Showing 33001 words to 36000 words out of 41935 words
tabbatar da lafiyar Model's ɗin mu. Muddin wani abun ya shiga tsakaninsu da Maza to za'a gane kuma matsala ne, abun tsoron ma shine shigar ciki shine babbar matsalar, shine ma yasa ake kiyayewa. Adawiya da take jin ita da ta riga da ta gama aiki dasu muddin VIP London suka amshi komai nata, ta ce "Zanyi tunani akai" Alesx ya kalleta da mamaki ya ce "Ban gane zaki yi tunani ba kamar wacce aka bata shawara? Yaci gaba da faɗin Wannan dokar aiki ne ba wai shawara ake nema daga gareku ba, duk wacce taga bazata iya ba babu dole ta sanar tun da wuri mu nemo wata. Yayi maganar da ɗan ɓacin rai a muryarsa, kasancewar wannan dama ce da duk wata Model's ke fatan samu shiga a cikin wannan aikin na karshen shekara. Kafin kowa yayi magana wata daga cikin matan kai da gani kasan baturiya ce ƴar ƙasa ta ce "Yes mun yarda zamu iya, idan lokacin yayi sai a sanar mana sai mu kiyaye. Adawiya kuwa babu wani tunani tace bazata iya ba. She kansa Alesx ta bashi mamaki, amma bai ce mata komai ba har ta bar gurin suka bita da kallo. Wata daga cikin Model's ɗin ta ce Afirkan Model's. ta faɗa tana jan tsaki, sauran kuma suka kwashe da dariya...📝
Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza write
[7/16, 3:54 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
_By S-Reza_
_FCWA_
*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*Page 1️⃣0️⃣*
Duk da Alesx yaji zafin rashin shigar Adawiya cikin tawagar aikin nasu amma haka ya haƙura suka fara neman cikon ta huɗun ƴar Afrika wacce zata wakilceta. Dama shi yarinyar na basa mamaki tun ba yanzu ba, tana yin wasu abubuwa kamar bata tsoro, amma a ransa ya yanke shawarar wannan karan zai koya mata hankali, sai tayi nadamar ɓata musu lokaci da tayi. Bayan ta fita ne ya sallami sauran ƴan matan shima ya tashi. Daga nan VIP ta nufa ranta fess tana jin ai ita dama ce mai kyau tazo mata kuma tabbas zata dama harda sikari tasha kayanta. Lokacin da taje get ɗin shiga VIP kuwa duk da cewar an ganta Model domin kallo ɗaya take buƙata duba da irin shigarta zaka gane ita ɗin Model ce. Amma hakan bai sa an barta ta shiga ba sai da ta nuna shaidar da aka bata lokacin da suka zo gurin nata. Lokacin da ta ƙarasa ciki sai aka tsayar da escort ɗinta (Mai tsaron ta) aka nuna musu hanya ita da manager dinta suka shiga ciki, shi kuma ya tsaya waje.
******
*SIYAMA*
Yau kwana biyu da zuwan su Oga Fita gidan su, kuma har yanzu babu wani cigaba daga gurin Umma na amincewarta, hakan yasa tun jiya Siyama ta je gidan Kawu Inuwa da kuma Baba Hassan mahaifin Binta. Sosai tai musu ruwan ihisani da yasa kowa a cikin su sai da ya rikice. Shi Kawu Inuwa farko da taje kamar zai dake ta, domin haushi ta basa, amma lokacin da ta faɗa masa irin samun da ake yi, sai ya fara sakkowa. Bai sakƙo daga kan bishiyar kwakwan bama sai da yaga ta sauke masa rafar yan dubu-dubu guda biyar wato dubu ɗari biyar lokaci ɗaya ya duro daka saman, ya rikice har bai san lokacin da yake ce mata "To ai dama wannan aikin da moda shi ya dace da ke, yarinya fara kyakkyawar gaske, ai itama Umman taku wasa take, to wa zai ƙi nasa da abun arziki. Bari na shigar da su sai mu tafi gidan yanzu, to ai wannan sana'a ce ta rufin asiri, shekara ta nawa ban taɓa riƙe irin wannan kuɗin ba, amma ke daga rana ɗaya kawai kin riƙe, dama ana cewa wani lokaci idan kaga kana addu'a akan kayi arziki to kuma baka yi ba, to malamai sun ce tana komawa kan ƴaƴa ne, to babu shakka nawa kanki ya faɗa wallahi. Sosai ya shiga zaro zance ita dai Siyama tana sunkuye a ƙasa tana mamakin mai ya hana ta tun farko bata fara aiki da kuɗin ba, ai da tuni ba wannan maganar ake ba. Daga nan gidan Baba Hassan ɗan biyun mahaifinsu taje. Lokacin da ta isa gidan kasancewar shi yana da ɗan hali domin harda mota garesa dukda cewar tsohuwa ce amma dai yana da ita. Shima ganin ta a cikin wannan Motar sai da ya shiga boɗe baki. Bayan ta gama zaiyana masa komai ne ya shiga girgiza kai alamar tunani. Ganin kamar bai yarda bane yasa kafin yace komai ta sanar da shi irin alkarin dake cikin aikin nata, ta fara faɗa masa irin kuɗaɗen da zata samu, tana gamawa shima ta zaro guda shida ta ajiye masa, ta sanar da shi abun da take so yayi mata. Baba Hassan ya kalleta ya kalli kuɗin ya ce "Yanzu iya wannan abun da kika yi ne har kika samu wannan kuɗaɗen?" Siyama ta ce "Eh ai Baba wannan ma iya kyautar da na samu a gurin ne ba ma wanda aka bani na gasar bane". Jin haka sai yace "to shi kenan zuwa gobe zan je na sameta". Sai da ta shiga suka gaisa da Mommy itama ta bata rafa ɗaya kafin ta bar gidan. Tana fita Mommy ta dau waya ta kira Binta. Taso shiga gidan su Ibrahim lokacin da tazo wucewa, domin so take ta jawa tsohuwar sa kunne ganin shi baya jin magana. Amma ta bari har sai ta samu Umma ta yarda. Shi kuwa Nasiru babu wata-wata kuɗaɗe ya amsa daga gurin ta ya fara hutawa abun sa, har Allah-Allah yake ya warke ya ƙwace wannan motar ta zama tasa.
Zaune suke a sashen Umma Kawu Inuwa da Baba Hassan sai wani abokin Kawu Inuwa da ya gayyato acewarsa wai Malami ne, zaiwa Umma bayani yadda zata fahimta. Sai yaya Bala da shima har yanzu yaƙi amincewa da wannan aikin a ransa. Bayan an gama gaisawa ne Kawu Inuwa ya fara da faɗin "Uwar yara gurinki muka zo akan yarinyar mu, izuwa yanzu dai kowa yaji abubuwan da suka faru da ita, to mun zauna munyi shawari nida babanta gashi. Ya faɗa yana nuna Baba Hassan. Yaci gaba da faɗin "To shine yasa nace a matsayin ki ta uwa shine muka ga ya dace musanar dake karmuyi gaban kanmu dukda cewar mun isa da yarinya, koba haka bane Malam Hassan? Ya karasa yana tambayar Baba Hassan da gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi ganin yanayin Umma da Yaya Bala. Baba Hassan ya ce "To dama ba komai bane sai kawai abar yarinyar nan tayi sana'ar ta, tunda dai ba zai hanata karatu ba, kuma wannan sana'ar sana'a ce ba mai muni ba. Umma ta ɗaga kai ta kallesa sai ta kawar da kai ganin sun haɗa ido. Ai kuwa shi kaɗai ya duburburce ya kasa ci gaba da jawabin. Sai Kawu Inuwa ya ɗora da "Yanzu muna so a matsayin ki ta uwa maba da mama, mai son cigaban ƴaƴanta kiyi hakuri kibi Siyama da addu'a akan aikin ta, kinga kema sai ku huta, nasan har gida sai ta sauya muku, dama gata yarinya ce mai kyauta da sanin yakamata, sam abun hannunta baya rufe mata ido. Umma ta ce "Yanzu tsakanin ku da Allah idan Siyama ƴarku ce ta cikinku zaku yarda tayi wannan sana'ar ta ƴan isa ta tallan jiki, ai duk kuna da yara mai yasa ba zaku tura su suma suje su samo abun arzikin ba kamar yadda kuka ce, to ni dai ban yarda Siyama ta ƙara aiki da wadannan mutanen ba, wanda tayi a baya ma kuskure ne kuma yarinta ne, amma in sha Allah ba zata ƙara ba. Ku kuma wallahi kun bani mamaki akan abun duniya zaku salwantar min da rayuwar yarinya har kuna iya kallon idona kuce wai na bar ta tayi talan tsaraici, A'uzubillahi-mina-shaiɗanunrajin, tuf da wannan tunanin naku. Kawu Inuwa ya ce "Yanzu mune shai ɗanunn kenan Aisha? Kuma mune kike wa gorin yarinya, shi kenan babu komai ba laifinki bane, ai mu ne marasa mutuncin da muka tako har cikin gidan ki, dole ki zagemu san ranki. Umma ta ce "Ni ban zageku ba, kuma babu yadda za'ayi nayi muku gurin aihuwa domin duk kun haifa. kuma Siyama ƴar kuce ban isa na shiga tsakaninku ba. Kawai dai abun da kuke nufi ne ba zan taɓa yarda ba."To me kike nufi da a'uziya da kika jawo mana yanzu na neman tsari da sheɗanu, ko ake ce miki bamu je islamiyya bane, to bari kiji babu wata addu'a da zaki yi wacce ban san ina ta dosa ba, dan haka karki ƙara mana addu'ar shaɗanu tun girma da arziki domin mu ba su bane, ya daga abun kirki a fara danganaka da jinsin tsinannu. Sosai wannan addu'ar ta ɓatawa Kawu Inuwa rai domin ji yake kamar shi ta kira da shaɗanin. Umma ta ce "Kayi hakuri ni ba nufi na kenan ba. Ta faɗa tana jin nauyin sa da take ji yana raguwa. Sosai take kunyarsu su duka su biyun amma wannan abun yasa take jin nauyin nasu na raguwa a ranta, dama shi Kawu Inuwa ya iya daukar abu da zafi kamar dai ita, shi dai Baba Hassan bai ma cika tsoma baki a lamarin gidan ba sai dole. Kawu Inuwa ya kalli Yaya Bala da yayi shiru yana ta tunani ya ce "Yanzu Bala a gabanka ina matsayin ƙanin ubanka kana ji uwarka na kirana da shaɗani amma kayi shiru ko? Kai Bala kana so ka gama da duniya lafiya kuwa. Sosai yaya Bala ya danne abun dake taso masa ya shiga basa hakuri har dai akayi sa'a ya tsaya da mitar kamar mace. Mutumin da suka zo da shi ne ya fara magana cikin natsuwa da dole kai mai sauraron sa ka tsaya ka ji abun da yake cewa domin ya iya magana. Ya ce "Duk na fahimce ku, kuma na gane inda zancen naku ya dosa. Yanzu ina so ku ɗan bani dama nace wani abu? Duk suka basa dama ya buɗe baki zai yi magana suka ji anyi sallama. Amsawa sukayi sai ga Hajja ta shigo ɗakin cikin sauri idanunta duk sun yi jaa, sai kuka take. Gata dai tsohuwa amma jikinta bai tsofe sosai ba, amma kallo ɗaya zakai mata ka tabbatar da tana cikin wahala. Ganin mutane da yawa a palon yasa ta cire taƙalmi ta shiga gaisuwa da sauri-sauri. Kawu Inuwa ne ya fara faɗin "Baiwar Allah lafiya kuwa me kike buƙata gurin wa kika zo da zaki shigowa mutane cikin gida haka kamar sauƙar aradu babu neman izini?. Kallo ɗaya Umma tayi mata ta gane ta, ta ce "Sirikarku ce kakar yaron da yake zuwa gurin ita ƴar taku da kuka zo karewa" Da ƙarfi ya ce "Ita dai wannan ɗin, to wallahi wuce nan, ina dangin wannan matar ina Siyama da take shirin zama tauraruwa sha kallo. Hajja ta ce "Hajiya Aisha Ibrahim ne ba shi da lafiya kamar zai mutu sai sunan Siyama yake kira, dan Allah ki taimakeni Siyama tazo muje ko ganinta yayi dan Allah a taimaka.
Da ƙarfi Umma take furta innalillahi tana faɗin "Mutuwa fa kike cewa Hajja? To meye ya sameshi haka? Umma tayi tambayar tana ƙarasowa gurin Hajja. Hajja tayi ƙarfin halin faɗin "Wallahi shida ita Siyama ɗin ce, wai inaga yanzu ta daina sonsa ne, shine ya shiga wani hali, yau kusan kwana biyar kenan mun kasa gane masa, dan Allah ku taimaka ko ganinsa tazo tayi zai samu sauki domin sunanta kawai yake kira. Umma ta kalli Yaya Bala da bai iya cewa komai ba ta ce "Kaji zancen da Nasiru ya gama faɗa jiya ko, dama nasan wannan yarinyar wallahi ba dan Allah take son wannan yaron ba, kawai tana so ta yaudaresa ne, kuma wallhi bata isa ba, muddin nine na haife ta to wallhi sai ta auri wannan yaron ai ita ta kawo mana shi akan shi take so, to dole ne sai ta aure sa. tace "Je ka kira min ita. Dama tana jin duk abun dake faruwa domin tun shigowar su Kawu Inuwa ta laɓe tana sauraron su. Umma ta ce "To ga kakar yaro ga ni uwar yarinya ga kuma iyayenta maza, sabo da haka a tsayar da magana yanzu, ni na yanke shawarar aurar da Siyama idan yaso ta ƙarasa karatun nata a gidan shi yaron, domin na gaji da wannan masifar da take ƙoƙarin tun karomu. Idan yaso ko bayan auran ne mijin nata ya barta sai tayi duk abun da zata yi, amma tana gabana dai ba zan yarda ba, Umma ta ce "Kuyi shaida ni Aisha na bawa Ibrahim auran Siyama ko bana raye. Da sauri Kawu Inuwa ya miƙe tsaye shima cikin masifa ya ce "Wannan wani irin rashin hankali ne haka Aisha? Haka ake aurar da yarinya dama, ko kin taɓa ganin inda mace ta bada aure ne? Cikin masifa da haushin da Siyama ta gama bata domin ta lura kamar kuɗi ta basu domin su zo su shawo kanta ta ce "To yaya zanyi da Siyama, so take sai ta kashe ni kuma in sha Allah bazata iya ba har sai lokaci na yayi, yaro kuma ita ce ta kawo shi ba dole za'ayi mata ba, kuma gata nan ku tambaye ta, har gida ta kawo shi a matsayin shi ne zabin ta. Lokaci ɗaya kowa ya kalli Siyama da ta sunkuyar da kai. Ita dai Hajja sai kuka take burinta kawai Siyama tazo suje tayiwa Ibrahim magana ko zai tashi ya samu ko abinci yaci. Cikin fushi Kawu Inuwa ya ce "Siyama wai da gaske ne kece kika kawo yaron matsayin wanda zaki aura? Kowa ya zuba mata ido, domin jin abun da zata ce. sai da tayi kamar baza ce komai ba sai cen ta ce "A'a ni ban turo kowa ba, kuma ai dama ba soyayyar gaskiya muke yi da shi ba ta wasa ce domin ai shima ya sa..."Bata ƙarasa ba taji sauƙar mari a kumatunta wanda yasa ta tsayar da maganar. Kawu Inuwa yace "Wallahi idan ka ƙara taɓata sai na rama mata babu ruwana da ciwon hannunka, yaya yarinya ba ƙarama ba da wayonta kuna so kuyi mata ƙarya a gaban ta. "Umma cike da mamaki kamar zata yi kuka ta ce "Siyama karya nayi miki kenan ko? Siyama ni kike ƙaryatawa? Siyama dai sai kuka take tana jin tsanar Yaya Bala a ranta na marin da yayi mata domin kuwa ya shige ta da kyau. Yaya Bala yaci gaba da faɗin "Ƙarya kike dan ubanki wallahi kinyi ƙadan Siyama yau she aka haife ki, kizo da yaro kice shi kike so yanzu sabo da wani dalilinki kece karya akai miki, to bari kiji wallahi Ibrahim shine mijin ki sai dai idan gidan nan zaki bari kije ki nemi wasu iyayen amma dai idai mune iyayenki Ibrahim zaki aura, wawiya sokuwa mai baƙin hali kawai. Ita dai Hajja tana tunanin waye zai yarda ya zama sirikar wannan mara kunyar da bata bar iyayenta bama bare na wasu, ita dai badan halin da jikanta ke cikiba wallhi ba zata yarda Ibrahim ya auri wannan mai ido a tsakiyar kai ɗin ba. Babu kunya ko tsoro Siyama ta ce "Ni dai wallahi ba aure zanyi yanzu ba, kuma babu wani zancen soyayya tsakanina da shi Ibrahim ɗin, kuma ko aure zanyi na rasa wa zan aura sai wannan dolo wawa ƙazami ɗin, wallahi ba wanda zai aura min shi, kuma ni ba aure zanyi ba yanzu. Tana faɗa ta miƙe zata fita amma Umma tayi saurin jawota ta sauke mata mari tana faɗin "Wallahi baki isa ba Siyama kinyi kaɗan ki raina ni har haka, nice nan na haifeki ba ke kika haifeni ba, kuma ban haifi wata ƴar da zan faɗa tana faɗa ba, kinyi ƙadan idan kuma kina ganin karfin ki ya kai to Siyama tashi ki dake ni, nace tashi Siyama. Umma na faɗa tana kuka tana kuma naushin Siyama ta ko ta ita ga wani irin kunya da ta tsinci kanta a ciki, dukanta take yi tana faɗin ta rama. Siyama na kuka tana kare kanta kuma taƙi guduwa har Nasiru da su Fati da Binta dake cikin ɗaki suka fito. Da ƙarfi su Kawu Inuwa suka shiga tsakaninsu domin Yaya Bala ba zai iya ba saboda ciwon hannunsa. Su kansu su Kawu Inuwa da Baba Hassan jikinsu ya mutu ganin abun da ke faruwa. Ganin haka Umma ta ce "Ki fito ki bisu kije chan gidan su kiyi abun da kika ga dama amma ba a nan gidan ba. Siyama da bakinta yaƙi mutuwa tace "Babu inda zance kuma ni ba aure zanyi ba. Wani irin tsawa da zagi Yaya Bala ya kutuntuma mata yana jin yau da babu ciwo a jikinsa wallahi sai ya kusa karya wannan yarinyar. Shi kansa Nasiru abun ya basa mamaki gashi duk hannunsu na ciwo. Kawu Inuwa da ya shiga tunanin to ko dai ya lallaɓa Siyama ɗin ta auri Ibrahim ɗin ne, idan yaso sai shi Ibrahim ɗin ya barta ta yi sana'ar tata. Nasiru ne ya kama hannunta suka shige ɗakinta tana kuka kamar ranta zai fita. Umma ta ce "Ki fito ki bar min gida ai ba gidan ubanki bane, kije gurin masu zuga ki ɗin ko kuma ki tafi gurin su iyayen da kika sake su arnan da kika nunawa duniya cewar sun fimu daraja a gurin ki" Yaya Bala dai sai bata hakuri yake, dama Umma akwai faɗa idan ranta ya ɓaci bata jin rarrashi. Kawu Inuwa ya bita ɗakin bai lura da irin kukan da take yi ba ya ce "Siyama mai zai hana ki yarda da shi Ibrahim ɗin tunda ba auran za'ayi yanzu ba, daga baya sai ki saye shi da kuɗi shi da