna Umma ta bita da kallo domin kuwa tasan ba'a gama ba ta ɗebo. Umma ta sake cewa da Yaya Bala "Yanzu wacce sana'ar kake ganin zaka fara ? Kafin yayi magana suka ga an turo ƙofar an shigo, gaba ɗaya suka mai da kallonsu ga ƙofar. Siyama ce riƙe da kin mota a hannu. Itama kallonsu take, ganin yadda suka haɗu family amma babu ita a ciki sannan babu Anty Zainab. Sallama tayi tana kallon hannun yaya Nasiru da yayi wani irin kumburi wanda bata taɓa kula ba. Kusa da shi taje ta zauna tana ta kallon hannun. Umma dai tun kallo ɗaya bata ƙara bi ta kanta ba. Yaya Bala a karon farko da zai yi magana da ita kenan tun da abun ya faru. Ya ce "Daga ina kike? Wa kika fadawa zaki fita? Kamar daga sama taji tambayoyin nasa domin sai yanzu ya shiga sha'anin ta tun da komai ya baiyana. Sai da ta tabbatar da ta haɗa maganar a bakin ta tsabar rudewa kafin ta iya cewa "Dama da dama dama naje gurin mutumin da yayi min Sherri ne ku... "Wani tsawa da Umma ta daka mata ne yasa ta bata san lokacin da ta zamo ƙasa ba. Sosai ran Umma ya ɓaci jin tana neman raina musu wayo wai yayi mata Sherri. Ta ce "Da baki je kin sanar da shi komai ba yaya za'ayi ya sani, idan baki fito kin faɗi gaskiyar inda kika je ba, Allah zan shayar dake ruwan mamaki, kuma daga nan zaki haɗa kayan ki ki koma gurin shi arnen uban naki. Umma ta faɗa tana miƙewa tsaye domin Umma nada zafi sosai, abu kaɗan ke ɓata mata rai. Yaya Bala da shima saida ya tsorata da irin wannan tsawar da Umma tayi ya ce "Wannan makullin motar ta waye? Siyama da ta gama tsorata ta ce "Mota ta ce" kallon-kallo aka fara yi a palon. Ya ce "Waye ya baki? Sai a lokacin Siyama ta ɗago ta kalli Umma ganin ita take kallo sai tayi saurin yin ƙasa da kai, sosai take son aro jarunta tasa a kanta amma da ta haɗa ido da Umma sai ta kasa, tabbas tsoron da Umma ta saka musu nata tun suna yara yayi tasiri akan Siyama, domin duk yadda takai da son yin magana mai ma'ana da ta kalli Umma sai komai ya kwance mata. Sosai Umma ta daure bata sharara mata mari ba jin ana tambayarta ta yi shiru.
Yaya Bala ya ƙara maimaita tambayar ta ce "Tawa ce da na samu bayan nazo ta biyu" Sosai yanzu harda Yaya Bala ɗin suke mamaki. Ita dai Umma bata fahimta ba, haka kawai sai a bata mota dan tazo ta biyu dole akwai dai wani bayanin. A lokacin wayar Siyama ta shiga ƙara ta duba taga Aida sai ta kalli Umma da Itama ita take kallo suna haɗa ido ta kawar da nata. Yaya Bala yace ki ɗaga mana. Kafin ta ɗaga kiran ya katse. Nan sai ga wani kiran. Tana ɗagawa Aida ta ce "Ke a kwai matsala fa, babu yadda banyi da Oga Fita ba amma yace Wallahi sai na kawo su gidan ku, wai masu aikin ne suka matsa sosai, shi kuma baya so ki rasa aikin yanzu haka gamu a hanya, domin kina fita yazo Allah ne ma yayi ba zaku haɗu ba. Siyama ta gama shiga ruɗu ta ce "No dan Allah karki kawo shi please " Aida kuwa ta miƙawa Oga Fita waya shi kuwa ya ce "Naga ke ɗin ce har yanzu baki yi serus bane, kawai yau ayi komai. Yana faɗa ya ka she wayar. Lokaci ɗaya hawaye suka zubowa Siyama. Yaya Bala ya riga Umma yin magana ya ce "Su waye zasu zo?" Ba tare da ta kalli kowa ba ta ce "Oganmu ne zaizo yayi muku bayani domin ni bazaku yarda da niba. Umma dai sai kawai taji Siyama ɗin ta bata tausayi ganin tana hawaye. Binta ce ta fito daga kicin tana faɗin an gama abinci a kawo yanzu ne? Yaya Bala ya ce "Bari tukunna baƙi zasu zo yanzu sai kawai a kawo idan sun zo. Yaya Bala ya dawo da kallon sa izuwa ga Siyama ya ce "Kenan shine yasaka ki a wannan abun shi ogan naki?* Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da wanda yasa mata kwadayin abun, sai kawai taji wani irin ƙwarin gwuiwa yazo mata ta ce "Babu wanda ya saka ni, kawai ina son abun ne tun ba yanzu ba. Ta faɗa a dake. Binta dai sai bin Siyama da kallo take, sannan a karo na farko da take wa Yaya Bala kallon ƙurulla tun bayan da Momy (wato mahaifiyarta) ta ɗarsa mata a kan cewar ta dinga manne masa komai tai masa ko Allah zai sa ta maye gurbin matarsa Zainab. Farko Binta taji tsaro domin bata taba harsaso haka a ranta ba, kuma tana ganin yayi mata girma, mai zai hana ace Nasiru amma Yaya Bala ina zata kai shi. Sai da Momy tai mata dogon bayani sosai kamar yadda itama akai mata akan cewar ai yanzu Siyama zata fara samun kuɗi na bam mamaki domin yanzu ta zama salebiriti. Hakan yasa take so aci kuɗin da ƴarta. Sosai Binta ta yarda Duk da bata jin sonsa ko na ɗugo ɗaya. Yaya Bala ya ce "Siyama shekarar ki nawa? Kin gama karatu? Mai muka rageki dashi da har kika zaɓi wannan aikin na zubar da mutunci? Siyama ta ce "Yaya wallahi babu abun da kuka rageni da shi, kuma banyi komai ba sai sabo da ku, duk abun da nake yi sabo da kune wallahi yaya. Yanzu haka na mallaki abubuwa da dama harda motoci da kuɗaɗen da ban san a dadin su ba, kuma yanzu haka na samu wani aiki shine nake tsoron tambayar ku, dan Allah karku hana ni, wallahi zan kula da kaina nasan me nake yi, please dan Allah yaya, kuma wannan maganar da tsohon nan yayi duk ƙaryace wasu maƙiyan nawa ne suka haɗa baki dashi domin aci mani mutunci amma zan gano koma su waye, kuma zaku gani please Umma. Ba Nasiru da Fati da Binta ba, har Umma da Yaya Bala saida suka shiga mamaki. Lokaci ɗaya Nasiru ya tashi daga ƙasa ya zauna a ransa yana jin ya samu mota. Ita kuwa Binta gaba ɗaya ma ruɗewa taso yi, domin kaɗan ya rage ta nuna kanta a gurin. Yaya Bala ma dai jin abun da take cewa yasa ya kalli Umma. Umma ce ta fara buɗe baki zata yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa akayi kafin Aida ta shigo, sai Oga Fita sai wani mutumi sanye da bakaken kaya. Guri aka basu suka zauna aka shiga gaisawa. Fita baya jin Hausa shida baƙon nasu. Umma kuma bata jin turanci. Hakan yasa lokacin da suka gai data sai kawai ta ɗaga musu hannu. Yaya Bala yasa Binta da Fati suje su fito musu da abinci. Lokaci ɗaya Siyama ta tuno da Jamil da jamilu yanzu haka suna cen suna aikata iskancin su, kallon Aida tayi ganin tana ta sunne kai, lokaci ɗaya suka haɗa ido kowa na tausayin junan su da irin nufinsa. Yaya Bala yayi wa su fita tayin abinci. Suka sha abun sha suka ce a ƙoshe suke. Yaya Bala dai sai kallon Siyama yake akan tayi musu bayanin mutanen, kaman kuwa tasan abun da yake nufi ta fara jawabi.
Ta nuna Oga Fita tace "Wannan shine Oga Fita ogan mu. Ta nuna Aida ta ce "Wannan sunanta Aida abokiyar aiki nace, kuma ƙawata. Waccen kuma ban san sa ba. Ta nuna gurin da wannan mai baƙaƙen kayan yake. Umma sai kallo Aida take ganinta kyakkyawa da ita, a ranta tana faɗin Sai dai babu kyawun zuciya. Oga Fita ya fara maganar abun da ya kawo su. Ya fara basu labarin yadda akayi yasan Siyama da kuma lokacin da suka fara aiki tare, har dalilin da yasa suka ƙirƙiri iyayen ƙarya akan tana tsoron a gano cewar itace a gidan su domin tana tsoro sosai. Har dai lokacin da ta samu nasarar zuwa ta biyu da irin kyautar da ta samu da kuma aikin da ta samu na Model. Sannan ya warware musu gaskiyar magana akan abun da Olusha yayi cewar ƙarya ne. Yana yi Nasiru na fassarawa Umma. Bayan ya gama jawabin ne ya ɗora da faɗin abun da ya sani iya gaskiyar sa akan aikin Model..."Aikin Modelling aiki ne mai kyau wanda mutum zai tara kuɗi sosai, kuma mutum zai zama salebiriti a duniya, duk inda ka shiga za'a san ka. Kuma aikin kowa nayi muddin kana da jiki mai kyau. Saboda haka ina baku shawarar da kuyi hakuri kubar Siyama ta fara wannan aikin zakuyi alfahari da ita kuma zaku samu kuɗi. Fita ya nuna wannan mutumin ya ce "Wannan ɗaya daga cikin mutanen da zata yi aiki a campanin su ne, to suna ta damu na akan sai tazo an fara ni kuma na sanar da shi cewar ai tana da ɗan matsala da iyayenta ne, shine ya ce azo tare da shi yaji meye matsalar ku. Ya ƙarasa yana bawa mutumin damar yin magana. Mutun ya ɗaga musu hannu ya fara da faɗin "My name is Dele Ali I'm from England London, I'm the manager of the Baby and me Company for Nigeria and Marocco. Yaci gaba da faɗin...mun ga Siyama a taron kyau na nan ƙasa Nigeria kuma tayi kyau da irin kalar da muke so mu dora a fuskar tallan kayan mu, shine muka zo neman yarda ta da ta iyayen ta, zamu yi aiki da ita a duk inda muke da gurbin kamfani. Kuma mun dauki nauyin baku jari daga garemu, harda gida kyauta anan garin Abuja duk daga garemu. Sosai Nasiru yake aikin fassara, ita dai Umma sai saurara take har aka zo karshe. Binta kuma ta gama cika da mamakin jin irin abun Alkairin dake tunkaro wannan ahalin. Kafin kowa yayi magana Oga Fita ya ɗora da faɗin... "Yarinyar ku tana da hankali domin tasan me take yi, kar kuji komai a kanta ko ni na yarda da ita...📝
Love all
One love
Comments
Ana shering
Love my fan's
By S-Reza writer
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza_
_FCWA_
*TA'AZIYA!*
_Ina miƙa saƙon ta'aziya ga ƴan uwan Marubuciya *Rahama na lale* da masoyanta da ma ƴan uwa marubuta na wannan rashin da mukayi. Allah yaji ƙanta da rahamarsa ya gafarta mata, Allah ya kyautata makwancinta, Allah ya sadata da Annabin rahama, Allah ya amshi baƙuncin ta. Muma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani, Allah yasa muyi kyakkyawan ƙarshe. Ilahiran mamba na kungiyar first class suna ƙara bayar da saƙon addu'ar rahama da jin ƙai cikin ga Rahama na lale, Allah yasa ta hutu. Amin ya Allah rabil alamin._
*Page 9️⃣*
Yaya Bala ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Nasiru da yake ta murmushi yana karasa fassarawa Umma maganar Oga Fita. Siyama dai kanta na ƙasa tana addu'ar Allah yasa Umma ta yarda da wannan aikin. Yaya Bala ya ce "Umma me kika ce? Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ka sanar dasu cewar bazata yi ba, kuma Aure zamu yi mata, sannan karsu ƙara zuwa gidan nan daga yau. Tana faɗa ta miƙe tsaye tabar palon tana jin ta kaicin rashin jin yaran nasara da ba tayi, wallahi yau da sai taci uban mutanen nan mai baƙaƙen kayan nan, wato su ga mayun kuɗi talakawa sai su salwantar da rayuwar ƴarsu akan wasu kuɗi, har suna kallon idonta a matsayin ta na uwar yarinya wai jikinta yayi kala da irin jikin da suke so, ita tun kafin ma ayi nisa taso ta tsayar dasu amma bata san me zata ce ba. Sosai Umma ta shiga damuwa jin yadda abun yake, tunda har ake kashe kuɗi har haka to tabbas wannan sana'ar bata kirki bace, kuma ma dole sai yara mata kuma suma dole ne sai yara ƙanana mai zai hana su nemo manya idan ma dole sai mata ne ai sai a nemo masu hankali ba irin su Siyama ba. Yaya Bala ya dawo da kallon sa izuwa ga su Fita cikin harshen nasara ya ce "Mahaifiyarta bata yarda ba, wai karatu take yi yanzu, saboda haka kuje duk yadda ake ciki ita Siyama ɗin zatayi muku ƙarin bayani. Oga Fita yace "Kafin ranar Alhamis ake so a fara aikin fa, yau kuma kaga muna Litinin ne? Yaya Bala yace babu damuwa. Haka suka fita harda Aida da ta mugun tausayawa Siyama, domin zai yi wahala Umma ta yarda. Suna fita Nasiru ya ce "Kai wallahi wannan karan harda ni za'a shawo kan Umma, irin wannan abun Alkairin haka, ke kuma dan ƙaniyarki tun tuni dama kina da kuɗi shine kika barmu kina gani bama da lafiya ko ki ɗan sayo mana kaji muci, amma dai ke anyi ƴar ɓakin ciki. Yanzu dai bani makullin motar naje na gani, kinga da lafiya nake ai ko ɗani sai na tafi. Yana faɗa ya amshi makullin motar ya fita. Yana fita yaya Bala ya miƙe yayi hanyar ɗakinsa ba tare da yace wa kowa komai ba. Binta kuwa gyara zama tayi ta fara cin abincin ta. Ita kuma Aida taso tayi magana da Siyama ganin ko motsi batayi ba amma har suka bar gidan bata samu damar yin hakan ba.
******
*SIYAMA*
Sosai take addu'ar Allah yasa Umma ta yarda da wannan abun, jin yadda fita yake faɗar maganar sam babu karsashi, sai ambaton za'a samu kudi yake ta yi. Da mamaki taji Umma tayi wannan furricin, hakan yasa ta ɗago tana kallon Umma karo na farko da ta iya kallonta cikin ido tana jin zata iya cewa komai yanzu. Bata ƙara shiga rikici ba sai da taji cewar wai aure za'ayi mata, sosai tayi suman zaune tana aiyana abun da zai faru idan suka ce aure zasu yi mata. Ita fa sabo da irin haka ne fa yasa bata bawa kowani Namiji damar shiga rayuwarta ba bayan wannan ƙazamin, shima tayi haka ne domin tasan babu yadda za'ayi ya iya mata komai koda ta nuna masa bata son sa, domin kuwa shi ɗin dole ne kaman yadda ake faɗa, sosai ta shiga tunani har bata san lokacin da su Fita suka bar gidan ba, haka bata san lokacin da yaya Nasiru ya ƙarbi makullin motar ba, haka bata san lokacin da yaya Bala ma ya shiga ɗaki ba, sai ji tayi ana