Showing 15001 words to 18000 words out of 41935 words

Chapter 6 - TSINUWAR UWA Book Complete Document by S-Reza .txt

S Reza   

29 Nov 2024

2666

ƙwarin gwuiwa yazo mata, hakan yasa ta sake daga takurewar da tayi ta kallesa cikin ido ta ce "Eh nice wannan da kake kallo yanzu, kuma in sha Allah na fara kenan har zuwa na ciga dukkan burikana na rayuwa, ina son zama Model bama a iya nan ƙasa Nigeria ba har kasashen Turai in sha Allah. Tana faɗa ta kama hanyar gida tana jin mai ma yasa da take neman kada kanta a gaban wannan talakan. Sai dai ko taku uku mai kyau bata yi ba, Ibrahim ya dawo da ita baya, ya kalleta cikin ido, babu wannan tsoron nata yau a cikin idanunsa da ta saba gani kullum, zata iya rantsewa ma kamar ba fuskarsa ba ce."Mai kike nufi da wannan maganar taki? kina nufin dama ba sona kike ba kawai kina amfani da nine ko yaya? Siyama ta ce "Na godewa Allah da yasa har kayi saurin ganowa da kanka. Sai da ta dawo kusa da shi kafin ta fara faɗin... "Dubeka dubi zubin tsarin halintarka sannan ka kalleni, kai ko giyar wake kake sha har zaka yi tunanin ni Siyama zan iya yin soyayya ta gaskiya da gaskiya da kai, to wallahi bari kaji na faɗa maka, tun da nake tare da kai Ibrahim ban taɓa sonka ba, ban taɓa jin zan iya son ka ba, ina yin amfani da kai ne domin yaya na da kuma mahaifiyata, sannan daga yau ina so na sanar maka da cewar babu ni babu kai, karka ƙara nuna kasanni, kaje kayi lissafin abun da ka kashe min tun daga haɗuwarmu ni kuma zan ninninka maka su, amma dan Allah daga yau karka ƙara nuna ka sanni please, sama tayiwa yaro nisa. Tana faɗa tai masa wani irin kallon sama da ƙasa kafin ta saki wani wawan tsaki ta shiga cikin gidan ta barsa a gurin tsaye yana kallonta, a lamar abun yazo masa a bazata.


******
*IBRAHIM*
Duk yadda ya kai da zafin zuciya da zafin rai amma lokaci ɗaya yaji duk sun zube, take yaji jikinsa kamar an zare masa dukkanin lakar sa, babu abun da ya fi taɓa masa rai kamar da tace tun da take bata taɓa jin sonsa ba, kuma bata taɓa masa kallon wanda zata iya so ba. Tabbas jin wannan kalmar daga bakin wanda ka gama yarda dashi ka gama basa amanarka a kwai ciwo. Shi kansa ya sha yiwa kansa tambayar dalilin da zai sa Siyama ta ce tana sonsa, amma idan ya duba yadda take kula sa, kuma take jin maganar sa take basa mutuncinsa sai ya bari akan kawai haduwar jinine, amma ashe ba haka bane. Shiru yayi yana tuna abun da tace wai dama tayi amfani da shine domin cika burinta na zama Model, kuma gashi ta zama, tayi amfani da shi ne domin Yayanta da Mahaifiyar ta. A fili yace "Menene Model! Shiru yayi ya kai minti goma a gurin kafin ya bar unguwar zuciyarsa nata saka masa abubuwa.


Har sai da ya wuce ƙofar gidan su kafin wani yaro ya ankarar da shi, haka ya dawo da baya ya shiga zauran gidan su kafin ya sunkuyar da kansa yana tunani. Bai san adadin mintinan da ya kwashe a gurin ba sai ji yayi ana kiran sunansa. Da mamaki yake kallon zauren ganin duhu alamar dai dare ne yayi sosai, fuskarsa yaji danshin lema, koda ya kai hannu ya shafi sai yaji hawaye ne. Cikin mamaki Hajja ta ke faɗin "Kai Ibrahim meneke gani haka, wai dama kana nan ne ko dai yanzu kazo, tun ɗazu muna ta jiran dawowarka ashe ma kana gidan, me ke faru da kaine?" Hajja kenan kaka ce a gurin Ibrahim wacce ta haifi Babansa yanzu haka tare suke zaune shida ƙanwarsa da ita Hajja ɗin kasancewar iyayensa duk sun rasu, yanzu shi da ƙanwarsa Nana da Hajja suke rayuwa a gidan.


Ya ce "Hajja Siyama ce" Cike da mamaki ta ce "Me ya sami Siyamar? ina ance matar Yayan nasu ce ta rasu, ko itama wani abu ya sameta ne? Lokaci ɗaya Ibrahim ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Hajja kwaɗa wani irin salati haɗi da kiran sunan Nana wacce har barci ya fara ɗaukarta. Da sauri ta fito tana tambayar lafiya, haka suka kama shi har cikin ɗakinsa suka kwantar da shi kafin suka fara tambayarsa abun da ya sami Siyama ɗin, domin kuwa babu wanda bai san shi da Siyama ba, daga gidan su Siyama ɗin har gidan su da kuma mutanen unguwa. Ita kanta Hajja farko bata yarda da cewar Siyama tana son Ibrahim ba, domin babu yadda bata yi ba ganin ta raba su, amma ganin yadda ya dage, itama kuma Siyamar har gida take zuwa ta gaidata yasa ta hakura. Ita kuwa Nana dama basa shiri da Siyama kasancewar tana da girman kai ga raini, ko a hanya suka haɗu sai dai ta wuce ta wuce. Ganin yadda suka shiga damuwa ne yasa Ibrahim daurawa ya miƙe yace Nana ta dafa masa ruwan zafi zai yi wanka. Kasancewar akwai wutan nefa yasa ta miƙe domin jona masa. Babu yadda Hajja bata yi da shi ba amma bai ce mata komai ba hakan yasa ta hakura tana ce masa karya sa damuwar mace a kansa fa, ya rufa musu asiri dan Allah shi kaɗai ga resu. Hajja na fita ya ɗauko wayarsa ya danna kiran number Siyama, amma ya jita a kashe ya ƙara kira nan ma a kashe, take ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke babbar wayar abokinsa da ya nuna masa wannan video ɗin. Kunna wayar yayi yaga ta shiga ki, ya cire kin kasancewar yasan ki ɗin wayar, Yana budewa vedio ɗin ya shiga aki kasancewar dama a kai yake, sosai yake ta bin ta da kallo yana so ya gano tayaya haka ta faru, mai yasa bai taɓa lura da cewar Siyama tayi amfani da shi ne domin cika muradanta ba. Yana cikin haka Nana ta shigo ta sheda masa cewar ta shigar masa da ruwan.


******
*ADAWIYA*
Kallon Badawiya tayi ta ce "Ni matsala ta dake kenan wallahi shegen jiji da kai, yanzu dan Allah meye laifin kamfanin Baby and me da zaki ce bazayi aiki da su ba, ai ko domin mu wulakanta wannan yarinyar ai kya karɓa. Badawiya ta ce "Ni kaina sai yanzu nake da na sani, domin na bibiyi aikin naga a kwai tsoka, kuma ba wai aikin Contract za'ayi ba, zaka iya haɗa aikin su da na wani ba kamar na Magazing bane da babu dama kayi aiki da wasu har sai lokacin da ka basu ya cika. Adawiya ta ce "You see ni wallahi lokacin da naji Fita na faɗin wai ke kince bazakiyi aiki da ƙaramin kamfani ba abun ya bani manaki domin Baby and me suna biya sosai kuma suna da costoma a ko'ina. "To yanzu yaya kike so ayi domin gaskiya ina son wannan aiki? Badawiya ta faɗa tana kallon Adawiya da ta cika tayi famm. Ta ce "Ai kin gama zubar da damar ki wallahi, amma bari zan samu Fita idan yaso sai a cire wannan Nusee ɗin dan nasan babu yadda za'ayi da zai sa Shara ta fita. Sai a lokacin Badawiya ta ce "To ko dai musan yadda za'ayi a cire ita Munafukar Siyama ɗin sai kawai a saka ni. Adawiya ta ce "Ta yaya? Tayi dariya ta ce "Olusha" Adawiya ta riƙe baki tana dube-dube ko wani ya jisu. Take suka tafa suna ganin ashe ma ga hanya mai kyau da zasu bi su rusa wannan banzar.


******
*SIYAMA*
Duk da irin faɗuwar da gabanta keyi bai hana taji tsoron kar Ibrahim ya shaƙota ta baya ya fara dalla mata mari ba, sosai take tafiya ta ankare da shi, har sai da taga ta shiga cikin palon gidan nasu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana jin in sha Allah ta rabu da ƙaya. A fili ta furta "Na tsallake ƙofa ta farko a cikin ƙofofin matsalolin da zan fuskanta. Tana ɗaga kai taci karo da matar kawu Inuwa wato mahaifiya Binta wacce suke kira da Momy. Kallo ɗaya tai mata ta kawar da kai gefe tana ƙoƙarin wucewa domin kuwa basa shiri da matar. Ganin tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinsu ne yasa ta faɗin "Ke Siyama dan ubanki bakya ganina ne da har zaki kama hanya ki wuce ni ko gaisuwa babu? To ke nake jira dama tun ɗazu nake zaune anan an kira number ki bata tafiya, idan har kina son kanki da arziki ki juya mu tafi gidana idan kuwa ba haka ba wallahi sai Ummar ku ta kusan hallaka ki, gata cen babu yadda ba'ayi da ita ba amma taƙi hakura, shi kan sa Bala da baida lafiya bata kyale sa ba, to sabo da haka ki juya yanzu mu tafi. Momy ta faɗa tana ƙarasowa gurin da Siyama take. Siyama da gabanta ya fara dukan goma sha tara-tara jin cewar yanzu kowa na gidan su yaji kuma ya gani kenan. Duk da cewa tana tsoron Umma sosai amma bata jin zata bar gidan nan ba tare da ta nemi amincewar ta akan fara aikin Model ba, ko da kuwa tsriranta zata yi ta cinye to wallahi sai ta tsaya ta ƙwaci yancin kanta. Momy ta ce "Wuce mutafi" Siyama ta ce "Babu inda zan je, yau ko soyani Umma zata yi sai dai tayi, aikin gama ne ya riga ya gama, kawai ki barni" Cikin tsawa da masifa Momy ta ce "Dan ubanki kin san halin da kika jefa ahalinki kuwa? Ina so na tafi dake domin zuciyarta tayi sanyi karta aikata miki abun da zai dameki keda ita amma kina cewa babu inda zaki, Siyama mai kike so ki zama ne, kije kina baiyana kanki a duniya akan kuɗi, to wallahi ina baki shawara akan karki yarda ki shiga cikin gidan nan har ki haɗu da Umma na faɗa miki. Momy na faɗa ta koma ciki ta bar Siyama tsaye idanunta na ta kallon mashiga sashen Umma ɗin...📝




Yanzu aka fara shiga labari, kudai kuci gaba da nuna goyon baya masoya.




Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza writer ✍️
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*


_By S-Reza_


_FCWS_


*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a





*PAGE 6️⃣*
A hankali ta fara nufar ɗakinsu tana tafiya kamar mai ciwon ƙafa, tana tura ƙofar ɗakin nasu sukayi ido biyu da Binta da take ta chatting abun ta, domin ita abun ma wani abun alfahari ya zama mata, sai posting hotonta da suka taɓa ɗauka da Siyama ɗin take yi tana faɗin ai ita ɗin ƙanwar Siyam Olusha ce. Tana ganin Siyama ta miƙe ta nufo gurinta tana kallonta itama sai binta da kallo take. Kafin tayi magana ta ce "Ina Fati?" Binta ta ce "Tana sashen Umma tun ɗazu" Tana jin haka ta sauke ajiyar zuciya ta zauna a gefen gadon ta sauƙe jakar dake jikinta sannan ta kwanta a kan gadon tana mai kallon saman rufin ɗakin. Ita dai Binta sai binta da kallo take amma ta kasa ce mata komai, ganin shirun yayi yawa yasa Binta faɗin "Anty Siyama ko zamu ɗanyi salfi guda biyu ne? Ta faɗa domin tambayar da ake mata na cewar tayi hoto da ita yanzu idan har da gaske ne ita ɗin ƙanwarta ce. Kafin Siyama ta bata amsa sai ji sukai an turo ƙofar an shigo da sauri.
Da sauri Siyama ta miƙe zaune tana kallon Fati da take ƙoƙarin saka saƙata sama da ƙasa a ƙofar ɗakin. Siyama dai sai binta da kallo take. Itama dai Binta a tsorace take sosai ganin yanayin Fati ɗin. Fati cikin rawar murya ta ce "Anty Siyama Umma ce wallahi tace sai ta yanka ki, wai sai kin bar mata gida, ga cen Momy da Mama suna bata hakuri amma sai kuka take yi, shima Yaya Bala bata gyalesa ba, duk da ciwon hannunsa amma haka take ta dukan sa, shima Nasiru sai kulle shi akayi a ɗaki. Siyama ta ce "Buɗe ƙofar" Fati ta kalleta ceke da madarar mamaki ta ce "Baki da hankali ne, bakiji me nace ba?" Cikin zafin hannu Siyama ta miƙe ta shiga ƙoƙarin cire saƙatan da Fati ta sa, amma Fati ɗin tana hanata domin ita tasan abun da ta gani daga Umma. Kasancewar ƙarfin su ba ɗaya ba yasa Siyama ta tureta gefe ta cire saƙatan. Daidai lokacin kuwa Umma ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Turus suka yi kowa na kallon kowa, lokaci ɗaya Umma ta tsaya da kukan da take yi tana ƙarewa Siyama kallo, ganin irin kayan dake jikinta. Itama Siyama kallo Umma ɗin take yi, tana ganin yadda ta rame lokaci ɗaya a cikin kwana ɗaya kawai, ga wannan kwarjinin da take mata yauma dai an ninninka shi, sosai take tsoron Umma domin mace ce mai zafin gaske, bama ita ba, dukkanin su suna taron ta sosai. Lokaci ɗaya Umma ta ɗauke fuskar Siyama da mari sannan ta kamo ta ta turo ta baya ta fara faɗin..."Siyama mai muka rage ki da shi? So kike Allah yayi fushi dani yace ban kula da tarbiyyar Kuba, duk irin ƙoƙarin da nake yi a kan ku amma Siyama sai kin wulaƙanta ni, Siyama ki fito bainar duniya tsirara Siyama, kina ƴar musulmai akan kuɗi, ko mun faɗa miki bamu gode a yadda Allah ya yimu bane? Sosai Umma ke kuka tana dukan Siyama wacce itama kukan take yi. Itama Fati kuka take yi kaman ranta zai fita. Umma ta ce "Faɗa min waye ya baki wannan shawarar kuma mai ya kaiki aikata wannan abun? Ganin taƙi yin magana yasa Umma ɗin ƙara mata mari ta na faɗin "Na rantse da Allah idan baki min bayani ba sai na yankaki kowa ya huta, ina miki magana kina kallona tsabar raini. Ana cikin Haka Kawu Inuwa ya shigo dalilin kiransa da Nasiru yayi. Ai kuwa yana zuwa ya hau Umma da faɗa kamar zai mareta, sosai yayi mata kace-kace ganin yadda duk ta bi ta ɗaga hankalin gidan. Sosai Siyama ke kuka Kawu Inuwa nata rarrashin ta. Haka dai Umma ta koma sashen ta Momy nata bata hakuri amma ina idan Umma ta tuno da yadda taga Siyama sai hankalinta ya ƙara tashi. Sosai Kawu Inuwa ya shiga lamarin har dai komai yayi sauki har akayi sadaƙar bakwai, har lokacin kuwa Umma bata ƙara bi ta kan Siyama ba, itama Siyama ɗin bata ko ƙara fita waje ba, haka zalika tun lokacin da ta kashe wayar ta a gidan Aida bata ƙara ko bi ta kan wayar ba, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kamata tun lokacin da Umma ta jibgeta. Sosai Fati ke ta ɗawainiya da ita, shima Nasiru ya yi fushin ya haƙura yanzu har ɗakinta yake shigowa suyi hira, amma har yanzu basu magana akan abun da ya shafi matsalar ba, shi kansa yanzu Yaya Bala abun ya haɗar masa goma, ga rashin matarsa ga ciwon jikinsa ga wannan abun da Siyama tayi, yasa kowa sai kiransa yake yana tambayar sa, ga kuma fushin da Umma take yi da shi yanzu, ko yaje gaidata bata amsa wa babu yadda bai yi da ita ba amma taƙi sakar masa fuska.


Washegarin ranar da akayi sadaƙar bakwai ne Fati da Siyama da Binta na cikin daki suna hira sama-sama sai ga Nasiru ya shigo ya kalli Siyama ya ce "Ina wayarki?" Siyama da har yanzu jikin nata baiyi daidai ba tace "Tana cikin jaka" Nasiru ya ce "Ibrahim ne ke ta kiranki yanzu haka yana waje, ya dade ki tashi kije. Yana faɗa ya juya bai ko bi ta kan maganar da take na cewar yace masa bata da lafiya ba. Fati ta ce "Ki tashi kije kice masa bakya da lafiya ne. Siyama ta kalli Binta ta ce "Binta fita kice masa bana da lafiya" Har Binta ta tashi Fati ta ce "A'a anty Siyama dan Allah kije da kanki please. Siyama ta miƙe zaune tana jin ai wallahi ba zata taɓa ƴarda ta ƙara haduwa da shi ba, ai tunda Allah ya taimake ta ya rabata da shi cikin ruwan sanyi to wallahi ta gode. Siyama ta ce "Ke wallahi ba zan iya fita a haka ba" Fati da ta cika da mamaki ta ce "Ibrahim ɗinki ne fa IB dai naki makaniki? Siyama ta ja tsaki ta koma kwanciyarta. Fati da ta buɗe baki da mamaki ta rufe ta ce "Ai wallahi anty Siyama bana tare da ke wajen yaudarar wannan bawan Allah ɗin, ai wallahi zunubin ki sai ya shafi mu muda muke kusa da ke, ki hana mutun kula kowa tsawon shekaru amma yanzu lokaci ɗaya kice zaki guje masa, dan Allah Karki fara. Siyama ta ce "To bari kiji wallahi ban taɓa son Ibrahim ba ko na minti rabi, dama nayi haka ne domin kar kowa ya gano shiri na, yanzu kuma na gama, abu ɗaya zan iya masa yanzu shine zan basa kuɗi masu yawa da zai ja jari idan kuma yaƙi ya fita a sabgata to Allah zan sa a ɓatar da shi. Yanzu haka saboda bani da lafiya ne yasa kika ga nayi shiru amma zuwa na warke komai zai cigaba, itama kanta Umma idan taji kuɗi duk wannan abun mantawa da shi zata yi, yanzu haka ina da Contract ɗin aikin Model da zan fara in sha Allah. Lokaci ɗaya Fati da Binta suka haɗa baki gurin cewa "Model" Siyama ta ja tsaki ta juya musu baya. Suka kalli juna suna mamakin Siyama.


*IBRAHIM*
Haka ya kwanta a wannan daren yayi barci rabi da rabi, ko da ya tashi da safe number ta ya fara kira amma dai har lokacin a ka she. Kamar da wasa ya tashi da ciwon kai mai zafi har baya ko iya magana sosai. Hajja dai gaba ɗaya ta rikice gashi ya ƙi sanar da su abun da ya faru. Haka tasa Nana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login