Showing 6001 words to 9000 words out of 41935 words

Chapter 3 - TSINUWAR UWA Book Complete Document by S-Reza .txt

S Reza   

29 Nov 2024

2677

su suka gane ta. Dukda kuwa sunji an kirata da wani sunan daban ba wannan ba. Cikin wani irin tashin hankali yaya Bala ke kallon gurin da Siyama ke karkaɗa mazaune, sannan ga duk wani sirrin da Allah yayi mata na ƴa mace nan sun gama fallasa kansu a waje. Bai tashi rudewa ba sai da yaji yadda Siyama ke zubo turanci tana magana tana gaisuwa ga shuwagabannin gasar da manyan mutanen da suka halarta da gwamnonin dake gurin. Shi kansa Nasiru abun neman hana shi nutsuwa yake yi, anty Zainab kuwa ta gama cika da mamaki, badan muryarta da taji da bazata yarda cewar wannan Siyama ce ba. Siyama Alhasan ce ta koma Siyam Olosha! Ta yaya? Anya ma kuwa ita ce, ko dai mai kama da ita ne? To waye kuma Olosha? Haka dai take ta zancen zuci, jin tana neman zaucewa da mamaki yasa ta ce


"Yaya Bala wannan ba Siyamar mu ba ce? inaga mai kama da ita ce dai, domin Siyamar mu wallahi ba zata iya haka ba, kuma ai mun barota a gida ita, dan Allah kira mana Umma ko ita Siyama ɗin domin tabbatarwa. Cikin ihu da wani irin tsawa ya ce "Ya isa haka! Wacce idan ba ita ba, ke a tunanin ki a kwai abun da Siyama zata yi ne na kasa gane ta. Ya faɗa idanunsa na cikowa da ruwa na takaici da ganin irin tozarcin da wannan yarinyar ta jawo musu. Lokaci ɗaya Anty Zainab ta kafe Siyama dake ta murmushi ana daukar ta hoto da kallo, sosai ta kafe ta da ido tana son gano gaskiya. Tabbas ita ce ga yanayin dariyar ta, ga yanayin tsayuwar ta da ɗan dogon hancinta. Lokaci ɗaya itama ta fashewa da kuka. Shi dai Nasiru sai kallon ta yake yana ta tunani, ta yaya haka ta faru a garin yaya.


Sosai a kayi taro na ban mamaki a cikin garin Abuja, wanda yanzu an gama komai sai faɗin sakamako, daga na ɗaya zuwa na uku sune keda kyauta, ta karramawa, sai kuma daga na huɗu zuwa na goma suma za'a basu tasu kyautar wacce bata kai ta ƴan farko ba. Daga na goma aka fara kira zuwa na huɗu. Siyama jin bata ji sunanta a cikin na goma zuwa na huɗu ba yasa ta haƙura domin tasan ta faɗi. Hakan yasa ta ɗaga kai ta kalli ƴan team members ɗin ta da jagororin su sai taga suma duk jikinsu ya mutu. Amma ƙawarta mai ƙara mata kwarin gwiwa tana daga mata hannu alamar in sha Allah bata fadi ba. Nan dai aka kira sunan wacce tazo ta uku wata Kirista daga garin Benue mokordi. Ana kira aka fara karanto tarishin matar da matakin karatun ta, da irin ƙoƙarin ta. Ana gamawa aka kira sunan ta biyu wato Siyam Olosha. Zo kaga ihu daga gurin ƴan team members ɗin ta harda masoyan da ta samu a gurin. Sosai itama ta fara kukan farinciki da murna. Hakan yasa ta fara ɗaga kai ko zata hango family's ɗin ta, amma ina duk inda ta duba bata hango kowa ba. Nan aka fara karanto tarishin ta itama da matakin karatun ta da inda take zaune. Ana gamawa aka kira ta ɗaya, wannan ƴar Lagos ɗin. Nan take aka basu takardar yabo da lambobin yabo da zunzurutun kuɗaɗe banda kyaututtukan da ta dinga samu a gurin, daga mota sai kuɗaɗe. Sosai Siyam Olosha ta bada mamaki domin wannan shine karon farko da ƙaramar yarinya kamarta ta shiga gasar, sannan kuma musulma kuma ta wakilci Abuja, sai hakan ya zama kamar ma itace tazo ta ɗayar domin tafi bada mamaki. Haka manyan mutane kowa sai hoto yake son ɗauka da ita ko ina sai kiran sunan Siyam Siyam Siyam ake yi...📝




(Muje zuwa masoya)
Bana yin posting ranar juma'a da Lahadi kamar yadda kuka sani.




Love all
One love
Comments
And shering
Love my fan's
By S-Reza writer ✍️
[7/16, 3:53 PM] S Reza: *TSINUWAR UWA!*
3


_By S-Reza_ ✍️


*FCW*


*My WhatsApp channel*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a




*Page 3️⃣*
Sosai Siyama ta samu alheri ga kuma mutane masu neman lambar ta, wasu kuma burinsu suyi hoto da ita, haka dai al'umma suka hanata samun lokacin da zata zanta da ƴan team ɗin ta har sai da komai ya lafa. Shugaban team ɗin nasu mai suna Oga Fita shine ya fara zuwa gurin ta, yana zuwa kuwa ya ware hannuwa cikin farinciki itama baki har kunne ta shige jikin sa har yana ɗaga ta yana yawo da ita a sama kamar ƴar Baby, ya ce " You are the best Siyam! I no you can do it thank you Siyam! Ya faɗa yana ƙara ɗagata. Itama sai dariya take tana jin daɗin yabon da kowa yake mata. Bayan ya gama ne sauran ma suka zo suka fara nasu suna ta murna ana rungume ta. Ita dai tasan masu taya ta murna har zuciya, kuma tasan munafukai karmar dai wannan ta gaban nata mai suna Adawiya da ɗaya ƙawar tata mai suna Badawiya, tasan yarinyar bata sonta tun lokacin da Oga Fita ya fitar da ita akan ita zata wakilci team ɗin su, tun daga lokacin yarinyar ta fara gaba da ita, kuma ta hana sauran members ɗin ma, yanzu ma ta tabbatar da cewar basu ji dadin wannan nasarar ba, kawai dai babu yadda za suyi ne. Wani irin kallo Adawiyar tabi Siyama da shi, har tana cije baki, ita dai bata ko ce mata komai ba, domin yau ranar farinciki ce.Aida ce ta ce "Ke manta da ita aniyar ta ta bita, duk zakaran da Allah ya nufa da chara, to wallhi ko ana ruwan muzuru da shirwa sai yayi". Aida ita ce babbar ƙawar Siyama, kuma a bokiyar shawarar ta, sannan tafi kowa bada gudunmawa a wannan nasarar ta Siyama domin kuwa ita ke tsaya mata a komai duk da cewa itama taso ta wakilci team ɗin nasu amma Allah bai yi ba. Siyama tayi dariya suna ci gaba da hotuna.


******
*YAYA BALA*
Ana gama komai
ya samu ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin nasu ya sanar da shi zai tafi gida yanzu idan an gama komai sai yasa a gyara gurin, mutumin ya amsa da to in sha Allah. Haka Yaya Bala ya tattara iyalan sa suka bar gurin duk ransa a ɓace. Ita dai Anty Zainab jikinta ne yayi sanyi sosai tana so ta sake yiwa Yaya Bala magana amma tana tsoro, ko da suka zo zasu shiga motar sai da tace karyayi tuƙi a haka ya bata ko ya bama Nasiru amma Yaya Bala ya daka musu tsawa. Haka dai suka ja baki suka fara tafiya duk a tsorace.


******
*SIYAMA*
Siyama kuwa basu bar gurin ba sai bayan sallar magriba, bayan sun gama amsar duk kyaututtukan su. Lokacin da suka isa office ɗinsu ko nace gidan su da suka saya na team ɗin su, sai Oga Fita ya nemi da Siyama ta kwana a nan zuwa gobe sai ta tafi, saboda yanzu dare yayi kuma wasu zasu iya bibiyar ta, duk da kuwa yasan bata kwana a gurin, kuma yasan duk wannan abun da take yi babu sanin iyayenta. Siyama ta ce ita ba zata kwana a gurin ba, gida zata tafi yanzu ma haka tsoro take ji. Haka dai Oga Fita ya sako ta a mota ita da Aida, bayan ya sauke Aida ne ya faka a gefen titi ya juyo ya kalli Siyama wacce ta yi nisa a tunanin halin da zata shiga idan taje gida. Cikin harshen turanci ya fara mata magana kamar dai yadda tun tuni ya saba akan ta bar gidan iyayen ta dawo nan da zama tana da kyau zata iya zama komai da ta ke son zama a duniya, kamar yadda tun farkon haduwarsu ta sanar masa da ƙudurinta, amma yanzu iyayen ta sun hana ta sakewa, bata ganin sauran ƴan matan da suke tare da shi ne. To duk idan yayi mata irin wannan maganar bata yarda domin ita batayi wannan ƙwarin kan da zata ma iya mayarwa da yaya Bala magana ba bare kuma ma Umma. Lokacin da ta tuno da Umma sai da gabanta ya faɗi domin ba karamin shakkar ta suke yi ba. Ya ce "Siyam yanzu ke ba kamar yarinya bace, ki sani yanzu sunanki da fuskar ki sun zagaya duniya, saboda haka yanzu kin fara zama salebiriti, babu inda zaki shiga a duniya da za'a wulaƙanta ki, kuma babu abun da zai iya gagaranki yanzu a gidan duniya. Kin ga yanzu kina da motoci sun kai goma, ga zunzurutun kuɗaɗe wanda har yanzu babu wanda yasan lokacin da zasu daina zuwar miki, saboda haka, ina so kiyi amfani da kuɗin ki ki jawo hankalin iyayenki, idan kuma basu yarda ba, to yanzu ba da bace, kizo duk irin gidan da kike so a garin Abuja zaki saya. Siyama dai sai jin sa take yi, tana sauraron shirmen sa, domin kuwa ita tasan ko giyar wake tashs ba zata iya duk wadannan abubuwan ba. Ita yanzu Babbar damuwar ta ma ta ƙarass gidan ko yankanta ne Yaya Bala yayi kowa ya huta. A haka Oga Fita ya kaita har ƙofar anguwarsu domin bata yadda yaga gidan su ba, Kallonta yayi ya sake cewa "Dubi unguwar da kike dan Allah Siyama, ki tsaya dai kiyi tunani. Yana faɗa ya mika mata wayar ta da take a kashe tun lokacin da ta isa gurin taron.


A hankali ta tura ɗan ƙaramin ƙofar gin nasu mai ɗauke da wani tsohon get ɗan ƙarami ta shiga, ta kalli gurin da yake ajiye tsohuwar Motar sa amma bata ganta a gurin ba, lokaci ɗaya gabanta ya fadi, basu dawo ba kenan, ta ci gaba da tafiya tana jin gabanta na ƙara faɗuwa. Kafin ta ƙarasa cikin gidan taji ana kiran sunanta. A ɗan tsorace ta juyo jin muryar Ibrahim, ai kuwa dai shine, yau ma dai kamar jiya ko wanka bai yi ba, waɗannan kayan ne dai na aikin sa, dukda kuwa yace yau basu da aiki domin yau Lahadi ranar hutu ce, amma gashi da kayan aiki, take ranta ya ɓaci. Ya ce "Zuwa na kenan sai kuma na hango ki zaki shiga gida shine na kira ki". Ya faɗa yana murmushi yana binta da kallo ganin yanda yau ta rufe gashin kanta, ga kuma wani irin kyau da tai masa, ga doguwar rigar ta tasa bai taba ganin ta da ita ba. Sosai asalin kyawun Siyama ya baiyana wanda shi kansa sai da ya ƙara tabbatar da cewar gaskiya Siyama matar manya ce, domin shi wallhi sai yaga yau ma kamar ba zai ma iya kallon cikin idon ta ba tsabar kwarjini. Sai kawai ya tafi tunanin shin me Siyama ta gani a tare da shi tace tana sonsa, gashi baƙi, talaka ƙazami,mara wayo kamar yadda ake cewa, anya kuwa bai yaudari kansa ba, to dama yana da kuɗi ne sai yace sabo da kuɗin sa ta ke sonsa. Ta ce "I B (Kasancewar wani lokaci bata ce masa Ibrahim sai tace IB)jiya fa na ƙara tabbatar maka da cewar ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, kuma gashi ka ƙara zuwa haka" Ta faɗa da ɗan damuwa a muryarta. Wani suna da ita ta saka masa wanda yanzu kusan duk unguwar haka suke kiran sa da shi, duk lokacin da ta kira sa da I B wani irin farin ciki yake ji. Ya ce "Wallhi aikin motar jiya ne, sai yau muka ƙara sa ta, ina gida oga ya kirani wai dan Allah muzo mu ƙarasa masa yau zai tafi da ita ne, to shine fa naga yauma dare yayi, kin ga kuma idan takwas ta wuce bazan samu damar ganin ki ba shine yasa na ce ko ganin ki nayi. Ya ƙarasa yana ƙoƙarin ganin ta ina suka dace da Siyama. Ta ce "To sannu da aiki, yau dai an gama da wannan motar kowa sai ya huta ko? "Hamm sosai fa, ai gobe idan na fara hutu sai rana ta fito. Ya faɗa yana dariya. Kafin tayi magana wayarsa ta fara ƙara. Yana dagawa ya ce "Ina zuwa gani nan. Siyama ta kalli wayar hannunsa, a fili ta ce "Wannan wayar dai kai jin daɗin ta kake yi ko? Ibrahim ya ce "To yaya zan yi ko bana jin daɗin ta, bari dai kuɗi su shigo in sha Allah zan samu ƴar babba nima na siya ko fecbook da TikTok ɗin nan da ake faɗa nima na fara. Ya na faɗa ya miƙa mata ledar hannunsa yana fadin sai da safe. Karmar ta ce a'a, amma ta amsa tana masa sai da safe ganin yana ta sauri. Ya juya yana ɗaga mata hannu itama haka har ya tafi. Sai da taga ya fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta nufi ciki.


Da sallama ta shiga cikin falon, sai dai bata ga kowa ba, hakan yasa ta fara sanɗawa tana yin hanyar shiga ɗakin su. Har ta shiga babu wanda ya ganta. Tana juyawa ta ga Fati a gefen gado tayi kuka har idanuwanta sun yi jaa! Tana shiga itama Fati ta ɗago ai kuwa suna haɗa ido Fati ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana faɗin Aunty Zainab ta ta ta rasu! Cikin wani irin shok da faɗuwar gaba Siyama ta saki ledar hannunta tana tambayar ta wacce anty Zainab ɗin, mutuwa kamar yaya me take nufi? Fati ta ce "A hanyar dawowarsu daga gurin gasar ne sukayi hatsari shine wai ita ta mutu, yaya Bala kuma yana kwance rai a hanun Allah ga Nasiru shima ya samu karaya a kafaɗa da hannun". Siyama ta kurma wani uban ihu tana kiran sunan Yaya Bala da anty Zainab. Tashi tayi ta nufi sashen Umma tana tafiya tana kuka koda taje sai ta tarar da ƙofar Umma ɗin a rufe alamar bata gidan. Da sauri ta koma ɗaki tana tambayar fati wani asibiti suka tafi. Nan ta sanar mata da yadda itama taji wai kusa da gurin da aka yi taron ne domin waɗan da suka kira number Umma sune suka fadi sunan asibitin. Haka ta shirya ta saka hijjab ɗin ta ta fita, bayan ta sanar da Fati cewar ta rufe gidan.
Ko da ta fita wani asibiti da ke kusa da gurin da a kayi taron ta fara zuwa, ai kuwa tana ta tambaya aka tabbatar mata da cewar gurin ne. Koda taje asibitin ta tarar da Umma nata kuka domin da gaske anty Zainab ta rasu, sai yaya Bala da har zuwa yanzu bai farka ba. Umma tana ganin Siyama ta ƙara fashewa da kuka. Haka Siyama tazo suka zauna sai sharar kuka suke yi A nan asibitin suka kwana sai washegari Umma ta tafi gida ta bar Siyama a gurin, kuma har lokacin babu wanda ya farka.


Tana zaune a gurin kafin Umma ta dawo ita kuma ta ciro wayar ta. Ganin babu abun da take yi ne yasa ta kunna Data. Lokaci ɗaya ta dinga ganin saƙonni suna shigowa tako ta ina fecbook da TikTok da Whasopp. Sosai hankalin ta ya tafi kan wayar har bata san lokacin da likitan ya shigo ba. Har sallama yayi amma bata ko sani ba.tana kallon daga iya jiya zuwa yau ta samu mabiya a TikTok da fecbook na ban mamaki har yanzu ma ƙaruwa suke yi. Tana shiga Whasopp taga group ɗin su na ƴan team ɗin su, sai posting hoton ta na jiya a keyi, ga sitatus ɗin mutane ma, nan take taga message ɗin Oga Fita tana shiga tagan su da yawa, ta fara buɗe na farko taga saƙon magana ne yana cewa ta ɗora wannan bidiyo ɗin da hotuna a shafin ta na TikTok da fecbook tayi jawabi domin har mutane sun fara buɗe account da sunanta, duk da cewar dama tana da nata mai suna Siyam Olosha wanda babu wanda yasan ta da shi a gidan su. Ai kuwa nan take ta fara posting, kafin ta yi na biyu ta fara samun like da comments, bata da lokacin dubawa hakan yasa tana gamawa da fecbook ta koma TikTok, shima bayan ta gama sai ta fara shiga comments tana kallon masu yabo da zagi. Likitan ne ya ƙara faɗin "Madam kina tare da ni kuwa?" Sai a lokacin ta jisa. Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace ta ce "Yes ina tare da kai". Ya ce "Ina ta magana kin mai da hankalin ki izuwa waya, alhalin zaman jinya kike yi. Kafin tayi magana taji kira na shigowa wayar ta amma ta share ta ce "Eh ina yin wani abu ne" Sosai likitan ya kafe ta da ido kamar dai itace yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya, kamar kuma ba ita ba, domin daga jiya zuwa yau indai kana yin media to zaka ci karo da hotunan ta. Siyama da ta lura da irin kallon da yake mata sai ta ce "Yanzu me ake buƙata?" Cikin diriricewa ya ce "Amm umm dama ɗaya ne ya farka daga cikinsu, kuma yana buƙatar abinci mai ruwa-ruwa kafin mu ƙara masa allura. Siyama ta kai kallonta izuwa gurin ai kuwa suka haɗa ido da Nasiru da ya buɗe ido yana kallon ta tun ɗazu ita bata sani ba. Ta ce "Sannu yaya Nass ya jikin? Me zaka ci? Ina yake maka ciwo? Nasiru ya lumshi ido ya buɗe yana jin jikinsa ya masa nauyi. Sallama suka ji anyi Umma da wasu daga cikin kawunansu suna biye da ita, sai Fati da ta ɗauko kwanukan abinci. Ganin haka likitan fita yana satar kallon Siyama. Daidai lokacin shima yaya Bala ya buɗe ido yana bin ɗakin da kallo. A hankali ya ce "Ina Zainab?" Kawunsu ƙanin mahaifinsu mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login